Showing 36001 words to 39000 words out of 512766 words

Chapter 13 - Asanadin Makwabtaka Book 3 Hausa Novel Complete

Unknown   

27 Dec 2024

1591

kai ita sai lokacin ma ta tuna da ba hakan ta fito ba da sauri tace bari taje ta maida kayanta ta juya sam ya kasa janye idon shi daga kanta har ta shige wurin, lokacin data fito ta maida kayanta bata ganshi a wurin ba hakan yasa ta nufi hanyar fita saida ta fita can waje ta hango shi a tsaye jikin Mota yana ganinta ya bud'e ya shiga itama ta k'arasa ta bud'e ta shiga ba tare da ya ce mata komae ba yaja suka tafi..........




_Littafin A Sanadin Makwabtaka part 2 Naira 300 ne za'a tura ma Mutum har part 1 ga mai so zai turo kudin ta wannan Account din, 1509618776, Zainab Bature Access Bank, za'a turo shedar biya ta wad'annan nos din 09013804524 ko 08169856268
[5/8, 19:28] +234 901 700 4868: *ASM Bk2040*

_Destiny may be delayed but cannot be changed...._


*DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI*






............Washe gari Fatuu na gama sallar Asuba bata koma bacci ba kasantuwar ranar Monday ce ta hau yin shirin tafiya School, Misalin k'arfe bakwae saura tana cikin yin breakfast jikinta sanye da Uniform wayarta dake a gefenta ta fara ringing ta kai hannu ta d'auka sunan Ya Haisam ta gani a screen d'in har saida ta d'an yi mamaki kafin tay picking, gaishe da shi tayi bayan ta d'aga ya amsa yay mata ta tashi lpy tace lpy Lou tambayarta yay k'arfe nawa zata je School tace mashi yanzu tana yin Breakfast ne sai wurin kaman k'arfe 7:15 zata tafi yace Ok zai zo ya kai ta daga haka yay cutting kiran, bin wayar tay da kallo bayan ta cireta daga kunne tana kallo can kuma ta d'an ta6e baki ta ajeta taci gaba yin breakfast d'in ta, K'arfe bakwae da Minti goma ya kira yace in ta gama yana waje ta amsa mashi da to dama Hijab kawae zata saka sai jakar goyon ta ta nufi gaban dressing mirror ta dan k'ara gyara fuskarta ta saka glass d'inta daga haka ta fita, sai da ta lek'a d'akin gwaggo tay mata sallama ta bata kud'in abun hawa da Abinci tace ta barsu Ya Haisam ne yazo zai kaita kuma dama akwae wasu canji zata yi break d'in dasu tana murmushi ta d'aga mata kai kafin tay mata Allah ya tsare ya bada sa'a ta amsa da Amin tana nufar Kopar fita, bayan ta shiga Motar ta rufe ta juya ta kalle shi yana sanye da jallabiya ash mai gajeran hannu da d'an murmushi ta gaishe shi fuska a sake ya amsa yana kallonta kafin ya juya ya ja Motar suka tafi, shiru ba wanda ya k'ara tankawa sai itace ke ta d'an kallon shi sai kuma ta juya duk yana lura da ita ta mirror can ta k'ara juyowa shima ya juya karaf suka had'a ido ya d'age mata gira yace "What?" d'an motsa baki ta fara yi a marairaice tace "dama akan wayan da ka siya man jiya ne" idonshi akan hanya yace mi ya samu wayan tace "ba komae, d..dama Kawu Amadu ne ya fad'i mana kud'inta to shine muka ga tayi kud'i da yawa don har gwaggo ma tana cewa zata yi maka magana kud'in sun yi yawa sosae" d'an guntun murmushi yay kaman bazai ce komai ba yana ta driving ita kuma ta kafe shi da ido can yay sigh yace "yanzu ya za'ai da shi kenan?" Da sauri tace "a barta kayi wani abun da kud'in" d'age gira yay yace "to in ba abunda za'ai da kud'in fa?" Tura baki tay yana kallon ta ta mirror a shagwa6e tace "ya za'ai ace ba abunda za'ai da kud'i?" shiru yay yana cigaba da driving da d'an murmushi akan face d'in shi ita kuma sai faman k'unak'uni take tana yamutsa Fuska sai kace abun tsiya akai mata bana Arziki ba duk yana kallonta ta mirror can taji yay sigh yace shikenan akwai yadda za'ai to, da sauri tace to ta kai hannu k'asa ta d'aukko jakarta ta bud'e dama ta sako wayar don ta bashi, fiddota tay ta maida jakar ta mik'a mashi d'an kallon wayar yay ya maida idon kan hanya taji yace "ai ba nine zan yi ba kece" da d'an mamaki kan fuskarta tace "ni kuma, to ni zanje in maida masu ne?" girgiza mata kai yay kafin yace "I mean zaki iya bayar da shi in baki so" waro ido tay da alamun Al'ajabin jin abunda yace ya d'an kalleta ya d'age gira alamun tabbatar da abunda yace d'in ta cuno baki tana mashi wani kallo batare da ya kalleta ba taji yace shi take harara a shagwabe tace ita ba hararan shi take ba, tasan tunda ya fad'i hakan ba amsa zai yi ba dole ta maida ita cikin bag d'in, Lokacin da suka iso ya parker tay mashi godiya tana niyyar juyawa ta bud'e kopar yace mata wait ta dakata ya bud'e glove box tana ganin kud'i zai ciro ta tsuke fuska bayan ya d'aukko 5k ya mik'a mata yace tay break tak'i amsa tana kallon shi yace ta amsa mana kawae sai ta fara jujjuya mashi kai tana mashi magiyar ya bassu gwaggo ta bata, bin ta da ido kawae yake yace tunda ya fiddo ta amsa sai ta k'ara kawae sai ta juya mashi k'eya still yay yanata kallonta irin abubuwan shagwabar nan da take yi ba k'aramin tafiya take dashi ba sai tai ta burge shi, jin yayi shiru yasa ta juyo ganin kallon da yake mata ne yasa itama ta kafe shi da nata idon suka cigaba da bin juna da wani irin kallo mai wuyar fassarawa dole Fatuu ta sare don bazata iya jurewa ba ba shiri ta sadda kanta jikinta duk yayi weak d'an guntun murmushin gefe yay ya kira sunanta ta amsa jin bai k'ara cewa komae ba yasa ta d'ago ta kalleshi alamar ta amshi kud'in Yay mata da kai sai ta kasa k'ara yi mashi gardama don duk ya kashe mata jiki a sanyaye ta mik'a hannun ya bata ta furta ta gode ta kai hannu ta d'aukko jakarta zata fita taji ya tambayi k'arfe nawa zasu tashi d'an kallon shi tay tace k'arfe biyu ya d'aga kai ta juya ta bud'e Motar ta fita, nufar class area tay tana yi tana waiwayen Motar yana kokarin juyawa har ya tafi, tunani iri iri a ranta har ta isa Class tana shiga Fauzy dake ta zuba idon ganinta ta mik'e da sauri ta nufo ta tana mata welcome ta d'an mata side hug Fatun na murmushi suka nufi seat d'in su, bayan sun zauna Fatuu tace da wuri ta taho kenan tace mata a'a ai tun jiya da daddare ta dawo suna haka malamin su ya shigo, basu k'ara samun daman yin hira ba har saida akayi break sannan Fauzy ta shiga tambayarta ya Haisam Fatuu tace mata shine ma ai ya kawo ta da d'an mamaki tace "kai haba, shi dae bai gajiya da yin hidima dake bawan Allah amman mudae ba wannan muka fi so ba kawae ya fito ya mana Wuff da ke don Allah" d'an ta6e baki Fatuu tay tace "Uhm ai ke Fauzy wannan ba komae bane hidima ai sai jiya da muka fita dashi" cike da k'aguwa tace "ya kai bani in sha" nan Fatuu ta kwashe komae na kayan da ya siya mata har zuwa wayar daya siya mata hannu Fauzy tasa ta rufe baki da tsananin mamaki ta maimaita sunan wayar Fatun tace wllh bari ma ta gani ta kai hannu ta d'aukko jakarta bayan ta bud'e ta zura hannu ta fiddo da kwalin wayar ta mik'a mata, zaro ido Fauzy tay baki bud'e da d'an k'arfi tace "Wllh iPhone 15 d'in ce da gaske" wannan Maganar da tay ta jawo hankalin yan seat d'in bayan su wata Aisha ta ja hijab d'in Fauzy ta waiga tace taji tana iPhone 15 su ganta ta mik'a masu kan kace mi sauran wad'anda suke cikin ajin basu fita break ba harda maza duk suka taso ganin wayar ana tambayar wake da ita Fauzy na nuna masu Fatuu wani harda cewa ashe dae ita big girl ce mai babbar harka haka, wata student ma tace ashe dae ita babbar Hajiya ce basu sani ba wani dake gefe ya tambayi wai nawa take ne 15 d'in na kusa dashi ya bashi amsa nan fa wasu suka zaro idanu wasu suka hau jinjina kai, lokacin da Fauzy ta amshi wayar ta juya don ta ba Fatuu ganin yanayin fuskar ta yasa ta tambaye ta lafiya miya faru ne kaman zatayi kuka tace "ni fa Fauzy ban so aka san da wayar nan ba wllh don ni tsoro nike ji ina zaman zamana in ja ma kaina bala'e" dafa Shoulder d'inta tay tace "in sha Allahu ba abunda zai same ki ki kwantar da hankalin ki" a sanyaye tace Allah yasa, don ta k'awar mata da damuwar tace "Amman fa gaskiya Zarah ina tunanin Ya Haisam son ki yake wllh" waro ido Fatuu tay tace "ke waya fad'a maki da har zaki rantse" tace"uhum haba Zarah kiyi tunani mana nasan ba yau ya fara maki hidima ba amman fa hidiman ta canza salo ke baki fahimta ba tunda yake dake ya ta6a maki hidima irin wannan ya d'auki abun har million kacukam ya baki, je ki asa ma shi mai yawan Alkhairi ne mizai sa bazai siya maki wata irin waya ba tunda gasu nan iri iri in ma masu uban kud'i ne duk akwae su amman sai ya za6i wannan da fitowarta kenan kuma ba kowa ne zai iya riketa ba ke in ba don kina da wani matsayi a wurin shi ba da yafi wanda kika sani taya zai maki hakan?" bin ta da ido kawae Fatun take dama kanta duk a d'aure yake game da sabbin abubuwan da yake mata Fauzy ta ci gaba "ba fa wani abun mamaki bane don ya kamu da son ki kema da ai yadda ya d'auke ki kika d'auke shi ko ta zo ta canza zani to shima d'in zai yuwu hakan ce ta faru dashi ni wllh in hakan ta kasance sai nafi kowa farinciki ko ba komae Allah ya amshi Addu'ar mu zuciyarki kuma ta samu abunda take muradi" sai lokacin Fatuu tay d'an murmushi had'i da yar ajiyar zuciya,

"Yanzu ace sai ya bayyana maki yana son ki kuma yana son kuyi aure zaki hak'ura da karatun ki bi shi?"Fauzy ta tambaye ta had'i da d'age gira wani kallo Fatuu ta jefa mata kafin tace "har ma sai na baki amsa ai kema kinsani" dariya Fauzy ta sa tace "baki tsoron matar shi kawae sai ta ganki da mijinta matsayin Matar shi?" Fatun tace "to ai cewa kikae in yace yana sona kuma ya aure ni kinga tunda shi ya 6allo ruwa ai shi zai san yadda zai da ita ko" duk suka sa dariya Fauzy na fad'in uwar wayo wato shi yace yana so sai kace ita irin bata so d'in nan Fatun na dariya tace to ai irin hakan saida basaja suka ci gaba da dariya har Fauzy na Addu'ar Allah ya nuna mata ranar da zaice yana son ta a kur kusa Fatun tace shida ma zai tafi yau tace ai duk inda yake zai iya furta mata hakan ba wata matsala bace, daga baya Fatun tace suje suyi break lokaci nata tafiya kar a dawo suka tafi, k'arfe biyu daidai Haisam ya kirata yace yana inda ya ajeta da safe, tare da Fauzy suka taho suka zagaya d'ayan side d'in Fatuu ta bud'e gaban ta shiga Fauzy ta leka tana murmushi ta gaishe da shi fuska a sake ya amsa mata tace Zarah ta fad'a mata yau zai tafi Allah ya kiyaye a gaida Aunty Fanan ya amsa da Ok zata ji daga haka tace ma Fatuu sai sun had'u Gobe tace to, tun bayan da ta shiga cikin Motar ta gaishe da shi ya amsa bata k'ara cewa komae ba har suka hau hanya can ta kalleshi tace "sai k'arfe nawa zaka tafi?" Fuska sake yana kallon hanya taji yace ta k'osa ya tafi ne da sauri tace a'a ta dae tambaya ne kawae gyad'a kai yay suka d'an yi shiru sai kuma taji yace "ko za ki ne?" da sauri ta kalleshi tace ina yace "U.s" d'an bud'a ido tay tace "ni da nike karatu" shiru ya d'anyi still bai kalleta ba can yace "da ba karatun za ki je kenan?" itama shirun ta d'an yi har saida ya d'an juyo ya ce mata bata ji bane cike da jin kunya a hankali ta d'aga mashi kai alamar eh kawae sai gani tay yay d'an murmushi ya maida idon shi kan hanya saida ya d'an d'auki lokaci sannan ya sake cewa "kin daina tsoron matana kenan" tsuke fuska tay ta d'an tura baki tace "ai ni dama ba tsoron ta nike ba kawae dae ina ganin in naje bazata ji dad'i ba taga bamu had'a komai ba na bika har can karshe ma ta koro ni" d'an murmushi yay kafin yace "to yanzu da kika ce da ba karatun zaki kin daina tunanin zata ji ba dad'in ne?" d'an watsa hannu tay tace "to ai kaine ka tafi dani ko bani nace ba in ma taji ba dad'i kai kasan yadda zaka yi" wani kallo ya juyo yay mata duk sai tasha jinin jikinta ta fara sussuna kai kamar daga sama taji yace "yanzu in tafi dake d'in kenan?" Da sauri ta kalleshi suka had'a ido ya d'age mata gira alamar ta bashi amsa da sauri ta girgiza mashi kai tace "ni fa ba so nike in bika ba tun farko na tambaye ka lokacin da zaka tafi ne don in raka ka Airport" murmushi kawae yay yaci gaba da driving d'in shi itama ta juyar da kanta taci gaba da kallon hanya har suka iso gida ba wanda ya k'ara tankawa tay mashi godiya ta d'auki jakarta tana kokarin bud'e kopar ta ji yace mata before 4:30 zai tafi ta d'aga mashi kai ta fita yaja Motar ya wuce gida. Tana shiga gidan ta wuce d'akin gwaggo tay mata sannu da gida anan ta sanar mata zancen tafiyar Haisam gwaggon tace bari ta tashi to taje tay mashi sallama, d'aki Fatuu ta nufa ta aje jakarta kafin ta wuce kitchen ta zubo Abinci ba wani mai yawa ta ci ba don sunci abubuwa sosae da break ita da Fauzy tana gamawa ta wuce toilet don yin wanka, Misalin karfe hud'u da yan mintuna lokacin angama sallar la'asar Fatuu ta isa part d'in Haisam tana sanye da riga da skirt na atampa mai jajayen flowers had'i da mayafi mahad'in su tayi d'aurin kallabi mai kyau ga glasses d'inta manne a idanun ta, a hankali ta tura kopar parlon ta shiga da yar sallama idanun ta suka sauka kan Abbas dake zaune kan L-shape yana sanye cikin k'ananun kaya kasumbar shi tasha gyara gashin sai kyalli yake suna had'a ido suka sakar ma juna murmushi yace mata ta shigo mana tayi tsaye a bakin kopa ta nufi armchair ta zauna ta gaida Abbas d'in da murmushi ya amsa mata ta tambayi Abdul yace yana school bai dawo ba da yake yana yin lesson ta jinjina kai shiru suka d'an yi ta juyar da kanta can taji yace tazo raka mutumin nata ne d'an murmushi tay kawai bata ce komae ba shima yar dariya yay bai k'ara cewa komae ba can kuma sai ya mik'e yace yana zuwa in Haisam ya fito tace mashi yana Mota ta d'aga mashi kay ya nufi hanyar fita, after few seconds sai gashi ya fito yana janye da d'an trolley da kuma jakar laptop yana sanye da kananun kaya kai idonta tay kan shi har ya k'araso cikin parlon ya tsaya gefenta yana kallonta ganin hakan yasa ta mik'e tana cigaba da kallon shi da d'an murmushi ta gaida shi ya amsa ta fad'a mashi Ya Abbas yace yana Mota yana dai ta kallon ta tana Maganar kawae sai ji tay slowly yace "baki tsawo ne?" bud'a ido tay alamar mamaki sai kuma ta d'an tura baki tace "duk tsawon da nayi, dafa a iya nan d'in ka nike yanzu kuma kad'an ya rage in kawo shoulder d'in ka" tay Maganar tana nuna mashi inda ada tsawonta yake a jikin shi daga inda take, shiru bai ce komae ba yana cigaba da kallonta fuska a sake ganin bai ce komae ba yasa a d'an shagwa6e tace "to tunda baka ganin tsawona kai sai ka samman naka tunda kana dashi kai sosae" shirun dai yay sai kuma ya d'age gira yace tana so ta d'an k'ank'ance ido ta d'aga kai alamar eh, aje jakar laptop d'in dake a d'ayan hannun shi yay kan d'ayar armchair d'in dama ya saki trolley d'in tunda ya tsaya kawae sai gani tay ya kai hannu d'aya ya jawota jikin shi a razane ta zaro ido tana kallon shi shima haka still holding onto her motsa baki ta fara amman ta kasa cewa komae bata ankara ba sai ji tay ya ida yin hugging nata sosae ta yarda har ya d'aura Ha6arshi a saman kanta, zaro ido Fatuu tay ta d'an bud'e baki alamar Al'ajabi k'amshin turaren shi ne ya cika mata hanci har bata san lokacin da slowly ta lumshe idanunta ba zuciyarta ta fara melting sun d'an d'auki lokaci a haka can wata zuciyar ta fara raya mata hakan fa da sukae ba kyau miyasa zata bari ya rungume ta haka bacin tasan ba matar shi bace ita ko har ta manta da labarin yaudarar da aka ma Fauzy ne da sauri ta bud'e idonta jin tana kokarin d'ago da kanta yasa shi cire beard d'in nashi daga saman kanta ta d'ago ta kalle shi sam bazata iya karantar yanayin fuskar shi ba, ganin baida niyyar sakinta yasa ta kira sunan shi cikin disasshiyar murya ya d'an bud'a ido alamar amsawa da ido tay mashi nuni da rok'on da yay mata alamar ya saketa ya kafeta da ido kamar bai gane

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login