Showing 39001 words to 42000 words out of 512766 words

Chapter 14 - Asanadin Makwabtaka Book 3 Hausa Novel Complete

Unknown   

27 Dec 2024

1559

mi take nufi ba hakan yasa ta d'an 6ata fuska sigh yay slowly ya saketa had'i da furta "am sorry" shiru tay ta sadda kanta ya kai hannu zai kama trolley d'in ta d'ago tace mashi bari ta rike bai ce komae ba ya d'auki jakar laptop d'in yay gaba ita kuma taja trolley d'in tabi bayan shi, saida suka je part d'in Hajiya harda Abbas ta rako su har bakin Mota tana ma Haisam Allah yasa a sauka Lafiya ya gaida su Farha da yake Lagos zai sauka daga can gobe zai wuce Us, Abbas ne ya shiga driver seat sai Haisam na gefen shi ita kuma Fatuu ta shiga baya ya tashi Motar Hajiya nata d'aga masu hannu har suka fuce, bayan sun hau hanya sama sama Abbas da Haisam d'in ke yin hira can Abbas ya kalli Fatuu ta cikin mirror yace "Mom Zarah yau ba kuka kenan Ya Handsome zai tafi" dariya tay mashi bata ce komae ba Haisam ya d'an juyo ya kalleta ta rufe Fuskar ta da gyalen ta Abbas duk yana kallon ta ta cikin mirror yana dariya yace "yakamata yau ma a d'an rera mana gaskiya" d'an tura baki tay tace "ai ko wanccan lokacin ma don ina tunanin ya tafi kenan ko zai zo sai an dad'e" Abbas yace "Hajiya na raye ai dole zai rink'a zuwa ko don ita yanzu ma ai in ya tafi baza'a dad'e ba sosae zai dawo don akwai bikin wani Friend d'in mu da za'a yi bayan babban salla kuma shine best friend d'in shi a cikin musulmai" waro ido Fatuu tay tace shi kenan ba musulmi bane yace eh Christian ne d'an sarkin inyamurai ne sun d'an zauna anan amman yanzu ba'a nan suke da zama ba amman shi wanda zai auren shi ke kula da wasu wurare na mahaifin shi kamar Hotels da wasu kamfuna tare sukae Secondary da shi, jinjina kai Fatun tay kawae shi dai Haisam bai tanka masu ba, bayan sun iso Airport d'in gaba d'aya suka fito Haisam ya zagaya wurin Abbas ya bashi hannu yay mashi godiya shima yay mashi fatan sauka lpy ya juya ya kalli Fatuu dake d'ayan side d'in tana kallon shi da d'an murmushi shima yay mata daga haka ya juya ya tafi har ya d'an yi nisa Fatun ta k'wala mashi kira ya tsaya ya juyo ya kalleta da faffadan murmushi ta d'aga hannu tana yi mashi bye bye yana murmushi ya jinjina mata kai kafin ya juya Abbas dake dariya ya kalleta suka had'a ido ganin dariyar da yake mata yasa ta d'an cuno mashi baki yace shidae ai bai ce komae ba ta shige cikin Motar shima ya bud'e ya shiga ya ja suka tafi. Sati biyu da tafiyar Haisam aka fara Azumi saida ya turo mata kud'i masu yawa na siyan kayan Azumi tuni ta kai kayan da ya siya mata wurin Kb don a d'inka da aka fara Azumin har tana zolayar gwaggo wai ya taga bata da niyyar yi mata d'inkin salla tana dariya tace ai ita Haisam ya d'auke mata nauyin wannan kuma, a cikin kayan da ya siya mata taba gwaggon atampa da lace amman sai ta amshi lace d'in kawae tace ta bar atampar ta k'ara ba yadda bata yi da ita ba amman tak'i karba sai taba Fauzy ita kawai dama tana da wani material da bata d'inka ba ta had'a mata sosae Fauzy taji dad'in kayan tay ta godiya a tare suka kai d'inkin bayan Fauzy tasa Fatuu ta rakata itama shagon Zee ta siyo kayan sallanta har Fatuu ta k'ara siya mata wasu abubuwan Zee taji dad'in kawo mata Customer da Fatun tay har tay adding nasu a groups d'inta da take business koda zasu ga abu suna so, Alhamdulillah angama Azumi lpy ranar salla tare da Hajiyar Sanata harda Fauzy suka je Masallaci ko k'unshi ma tare suka je gidan su Nanah kamar kowacce Salla, da Fauzy gida zata tafi yin salla amman Saboda tana son su yi yawo tare da Fatuu ta fasa sai bayan sallan zasu tafi tare da Aunty Mareeya, su Fatuu an zama yan mata sun dai sha kyau da sallar abun ba'a Magana Tk ne ya kaisu wurare kamar yadda Haisam ya bashi umarni ko ina tare da Fauzy take zuwa har gidan Abbas suka je da sauran wurare sun sha zafafan hotuna da iPhone d'in Fatuu harda Vedios suka daddaura a status anan Haisam ya gani har ya yaba sosae taji dad'in yabon da yayi har saida ta kasa hak'uri ta ma Fauzy forwarding sai ga Voice note d'inta harda su shewa tana fad'in "Zarah da alamu mutumin nan fa ya kamu wllh kawae miskilanci ne ke d'awainiya da shi amman muje zuwa gab yake da ya shigo hannu" ita dae Fatuu dariya kawae take, har gida Aunty Mareeya tazo tayi ma gwaggo an sha ruwa lpy bayan salla haka ma Abbas ya kawo Feenah da suka zo gidan Hajiya, ana gama salla Fauzy ta tafi Funtua Fatuu taso ta bita amman gwaggo ta hana satin ta d'aya ta dawo suka koma Makaranta sun ci gaba da karatu ba tare da wasa ba a haka har babbar salla tazo wannan lokacin Yola gwaggo tace zasu je yin salla Fatuu taji dad'i sosae ana saura kwana biyu suka tafi Hajiya ma wannan karon saida babbar salla taje Abuja don da k'arama cewa tay bazata je ba ai bata dad'e da dawowa ba Fauzy a Katsina tay salla cike da kad'aici saida suka gama aikin naman layya sannan suka tafi Funtua, su Yadikko sun matuk'ar yin murna da zuwan su kar ma Mino taji ta kasa boye murnarta harda d'inki gwaggo tayi masu su duka harda baffan Fatun da shima yay farin cikin ganin su, kud'i masu yawa da zasu siya lafiyayyun raguna biyu Haisam ya turo ma Fatuu yace suyi layya harda kud'in da zatayi hidiman salla lokacin da ta kira don yi mashi godiya yake sanar da ita sun zo suna Abuja har tana ce mashi zai je katsina ne yace ai Hajiya bata nan kuma suma basu nan wurin wa zai je tace ai da an gama salla zasu koma yace suma bazasu dad'e bane amman yana nan zuwa bikin abokin shi da Abbas ya fad'a mata tace Allah ya kaimu, ana gama salla da kwana biyu suka dawo don ba wani Hutu suka samu ba just salla break ne, washe garin da suka dawo Fauzy ma ta dawo suka cigaba da karatun su.

A bangaren mutanen Us ma tuni sun koma lokacin Auren su ya cika shekara harda kusan wata a lokacin Fanan ta matsa lamba kan lalle sai suje a duba lafiyar su ta bangaren haihuwa don tun auren su bata ta6a yin 6atan wata ba koda kuwa sau d'aya gashi tana period lpy lau, wannan karon ma dai kaman sauran lokutta Haisam d'in cewa yay basu bukatan hakan yanzu ta bari a k'ara lokaci in bata samu ba sai su je amman shi a wurin shi still yayi wuri amman tak'i gaba d'aya ta burkice mashi wai dole tasan wani cikin su bai rasa matsala tunda har sun shekara amman har yanzu batai conceiving ba, sosae ta hana mashi zaman lafiya harda su koke koke to shi mutum ne mara son yaga wani cikin damuwa balle ma ace shine sila hakan yasa yace tayi duk abunda ya kamata sai su je d'in, sosae taji dad'i ba 6ata lokaci tay making appointment da Doctor d'in da zasu gani a Asibitin da take aiki washe gari suka je aka fara masu diagnosis daga baya kuma yay referring nasu wani Asibitin suga Fertility specialist anan aka cigaba da yin binciken tun daga Family history nasu ko akwae wanda bai haihuwa zuwa su awon jini da hotuna sosae akai investigations saidae an fi yi ma Fanan don ita yake ganin kaman in ma matsala ce to daga ita ne sakamakon wasu tambayoyi da yay mata sai washe gari suka gama likita ya fara masu bayanin result na binciken da akayi masu anan yake fad'i masu Fanan ce mai matsalar don tana da Polycystic ovary syndrome (PCOS) Wato matsala ce data shafi kwan da take saki har saida Fanan ta firgita jin wannan Maganar a razane tace how comes ita da take having regular periods! Shima Doctor d'in yayi mamakin hakan daya kasance bata ga wani symptoms ba don yawanci indai mace nada matsalar to zata rink'a samun irregular periods ne bazata rink'a yin period very often ba saidae kuma a tambayoyin da yayi mata farko ta tabbatar mashi wani lokacin periods d'in yana d'an dad'e mata in yazo amman bata maida kai kan hakan matsala bane don tun kafin tay aure ma tana hakan wanda hakan ma na daga cikin alamomin matsalar tata sai kuma a Family history nan ma ta tabbatar mashi da Kakarta wato Hajiyar Sanata tana da Matsalar yawan miscarriage lokacin tana haihuwa hakan yasa iya yara biyu ta Haifa a rayuwarta daga Mahaifin Haisam d'in sai kuma Mahaifiyarta hakan ma ya k'ara tabbatar da yuwuwar tayi gadon matsalan ne daga wurinta, tuni hawaye suka wanke mata fuska don tasan tabbas indae tanada wannan matsalar to zata iya hana ta samun ciki balle harta haihu rarrashinta suka fara yi suna bata hak'uri Doctor yace bai kamata ta tashi hankalinta ba tunda is treatable za'a iya dacewa ta samu cikin nan ya shiga bata shawarwari da abunda yakamata ayi, tun bayan da suka baro Asibitin take ta cizgar kuka tana fad'in "Ya Haisam am barren! I cannot give birth I can't give u child!!!" Duk ta firgice abunka da fara jijiyoyin kanta duk sun firfito fuskarta ta yi jajir ya kai hannu ya ruk'o nata yana d'an murza shi alamar rarrashi sai faman kuka take tana fad'in ta bani bazata iya haihuwa ba shikenan bazata bashi d'a ba har shakewa take wurin yin Maganar Saboda kuka shi kam sai faman rarrashinta yake a nutse yake fad'in ta kwantar da hankalinta hakan ai ba yana nufin kwata kwata bazata haihu bane Allah na iya nuna ikon shi a kowane lokaci a haka har suka iso gida still yana ruk'e da hannunta suka shiga Parlor a saman 3 seater suka zauna ya rungumeta yana cigaba da rarrashinta sai faman fad'in tasan da wuya ta haihu tunda tayi gadone kuma gara ita Hajiya ma tana yin miscarriage amman itafa ko sau d'aya bata taba samun cikin ba balle ma tayi 6arin, suna cikin hakan can ya ji ta tayi tsit kamar ba ita ke rizgar kuka ba da sauri ya d'ago fuskarta da tay jage jage yaga idanunta a rufe alamar ta suma a razane ya mik'e ya kwantar da ita akan kujerar ya nufi fridge ya d'aukko bottle water ya dawo bayan ya cire murfin ya d'an zuba a cikin hannun shi ya yayyafa mata a fuska sai gashi ta ja wata irin doguwar ajiyar zuciya da sauri ya rufe robar ya aje gefe ya duk'a a gabanta ya kai hannu yana d'an bubbuga face d'inta had'i da kiran sunanta slowly ta bud'e idanun suka k'ura ma juna ido can kawae sai ta k'ara fashewa da wani Sabon kukan daga kwancen tana girgiza kai hannu yasa yana shafa gefen fuskarta a hankali yaci gaba da rarrashinta can ta yunk'ura ta mik'e da gudu ta nufi d'aki ya mik'e ya bi bayanta..........



_Littafin A Sanadin Makwabtaka part 2 Naira 300 ne za'a tura ma Mutum har part 1 ga mai so zai turo kudin ta wannan Account din, 1509618776, Zainab Bature Access Bank, za'a turo shedar biya ta wad'annan nos din 09013804524 ko 08169856268
[5/8, 19:28] +234 901 700 4868: *ASM Bk2039*

_Destiny may be delayed but cannot be changed...._


*Wannan page tukuici ne agare ki Mrs Haisam Kano ina matuk'ar godiya Allah ya k'ara dankon kauna keda Haisam ya sauke ki lpy Amin🤲😍*


*DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI*





.........Tunda suka hau hanya ba wanda yace uffan idon shi na akan hanya ko ta mirror bai kalleta ba yanata driving itace ke d'an juyowa ta saci kallon shi, a hanya ya tsaya bakin wani Masallaci ba tare da ya kalleta ba yace zai yi salla ta d'aga mashi kai tana ta kallon shi har ya fita, bayan an gama ya dawo suka tafi saida ya k'ara tsayawa bakin wani Cafe ya fita bada jimawa ba ya dawo hannunshi ruk'e da ledoji masu d'auke da tambarin wurin guda biyu ya bud'e back door ya saka sannan ya dawo ya shige driver seat ya ja suka tafi duk jikin Fatuu yay sanyi ganin ko kallonta bai yi, a bakin kopar gidansu ya tsaya ta kalleshi a sanyaye tace "Nagode" sai lokacin ya d'an kalle ta ya jinjina mata kai kawae har ta bud'e Motar taji voice d'in shi yana fad'in ta d'au abun dake baya a hankali tace to ta idasa fita ta rufe kopar, ganin ledojin biyu ne yasa ta d'auki guda d'aya ta k'ara mashi godiya still kan ya jinjina mata ta rufe mashi kopar ta nufi gida shi kuma yaja ya tafi, tsaye tay a bakin wurin tana kallon bayan Motar har saida yasha kwanar gate d'in gidan sannan ta juya sukuku da ita ta nufi cikin gida, d'akin gwaggo ta nufa ta shiga da yar sallama lokacin tana zaune akan abun salla tana yin tasbih Fatun ta nufi ciki ta zauna akan kujera, juyowa gwaggo tay da d'an murmushi tace sun dawo Fatuu ta d'aga mata kai ta k'ara cewa "Amman dai ba iya gidansu Fauziyyar kuka je ba ko" kai Fatuu ta d'aga tace "Eh daga can gym muka wuce" cikin rashin fahimta gwaggo ta tambayi ina ne hakan tace mata wurin motsa jiki gwaggon ta jinjina kai suka d'an yi shiru sai kuma tace ma Fatun ya taga kamar wani abu ma damunta da sauri ta k'ak'alo murmushin yak'e tace ba komae ta gaji ne ta yunk'ura ta aje ledar hannunta a gaban gwaggon tace shine ya siyan mata gwaggo ta hau godiya tana shi Albarka, ganin Fatun na niyyar mik'ewa tace ta d'auka ta d'iba sai ta d'ibar ma Amadu shima ta mik'a mashi tace to ta d'auki ledar ta nufi kopa ta fita, bayan ta d'an d'iba su shawarma ne harda ice cream ta kaima Kawu Amadu waje har yana tsokanarta yana fad'in Amaryarmu harda tsaraba ta d'an tura mashi baki yasa dariya don yasan bata so shiyasa yake tsokanarta yana ce mata hakan tun bayan da aka fasa aurenta, da k'yar ta ci don duk komae bai mata dad'i bayan tayi sallar isha ta watso ruwa ta canza kaya zuwa na bacci ta haye gado, tana son ta d'an duba littattafan ta amman ta kasa tay kwance kawae. Tun bayan da ya koma gidan saida ya fara zuwa part d'in Hajiya ya kai mata d'ayar ledar ganin yana niyyar tafiya tace ya tsaya yaci Abinci mana sai ya tafi gaba d'aya yace Ok tasa Saude ta kawo mashi anan Parlor yana ci Hajiya dake zaune tana mashi fira har ya gama sukae bankwana ya koma part d'in shi, wanka yayi ya shirya cikin sleeping dress yana son ya d'an yi wani aiki a computer amman sai yaji bai iyawa ya haye gado kawae ba tare da ya kashe Switch d'in d'akin ba ya kwanta yana facing sama hannunshi na dama ruk'e da beard d'in shi kafarshi d'aya a mik'e d'ayar kuma ya d'an d'agata a lankwashe yana d'an girgiza ta da gani akwae abunda yake tunani. Sai faman juyi take don ta kasa ma yin bacci ga Maganar Aunty Mareeya dake ta mata yawo ta d'azun da tace kar ta rink'a 6ata mashi rai gashi ta fahimci kamar ranshin ya 6aci ta ayyana ita sam bata san hakan zai 6ata mashi rai ba ai da bata fito hakan ba ta tsaya ta canza kayan, wata zuciyar ce ta bata ta kira shi kawai ta bashi hak'uri zai fi kaman bazata yi hakan ba can kuma sai ta tashi zaune ta kai hannu ta janyo wayar ta bud'e ta shiga call log sai da ta d'an yi jimm kafin can kuma tay sending mashi kira, yana a yadda yake kiran ya shigo ya juya ya kalli wayar dake akan bedside kafin ya mik'a hannu ya d'aukko ta idon shi suka sauka kan screen d'in ya bi kiran da kallo kaman bazai picking ba can ya d'aga yasa speaker ya juya daman shi ya aje wayar saitin fuskar shi, shiru sukae ba wanda ya tanka har bayan d'an wani lokaci sannan yaji cikin sanyin murya ta fara Magana "Ya Haisam dama ina so in baka hak'uri don Allah in ranka ya 6aci am sorry" yanayin fuskar shi ne ya canza kamar zai yi murmushi kafin yay sigh taji yace "kin man wani abu ne?" d'an yamutsa fuska tay tace "Abunda ya faru d'azun naga kaman kayi fushi" lumshe ido yay sai kuma slowly ya ware su taji yace karta damu bai yi fushi ba har saida ta d'anyi murmushi,

"Miyasa baki bacci ba har yanzu?" Tura baki tay a shagwa6e tace "ba Kaine ba ka canza man fuska" d'an murmushi yay har saida ta jiyo sautin shi a ranshi ya ayyana har yanzu bata canza ba kaman yadda ya san ta da bata son taga anyi fushi da ita duk sai ta damu, ce mata yay ya wuce ta daina damuwa tace to suka d'an yi shiru can taji yace yanzu sai tay baccin ko tace ai bata fara jin baccin ba yace Ok suka d'an k'ara yin shirun, kaman daga sama taji yace to ta bashi labari ba shiri ta waro ido don abun da bata zaci jin shi ba daga bakin shi bane tana murmushi tace "to ai ni banda labaru don daga gida sai Makaranta nike zuwa saidae in baka na Asibiti" sosae yake jin dad'in voice d'inta in tana Magana a shagwa6e, shima murmushin yake yace mata bai son wannan ta manta matarshi Doctor ce tace Shikenan suka k'ara yin shiru,

"Baki fad'a man yadda akai calling off Auren ki ba" wannan karon k'irjinta ne

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login