Showing 153001 words to 156000 words out of 512766 words

Chapter 52 - Asanadin Makwabtaka Book 3 Hausa Novel Complete

Unknown   

27 Dec 2024

1593

curo Hijab ta fara k'ok'arin saka wa ya mik'e ya daidaita kan abun sallar gaba ita kuma ta hau kan ta baya ya kabbara salla, Nafila raka'a biyu sukai sam Fatuu batayi mamakin jin yadda yake sakin kira'a ba don ba yau ta fara jin shi yana karatun Qur'ani ba yana yawan yi ta cikin wayar shi, gaba d'aya Allah ya bashi ilimin boko dana Addini abun saidae ace ma sha Allah, zama sukai suna lazimi tana ta kallon sumar bayan kan shi ba zato sai gani tay ya juyo har saida gabanta ya fad'i don sun yi gab da juna, had'a ido sukai ta d'an waro nata yay mata alamar ta matso da kan shi, matsawa tay dab da shi ya kai hannu ya dafa kanta ta d'an sunkuyar da kan tana kallon k'asa gaba d'aya k'amshin shi ya gama cikata, Addu'ar da Manzo (S.A.W) ya koyar mutum yayi in yay Amarya ya shiga yi bayan ya gama ya sauke hannun nashi ta d'ago suka k'ara had'a ido, bai yi tunanin tambayar ta wani abu ba don duk abunda yake son sani game da ita ya sani, juyawa yay ya d'aga hannu ya fara jero Addu'oi da sauti kad'an itama ta d'aga nata hannuwan bayan ya gama a tare suka shafa ya yunk'ura ya mik'e tana dai ta bin shi da ido, har yayi taku d'aya zuwa biyu ya dakata ya juyo ya furta akwai abu akan dining table daga haka ya juya ya nufi kopar ya fita, zugudum tay ta bi k'opar da ido tama rasa tunanin da zata yi, gaba d'aya ta kasa gane mashi duk ya canza mata sai kace ba Ya Haisam d'in da ta sani bane, in don abun da tayi ne ai taje ta bashi hak'uri kuma ya nuna ya hak'ura to miyasa taci gaba da ganin shi haka wanda ada da ta bashi hak'uri yake hak'ura kuma bata ganin canji a tattare dashi kamar yanzu, gaba d'aya jikinta ne ya k'ara yin sanyi, tunowa da Abincin da su Hajiya suka kawo yasa ta yunk'ura ta mik'e, cire Hijab d'in tayi ta linke ta mayar ta dawo ta kwashe abubuwan sallan suma ta linke ta je ta ajiye ta d'auki kallabin ta dake a saman gadon ta yafa saman kan nata ta nufi hanyar fita, d'an jimm tay a bakin k'opar tana zullumin fita can dai ta kama handle d'in ta ja kopar ta bud'e a d'arare ta fita,

Tana zuwa bakin corridor d'in ta hango shi zaune akan L-shape ya d'an kishingid'a yana kallo, had'a ido sukai da sauri ta kawar da nata sum sum ta nufi hanyar dining d'in, tana zuwa taga manyan ledoji guda biyu ta fahimci sune yay mata magana akai ta kai hannu ta fara bubbud'a su taga miye a ciki, d'aya su ice cream da Youghort da kuma snacks d'ayar kuma fruit ne, shiru ta d'anyi tana tunanin yadda zata yi dasu can ta d'auki guda ta nufi freezer ta bud'e ta saka, dawowa tayi ta d'auki d'ayar ma taje ta kai ba tare data d'au komai ba don ta ci, bayan ta dawo tsaye tay gaban table d'in tana tunanin ko zai ci Abincin ma, wata zuciyar ta bata taje ta fara tambayar shi, kamar bazata je ba sai kuma ta tafi tana tafiya kamar wadda k'wai ya fashe mawa a ciki, bata zagaya cikin parlon ba sai ta bi ta bayan kujeru ta tsaya a d'an gefen bayan kujerar da yake zaune ta bi shi da ido ta kasa cewa komai, kamar yaji ajikin shi da mutum a wurin ya d'an juyo da kan shi suka had'a ido, d'an kikkafta idanu ta shiga yi da k'yar tace mashi dama Abinci ne aka kawo daga part d'in Hajiya, shiru ya d'anyi still idon shi na akan ta sai kuma ya d'an girgiza mata kai alamar bazai ci ba, maimakon ta tafi sai tay tsaye tana kallon shi ganin haka yasa shi cewa "Dare yayi" saida ta had'iyi abu kafin a sanyaye tace "ai Abincin ba mai nauyi bane" yanayin kallon da yake mata ne ya sauya da sauri ta maida nata idon k'asa tana haka taji ya mik'e ta d'ago tana kallon shi, saida taga ya zagayo sannan itama ta nufi Dining d'in ta d'ayan side d'in da ba ta nan ya bi ba.............



_Littafin A Sanadin Makwabtaka part 2 Naira 300 ne za'a tura ma Mutum har part 1 ga mai so zai turo kudin ta wannan Account din, 1509618776, Zainab Bature Access Bank, za'a turo shedar biya ta wad'annan nos din 09013804524 ko 08169856268
[5/8, 19:28] +234 901 700 4868: *ASM Bk2062*

_Destiny may be delayed but cannot be changed...._


*DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI*



......... Zama yay akan d'aya daga cikin chairs d'in sai lokacin ta tuno da bata d'aukko plates ba da d'an hanzari ta juya ta nufi hanyar corridor Slowly ya juya yana kallonta har ta shige sannan ya janye idon, bada Jimawa ba ta dawo hannuwanta ruk'e da plates da bowl sai serving spoon da kuma spoons da forks duk ta d'aurayo su don da alamun lemar ruwa a jikin su, bayan ta aje ta bud'e babbar warmer d'in ta fara zuba mashi tana sa kaman rabin plate taga ya d'an d'aga hannu alamar ya isa ta d'aukko k'atuwar tsokar nama ta d'aura tana niyyar k'ara wata nan ma ya k'ara dakatar da ita ta hanyar k'ara d'aga mata hannu ta tsaya, saka mashi fork tay ta tura gaban shi ta bud'e Warmer d'in farfesun ta zuba mashi kad'an ta tura mashi, Fridge ta nufa ta d'aukko bottle water da lemu ta dawo ta aje daga gaban shi ta sake juyawa ta koma ta d'aukko glass cups daga cikin fridge d'in ta dawo, tana niyyar bud'e robar lemu ya dakatar da ita a hankali ya furta ruwa kawae yake buk'ata ganin zata bud'e nan ma yace sai ya gama a hankali ta furta to, zuba nata abincin tayi bada yawa ba tasa fork ta d'auka tana niyyar juyawa ya d'ago ya kalleta suka had'a ido ta kasa tafiya,

"zaki je ina ki ci Abinci?" taji cool voice d'in shi ya tambaya, shiru kaman bazata ce komai ba ganin ya kafe ta da ido yasa tace d'aki zata je, still yay yana kallon ta can taji yace "shi nan don me aka yi shi?" Shiru bata ce komae ba ta maida idon ta k'asa, "Sit!" cike da bada umarni taji ya fad'a, ba yadda ta iya dole ta aje Abincin ta zauna, duk da tana jin yunwa ta kasa cin Abincin sosae don duk sai taji ya fitar mata a rai sai d'an tsakura take tana yi tana satar kallon shi yanata cin nashi a nutse, bata wani ci da yawa ba ta mik'e ta d'auki Abincin yana kallonta tun kan yace wani abu tace mashi ta k'oshi zata kai kitchen ne ya d'an d'age mata gira "da kika ci mi?" yanayin Fuskar ta ne ya sauya idanuwan ta sukai rau rau kaman zatai kuka yace ta zauna ta cinye shi, komawa tay jiki a sanyaye taci gaba da ci ba don tana jin dad'in shi ba don ta rasa mike mata dad'i kamar ta fashe da kuka take ji, ya rigata gamawa amman sai yay zaune ya kafe ta da ido har saida itama ta cinye sannan ya mik'e ta bi shi da ido, Fridge ya nufa ya bud'e ya d'aukko babbar robar ice cream da wasu daga cikin Snacks ya dawo, aje mata yay gabanta da sauri ta kalle shi ba tare da ya kalle ta ba yace suma ta cinye aikuwa kaman jira take ta fashe mashi da kuka ta kife kanta a kan table d'in kallabin ta ya zamo ya baro saman kan ta, bin ta da ido yay yana kallon ta da alamun mamaki ita kan ta kawai ji tay kukan yazo mata, d'an kwankwasa saman glass table d'in yay ta d'ago fuskar ta jage jage da hawaye ta kalle shi,

"na buge ki ne?" Ya tambaya had'i da d'age mata gira ta girgiza mashi kai alamar a'a, "then miye abun kuka?" cikin muryar kuka tace "ni na k'oshi" bin ta da ido yay can yace "shine na kuka, ko akwai abunda ke damun ki ne?" Da sauri ta girgiza mashi kai alamar a'a, "Ok, kin ci wani abu ne before I came?" Kai ta sake girgiza mashi, "kuma shine har kin k'oshi?" tana d'an tura baki tace to ba ta ci Abinci ba yanzu, yanayin fuskar shi ne ya sauya kaman zai d'an yi murmushi "ai baki k'oshi ba so ki k'ara da wannan" kallon shi tay ba dama tay mashi musu don kuwa yasan yanayin yadda take cin Abinci, ganin ya kafeta da ido yasa da sigar shagwa6a ta d'an juya kai tana yamutsa fuska tace to ai sunyi mata yawa dare yayi sosae bazata ci Abinci da yawa ba tunda kwanciya zata yi, ganin yadda yake kallon ta tana Maganar yasa ta juyar da fuskar ta gefe can taji yay sigh ya furta Ok, komawa yay ya zauna duk abunda ya d'aukko ya raba biyu saidae d'aya yafi d'aya girma ya bata wanda suka fi girman shi kuma ya fara cin sauran itama ta fara ci tana yi tana d'an kallon shi har lokacin ba kallabi a kanta, kusan a tare suka gama ya bud'e mata robar ice cream d'in ya tura mata ganin yana niyyar mik'ewa da sauri tace to shi bai rage ba ai yayi mata yawa shi ma, wani kallo ya jefa mata sai taga kaman ya harareta ta d'an tura baki ta sauke idon ta k'asa, d'an guntun murmushin da iyakar shi lips d'in sa yay taji yace in ta rage tasa a fridge daga haka ya juya ta d'ago ta bi shi da ido, dakatawa yay ya juyo yace in ta gama yana buk'atar fruit bada yawa ba ta d'aga mashi kai ya juya ya tafi, sai gashi ta shanye ice cream d'in duka dama harda rashin sake mata fuska da ta ga baiyi ba yasa taji komae ya fitar mata a rai, bayan ta gama ta nufi Fridge ta fiddo ledar fruit d'in tunanin ko ta had'a mashi fruit salad tay tasan zai fi jin dad'in sha tayi ta juya tana ruk'e da ledar ta nufi hanyar corridor yana zaune a inda yake da kafin ya tashi ya d'an kai idon shi kanta kafin ya maida su kan tv, ba 6ata lokaci ta had'a mashi ba mai yawa ba sosae a cikin d'an bowl mai kyau ta bud'e fridge d'in cikin kitchen ta d'aukko k'ank'ara ta d'an kwankwatsa ta a ciki ba mai yawa ba don tasan bai son abu mai sanyi sosae, saka ledar fruit d'in tay a cikin fridge d'in nan ta d'auki bowl d'in ta nufi parlon, tunda ta fito ya maido idon shi kanta itama kallon nashi take tana isa ta d'aura saman c-table ta ja shi gaban shi ta d'ago suka had'a ido tace gashi nan da d'an murmushi ya jinjina kai tare da furta thanks, juyawa tay ta koma Dining Area ta fara kwashe kayan Abincin, wanda zata saka a fridge ta saka tay clearing wurin, saida ta wanke duk abunda suka 6ata a cikin kitchen ta maida su ma'adanar kowanne sannan ta fito ta nufi bedroom, tana shiga ta koma can bakin gado inda ta zauna d'azun ta zauna tay shiru kaman mai tunanin wani abu, gajiya tay da zaman ta kai kwance amman k'afafun ta na a k'asa, har bayan wani lokaci tana a hakan can taji an bud'e kopar da sauri ta tashi zaune suka had'a ido, rufe kopar yay ya nufo ciki ya tsaya gaban dressing mirror ya fara k'ok'arin cire Diamond Watch d'in wrist d'in shi, bayan ya cire a saman wurin ya aje ta ya juyo idanunshi suka sauka cikin nata da take ta faman bin shi dasu taga ya nufi hanyar Laundry room tana ta kallon shi har ya shige sannan ta juyo, komawa tay yadda take kafin ya shigo taci gaba da wurga ido tana tunane tunane, kusan Mintuna 15 ya d'auka sannan taji ya turo kopar ya fito tana kwancen ya zagayo wurin gadon, wani irin bugu k'irjinta yay mata don kuwa daga shi sai towel d'aure a k'ugun shi ya fito, tunda take bata ta6a ganin namiji haka ba balle shi da yake Tubarkallah, a rud'e ta juya ta yadda ta bashi baya yana jin mutsu mutsun ta bai ko kalle ta ba ya nufi gaban dressing mirror, duk mayuka da turarurrukan da yake amfani dasu suna a wurin saidae an k'ara wasu dasu kwalaben humra da turaren wuta, mai din shi ya d'an shafa sama sama bayan ya gama ya hau feshe jikin shi da turare Fatuu da tay lamo tana ta kikkifta idanu tana jin yadda yake fesa turarurruka ta d'an lumshe ido had'i da d'an yin murmushi, yana da son k'amshi sosae har da hakan ke k'ara mata k'aunar shi gashi koda yaushe zaka ji k'amshin shi na daban ne, bayan ya gama closet ya nufa ya bud'e bayan ta zuge ya fiddo sleeping dress riga da wando ya juya ya k'ara nufar laundry idon shi akan Fatuu da ta takure guri guda ya d'an ta6e baki da yanayin murmushi kan face d'in shi ya wuce, jin k'arar k'opa yasa ta d'ago da sauri ta kalli kopar Bedroom d'in sai dai bata ga alamar ita aka bud'e ba nan ta gane laundry ya shiga, bada jimawa ba taji motsin zai fito aikuwa da sauri ta maida kan yadda take da, fitowa yay ya saka kayan baccin ya nufi k'opar fita, har ya kama handle d'in sai kuma ya dakata ya juyo yana kallon ta, ta ji lokacin da ya kama k'opar amman bata ji ya rufe ba hakan yasa ta d'an d'ago zata saci kallon shi karaf suka had'a ido nan take ta kama kanta ta k'arasa d'agowa ta tashi zaune sai waro ido take tana d'an motsa baki,

"Zaki kwanta haka ne?" taji ya fad'a, shiru tay tana kallon shi ba tare da ta ce komai ba, d'age mata gira yay "am I not talking?" abu ta d'an had'iya a hankali tace "a'a",

"U should go and take bath" kai ta d'aga mashi alamar to ta mik'e sumimi sumimi ta nufi wurin wardrobe, towel d'in da ta gani saman jakunkuna ta d'auki wani light blue ta juyo idanun ta suka sauka cikin nashi yana tsaye har lokacin da sauri ta sauke kanta k'asa ta wuce, tana kaiwa bakin k'opar zata shiga taji k'arar bud'e kopar shi ta juya lokacin ya fita, After some minutes ta fito tana d'aure da towel d'in a k'irji da yake yana da d'an girma ya saukko mata ta yafo kallabin lace d'in da ta cire, nufar wurin jakunkuna tay ta duk'a ta bud'e wadda ke d'auke da kayan bacci, wata doguwar riga cotton ta fiddo cikin kayan da Hajiya ta aiko jikinta gwanin taushi ta bud'e cikin Akwatunan ta ta d'aukko hula ta mik'e ta koma bakin gado, saida ta d'an shafa mai sannan ta shafe jikinta da wata humra mai Masifar k'amshi don kuwa nan da nan k'amshin ta ya karad'e d'akin ta d'aukko roll on ta goggoga a hammata, bayan ta gama yan shafe shafen da goge gogen ta dawo bakin gado ta saka rigar, komawa tay gaban dressing mirror d'in ta hau feshe jikin rigar da turare saida ta fesa kaman kala ukku sannan ta dawo bakin gadon ta d'auki towel d'in ta nufi laundry don ta baza shi ya bushe, bayan ta fito zama tay a bakin gado tay shiru gaba d'aya bata jin bacci gashi dare yayi sosae don tuni k'arfe 12 tayi ko don Saboda bak'unta ne oho, tana ta zaune can ta idasa hayewa gadon ta kwanta tay k'uri tana kallon bangon da k'opa take, bata dad'e da kwanciyar ba ya turo k'opar ya shigo suka had'a ido ya tunkaro gadon har saida gabanta ya fad'i, yana isa bakin gadon ya kai hannu ya d'aukko babban pillow guda ya d'ago idon shi a Kanta ya furta mata "Gud nyt" kai ta jinjina mashi kaman yar k'adangaruwa, har zai juya sai kuma ya kai hannu jikin lamb dake gefen gadon ya kunna sannan ya juya Fatuu dai nata kallon shi, saida ya kashe switch hasken d'akin ya d'auke sai na fitilar da ya kunna sannan ya bud'e kopar ya fita, zuru Fatuu tay a ranta ta fara tunanin kenan a parlor zai kwana Saboda ita, sam ran ta bai mata dad'i ba ba kuma don wani abu ba sai don kwanan da zai yi a parlon tasan ba lalle yaji dad'in kwanciyar ba duk da kujerar nada taushi sosae amman zai iya takura, tana ta zancen zuci can zuciyar ta ta raya mata wani abu tay d'an jimm tana tunanin tayi ko kuwa, tashi tay zaune ta saukko daga saman gadon ta nufi hanyar fita har ta kusa kaiwa kopa sai kuma ta dakata ta juyo ta koma wurin kayanta, golden gyalen da ta cire ta d'auko ta yafa sannan ta nufi kopar fita.

Lokacin da ta fito cikin Corridor d'in tsayawa tay tana kallon cikin parlon ya kashe hasken cikin shi sai na wasu da ya bari na gidajen wurin su Tv sune suka d'an haska parlon, nufar cikin parlon tay sai kace mai yin sand'a ta hango shi kwance kan L-shape side d'in da ya fi zama, tunda ta bud'e k'opa ta fito ya hangota ya zuba mata ido yana ta kallon ta har ta k'araso, daga bakin kujerar taja ta tsaya tana kallon shi ta gane kallon ta yake shima, kasa isa wurin shi tay tayi tsaye sai d'an wasa take da yatsun hannunta tana d'an kikkafta ido had'i da motsa baki alamar tana son fad'in wani abu, yunk'urawa yay ya tashi zaune idon shi akanta yay mata alamar ta zo da hannu ta matsa a d'ayan side d'in ta tsaya ya k'ara mata alamar ta zauna a hankali ta d'an d'osana

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login