Showing 204001 words to 207000 words out of 512766 words

Chapter 69 - Asanadin Makwabtaka Book 3 Hausa Novel Complete

Unknown   

27 Dec 2024

1652

tsoki tare da murmushi.

Washe gari Baffan su Fatun ya tafi. A cikin satin Abbas ya gama yi ma Mino cuku cukun Makaranta ya kawo mata Uniform da su School back nan yake sanar da gwaggo Makarantar da zata cigaba wadda babbar private school ce da kusan duk an santa, da alamun damuwa gwaggo tace ya zai d'auki wannan babban nauyin ga dawainiyar iyalin shi nan yake sanar mata bashi ne zai d'auki nauyin Karatun ba Haisam ne shi yace akaita can tace to ai da ko wadda bata kaita ba tunda ita mai tsada ce yana murmushi yace mata tunda shi yace kar ta damu, bayan ya tafi tasa Amadu ya kira mata Haisam d'in bayan sun gaisa tayi mashi Maganar Makarantar tace dawainiyar zata yi yawa da asaka ta wadda bata kai ta ba yace mata ba wani abu, sosae tayi mashi godiya tare da Addu'oi. Cikin sati guda Mino har ta goge komai na part d'in Fatuu tasan yadda ake amfani dashi, anan take taya ta kwana da safe sai ta koma gida don taya gwaggo aiki, cikin satin daya kama ta fara zuwa Makaranta, sosae Uniform d'in suka kar6e ta kai kace itama d'iyar Senator d'in ce, Tk ne ke kaisu gaba d'aya kuma ya d'aukko su da yake kusan lokaci guda ake tashin su, duk wanda ya gan su sai yayi Maganar Kamannin su.

Ranar Juma'a daya kama wata guda da sati d'aya da tafiyar Haisam bayan Fatuu ta dawo daga Makaranta an sauke Mino ta nufi part d'in su, Bedroom ta wuce ta aje jakarta ta nufi toilet, bayan ta fito ta fara shiryawa ta saka riga da skirt na lace da yake period take bazata je Masallaci ba kaman yadda suke tafiya tare da su Hajiya, bari tayi a gama sallar sai ta tafi part d'in Hajiyar taci Abinci don bata son taje tayi mata Maganar zuwa Masallaci, tana kishingid'e tana latsa wayarta har aka gama sallan, da yake ba wata yunwa take ji sosae ba sai can bayan an dad'e da gamawa sannan ta tashi don ta tafi, saida ta yafa d'an gyale mahad'in kayan jikinta sannan ta tafi, Tana shiga parlon Hajiya ta hango ta zaune tayi kwalliyar Juma'a daga d'ayan bangaren kuma wata ce zaune wadda Fatun bata gane ko wacece ba, tana kaiwa bakin kujerun taja ta tsaya sakamakon wadda idanun ta suka gani, Farha ce zaune tana sanye da wasu matsattsun jeans da top kanta ba kallabi kunnuwan ta sak'ale da earpiece idanuwan ta na akan wayarta dake ruk'e a hannun ta tana d'an taunar cingam sam bata ji shigowar Fatun ba, kallonta Hajiya tay fuska a sake tace mata an dawo tace eh tun d'azu ma tace to taje ta ci Abinci, suna cikin Maganar Farha ta d'ago ta kalli Hajiya ganin tana Magana yasa ta kai idon ta kan wanda take Maganar da shi suka had'a ido da Fatuu, wani mugun kallo ta jefa mata nan take Fatuu tasha jinin jikinta, maida kanta tay kan wayar har Fatuu zata juya Hajiya tace mata bata gane Farha bane, dakatawa tayi da d'an murmushin yak'e tace ta ganeta tace to basu gaisa ba, ce mata tay taga kaman bazata ji ba tunda ta saka earpiece shiyasa bata yi mata magana ba Hajiya tace ina ruwan uwar son kad'e kad'e, ce mata tayi taje sun gaisa daga baya hakan ba K'aramin dad'i yay ma Fatuu ba ta juya, ji tay kaman ta koma part d'inta kawai ba sai ta ci Abincin ba saidae ta san Hajiya dole tayi Magana, bayan ta shiga Kitchen tsaye tay gaba d'aya ta rasa mike mata dad'i don tana zargin ba hakanan Farhar tazo ba ba kamar data ganta ita kadae, ita dake dad'ewa bata zo ba kuma saidai suzo gaba d'aya, zuciyar ta ce ta raya mata k'ilan ma yanzu d'in ba ita kad'ai tazo ba sai kuma ta sake raya ai kuma da taga sauran a parlorn, yanke tafiya da Abincin part d'in su tayi ta ci acan, bayan ta zuba har saida tay d'an jimm a bakin k'opa kafin ta fito, ganin hankalin Hajiya na akan tv yasa ta bi ta kopar baya idanun Farha a kanta, bayan fitar Fatun da d'an lokaci Farha ta mik'e ta nufi Hanyar Bedroom, tana zuwa ta d'an juyo ta kalli Hajiya ganin bata ganinta ta wuce itama ta bi ta kopar bayan ta fuce,

Bayan ta koma part d'in nasu kitchen ta wuce ta zubo Abincin a plate ta dawo parlor ta d'aura akan c-table ta fara ci, bata dad'e sosae da fara ci ba taji an turo kopar parlon da sauri ta kai idonta, Farha ce ta shigo har saida gaban Fatun ya Fad'i ta dakata da cin Abincin tana kallon ta, nufo cikin falon tay tana tafiya cike da isa ta tsaya daga gaban Fatun suka fara kallon kallo ta wani kalan had'e rai can ta ja wani dogon tsoki ta nuna Fatuu da yatsa a fusace tace "You bastard! how dare u married my sister's Husband!!!" Shiru Fatuu tay tana kallonta, a hasale ta matsa ta kai duka hannuwanta jikin c-table d'in ta d'ago shi ta kifa ma Fatun shi Abincin ya 6aro a jikinta da sauri ta mik'e don yana da d'an zafi ga c-table d'in ya dakar mata gwuiwa, hannu ta kai ta maida table d'in ta d'ago tana kallon Farhar tana fitar da numfashi da sauri da sauri ita kuma Farhar sai huci take, a zafafe taci gaba "U must leave dis house tunda ba gidan uban ki bane, wllh sai kin bar shi talakan banza talakan wofi a gold digger" tsoki ta k'ara ja ta juya har tayi d'an taku ta juya tana nuna Fatun tace "in na k'ara ganin kin je d'aukar Abinci sai na saka maki poison kin mutu kuma ba abunda za'ai man na kashe Banzaaa" tana fad'in hakan ta juya ta tafi, tsaye Fatuu tay a wurin tamkar an dasa ta zuciyarta sai harbawa take da k'arfi k'afafuwanta na d'an yin rawa, ta d'auki lokaci a hana kafin jiki a mace ta zauna kan kujera, sosae Maganar Farhar ta k'arshe tay tasiri a kanta don yadda take nuna mata tsana tasan zata iya aikata mata hakan, da k'yar ta mik'e gwuiwowinta a sanyaye ta nufi Kitchen don ta d'aukko abunda zata gyara wurin, bayan ta gama gyarawa Bedroom ta shiga ta nufi bakin gado ta zauna tay tsuru, in tace taji dad'in zuwan Farha tayi k'arya don tasan yanzu kwanciyar hankalinta ya k'are ba kamar data gane dalilin zuwan nata, k'arshe dai Abincin da bata ci ba kenan. Da daddare bata je part d'in ba balle taci Abinci sai kawae ta yanke ta dafa indomie taci, bayan ta gama dafawar bedroom ta wuce da ita, sam tama kasa sakin jiki taci indomie d'in don har bakinta ba dad'i take jin shi, yar kad'an taci ta mik'e ta maida ta kitchen, komawa tay Bedroom ta haye gado ta zauna ta shiga duniyar tunani, a ranta take raya ita bata ga amfanin wannan auren ba dama su rabu kawai ta huta don ba komai a cikin shi sai tashin hankali gashi wanda take zaune don shi ya yi tafiyar shi ya barta ko damuwa bai yi da ita ba, daga tafiyar shi zuwa yanzu zata iya k'irga sau nawa suka yi waya itama ba wani Magana mai tsawo ba iyaka ya tambayi yadda take ko chat basu yi, idanunta ne suka ciko da k'walla saidai bata bari sun zubo ba don itama yanzu har ta gaji da yin kuka, tana haka Mino ta shigo ta k'ak'alo murmushi tayi mata ta nufo ta itama tana murmushin, a bakin gadon ta zauna ta gaishe da ita, bayan ta amsa tace mata gwaggo na gaishe da ita ta d'aga kai, tambayar ta tay ko bata lafiya ne ko wani abu na damunta taga kaman fuskarta ta canza tana murmushi tace mata lafiyar ta lau ta tambayi taci Abinci tace eh bata dad'e data gama ci ba, ce mata tay akwae sauran indomie data rage a Kitchen in zata ci, mik'ewa tay tace to bari ta d'aukko. Bayan sun gama shirin kwanciya Mino ta kwanta ita kuma ta d'aukko jakar ta don tayi karatun test da suke cikin yi Saboda exam d'in su ta matso, tana zaune a kan gadon tana karatun aka turo kopar ta kai idon ta da sauri don bata tsammaci wani ba a lokacin mantawa ma tayi bata kulle kopar ba, Farha ce ta shigo tana sanye da rigar bacci iya gwuiwa kanta sanye da hula, nufo cikin d'akin tay cikin d'acin rai ta tsaya bakin gadon tana masu kallon rashin Arzik'i, nuna Mino tay a wulakance tace "Who is she?" shiru Fatuu tay kaman bazata tanka mata ba sai kuma ta bata amsa da kanwarta ce, tafa hannuwa Farhar ta shiga yi da alamun mamaki tace wato har talakawan yan'uwanta ke zuwa kwakwa suma kenan" banza Fatuu tay mata tay k'wafa a fili ta furta duk zata yi maganin su, ce mata tay anan zata kwana don haka ta tasheta ta bata wuri, Fatuu dake kallon ta tace mata ai ga wuri nan sosae ba sai ta kwanta ba, yamutsa Fuska tay ta furta "God forbid! ni zan kwanta da pauper kina son ta goga man talauci ne" ta d'age ma Fatun gira tana kallon ta shek'ek'e, tasan fitina take nemanta da ita hakan yasa ta kai hannu ta fara tada Mino d'in, bayan ta farka tace mata ta saukko daga kan gadon, tambayar ta tayi lafiya tace mata eh kawai, saukkowa tayi ta tsaya sai lokacin ta lura da Farha dake mata kallon k'ask'anci, ganin yanayin fuskar ta yasa bata ce mata komai ba, wardrobe Fatuu ta bud'e ta fiddo bargo tazo ta shimfid'a ma Mino a saman Carpet ta d'aukko mata filo, bayan ta gama tace mata ta kwanta anan, da alamun rashin fahimta tace mata miya faru bazata kwanta a gadon ba kafin ta bata amsa a fusace Farha tace daga gidan uban su aka kawo shi ne, waro ido Mino tayi baki a d'an bud'e take kallonta ba tare data ce komai ba dama ita bata da rigima Fatuu ce mai rigimar yanzu kuma tayi sanyi lakwas, kwantawa Mino tayi itama Fatuun ta zauna a gefenta taci gaba da karatun, bata dad'e da zama ba taji Farhar ta watso mata zanin gadon dake shimfid'e a kan gadon da duvet harda pillows, hannu ta kai ta cire bedsheet d'in daya rufe mata fuska rai a 6ace tace mata ba gadon take so a bar mata ba kuma gashi nan an bar mata miyasa zata watso mata kaya tana yatsina tace ta d'aukko mata wasu wad'annan an goga masu talauci, sosae ran Fatuu ya 6aci bata dai ce mata komai ba kaman bazata d'aukko ba sai kuma ta mik'e taje ta fiddo wasu ta kawo mata ta aje akan gadon ganin zata juya tace mata bazata shimfid'a mata ba ko banda gadon rashin Arzik'i harda gadon rashin iya tarbar bak'o tayi, bata ce mata komai ba ta shiga shimfid'a mata, bayan ta gama ta koma ta kwashe wanda ta watso ta linke su ta kai Wardrobe, gaba d'aya Fatuu ta kasa yin karatun don tun bayan data kwanta ta fara kunna wak'ok'i gashi ta k'ure volume, k'arshe mik'ewa tay ta d'auki books da jakar tata ta fita daga d'akin ta koma parlor, bata dad'e sosae da komawa ba sai ga Mino ta fito a gigice tana kuka jikinta sharkaf da ruwa sai kerma take ta nufo cikin parlon, da sauri Fatuu ta mik'e ta tarbeta tun kafin ta tambaye ta abunda ya faru ta shaida, rai 6ace ta tambayi mi tayi mata ta watsa mata ruwa tace itama bata sani ba kawai tana cikin bacci taji ta watsa mata su da yawa, duk yadda Fatuu ta so kar tayi kuka ta kasa jurewa sosae Mino ta bata tausayi, zaunar da ita tayi kan kujera tace tana zuwa, Bedroom ta nufa saida ta tsaya a bakin k'opa ta goge Fuskar ta sosae sannan ta shiga, tsayawa tay daga bakin gado rai 6ace take kallon Farha dake latsa waya tace "mi tayi maki kika watsa mata ruwa haka!" banza ta mata sai kace bada ita take ba, k'ara maimaita tambayar Fatuu tayi saida ta mula sannan ta d'ago ido cike da isa tace snoring take mata daga haka ta maida idon kan waya, shiru Fatuu tay tana mata wani kallo jin sharrin data ja ma Mino na wai munshari take mata ita tasan bata yin shi tunda tare suke kwana, tunowa da ta baro Minon a jik'e yasa ta juya ta nufi wardrobe, kayan da zata canza ta d'aukko da su bedsheet d'in da Farha ta watso ta kinkima ta fita, bayan ta bata kayan ta canza tayi mata shimfid'a akan Carpet d'in parlon tace ta kwanta, kallon Fatun tayi ta tambaye ta wacece Farha nan ta bata labarin ta harda dalilin daya sa take mata hakan,

"to ki fad'a ma Hajiya abunda take mana" shiru Fatuu tay tana nazari can tace mata suyi hak'uri kawai yanzu in ta fad'i ma Hajiya ta d'auki mataki akanta Mamar ta itama tana iya yi mata wani abun, kamar Mino zata yi kuka tace to yanzu haka zasu cigaba da zama tana masu haka, shiru Fatuu tay gaba d'aya ta rasa mike mata dad'i can tasa Kuka bak'in cikinta wanda duk ake mata haka Saboda shi baima damu da ita ba ganin tana kukan yasa Mino d'in ma cigaba da yi, daina yin kukan Fatuu tayi tace itama ta daina komai zai wuce bada dad'ewa ba, rok'onta tayi akan Kada ta fad'i ma gwaggo tace to tace ta kwanta, zaune Fatuu tayi ta kasa cigaba da yin karatun ma idon ta akan Mino dake kwance ta lullube, wani irin tausayin ta take ji tunani take ko tace ta daina zuwa kwanan saidae tasan dole gwaggo zata tambayi dalili, haka tay zaune tsawon lokaci sai can dare ya nitsa sannan ta kwanta,

Washe gari da wuri Fatuu tace ma Mino taje gida sai ta k'ara yin baccin acan tace to baiwar Allah harda ce mata to tazo suje tare tunda ba Makaranta itama tayi baccin tace mata a'a ko taje gwaggo korota zata yi, kaman bazata tafi ba tsoronta kada ta tafi Farhar tayi ma Fatun wani abu haka dai ta tafi, bayan tafiyarta Fatuu ta kwashe kayan shimfid'ar ta maida d'aki Farha na kwance baje baje ko salla bata tashi tayi ba, dawowa parlor Fatuu tay ta zauna tama rasa mi yakamata tayi, tsawon lokaci tana anan saiga Saude tazo kawo mata breakfast, akan c-table ta d'aura suka gaisa ganin yadda Fatun tayi tsuru yasa ta zauna tana tambayar ta miya faru a sanyaye tace mata ba komai, tana shirin k'ara yi mata magana sai ga Farhar ta fito duk suka kalleta ta wurga masu wata uwar harara ta wuce, bayan ta fita da alamun mamaki Aunty Saude ta kalli Fatuu tace mata mi tazo yi nan ne taga ta fito daga Bedroom, shiru Fatuu tay ta sunkuyar da kanta nan take Aunty Saude ta gane da wani abu dama gashi ta isketa tsuru a parlor, matsa mata tayi kan ta fad'i mata Fatun ta fara fad'i mata duk abunda tayi masu da cewar da tayi zata saka mata poison a Abinci tana yi tana goge kwalla, ran Saude ne ya 6aci tace aikuwa yanzu zata je ta fad'i ma Hajiya dama ita tasan ba abun Arziki ya kawo ta ba, rik'eta Fatuu tay ta hau yi mata Magiya kan karta fad'i na Hajiya tunda tasan ba dundundun ta zo ba ta k'yaleta tayi ta gama yanzu in aka fad'i ma Hajiya tana iya cewa ta koma gida kuma Hajiya Maryam zata ga an korar mata D'iya Saboda ita koma bata yi niyyar yi mata wani abu ba hakan na iya sawa ta cutar da ita tunda dama gani take suma kamar asiri sukai ma Hajiyar, shiru Aunty Saude tayi tana nazarin Maganar, da damuwa tace to yanzu haka zata k'yaleta tay ta mata rashin mutunci, d'an murmushi mai cin rai Fatuu tay tace mata ba komai kawae dai tana son ta taimaka mata zata daina zuwa cin Abinci bata son Hajiya ta gane koda tayi mata Magana tace tana zuwa amsa ala bashshi sai ta rink'a dafawa kawai, cewa Saude tay ta bari zata rink'a kawo mata tasan yadda zatayi Hajiyar bazata tuhumi dalilin daina zuwan nata ba Fatun tace ta barshi kawae tunda akwae kayan Abincin tace amman ya za'ai ace sai ta dawo daga Makaranta sannan ta dafa kawai zata cigaba da kawo matan in yaso randa ba Makarantar sai ta dafa tayi mata godiya.

A daddafe tayi Weekend d'in nan, Ranar Monday tunda taje Makaranta Fauzy ta lura da yanayin ta tana cikin damuwa don har fad'awa fuskarta tayi, bayan anyi break ne ta tambaye ta abunda ke damunta nan ta kwashe game da abubuwan da Farha take mata ta fad'i mata, tun kafin ta gama yanayin fuskar Fauzy ya canza bayan ta gama fad'i mata rai a matuk'ar 6ace tace "inta fasa kashe ki bata haihu K'wara ba don ubanta! ke kika k'yaleta wllh" yamutsa Fuska Fatuu tay tace to ya zatayi, a hasale Fauzy tace "wane ya zaki yi, ba ita take neman ki da rigima ba, kamata zaki ki lakad'a mata shegen duka kinsan dama irin haka sai kun had'a jiki mutum yaji a jikinshi sannan yake shiga taitayin shi" sakin baki Fatuu tay tana kallonta Fauzyn tace "ko tafi k'arfin ki ne? In tafi k'arfin ki ni ki bari in zo mu had'u mu had'a mata jini da mijina wllh zaki ga ta kiyaye ki" da sauri Fatuu ta hau girgiza mata kai tace ba zasu yi haka ba a kyaleta kawai, a hasale Fauzy tace "Wato kin fi son tay ta cusa maki bak'in ciki ko har wani ciwon yazo ya kamaki ga jarabawa a gaban mu" watsa hannu Fatun tay ta yamutsa fuska kamar zatai kuka tace "Fauzy ko mi zatai man tayi ba kowa yaja

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login