Showing 51001 words to 54000 words out of 512766 words
Chapter 18 - Asanadin Makwabtaka Book 3 Hausa Novel Complete
Unknown
27 Dec 2024
1566
sake lissafo mata Fatuu nata guntse dariya ta d'an waiga ta kalli Haisam shima murmushi ne akan face d'in shi bayan ta gama lissafawa Fatuu tace mata duk ya zatayi dasu tace kara'i zatay yaushe rabon da su ci kayan dad'i da yawa saidae suga ana kawo ma masu samari to suma tunda Ya Haisam d'in su yazo ai dole su ci dad'i, sosae Fatuu ke dariya jin irin dariyar da taken ne yasa Fauzy tace badai yana ji ba cikin dariya tace a'a sai ta dawo ta kashe, bayan sun je Eatery d'in duk abunda Fauzy ta fad'a saida yasa aka basu Fatuu nata ce mashi wasa fa itama take saidae yay murmushi kawai haka akai masu ledojin takeaways suka taho a bakin gate d'in Makarantar ya tsaya don an riga an tashi ba'a bari a shiga, juyawa tay ta kalle shi da d'an murmushi tay mashi godiya yay shiru har zata juya taji yace bazata koma gida ba ta rink'a zuwa ko tafi son ta zauna a school tana kallon shi tace "to in koman ne?" guntun murmushi yay jin tayi mashi tambaya cikin tambaya yace in tana so ya rink'a kawo ta kafin ya koma tace "to in kai mata Abincin sai in dawo?" shiru ya d'an yi kafin yace taje zai zo bayan Magrib ya d'auketa tace to daga haka ta fita daga Motar ta rufe ta bud'e back seat ta tattaro ledojin ta nufi cikin gate d'in tana yi tana d'an waiwayen shi duk yana kallonta ya juya Motar ya tafi, Fauzy baje saman gado tana latsa waya Fatun ta shigo da yar sallama suka had'a ido da sauri ta yunk'ura ta tashi zaune tana fad'in welcome ta Ya Haisam, a gabanta Fatuu ta aje dukkan ledojin tace "ga dukkan sak'on ki nan sai kita kara'in" waro ido Fauzy tay tabi ledojin da kallo kafin da mamaki ta kalli Fatuu tace "Wai badai fad'a mashi kikae ba?" zama Fatuu tay gefen gadon tana cire Hijab d'inta tace "kedai ba Kin fad'i abubuwan da kike so ba kuma an kawo maki kawae kici gaba da shagali" wani kallon rashin yarda take ma Fatun ba kamar data ga tana yin dariya magiya ta shiga yi mata kan ta fad'i mata ya akai aka siyo wannan uban kayan daga baya Fatun ta fad'i mata shi yaji da kunnanshi tace kenan speaker tasa ta tay shiru tanata mata dariya aikuwa tay kukan kura zata jawo ta Fatuu ta mik'e tanata kyalkyatar dariya Fauzyn na Fad'in "U'r wicked wllh yanzu don rashin Mutunci shine kika sa man speaker na saki baki inata maganganu don Allah ba sai ya d'auke ni acici ba kuma mai son abun duniya" ganin kaman ranta ya 6aci yasa Fatun ta koma gefen ta tana bata hak'uri tace ai shima yasan wasa take kar ta damu kawai suyi shagalin su aikuwa saida ta jawota ta d'uma mata dundu tana niyyar k'ara wani Fatuu ta k'wace tana fad'in daga abun arzik'i in dai ta k'ara bugunta to bazata ci komai ba a ciki Fauzy ta harareta tace "kin ma isa ki zubda man Mutunci kuma kice bazan ci komae ba" ta k'arasa Maganar tana fiddo takeaways d'in tana yi tana jinjina kai tana fad'in Fatuu ta gama da ita ganin duk abunda ta fad'a an siyo shi, saida suka wanke hannuwan su a jikin windown d'akin nasu dake a saman bene sannan suka zauna zaman ci Fauzy tana ci tana saka wa Haisam Albarka Fatuu nata dariya anan take sanar da ita zancen tafiyar ta anjima ta 6ata rai tace "Ya Haisam ya kuma zai mun haka don Allah na samu yanzu kina zama zai dawo mun da kad'aici" ita dae Fatuu dariya kawai take can Fauzy tace "na gano shi wato bai iya jure rashin ki kusa da shi shine zai d'auke ki yace wani zai rink'a kawo ki ke miyasa bazaki ce kin fi son zama nan ba don Allah" ta k'arasa a marairaice kafin Fatun tace wani abu ta sake cewa "koda yake saida hakan zaki janyo mana zuciyar shi don na lura bata jawuwa cikin sauk'i amman gaskiya ban ji dad'i ba" Fatun ta hau ce mata sorry, duk cin su basu iya cinye rabin Abincin ba don wasu abun ma Fatun bata ci ba tace ta bar ma Fauzyn ta rage loneliness da su. Zuwa bayan Magrib ta gama shirya kayanta a trolley d'inta tayi wanka ta shirya cikin straight skirt da riga na atampa sun mata k'yam ta kashe d'auri Fauzy sai yabonta take dama ba tun yanzu ba take fad'in bata ga wadda straight skirt ke ma kyau ba irin Fatuu, yar light make up tayi da ba zata ma yi ba Fauzy ta matsa mata ta d'an shafa humra a jikinta bayan ta gama ta zauna gefen gado suna d'an yin fira da Fauzy har tana fad'in yau dole ta nemo mai tayata kwana don yanzu ta riga ta saba kwana ba ita kad'ai ba Fatuu dai nata mata dariya ganin yadda take Maganar tana tura baki ita ala dole an mata laifi, suna zaunen saiga kiran shi ya sanar da ita yana a bakin gate tace to ta yafa gyalenta a kafad'a tare da Fauzy suka fito tana ruk'e da trolley d'in suka sauka k'asan benen, suna tunkarar gate Fauzy taja ta tsaya ta mik'a mata trolley d'in Fatuu tace "girlfriend bazaki idasa raka ni ba" yar harararta tay tace "in dawo ni da wa kuma ko bama haka ba Allah ban zuwa kin gama zubda man Mutunci" dariya Fatuu tay tace "ki share kawae tunda buk'ata ta biya anci dad'i har an ture" kafewa tay kan bafa ta k'arasawa gate d'in dole Fatun ta amshi trolley d'in tayi mata saida safe sai sun had'u gobe daga haka ta tafi itama Fauzy har ta juya sai kuma ta sake juyowa ta k'wala ma Fatuu kira ta tsaya cikin d'an d'aga murya tace "ki tabbatar kafin ya koma kin ida sace zuciyar ta yarda har ya kasa sukuni sai ya fad'i maki yana son ki don duk wannan kame kamen mun gano shi" dariya sosae Fatuu ke yi ta d'aga mata hannu kafin ta juya ta tafi itama Fauzy ta koma Hostel, tunda ta kusa isowa bakin gate d'in ya fara hangota sakamakon hasken fitilun dake a gefe da gefen hanyar data zo bakin gate saida ta tsaya suka gaisa da baba mai gadi da yake kusan ba wanda bai santa ba a Makarantar tun daga kan d'alibai har zuwa Malamai sosae take da farin jini uwa uba kuma tana da abubuwan dake sa mutum ya rink'a burge mutane kaman kokari ga kyau kuma tana da kirki duk da bata d'aukar nonsense yanzu ta sauke ma mutum kwandon bala'e, tunda ta nufo Motar ya zuba mata idanun shi da ya d'an lumshe su yana mata kallon k'urulla har ta k'arasa ta bud'e back door ta saka d'an trolley d'in kafin ta rufe ta bud'e kopar gaban ta shiga yanzu ma dae k'ananan kayan ne a jikinshi bayan ta zauna ta jawo kopar ta rufe da murmushi ta juya suka had'a ido ta gaishe da shi ya jinjina mata kai daga haka ya juya Motar suka tafi, tsit sukai ba wanda ya k'ara tankawa yanata driving ita kuma tana kallon gefen hanya a bakin wani Cafe ya tsaya yace mata yana zuwa ta d'aga mashi kai ya fita tanata kallon shi lokacin da ya zagayo har ya shige cikin Cafe d'in ta d'an lumshe ido tana murmushi bai d'auki lokaci sosae ba ya fito hannunshi ruk'e da ledoji guda biyu masu d'auke da tambarin wurin ya bud'e baya ta can side d'in driver ya saka sannan ya koma driver seat d'in yaja suka tafi, saida ya k'ara tsayawa wurin masu Fruit saidae bai fita ba ya sauke glass ya fad'i abubuwan da yake so aka cika manyan ledoji guda biyu yace ma mai fruit d'in ya saka mashi a baya bayan ya biya shi suka tafi, lokacin da suka k'araso kopar gidan su Fatuu anata kiran sallar isha ta kalle shi da murmushi tayi mashi godiya bai amsa ba sai ya jinjina kai had'i da lumshe ido har zata bud'e kopar taji voice d'in shi yana fad'in da safe zai zo ya kaita school ta kalleshi tace to ya k'ara ce mata ta d'auki abun baya, kowanne leda guda ta d'auka ta fruit d'in da ta Eatery d'in ta yi mashi godiya suka had'a ido ta mirror kasa d'auke idon tay tana ta kikkafta su can taga yay d'an murmushi duk sai kunya ta kamata ta janye kan ta ta rufe Motar saida ta fidda kayan can gefe sannan yaja Motar Amadu na ganinta ya fito ya zo gabanta yana washe baki yace "wato ya kasa hak'uri saida ya d'aukko ki kenan" wani kallo tay mashi had'i da tura baki ya kai hannu ya d'auki ledojin yana fad'in Juliet ta Romeo suka nufi gidan, d'akin gwaggo suka nufa suna shiga tana sallame salla ta d'aga kai tana kallon su tana ganin Fatuu tay murmushi Amadu yace "ga autar ki nan Romeo ya kasa hak'uri saida ya d'aukko ta" tur6une Fuska tay tace "kai Kawu Amadu miye haka" dariya yaci gaba da yi yana fad'in tuba yake kar a hana shi tsaraba yasan kayan dad'i ne, zama Fatuu tay kan kujera ta gaida gwaggo dake ta fara'a ta amsa mata tace an dawo Fatun tace eh Ya Haisam ne ya d'aukko ta yace zai rink'a kaita kafin ya koma gwaggon ta d'aga mata kai Amadu sai faman k'umshe dariya yake can ya juya yace bari ya d'aukko plate a bashi kason shi gwaggo ta d'an ta6e baki tana girgiza kai koda ya dawo da kan shi ya d'ibi komai harda fruit d'in ya mik'e yana fad'in Allah ya barta da Romeo suyi ta cin dad'i gwaggo ta kai hannu zata make shi ya nufi kopa yana dariya ya fuce gwaggo ta maida idonta akan Fatun tace "ai d'azun bayan ya iso ya shigo nan mun gaisa anan na fad'i mashi kina can Makarantar ashe zuwa yay" d'an murmushi Fatuu tay ta d'aga mata kai itama gwaggo murmushin take duk sai Fatun ta tsargu ta mik'e tace bari ta kai kayanta d'aki ta nufi kopar fita gwaggo ta bita da ido, bayan ta koma d'akinta saida ta cire kayan jikinta tasa na bacci bayan ta fito ta nufi kitchen ta d'aukko plates sannan ta dawo d'akin gwaggo ta zuba masu abubuwan suka fara ci tare suna yar hira har tana tambayarta Fauzy anan ta bata labarin abunda ya faru d'azun gwaggon tanata dariya tace amman bata kyauta ba Fatuu tace to ba gashi tayi kara'in ba, bayan sun gama ta fidda kayan wanda suka rage ta kai fridge ta zauna yin kallo dama ba salla take ba shiyasa bata yi sallar isha'i ba, Washe gari talata da safe Haisam yazo ya d'auketa kamar yadda yace yaci gaba da kaitan, Ranar Alhamis bayan sallar la'asar Haisam na zaune a Parlor tare da Abbas da ya kawo mashi dress code na Dinner d'in da za'ayi gobe Friday ta Abokin su Prince Obinna Eze ganin harda na mata lokacin da ya bud'e kayan yasa Haisam d'in cewa shida wa zai je da zai kawo mashi rigan mata kuma yasan Fanan bata nan dariya Abbas yay yace to haka aka tsara daya je amso kayan aka bashi su haka kowa da matar shi zai je ko budurwar shi don haka dole ya nemi wadda zai je da ita Haisam d'in na kishingide jikinshi sanye da jallabiya tun bayan da ya d'aukko Fatuu ya dawo ya watsa ruwa ya kwanta bacci saida akai la'asar ya farka ana gama sallar Abbas d'in yazo kawo mashi kayan, k'arshe ce ma Abbas d'in yay shi kadae zai je in yaje a koro shi Abbas na dariya yace "haba H,Zakee kaifa kana cikin manyan Abokan shi ya zaka kwafsa bayan ga yadda aka tsara kawai ka samu wata kuje tare badai na d'an lokaci bane" wani kallo mai kaman harara yake bin shi dashi jin Maganar da yay wai ya samu wata suna haka aka turo kopar duk suka kai idanuwan su Fatuu ce ta shigo tana sanye da riga da skirt na material kanta ba dankwali sai gyalen kayan data d'aura asaman kan shima baida wani girma sosae gashi sai zamewa yake gashin ta na fitowa tana rungume da k'aton littafi hard cover suna had'a ido ta sakar masu murmushi Abbas yace ta shigo mana ta nufi cikin parlon ta tsaya tana ta murmushi ta rasa ina zata zauna Haisam na kan L-shape Abbas na kan armchair guda Abbas ne yace ta zauna mana ga wuri nan yay Maganar yana nuna mata daga gaban inda Haisam yake zaune saida ta kalleshi suka had'a ido fuskar shi a sake ta nufi wurin ta zauna ta gaida shi ya jinjina mata kai ta kalli Abbas ma ta gaishe da shi ya amsa yana yar dariya yace "Mom Zarah ko ince Nurse Zarah" gumtse baki tay bata ce komae ba can taji ya sake cewa "Mom Zarah wannan dressing haka yakamata a rink'a sa babban mayafi" wani iri taji kunya ta kamata ta sadda kan ta k'asa ganin haka yasa shi cewa "am sorry gudun yin laifi yasa nayi maki Magana tunda an zama d'aya" d'agowa tay tana d'an murmushi tace "ba komae na fahimta yanzu ma don gwaggo bata ganni bane da bazata bari in fito da k'aramin gyale ba" jinjina kai yay yace "to yakamata ana kiyayewar" tace "in sha Allah dama don naga nan zan zo ne kuma inata sauri don kar ya fita Assignment ne na kasa nike so a nuna man" kai ya d'aga alamar ya fahimta ta juya ta kalli Haisam tace don Allah ya duba mata kafin yace wani abu Abbas yace "Mom Zarah ya zaki kawo ma wanda computer kawae ya sani Assignment d'in ku yan Asibiti" tana dariya tace ai tasan zai iya Abbas d'in yace in yayi browsing ko tace ko bai yi ba yace ta kawo ya ga Assignment d'in ta mik'e ta kai mashi ya amsa yana dubawa yana dariya yace wannan nashi ne bana Zakee ba ita dae dariya kawae take can ta mik'e tace bari ta kawo mashi lemu to yaji dad'in yi mata yace yauwa kaman tasan yana buk'ata H,zakee bai iya tarbar bak'o ba ta mik'e tana dariya ta nufi fridge d'in idon Haisam a kanta Abbas na d'an satar kallonshi yana guntse dariya slowly ya maida idon kan Abbas suka had'a ido ganin dariyar da yake yasa shi d'an ta6e baki ya maida idon shi kan Tv, bayan ta d'aukko lemun da glass cup ta tsiyaya ta ba Abbas ya amsa had'i da yi mata godiya daga inda take ta kalli Haisam tace zai sha shiru bai ce komai ba sai bin ta da ido da yake Abbas ne yace ta kai mashi kawai irinsu ba'a jiran sai sun yi magana tana dariya ta wuce saida ta janyo c-table ta aje a gabanshi sannan ta d'aura lemun ta juya ta je ta d'aukko wani cup d'in ta dawo ta duk'a tana tsiyaya mashi yau ma dae kaman rannan idonshi suka sauka akan boobs d'inta saidae yau sam ya kasa kauda idon har ta d'ago don ta mik'a mashi bai sani ba ta kama shi farko bata fahimci inda yake kallon ba har saida ta sadda kanta taga saman boobs d'in ya fito sosae duk sai taji wani iri ta mik'e tsaye hakan ya maido shi cikin hankalin shi ya d'aga ido ya kalleta tay mashi nuni da lemun da hannu ya d'an jinjina kai had'i da furta thanks jiki a mace ta koma inda ta taso ta zauna duk sai bata ji dad'i ba tasan da tasa babban mayafi ta rufe jikinta ko hijab da hakan bata faru ba, bayan Abbas ya gama shan lemun yace tazo taga yadda Assignment d'in yake saida ta gyara gyalenta sosae sannan ta nufi inda yake ta zauna akan d'ayar armchair d'in ya d'aura book d'in akan hannun kujerar ya fara nuna mata ba'a dau wani lokaci mai tsawo ba ta gane sosae tay mashi godiya had'i da mik'ewa tay masu sallama ta tafi, tana fita Abbas ya kalli Haisam yace "mi zai hana kaje da Mom Zarah kawai ma?" Kallo kawae Haisam d'in ya bi shi da shi Abbas yaci gaba "nasan bazata k'i zuwa ba kawae ka fad'i mata zata raka ka dinner party sai ka bata rigar nasan dad'i ma zata ji kuma hakan yafi da a maida masu rigan" shiru yay da alama nazari yake. Washe gari Juma'a bayan ya d'aukko ta daga school lokacin da suka k'araso kopar gidan kafin ta fita yay mata zancen Dinner d'in yace in ba damuwa yana so ta raka shi tace to yace amman ta fara tambaya nan ma to d'in tace ya kai hannu baya ya d'aukko jakkar da rigar take ya bata yace wannan zata saka amman ta fara dubawa in bazata yi ba sai a canzo before time d'in, bayan ta amshi jakar ta kai hannu ta fiddo rigar wadda doguwar riga ce Red colour mai bud'ewa daga k'asa hannun Net gareta d'an k'arami haka ma k'asan rigar inda ya bude hawa biyu ne yadin rigar da kuma irin net din hannun sai wuyan ta ma wani irin design akai mashi ba k'arya dae rigar ta had'u iya had'uwa Fatuu na ganinta ta saki k'ayataccen murmushi don harma ta hango ta cikinta, bayan ta gama dubawa ta kalli Haisam tace lafiya lou zata yi shiru ya d'anyi yana kallon ta yace amman kaman zatai tighting nata yaga tayi k'arama tace mashi a'a lafiya lou ai roba ce zatayi ya k'ara cewa tsawon ma kaman yayi mata yawa shima tace ai dogon takalma zata sa lafiya lou duk da haka saida yace in ta shiga ta gwada in bata yi ba ta kira shi sai a canzo tace to daga haka ta fita, tana shiga gidan cike da zumudi ta wuce d'akinta dama tasan gwaggo