Showing 456001 words to 459000 words out of 512766 words
Chapter 153 - Asanadin Makwabtaka Book 3 Hausa Novel Complete
Unknown
27 Dec 2024
1660
kafin ya wuce, wani kallo Hajiya tayi mashi tace "Humm, su Mani anga farar fata har an zurma da anaso ai man bariki" Dariya ya 6a66ake da ita harda buga ƙafa yace "Sai Hajjaju mai dalilin aure, saboda dai kina so ne kawai"
"To tunda hakane a barshi kawai na janye....." da sauri ya katseta "a'a Hajjaju ba'a yi haka ba tunda dai kinyi niyyar haɗawa kada kima kan ki buƙulun lada ki kiratan kawai sai inje mu gwada sa'ar" wani kallo mai kaman harara tayi mashi ya saka dariya, ce mashi tay ya bari ayi sallar la'asar ɗin zata kirata Kawu Manin harda ce mata to ai kada ta fita unguwa Hajiyar na dariya tace ya dawo wani lokacin,
"gara dai ayi komai yau hajjaju kinsan ance da zafi zafi ake dukan ƙarfe" Dariya Hajiya tay tare da girgiza kai, bada daɗewa ba aka kira sallar la'asar ya miƙe don yaje masallaci itama Hajiya ta tashi tana ruƙe da sandarta ta nufi hanyar Bedroom don taje tayi sallar, bayan ta gama ne ta kira layin Gwaggo wayar na fara yin ringing ta ɗaga cikin girmamawa ta gaishe da ita tare da yi mata barka da juma'a bayan Hajiyar ta amsa ta tambayi tana gida tace mata eh bata daɗe data dawo bama daga wurin aiki, an dawo lafiya tayi mata Gwaggon ta amsa da lafiya lau Alhamdulillah,
"to ga baƙo nan na turo zai zo ku gaisa" ɗan jimm Gwaggo tay a ranta ta maimaita abunda Hajiyar tace kafin ta amsa mata da to sukai sallama, zugudum Gwaggo tay ruƙe da wayar tana ta nanata zancen zuwan baƙon don abun sai taji shi wani iri saboda basu ta6a haka da Hajiyar ba wai tace mata ga wani nan zai zo su gaisa, Bayan sun gama yin wayar fitowa Hajiya tayi cikin falon kusan a tare suka dawo da Kawu Manin, bayan sun zauna ya gaishe da ita tana murmushi ta amsa tace yayi na yara duk sukai salla sai sun gaishe da mutum shima murmushin Yay yace ai haka yakamata kafin yace mata yanzu bayan ya fito ya kira Mahaifin yarinyar har ya bashi Address zai je ya same shi daga can zai wuce Daura duk yadda sukai dashi zai sanar mata ta amsa da to tare da yi mashi Allah ya kiyaye hanya, shiru suka ɗan yi bai miƙe ba can yace mata bata kirata bane tay dariya tace ai ta zata ya manta yaje ta kirata a waya, tambayar inda gidan yake yayi ta kwatanta mashi da shagon Amadu tace in yaje yaronta ne mai shagon sai yasa shi yaje yayi mata magana ya amsa da to tare da miƙewa tana murmushi tace Allah yasa taji Alkhairi ya amsa da Amin ta ƙara cewa zata turo mashi kuɗi yanzu sai ya zuba mai yayi mata godiya itama tayi mashi da fatan Allah ya kiyaye hanya tace ya gaida iyali daga aka ya fito,
A daidai shagon Amadu ya parker Motar shi lokacin basu daɗe da dawowa daga Masallaci ba, fitowa yay bayan ya kulle ƙopar Motar ya tunkari shagon, a gaban shagon ya tsaya fuskarshi ɗauke da murmushi yayi masu Sallama tunda ya fito Amadun ke kallon shi yana ganin kaman ya sanshi saida ya ƙaraso gaban shagon ya gane shi shima Amadun murmushin ya mayar mashi bayan ya amsa sallamar cikin girmamawa ya gaishe dashi Kamalu ma dake zaune kan plastic chair yana latsa waya ya ɗago kai ya gaishe dashi shima da murmushi ya amsa mashi, tambayar waye Amadu a cikin su yayi Kawu Amadu yace shine ya nuna Kamalu yace to shi kuma wannan fa ya bashi amsa da ɗan Yayarshi ne,
"Kenan ɗanka ne" Amadu na murmushi ya bashi amsa da eh,
"Ko shine Yayan Matar Haisam" da sauri Amadun yace mashi eh,
"Allah sarki, Allah yayi maku Albarka ya jiƙan Mahaifiyarsu da Mahaifin ka" a tare duk suka amsa mashi da Amin,
"Yauwa ka shiga ciki kace ga baƙon ya iso" ya faɗa still da murmushi akan fuskarshi, da alamun rashin Fahimta Amadun yace wa zai faɗi ma hakan Kawu Manin yace mashi ita mai gidan zaije yace ma ga baƙon da Hajiya tayi mata magana yazo da sauri ya amsa da to ya juyo ya buɗe shagon ya fito, lokacin daya shigo gidan Gwaggon na cikin ɗakinta tun bayan data yi waya da Hajiya dama tana kan abun salla ne bata tashi ba, da sallama ya shigo ta amsa tare da juyowa ta kalleshi ya sanar mata zancen zuwan baƙon tay ɗan jimm kafin a hankali tace mashi ya shigo dashi falo yace to ya juya, shiru tayi a ranta ta shiga tunanin to wane baƙo ne kuma wace irin gaisawa zasu yi kaman yadda Hajia tace, tana jin lokacin da suka shigo Kawu Manin yay sallama, bayan ya shigar dashi yazo ɗakin ya sanar mata gashi can a falo kai kawai ta ɗaga mashi ya juya ya tafi, miƙewa tayi duk tayi sukuku ganin Hijab ɗin jikinta lafiya lou dama gogagga ce ta ɗaukko tayi sallar da ita ta nufi ƙopar fita, lokacin data tunkari falon gabanta har ɗan faɗuwa yake, da sallama ta saka kai cikin falon ƙamshin turaren shi ya bugi hancinta yana zaune akan 2 seater ya ɗago yana kallonta da murmushi ya amsa mata sallamar suna haɗa ido ta gane shi ta nufi kujera mai mazaunin mutum ɗaya daga can gefen tashi ta zauna idon shi akanta yace mata "Barka da Fitowa", ɗan murmushi tayi ta amsa tare da gaishe dashi yana ta murmushi ya amsa, kanta ne ya ɗaure ganin shine don bata ta6a zaton shi zata gani ba matsayin baƙon don tunda tasan Hajiya tasan shi yana zuwa gidan matsayin ƙanin Hajiya tsawon lokacin kuma bai ta6a zuwa nan gidan ba sai yau, miƙewa tayi ta nufi Fridge ya bita da kallo bayan ta buɗe ta ɗaukko lemu da robar ruwa tare da glass cup bayan ta rufe tana juyowa suka haɗa ido ta maida nata ƙasa ta nufo inda ɗan table yake ta ɗaura sannan ta ɗaukeshi ta matsar dashi gabanshi, buɗe lemun tayi ta zuba a cikin cup ɗin ba tare data kalleshi ba tace gashi yasha yana murmushi ya furta "Shukran" ɗan murmushi tayi ta koma inda ta taso, ɗaukar cup ɗin yayi ya kai baki saida ya kur6a kamar sau uku sannan ya aje tare da furta Alhamdulillah ya ɗaura idon shi kan Gwaggo dake kallon Carpet yace "Fatan na same ki lafiya, ya gida ya yara ya aiki kuma" ɗago ido tayi ta kalleshi da ɗan murmushi ta amsa mashi da lafiya lau Alhamdulillah shima ta tambayi ya nashi iyalin da aiki yana sakin ƙayataccen murmushi ya amsa mata, shiru suka yi can ta miƙe tace bari a kawo mashi abinci da sauri ya dakatar da ita yace lemun ma ya isa a ƙoshe yake ta koma ta zauna,
"Yauwa, kamar yadda Hajjaju ta sanar maki ita ta turo ni don mu gaisa da juna kuma tunda mu ba yara bane nasan kin gane wace irin gaisawa ake nufi, ni dai na gan ki kuma kin mani don haka in an amince man Aure nike son muyi tunda duk naji duk wani abu dangane dake nima kuma in kina son sanin abunda ya dangance ni zaki iya yi ma ita Hajjaju magana da fatan za'a amince man" tunda ya fara Maganar ta sunkuyar da kanta har ya gama ta kasa ɗagowa balle tace mashi wani abu, ganin taƙi yin magana yasashi ce mata ita yake saurare ta taimaka ta bashi amsa, gaba ɗaya ya ɗaureta ta rasa amsar da zata bashi don sai taji bata iya ƙin amince ma buƙatar daya zo da ita kodan Hajiya gashi ita ta cire sake yin aure a ranta, a hankali ta ɗago suka haɗa ido tayi saurin kawar da nata kafin tace mashi tana buƙatar yin shawara ya ɗan bata lokaci, yana murmushi yace "Har sai anyi shawara kuma, to kodai ban samu kar6uwa bane?" kallon shi tayi da ɗan murmushi tace a'a kawai tana buƙatar yin shawara ne tunda tana da babban yaro, ɗan buɗa ido yay yace "dashi za'ai shawarar kenan karfa yasa aƙi amince man don kinsan wasu yaran sukan taya iyayensu maza kishi" yar dariya tayi kawai,
"Yanzu har tsawon wane lokaci zan jira Hajiya" yay Maganar yana mata wani kallo da gani shima za'a dashi ta bangaren soyayya, tana murmushi tace malama dai ya wani ɗage gira yace "Ni Hajiya na gani" shiru tay kawai tana murmushi ganin ya kafeta da ido tace mashi ko mi kenan zata sanar mashi ya furta Ok bari ya bata lambar shi amman don Allah kada a ɗauki lokaci asa ya kasa samun natsuwa tace uhmm kawai, wayarta ya tambaya yasa mata lambar tashi ta miƙe tace bari ta ɗaukko tana ɗaki, bada jimawa ba ta dawo ta miƙa mashi wayar ya amsa yana murmushi ya ɗan jujjuyata yace "amman Hajiya sai naga kamar kinfi ƙarfin wannan wayar" murmushi tayi tace tafi jin daɗin amfani da irinta ne yace to amman ga na zamani ai sai a haƙura da tsohon yayi gaskiya yakamata a canza ta tace mashi tuntuni yara keson canza mata ita ce bata so,
"To ai yanzu sai aba maigida dama ya canza" da sauri ta kalleshi ganin kallon da yake mata yasa ta kauda fuskarta yace "na cika azar6a6i ko tun ba'a sanar dani matsayi na ba har na yanke hukunci, ayi haƙuri abunda rai ke muradi ne" juyowa tay ta kalleshi tana ɗan murmushi, lambar tashi ya saka a tata ya kira kafin yayi mata saving tashi ya miƙa mata yace gashinan ya saka mata Alhaji Mani ya tambayi ita kuma Hajiya wa zai saka mata tace Dije ya ɗan yamutsa fuska yace "Wannan na zamanin da ne bari in saka na zamanin yanzu Khadija ko kuma Khadijatul Khubra" Gwaggo bata san lokacin da tayi yar dariya ba shima ita yake yi bayan ya gama saving ɗin ya ɗago ya kalleta yace "to Hajiya Khadija ni bari in zo in wuce inada wani uzuri da zan aiwatar kafin na hau hanya sai naji daga gareki ina fata kuma za'a duba man inji abunda nike fatan ji" murmushi kawai take, miƙewa yay ya zura hannu cikin yan cikin babbar rigar shi ya fiddo kuɗi masu ɗan yawa ya ɗaura akan table ɗin yace gashi nan a ba ɗan shi da jikanshi, da sauri ta kalleshi tace don Allah ya barshi yana mata wani kallo yace bata ji waɗanda yace taba bane dole tayi shiru, tafiya ya fara yi zai fita daga cikin falon ta ɗan juya tana kallonshi har ya kusa ƙopa ya tsaya ganin zai juyo yasa da sauri ta kauda idonta tana haka taji muryarshi yana faɗin bazata raka baƙon nata bane tay ɗan jimm kafin ta kalleshi suka haɗa ido yana mata murmushi, jiki a sanyaye ta miƙe ya furta yauwa ko ita fa ya juya tana biye dashi, saida suka kusa ƙopar fita ya juyo yace to ya gode ta koma kada ya wahalar da Hajiya ta ɗan yi murmushi tare da yi mashi Allah ya kiyaye hanya ya amsa, falo ta dawo ta zauna kan kujera tayi jugum ta rasa ma tunanin da zata yi ganin abun take kamar ba'a gaske ba duk da ba yau aka fara zuwa neman aurenta ba wannan sai taji yayi mata girma sosae ba kamar daya haɗa da Hajiya, tana haka Amadu ya shigo da sallama ta ɗaga ido ta kalleshi ta amsa a hankali, nufo inda take yayi ya zauna a kujerar dake gefen tata ya ɗan yi shiru yana kallonta kamar mai nazarin wani abu ita kuma ta kauda idonta daga barin kallonshi,
"Gwaggota lafiya kuwa?" taji muryarshi yana tambaya, kallonshi tayi da ɗan guntun murmushi tace mashi lafiya lou yace amman to ya ya ganta kamar wani abu na damunta ta ɗan yi shiru kafin tace mashi ba komai, shiru ya ɗanyi yanata kallonta can ya sake tambayarta to lafiya Kawu Mani yazo gidansu yaga bai ta6a zuwa ba tunda suke a gidan, shiru Gwaggo tayi tana tunanin mi zata ce mashi ya kawo shin tunda gashi yasan bai ta6a zuwa gidan ba can zuciyarta ta bata kawai ta faɗi mashi abunda ya kawo shi tunda dama ko ba yanzu ba dole zata faɗi mashi, ajiyar zuciya ta sauke tare da kallonshi kaman mai zullumin faɗi mashi shi kuma ya ƙura mata ido alamar ita yake jira tayi magana can dai tayi ƙarfin halin faɗi mashi Hajiya ce ta turo shi wai ya nemi aurenta, ɗan waro ido Amadun yay kafin da sauri yace "to kin amince mashi zaki aure shin???" a hankali ta girgiza kai kafin tace ce mashi tayi sai tayi shawara amman ita....kafin ta ƙarasa abunda take son faɗin kawai sai gani tayi ya kamo hannunta yace "Don Allah Gwaggota ki amince mashi kada ki ƙi kamar yadda kike yi a baya na roƙe ki, wllh ba wuce kiyi aure kikai ba tsofaffi tukuf ma zaki ga suna da aure tunda shi ibada ne, kinga in kika amince mashi muma a ƙalla zai zama muna da Baba a cikin gidan nan" shiru tayi tana kallon shi ta wani bangaren ta ɗan ji mamaki don bai ta6a nuna mata ya damu da tayi aure ba irin yanzu yawanci da anzo neman aurenta ta nuna bata so sai yace shikenan tunda haka take so, tana haka sai gani tayi ya saukko daga saman kujerar ya duƙa a saman guiwowinshi cikin marairaicewa yace "Don Allah Gwaggota ko don ni ki amince mashi nima dai ace inada wanda zan kira da sunan BABA ba tare dana haɗa da sunan shi ba, tun tasowa ta ba wanda nike kira da sunan Baba ba tare da nace Baba wane ba kamar Baba shehu, Baba musa da sauransu kinga yanzu in kika aure shi Baba zan rinƙa kiranshi ba yadda za'ai in haɗa da sunan shi nima a ƙalla in muna hira da wasu zance Babanmu ka za...." kasa ƙarasawa yay saboda ƙwallan da suka tarun mashi suna niyyar zubowa, wani irin tausayinshi ne Gwaggo taji ya kamata tun yana ɗan shekara shidda ya rasa mahaifinshi, girgiza hannunta yay ya furta "Don Allah Gwaggota..." ajiyar zuciya ta sauke tana ƙoƙarin ƙaƙalo murmushi tace "baka tunanin ba lalle ya zama kamar uba a garekan ba kamar yadda yake faruwa sau da yawa wasu ma sai kaga sun raba uwa da ɗanta..." da sauri ya tari hanzarinta,
"A'a Gwaggo ina da yaƙinin bazai yi hakan ba tunda kika ga Hajiya ta turo shi to tasan baida matsala ne, na tabbatar mutumin kirki ne ai ina ganin shi a gidan Hajiyar muna gaisawa, don Allah ki amince?" shiru tay tana kallon shi ƙwallan idon shi har sun zubo mashi can tace shikenan tunda haka yake so zata amince mashi, da sauri ya miƙe ya zauna gefenta tare da ƙanƙameta cikin tsananin farinciki ya shiga yi mata godiya harda su Kiss ya manna mata a gefen fuskarta ita dae sai dariya take zata iya cewa bata ta6a ganinshi cikin farinciki irin wannan ba in ma ta ta6a gani to ta manta, sakinta yay sai faman washe baki yake ya shiga laluban wayarshi yana faɗin bari ya sanar ma Fatuu wannan abun Farinciki, da sauri Gwaggo tace kada ya sanar mata yace a'a yakamata ta sani da zafi zafi, ƙoƙarin amshe wayar Gwaggon tayi ya miƙe yana dariya ya shiga yin safa da marwa a tsakar falon cikin harshen fullanci Gwaggon ke faɗin tana wasa dashi wai sai dariya yake itama yar dariyar take, tana fara yin ringing Fatun ta yanke sai gashi ta kira yana ɗauka ko gaisawa basu yi ba da sauri yace mata Albishirinta a ƙagauce ta amsa da goro fari ƙal yace banda shi ango sun ƙara samun Amarya a gidansu nan ya shiga faɗi mata zancen auren Gwaggo aikuwa wata uwar ƙarar murna ta saki tana faɗin Alhamdulillah abubuwan farinciki sai faruwa suke dasu Amadun yace Wllh kuwa da sauri tace mashi ina Gwaggon ya bata wayar bari ta maida Vedio call taga fuskar amarya yace to, duk Gwaggo na jin su da yake a speaker yasa kiran sai girgiza kai take tana ɗan murmushi, bayan an maida kiran na gani ya miƙa ma Gwaggon saida ta ɗan harareshi sannan ta amsa Fatuu na ganinta ta daddage ta rangaɗa guɗa duk da bama ta wani iya ba sosae Gwaggon tayi yar dariya, cikin washe baki ta gaishe da ita kafin ta shiga yi mata shaƙiyanci tana faɗin ashe dai da rabon za'a mata makeup na amare a ɗaura mata gwaggaro nan take Gwaggon ta tuna da lokacin da Fatun ta faɗi haka can shekarun baya kafin ta girma ta shiga yin dariya, da sauri Amadu ya fita ya kirawo Kamalu suka dawo falon nan suka haɗu suna ta mata iya shege har saida tace in suka isheta zata fasa Allah sannan suka shafa mata lafiya. Washe gari sai ga Kawu Mani ya kirawota wai ya kira yaji yadda suke nan take sanar mashi ta amince ma buƙatar shi, sosae ya nuna jin daɗin shi harda ce mata shi dama yasan zata amince don su jinin sa'a ne tayi murmushi kawai kafin tace mashi amman ko za'a ɗaura masu aure sai anyi na Amadu yace mata amman mi zai hana a riga yin nasu yadda zasu aurar dashi tare tace mashi ita dai tafi son a riga nashi kuma gidan nasu ma Haisam yasa za'a mashi gyara ne tunda anan zata zauna yace duk yadda take so haka za'ayi tunda anan take son zama lafiya lou ya rinƙa zuwa dama yana yawan zuwa katsinar ko can baya saida yayi tunanin yin mata anan yace alabashshi sai ya rinƙa biyanta kuɗin hayar zaman da take, da sauri tace mashi a'a ba sai yayi hakan ba yana murmushi yace to ai saboda ya fita hakkinsu tunda gidan gado ne tace mashi ai itama tana da kaso a