Showing 417001 words to 420000 words out of 512766 words
Chapter 140 - Asanadin Makwabtaka Book 3 Hausa Novel Complete
Unknown
27 Dec 2024
1669
lokacin ya bud'e baki yace mata ta barshi bai jin k'ishi ya mik'a mata jakar hannun shi ta amsa tare da bud'ewa, tsadaddun kayan zak'i ne a ciki su biscuits, chocolate, Sweet da dai sauran su a ido kawai mutum ya gansu sai ya had'iyi miyau tun ma kafin yaci, d'agowa tay tana murmushi ta furta mashi "Thank you Honey, I really appreciate" wani kalar kallo yay mata tayi yar dariya don tasan dalilin kallon yace ba haka zata rink'a mashi godiya ba ita kuma kunya take ji, da k'yar ta kai bakinta tay pecking gefen fuskar shi ta d'ago tana murmushi shima shi yake yi, shiru ta d'an yi tana kallon shi slowly yace mata da wani abu ne ta d'aga mashi kai, Maganar Mota da Aunty tayi mata tay mashi, farko shiru ya d'an yi kafin ya tambayi Motar na gidansu ne tace mashi eh, ce mata yay ita Aunty d'in nata bata amfani da ita ne tace mashi eh tunda ai ba tata bace, hannu ya kai ya d'an shafi beard d'in shi tare da shigar da lip d'in shi na k'asa bayan ya sake shi yace mata ta kirata tace mata ta d'auka in tana so, waro ido tay tace yana nufin ta zama tata yace eh ita in suka koma Nigeria d'in zai siya mata wadda zata rink'a amfani da ita a can, wani irin farinciki ne ya lullubeta har fuskarta ta bayyana bata san lokacin da ta kai hannu ta tallabo fuskar shi ba tana washe baki ta furta "Thank you Honey, Allah ya kara Arzuki mai Amfani, I love you more than words can say" tana gama fad'in hakan ta kai bakinta saitin nashi ta manna mashi kiss tana d'agowa suka had'a ido kawai sai ta fad'a jikinshi tana dariya, shima yar dariyar yay don yanzu bai ma sanin yana yin ta, sosae yaji dad'in hakan da tayi mashi don bata cika yi mashi ba Saboda kunya saidai shi yayi mata da wuya ta fara mashi abu irin hakan, abunda bai sani ba shine tsoron ta tak'alo ma kanta take don yawanci daga hakan zancen yake sauyawa, kiran sunanta yay ta amsa ba tare data d'ago ba yace ta d'ago ta kalleshi, d'agowar tay tana murmushi ya bita da wani kallo can sai ji tayi ya mik'e da ita anan aka bar jakar tsarabar.
Bayan sallar isha ta kira Aunty Mareeya lokacin data sanar mata zancen an bata Motar salati ta saka tace "Fauzy badai nuna mashi kikai a bani ba?" Da sauri tace mata a'a wllh ta kwashe yadda sukai ta fad'i mata, wata shewar farinciki Aunty tay tace "Sai surukina mak'erin rocket wato da alama ya fahimci ba K'aramin k'ok'ari nayi mashi ba wurin gyare ki wannan ina jin tukuici ne aka bani" dariya Fauzy tayi, godiya ta shiga yi cike da Farinciki ta tambayi yana nan tace mata a'a yaje salla amman tasan bada dad'ewa ba zai dawo tace Shikenan in ya dawo zata kira tayi godiya amman kafin nan don Allah ta fara yi mashi godiyar yadda ya kamata Fauzy na murmushi cike da Kunya tace ai tayi wannan, yar shewa Aunty tayi tace yauwa ko ita fa haka yakamata itama ta kasance da zafinta ita dai Fauzyn murmushi kawae tayi, suna cikin yin wayar ya shigo Fauzy ta nufe shi tana zuwa gabanshi ya kai hannu ya rungumota jikinshi tace mata gashi ya dawo kafin ta kanga mashi wayar a kunne k'asa da murya tace Auntynta ce, sosae Aunty tayi mashi godiya ya nuna mata ba komai. Satin su Fauzy biyu anan suka tafi Honeymoon wasu kasashen, daga cikin k'asashen da zasu je akwae, France, Germany, italy sai US kaman yadda Fauzy ta bukaci su kai ma su Fatuu ziyara sai Saudia da zasu je suyi umra daganan zasu dawo England. Bayan zuwan su Haisam Us yaso su d'an zaga wasu k'asashen tare da Fatuu suma matsayin Honeymoon da basu je ba to saidai Saboda aikin shi don yan tsakankanin nan yaje Nigeria sosae hakan yasa ya yanke bari sai bayan bikin su Nameer sai ya d'auki hutu suje duk da haka ya zagaya da ita wurare sosae a nan inda yake wato California daga baya kuma suka je wasu states na K'asar cikin wanda suka je akwai, Texas, New York, Florida, Washington sai Massachusetts.
98
~_*✊💋BOSS LADIES WRITERS💋✊*_~
............Wata d'aya da rabi da zuwan Fatuu Us wata ranar Lahadi ta tashi da wani irin ciwon kai har da yar juwa take ji ranar dama Haisam a d'akinta yake su twins kuma na wurin Fanan dama haka suke yi in yana d'akin Fanan to a d'akin Fatuu zasu kwana haka in yana d'akin Fatuu to a wurin Fanan zasu kwana duk da suna da Nursery wato d'akin su wanda aka k'awata shi da abubuwan da suka danganci yara amman basu kwana a ciki, ganin yanayinta yasa yace mata su tafi Hospital amman sai tace mashi tana ganin basai sun je ba tunda ciwon ba wani tsanani yayi ba dama kuma lafiya lou ta kwanta tana ganin in tasha magani zata warke k'ilan harda gajiyar zirga zirgar da suka yi ne ya nuna gamsuwa da Maganar ta, ganin basu kaiga yin Breakfast ba yasa ta bari in taci Abinci sai tasha maganin dama suna dasu a first aid kit d'in su, Saboda yanayin da take ciki yasa bata samu zuwa Kitchen ba don had'a breakfast tare da mai aikin su wadda take baturiya, dama mafi yawancin lokutta tare suke aikin Fanan ma wani lokacin takan shiga saidai ba kowane lokaci ba Saboda aiki da take zuwa, a daddafe tayi wanka ta shirya cikin k'ananun kaya riga da skirt bayan an gama shirya masu table aka sanar dasu, gaba ɗayansu kowa yayi wanka suna sanye da k'ananun kaya lokacin da suka zauna zaman yin Breakfast d'in har su twins ma an masu gayu in ka gansu a lokacin sai kayi tunanin sunyi shekara ɗaya Koma sun fi don gaba d'aya sun yi wani irin girma sunyi 6ul6ul dasu ga bak'ar sumar su a nad'e gwanin burgewa haka idanuwansu farare tass dasu lips ɗinsu ma sun k'ara cizawa ta bangaren fata kuwa tamkar ka ta6a jini ya zubo har wani sheƙi take don mayukan fata masu tsadar gaske ake masu amfani dasu haka na gashin kan su ma, Bayan sun gaisa da juna Fanan ta kalli Little Grandpa dake hannunta da turanci tace mashi "Say Hello to Mom" kallon Fatuu yay ganin tana mashi murmushi yasa shima yay mata Fanan ta k'ara ce mashi yace mata hello ya d'aga hannu cikin Maganar shi da bata fita yace mata hello d'in itama Fatun ta d'ago mashi, kallon Abie dake hannun Haisam tayi tace mashi shima yace mata Hello ɗin yay shiru yanata kallonta ta sake maimaita mashi still baida niyyar cewa hakan yasa Fanan tace da alama shi kalar Dad d'in shi ne don tana lura bai cika yin magana ba kamar grandpa duk sukai murmushi ƙarshe saidai Haisam ya kamo hannun shi ya d'aga ma Fatun itama ta d'ago mashi sai lokacin Abie ɗin yay kaman zai yi murmushi, bayan sunyi bismilla a nutse suka fara cin Abincin baka jin komai sai k'arar cokulla Haisam na ci yana ba Abie haka Fanan ma tana ba grandpa sosae yaran suke ci, tun bayan da Fatuu ta fara ci taji kaman zuciyar ta na tashi haka dai ta daure tana cigaba, basu dad'e sosae da fara ci ba da sauri ta aje fork d'in hannunta ta dafe k'irji jin kaman amai na taho mata, Fanan ce ta fara lura ta kalleta tana tambayar ta lafiya hakan yasa Haisam kallonta shima yana niyyar yin Magana suka ga ta tashi da sauri ta nufi hanyar corridor da zai kai ta inda Bedrooms d'in su suke saidai ko kafin ta shiga corridor d'in Aman ya zubo nan ta duk'a ta shiga kwarara shi, har Kusan rigen mik'ewa ake tsakanin su suna rungume dasu twins suka nufeta, sannu gaba d'aya suka shiga yi mata Fanan ta dafata grandpa na ganin halin da Fatuu take ciki ya fashe da kuka ganin yana kuka yasa Abie shima ya saka kukan, kallon Haisam Fanan tayi da alamun damuwa akan fuskarta ta tambaye shi dama bata lafiya ne ya fad'i mata yadda sukai da ita da safen nan sam bata kawo komai a ranta ba tace mashi gaskiya yakamata su tafi Hospital a duba ta sosae da sauri yace Ok don shima halin da take cikin ya d'aga mashi hankali, saida ta gama sannan Fanan ta taimaka mata ta mik'e ta nufi hanyar Bedroom da ita don ta shirya su tafi Asibiti Haisam yabi bayan su yana ruk'e da su twins da ya rarrashesu sun daina yin kukan, ba tare da 6ata lokaci ba suka fito don tafiya Fanan tayi ma mai aikin su magana kan tazo ta gyara wurin aman kafin suka tafi, Haisam ne ke driving Fanan na front seat gefen shi tana ruƙe da su twins ita kuma Fatun an bar mata baya ita kad'ai ta zame jikinta ta kwantar da kanta, akai akai suke juyowa suna mata sannu da d'an murmushi take amsa masu tace ai taji ta samu sauk'i ma da tayi aman can tace ma Fanan ta kawo yaro d'aya ta rik'e mata harda tambayarta zata iya tace mata eh ta mik'a mata Abie, Asibitin da Fanan ke aiki suka nufa bayan sun isa ya parker Motar a inda aka tanada duk suka fito, basu wani tsaya Jira ba wurin ganin likita tunda dama nan ne asibitin da suke zuwa duk da Fatun wannan ne zuwanta na farko bayan tazo ƙasar, bayan Fanan tasa anyi mata duk wani abu da ake yi kafin ganin likita aka tura sunanta, tare gaba d'aya suka shiga wurin likitan wanda Bature ne yana ganin Fanan ya washe mata baki yana mata Welcome itama murmushi ta yi mashi ta amsa mashi ya maido idonshi kan Haisam suka gaisa haka Fatuu ma, mik'a ma Fanan hannu yay alamar ta bashi Adam dake hannunta ta mik'a mashi sai gashi bai mashi ƙyuya ba ya yarda dashi, nuna ma Haisam leather sofa dake gefe Yay alamar ya zauna itama Fatuu ya nuna mata ta gaban table d'in shi Fanan ma ta zauna akan wadda take facing ta Fatuu, Fanan ce tayi mashi bayanin abunda ke damun Fatun tace tana ganin ya kamata ai mata aune aune shiyasa suka zo ya furta Ok, maida kallon shi yay kan Fatuu yace mata sannu ta amsa kafin ya shiga yi mata tambayoyi, cikin tambayoyin ne ya tambayeta yaushe rabonta da period tace mashi bayan data haihu ya dawo tayi sau d'aya daga nan bai sake dawowa ba, tambayarta watannin su twins yay ta bashi amsa da shidda da rabi, bayan ya gama yi mata tambayoyin ne yace ma Fanan ya tura tests da za'a mata ta amsa da Ok tare da mik'ewa ta kai hannu ta kamo Fatuu tace suje, kallon Haisam tay tace mashi bari suje su dawo ya d'aga mata kai, ganin zasu fita yasa Adam dake kan cinyar Doctor fashewa da kuka yana Mik'o masu hannu, dakatawa sukai Fanan ta nuna mashi saitin Haisam tana fad'in "Look at Dad he's here" juyawa yay ya kalli saitin Haisam da take nuna mashi yana ta6e baki kamar zai cigaba da yin Kukan, juyawa sukai suka tafi bayan sunje lab ɗin ba 6ata lokaci aka d'ibi jinin Fatuu don yin gwaje gwajen, bayan an d'iba dawowa sukai Office ɗin likitan Fanan tace ma Fatuu ta zauna kan kujerar da Haisam yake ita kuma ta koma kan ta gaban table d'in Doctor suka shiga tattaunawa irin tasu ta likitoci, ba'a d'auki lokaci mai tsawo ba aka turo results d'in Doctor ya sanar dasu gashi an turo duk suka maida idanun su kanshi, duk awon da aka mata ya nuna lafiya lou sai guda d'aya na ciki da yake nuna akwai na tsawon sati shidda wato wata d'aya da rabi kenan tunda tazo K'asar ta same shi, tsananin mamaki ne ya bayyana akan fuskokin su ba kamar Fatuu don ita a tunaninta tunda bata period bazata samu ciki ba, da mamaki Fanan tace ma Doctor ɗin is he sure about what he said cike da tabbaci yace mata haka result d'in ya gwada tare da juyo mata da computer d'in don ta gani, bayan ta tabbatar da sakamakon d'agowa tay ta kalli Fatuu da tayi zuru tana kallon su kafin ta maida idonta kan Haisam da shima mamaki ya bayyana kan fuskar shi tace mashi yaji wai Zarah is pregnant ya jinjina mata kai, Doctor d'inne yace masu ana yin hakan su kwantar da hankalin su Haisam yay sigh kafin yace ma Doctor ɗin gaskiya yayi wuri da yawa ace tana da ciki at least jikinta na buk'atar Hutu sosae tunda bata dad'e da haihuwa ba gashi kuma twins, jinjina kai Doctor din yay yace hakane yanzu ya za'ayi shiru Haisam ya d'an yi yana kallon Floor da alama yana nazarin wani abu ne can ya d'ago ya kalli Doctor ɗin yace ya yake gani in a fitar dashi, nuna mashi yay akwae risk sosae fitar da ciki amman kaman nata da yake k'arami sosae ba'a ciki samun matsala ba Magani kawai za'a bata in akai sa'a zai fita ba tare da wata matsala ba in sun amince, jinjina kai Haisam yay kafin yace a bata maganin a tare Fatuu da Fanan suka kalle shi da sauri kowa da yanayin mamakin jin Maganar, da alamun damuwa Fatuu tace "A...amma Hubby kai da kan ka zaka ce a zubar da shi bacin kasan ba kyau hakan laifi ne" shiru Fanan tayi yanayin fuskarta ya sauya kaman zatai kuka a yadda take ji inama ace cikin a jikinta yake don sai taji bata son a zubar dashi ji take kamar ta rok'e su kada a zubar dashi amman tana gudun aga ta zaƙe, shima Haisam da alamun damuwa ya shiga kwatanta mata duka yaushe ta haihu gashi tasha wuya dole jikinta na buk'atar Hutu kafin ace ta sake wahalar wani cikin ga wahalar rainon su twins suma tunda ba yaye su tayi ba, haka ya dingi kwatanta mata matsalolin yace tunda k'arami ne kuma zata iya cutuwa haka su twins ma ba laifi bane in an cire, shiru tay tana d'an tunani ita kanta bata ji tana son cikin ba amman kuma sai taji bata goyon bayan a zubar dashi, gaba ɗaya idanunsu na akan Fatuu da tayi shiru ta kasa cewa komai ganin haka yasa Doctor ce masu ko suje gida suyi shawara in still suna son a fitar dashi ko Dr Fanan zata iya d'aura su kan hakan, yana yin Maganar da sauri Fanan ta kalle shi zuciyarta ta shiga harbawa don bata jin da hannunta zata taimaka ayi abortion ga wata ma balle kuma wannan, Haisam ne yace ma Doctor ɗin a bata maganin kawai ya furta Ok yana k'ok'arin tashi a ruɗe Fatuu ta kalli Haisam tare da girgiza mashi kai tace "a'a Hubby a barshi kawai kar a cire ana iya zuwa kuma a samu matsala tunda Allah ya bamu kawai mu barshi muyi fatan ya zama Alkhairi kada mu cire kuma muzo daga baya muna so Allah yak'i bamu wasu ma da yawa suna nema basu samu ba" yanayin yadda ta k'are Maganar kamar zata yi kuka, shiru Haisam d'in yay idon shi akanta wani irin tausayinta yake ji na ratsa shi dama dalilin tausayin nata yasa yace a cire ba wai don bai son cikin ba, Maganar k'arshe da Fatuu tay ita ta ƙara karya ma Fanan zuciya har bata san idanunta sun ciko da kwalla ba saidai ji tayi sun zubo da sauri ta sunkuyar da kanta ƙasa, duk yadda taso kar tayi kuka abun yaci tura, jin sheshshekarta a hankali yasa su kallonta da sauri ganin yanayinta yasa Fatuu kiran sunanta ta amsa cikin Muryar kuka ba tare da ta d'ago ba aikuwa zumbur ta mik'e ta nufeta, a gabanta ta tsaya tasa hannu tana k'ok'arin d'ago da fuskar ta, bin fuskar Fanan da tayi sharkaf da hawaye tay da d'an rud'ewa ta hau tambayar "Aunty Fanan what happened? Miya sa kike kuka don Allah?" Girgiza mata kai tayi kafin cikin kuka tace mata ba komai, shiru Fatuu tay tana yamutsa fuska itama kamar zata yi kuka ta shiga tunanin miya sa Fanan d'in kuka lokaci guda zuciyarta ta tariyo mata da Maganar da tayi, waro ido Fatuu tay tare da ɗan buɗa baki da sauri ta shiga faɗin "Aunty Fanan wllh ba dake nike ba da nayi Maganar kawai na bashi misali ne ban san abun zai ta6a maki zuciya ba don Allah kiyi haƙuri" idanunta har sun ciko da ƙwalla, girgiza mata kai tayi tace "No Zarah, baki man laifi ba ai abunda kika faɗa gaskiya ne kuma ni ai nasan ba dani kike ba Saboda ni inada yara ko?" Da sauri Fatuu ta jinjina mata kai tare da kai hannu ta fara goge mata ƙwallan Fanan ɗin na ɗan murmushi, bayan ta gama goge mata hawayen ta tambayeta itama bata son a fitar da cikin ko farko shiru Fanan ɗin tayi kafin ta ɗan jinjina mata kai alamar eh, juyawa tayi ta kalli Haisam cikin harshen turanci tace mashi Auny Fanan ma bata so don haka koda ita bata son cikin to zata haƙura ta haife shi, murmushi yay tare da ɗan lumshe ido haka ma likitan don yanzu ya fahimci komai da bai gane abunda ke faruwa ba saboda da Hausa suke Maganar sai jefi jefi suke saka turanci, kama hannunta Fanan tay ta d'an girgiza mata kai tace duk da bata ta6a haihuwa ba tasan tun daga rainon ciki akwae wahala in dai itama taji tana son a cire d'in kada Saboda ita ta canza ra'ayi Fatun tace a'a da gaske bata son a cire har cikin ranta ta amince a bar mata suyi mata Addu'a Allah yasa kada ta sha wahala kuma ta haife shi lafiya Fanan na murmushi tace in sha Allah daga yanzu ta fara mata Addu'a kan hakan har