Showing 411001 words to 414000 words out of 512766 words

Chapter 138 - Asanadin Makwabtaka Book 3 Hausa Novel Complete

Unknown   

27 Dec 2024

1575

buk'atar taci Abinci sai tasha pain relievers, tambayarta yay tazo da magungunan tace eh akwai wasu da zata bata yace Ok taje kawai ta aje mashi su nan zai sakata a ruwan tace Ok amman yanzu wannan tasan yasha iska akwae buk'atar a canza wani yace Ok ta canza, har ta juya ya tambayi tsawon lokacin da zata yi a ruwan ta fad'i mashi kafin tace ya bita a hankali yadda ruwan zai shigeta yadda ake so yace Ok, da biyu ta fad'i hakan don a tunaninta yana iya cewa ya gwada mata k'arfi, bayan fitar likitan rarrashin Fauzy ya shiga yi cikin kwantar da murya kai kace bai iya hakan ba, kuka taci gaba da yi tana cewa ita dai bazata iya shiga ba zafi yake k'ara mata, shiru yayi ya rasa yadda zai yi mata idon shi akanta sai faman juye juyen ciwo take, k'arshe dai dole saidai k'arfin ya gwada mata ya d'auketa cak tana ta kuka kamar za'a ma k'aramar yarinya wanka, daga baya da ruwan ya shigeta sosae ta d'an d'auki lokaci a ciki sai gashi ta fara jin dad'in shi ta saki jiki, bayan ta d'auki lokacin da aka fad'i mashi ya canza ruwan ya shiga yi mata wanka bata yi yunk'urin hana shi ba don tasan ba lalle ya k'yaleta ba gashi dama gaba d'aya ba k'arfi a jikinta saidai kawai ta runtse idanunta, bayan ya gama yi mata yace mata tayi na tsarki yana tsaye tayi ta gama ya d'aukko babban towel ya rufa mata ya sake d'aukko wani short ya lulluba mata a kai ya kara d'aukkota suka fito cikin d'akin, a saman gado ya d'aurata ya mik'e ya nufi wurin dressing mirror, mai da yake amfani dashi ya d'aukko yazo ya shafa mata yana ta kallonta har lokacin idanunta a rufe suke, bayan ya maida mai d'in wurin press d'in shi ya nufa ya bud'e yay d'an jimm yana tunanin kayan da zai d'aukko mata tasa kafin zuwa da safe, wasu riga da wando masu taushi ya d'aukko mata duk da yasan zasu yi mata yawa sosae amman zata fi jin dad'in su, shi ya saka mata kayan ganin kanta ya tsane yasa bai yi tunanin a busar dashi ba, ana gama saka kayan ta kwanta duk wannan abun bata bari ta had'a ido dashi ba, ganin yadda ta takure ya ja mata Duvet tare da mik'ewa ya nufi hanyar fita daga cikin d'akin, lamo Fauzy tay duk ta damu tunaninta yanzu taya zata je wurin su Aunty Mareeya a haka ta fara yin gyangyad'i, ya d'an d'auki lokaci sannan ya dawo yana d'auke da wani madaidaicin tray ya aje a saman table, cup d'in tea ne mai k'auri sai bread da wainar kwai Kitchen yaje yasa aka had'o mashi, wurinta ya nufa har tayi bacci kana ganin yanayin da take yin shi zaka gane shi is not alright, bai sha wahalar tashinta ba don baccin ba wani mai nauyi bane, farko nunawa tayi ta k'oshi kaman zata yi kuka da yayi mata Maganar Abincin saida ya rarrasheta sannan da kanshi ya fara bata, ba laifi ta d'an ci da yawa don wani irin fayau cikin ta yay mata, bayan ta nuna ta k'oshi tana niyyar kwanciya da sauri yace ta bari tasha magani sai ta kwanta, a saman nightstand ya d'aukko su guda biyu ne kowanne an rubuta yadda za'a sha ya 6allo mata da sauran tea din data rage ya bata tasha bayan ta gama fuska a yamutse tace ruwa zata sha da sauri ya furta Ok ya nufi hanyar fita, a hankali ta juya tana kallon bayan shi ganin shi take kamar bashi ba, a parlor ya d'aukko bottle water tare da glass cup ya kawo mata bayan ya bud'e ya zuba mata ya kai bakinta zai bata ta d'aga hannu ta amsa fuskarta na kallon gefe, kaman rabi tasha ta mik'a mashi ya amsa suma ya aje su saman table, zaune tayi bata kwanta ba yay tsaye yana kallonta ya lura da kaman fushi take dashi don tak'i ta ko kalle shi, cike da k'arfin hali ta fara kokarin mikewa yana ganin haka ya tambayeta mi take so ne tace mashi d'akin da suke zata koma da sauri ya matsa ya kamata yana fad'in taya zata koma a wannan halin ta kwanta anan ai lafiya lou zuwa da safe in ta k'ara samun sauk'i sai ta koma, shiru tay dama dai kawai ta fad'a ne amman itama ba son komawa take a wannan halin ba kuma tunda su Aunty suka ga ta dad'e tasan tuni ma sun zargi wani abu, janyewa tayi daga kamatan da yayi ta kwanta yaja mata duvet, d'auke tray d'in yay ya nufi hanyar fita, a parlor ya zauna ya idasa cinye sauran data rage don shima yunwa yake ji bayan ya gama anan ya bar kayan ya dawo cikin bedroom d'in, toilet ya wuce bayan wasu mintuna ya fito k'ugunshi d'aure da towel ya nufi press d'in shi, shima riga da wandon ya d'aukko ya fara sakawa yana yi yana kallon Fauzy bayan ya gama kimtsawa ya nufi gadon saida ya kashe wutar d'akin sannan ya daidaita kwanciyar shi, hannu ya kai zai rungumota jikinshi kawai sai ji yayi ta k'i bari yayi hakan nan ya gane idonta biyu ko kuma baccin bai d'auketa ba sosae, matsawa yay ya had'e jikinsu tana ta son k'wacewa ya kai bakin shi saitin kunnanta cikin magana mai kamar rad'a ya fara magana, "I'm very sorry Wife, I know I hurt you kiyi hak'uri pls bansan ya akai komai ya faru haka ba I don't know what came over me" sheshshekarta da yaji k'asa k'asa yasa shi gane kuka take, k'ok'arin juyo ta ya shiga yi ta dawo suna facing juna da yake a d'an kwai haske ya kai hannu yana goge mata k'wallan yana k'ara bata hak'uri yana bai san ya akai hakan ta faru ba, cikin Muryar kuka tace amman ba saida taita rok'on shi ba kan yayi hak'uri ya k'yaleta ba amman ya k'iya, a rud'e yace mata ya rasa control ne he didn't know that's how it was gaba d'aya tun farko ma baida niyyar wannan, shiru tayi bata ce komai ba ya shiga shafa gefen fuskarta yana fad'in Pls she should forgive her husband yasan yayi mata ba daidai ba, aka ce tsakanin mata da miji sai Allah ce mashi tayi shikenan tayi hak'urin, rungumeta yay sosae yana murmushi yayi mata godiya tare da Fad'in he knows he is blessed daya sameta matsayin mata shiru ta d'an yi sai kuma k'asa k'asa ta furta itama haka ya k'ara k'ank'ameta cike da jin dad'i yace "I Love You so much Babes" yay Maganar tare da pecking kumatunta, rufe ido tayi a ranta ta raya wato dama daya ta6a ce mata ba yanzu zai fad'i mata hakan ba yana nufin sai wannan lokacin kenan, shiru sukai wani irin nishad'i suke ji ba ma dai kamar Sameer ji yake yau is the happiest day of his life, jin saukar numfashinta a nutse yasa shi gane tayi bacci ya gyara masu kwanciya bada jimawa ba shima baccin ya d'auke shi.

Kiran sallar Asubar farko alarm ya tashe shi, duk da bai jin k'warin jikinshi amman Saboda ya saba yin raka'atanil fajr yasa ya daure ya tashi bayan ya janye Fauzy a hankali, toilet ya nufa yayo Alwala bayan ya fito ya nufi press ya canza kaya zuwa jallabiya kafin ya nufo inda zai yi sallar, bayan ya gama zaune yay yana tasbih yana yi yana kai idon shi kan Fauzy dake ta bacci cikin Duvet fuskar shi a sake kaman zai yi murmushi, yana a wurin har lokacin sallar Asuba yayi ya tashi ya kabbara don ji yay bazai iya zuwa Masallaci ba, bayan ya gama yayi Addu'oi kafin ya mik'e ya nufi gadon, bayan ya haye yana k'ok'arin janyota jikinshi ta fara motsi a hankali ta fara bud'e idanuwan ta, tana bud'e su suka shiga cikin nashi ba laifi sun d'an k'ara washewa amman duk da haka yanayin su basu dawo daidai ba sunyi kalar na mara lafiya, bin shi da kallo tayi yay mata murmushi yace ta tashi ta d'an d'aga mashi kai, tambayarta yay ya take ji yanzu da k'yar ta bud'e baki ta bashi amsa da da sauki ya kai hannu yana shafa mata kai yace zata koma normal in sha Allah ta d'aga mashi kai, shiru suka d'an yi can yace mata ko tana jin yunwa ya samo mata abunda zata ci ta d'an girgiza mashi kai alamar a'a sai kuma ta tambaye shi gari ya waye ne yace mata eh anyi sallar Asuba ita ya gama yanzu, tana jin haka ta fara k'ok'arin tashi zaune ganin haka ya kai hannu ya taimaka mata, bayan ta zauna ya tambayi salla zata yi ta d'an yi shiru sai kuma tace mashi so take ta koma d'akin da suke in taje tayi sallar a can, ce mata yay miyasa ta damu da ta koma ne nan ba d'akin mijinta bane kuma ai ba komai don ta zo don anan ma zata zauna kafin su tafi UK, yamutsa fuska tayi kaman zatai kuka tace tafi son ta koma can in suka tafi sai ta dawo nan d'in yace Ok ta fara yin sallar, shi ya taimaka mata ta mik'e da k'yar ta fara taka k'afafun tana yin tafiya a hankali yana mata sannu k'arshe ma ganin yanayin tafiyar tata sai kawai ya d'auketa ya nufi toilet da ita, bayan anyo Alwalar Hijab d'in da tazo da ita ta saka kafin ta kabbara sallar, bayan ta gama ne ya nuna mata ya za'ai ta koma can a wannan halin ko tafiya bata iya yi sosae tace mashi gara dai ta tafi in ta zauna anan kowa zai san abunda ya faru gashi ba gama hidiman bikin akai ba ko yau ma za'a yi Walima, shi kan shi bai son abun ya bud'u hakan yasa yace suje ya rakata, farko kama mata hannu yay tana tafiya a hankali ganin bata sauri yasa shi d'aukarta tana ta fad'in don Allah ya ajeta kar a gansu yace mata ba wanda zai gansu tunda Asuba ne baza'a fito yanzu ba, suna zuwa bakin kopar Falon su tace ya ajeta shi da wai har cikin Falon zai shiga da ita ta kafe sai da ya sauketa, saida ta kalle shi sannan ta juya yay tsaye yana kallon ta har ta shige, tsaye tayi a bakin k'opar shiga Bedroom d'in da suke tana zullumin shiga can wata zuciyar ta raya mata to da tayi tsaye nan in kuma wani ya fito daga wani d'akin ya ganta fa, yin wannan tunanin yasa ta kai hannu a d'arare ta tura kopar a hankali, tana sa kai cikin d'akin suka had'a ido da Fatuu dake zaune akan abun salla bata dad'e da gamawa ba, har saida gaban Fauzy ya fad'i da suka had'a ido cikin kama kai da sauri ta janye idonta ta nufi ciki, cike da k'arfin hali take tafiya a k'ok'arinta na kada a gane saidai duk yadda taso tayi tafiyar sosae abun yaci tura dole a hankali take taka k'afafun, a bakin gado ta zauna tak'i yarda ta k'ara kallon Fatuu bayan d'an wani lokaci Fatuu ta taso ta nufo gadon itama ta zauna a gefenta tana kallonta da murmushi tace mata ta dawo, kai ta d'aga mata ba tare da tace komai ba sukai shiru can Fatuu ta dafa Shoulder d'inta tace mata ya akai ne wai sai lokacin ta d'an kalleta tana k'ok'arin k'ak'alo murmushi tace mata ba komai, Aunty Mareeya ce ta fito daga cikin toilet tana yarfe ruwa ganinta saida gaban Fauzy ya fad'i sosae tayi saurin janye idonta, nufo cikin d'akin tayi tana fad'in "Zarah kin gama sallar ki ara man Hijab d'in ita waccan mai amso sak'on ta tafin man da Hijab saida dama nace...." bata k'arasa ba sakamakon ganin Fauzy da tayi a gefen Fatuu, da sauri ta nufo inda suke ta tsaya daga gaban su tana fad'in ashe ta dawo Fatuu ta d'aga mata kai, tana kallonta tace "ke malama mai amso sak'o sai muji ki shiru kika sa munata zaman jira ko kayan dad'i ne ya siyo maki ki kawo mu tattamna muma" shiru bata ce mata komai ba bata kuma kalleta ba ganin haka yasa ta kirata "Fauziyya" shiru bata amsa ba, kallon Fatuu tay tace mata ya akai ne ta d'an rausayar da kai tace bata sani ba, tambayarta Fatun tayi yaushe ta dawo tace mata bada dad'ewa ba bayan ta gama salla itama tayi mata magana ta ganta haka, jinjina kai Aunty tay ta juya kan Fauzy ta kai hannu ta d'ago Fuskarta da d'an murmushi tace "Yar gidan Hajiya ya akai ne ko mun fara yar kunya ne" tana rufe baki Fauzyn ta fashe mata da kuka tare da kifa fuskarta a jikinta, d'an gwalo ido Aunty tay sai kuma ta fad'ad'a murmushinta ta kai hannu tana d'an bubbuga bayanta tana fad'in ya isa to miye abun kuka, jin yadda take ta kukan ne yasa ta d'ago fuskarta tana share mata hawayen tana fad'in ya isa Shikenan haka girma yake zuwa ma mutum, kukanta ne ya tashi Yaya Fareeda dake bacci da yake bata salla, tambayar Aunty tayi lafiya take kuka tana faffad'an murmushi tace mata ba komai Yaya Fareedar bata kawo komai a ranta ba don jiya tayi bacci aka tafi da Fauzyn, zama Aunty tay kusa da ita daga d'ayan 6angaren a hankali tace mata akwae abunda ke mata ciwo ne ta d'aga mata kai ta tambayi mike mata ciwon cikin muryar kuka tace duka jikinta, d'an jimm tayi tana ta kallonta can tace badai ta samu matsala ba ko tace mata likita tazo ta dubata tace wai ta rink'a zama a ruwan zafi sai magunguna da ta bata, a hankali suke Maganar amman duk su Fatuu na ji, jawota Aunty tay jikinta tana bata hak'uri tace zata daina jin ciwon bada dad'ewa ba sai faman murmushi take, tambayarta tayi yanzu ta zauna ruwan zafinne ta girgiza mata kai alamar a'a tace Ok bari tayi salla sai ta taimaka mata ta d'aga mata kai, mik'ewa tay tace ma Fatuu ta bata Hijab d'in jikinta bayan ta amsa da sauri ta nufi wurin yin sallar, bayan tafiyarta cigaba da yin sheshsheka Fauzy tay wani irin tausayinta ne ya kama Fatuu ta d'agata tana bata hak'uri tare da yi mata sannu haka ma Yaya Fareeda kai kawai take d'aga masu, bada jimawa ba Aunty ta gama sallar ta nufo su tana cire Hijab ta mik'a ma Fatuu kafin ta kalli Fauzy tace suje Toilet din, mik'ar da ita tayi har zasu tafi ta dakata tare da kai hannu tana fad'in a cire Hijab d'in ko, tana cirewa tabi kayan jikin Fauzyn da kallo kafin ta saki yar dariya tare da Fad'in "Sunan wani k'anin tsohon mu Baba Salmanu, wannan kayan fa?" tana rufe baki su Yaya Fareeda suka kwashe da dariya da sauri Fauzy ta fad'a jikinta tare da sakin wani sabon Kukan, rarrashinta ta shiga yi tana fad'in tayi hak'uri shegen bakinta ne da bai gani yayi shiru taga bada su ta tafi bane shiyasa ta tanka, da k'yar ta samu tayi shiru tayi ma su Fatuu alamar su daina yin dariyar kowa ya gumtse ta kamata har zasu tafi tace ma Fareeda ta bud'e akwatin Fauzy ta d'aukko mata towel ta kawo mata sannan suka nufi hanyar toilet tana tafiya a hankali Aunty Mareeyar tana ta mata sannu harda cewa ko ta goyata da sauri ta girgiza mata kai alamar a'a, Bayan sun je toilet d'in a cikin bathtub ta tara ruwan zafin bayan ta toshe tasa Fauzy ta cire dogon wandon baccin da yake rigar ta rufeta sosae ta kawo mata har wurin gwuiwa, itama saida ta tittirje mata wurin zauna ruwan ganin yadda take yi ne yasa Aunty ce mata wai ta tabbatar bata samu matsala ba cikin nishi tace mata eh likitar ta dubata amman tace ta samu rauni, yamutsa fuska Aunty ta shiga yi tana d'an Jujjuya kai alamar tausayi kafin tace "shi kuma surukina ya da gaggawa haka, duk da dai abun farinciki ne amman banji dad'i ba d'an jakar uba ya wahalar man dake" tana rufe baki cikin yamutsa baki Fauzy tace "Aunty ki daina zagin shi shima yace bada son ranshi hakan ya faru ba" gwalo ido Aunty tay da alamun Al'ajabi tace "iyyeee, ah lallai miji dad'i, to tuba nike your Excellency ayi hak'uri su6utar baki ce" tayi Maganar tare da d'an harararta Fauzyn ta d'an tura baki tana kikkafta idanu kaman zatai kuka, sosae ta sakata ta zauna ruwan daga baya ta baro mata toilet d'in tace tayi wanka, after some minutes ta fito d'aure da towel d'in da Aunty ta kai mata su kuma kayan baccin Sameer d'in ta ninkosu lokacin Fatuu bata a d'akin taje tay feeding su twins da yake wurin su Mom suka kwana sai Yaya Fareeda itama har ta koma bacci, taimaka mata Aunty ta shiga yi ta shirya cikin doguwar jallabiya ta d'aura kallabin Aunty tace mata tasan bata rasa jin yunwa ko ta d'aga mata kai alamar eh, shiru tayi tana d'an tunani kafin tace ina wayarta ta kira shi tace tana jin yunwa, sai lokacin ta tuna da ita taje part d'in nashi hakan na nufin ta manto ta can ta fad'i mata, ce mata tayi to ta d'an kwanta aga zuwa d'an anjima k'ilan a kawo masu breakfast da wuri ta d'aga mata kai ta fara k'ok'arin hawa gado ta kwanta Auntyn na k'ara yi mata sannu sosae take jin tausayinta don tasan dole ma taji jiki, bayan ta kwanta itama Aunty Mareeyar kwanciya tayi basu dad'e ba da kwanciyar akai sallama bakin k'opa Aunty ta d'ago kai tana bada izinin a shigo, wata yar dattijuwar mata ce ta shigo tana ruke da wani had'addan basket sai k'yalli yake jikinta sanye da apron Aunty na ganinta ta mik'e zaune, nufo ta tayi da murmushi ta gaishe da ita ta amsa mata itama tana murmushin tace dama

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login