Showing 498001 words to 501000 words out of 512766 words

Chapter 167 - Asanadin Makwabtaka Book 3 Hausa Novel Complete

Unknown   

27 Dec 2024

1670

masu da Addu'ar Allah ya ƙara girma da arzuki duk suka amsa da Amin, shiru falon ya ɗan yi kafin Baffan yace masu bari ya kai su bangaren shi sai su huta Haisam yace ai ba daɗewa zasu yi ba zasu koma Yola anjima zasu koma Abuja Baffan yace amman zasu kai azahar ko yana son bayan an gama sallar azahar lokacin duk yan uwanshi sun haɗu sai su gaisa dasu yace to, bangarenshi ya tafi dasu don su hutan kafin ayi sallar, bayan gama yin sallar azahar a ƙopar gida a fadar dake a cikin soro inda arɗo ke zama kafin ya rasu wadda yanzu Baffa ne ke zama don shine arɗon suka shiga harda sauran yan'uwan nashi, bayan sun gaggaisa Baffa ya gabatar masu da Na'eem, duk sun nuna farinciki kan al'amarin tare da Addu'ar Allah ya sanya alkhairi, da fulatanci Baffa yay masu bayanin lokacin da Aysha zata gama Makaranta yake son ayi auren ya kuma bada izinin a nemi auren a wurin shi mijin inna wuro kada zaryar tayi yawa, gaba ɗaya dai sun nuna hakan yayi Baban altine harda cewa ai Haisam ɗin yanzu shima na gida ne kuma ga abun alkhairi da yake ta kawo masu, bayan sun gama gaisuwar kuɗi masu yawa Na'eem ya aje masu yace suyi amfani nan fa suka shiga yin godiya Haisam ma ya ƙara aje masu wasu bandir bandir ɗin zo kaga godiya da addu'o'i, bayan sun fito bangaren su Baffa suka koma yasa Yadikko ta kaisu su gaisa dasu Yaya, cikin faram faram Yaya ta tarbesu akayi masu shimfiɗa suka zauna Yadikko taje tayo ma su Mairo Magana duk suka zo nan ɗakin aka shiga gaisawa dasu da tambayar Haisam yadda su Fatuu suke fuska a sake yake amsa masu daga baya ya gabatar masu da Na'eem, duk sun nuna farincikin su suma sunyi Addu'ar Allah ya sanya alkhairi ya kuma nuna masu, nan ma saida suka aje masu kuɗi masu yawa kafin su taso, basu daɗe ba bayan sun koma falon Yadikko sukai masu sallama suma saida suka aje masu kuɗi Baffa yace don Allah su bar shi kada hidiman tayi yawa wanda suka bada sun isa Yadikko tace mashi ko can wurin su Yaya ma saida suka bada masu yawa, duk yadda sukai dasu kan su barshi basu ɗauka ba dole sukai masu godiya, har bakin mota duk aka rakosu su suka yi bankwana dasu kafin suka tafi, a kan hanya ne Na'eem ke yabon Baffan su Fatuu yace ya burge shi wllh sosae kai kace ba mutumin ruga ba yana da natsuwa da wayewa in ba don haka ba bazai sake masu ba matsayin su na surukai Haisam yay murmushi yace haka yake ya fita daban a cikin su. Gab da sallar Magrib suka dawo Abuja sosae Na'eem yayi ma Haisam godiya da zasu rabu, saboda tafiyar da su Haisam ɗin sukai yasa wannan Weekend ɗin Fatuu ce tazo Abuja, da daddare bayan sun kwanta ne Haisam ke ce mata mi zai hana Baffansu ya baro ƙauye ya dawo ko Katsina tunda gasu Gwaggo sai ya siya mashi gida su zauna, itama Fatuu ta nuna tana son hakan tace zata tuntu6eshi kan hakan, Washe gari da safe ta kira Baffan bayan sun gaisa ne take mashi Maganar, farko shiru yayi kafin yace mata zai so hakan saidai barin ruga yanzu ba abu bane mai yuwuwa a wurinshi don arɗo ya bar mashi amanar gidan yace kada ya bari kan iyalin ya tarwatse yanzu in yace ya tafi yasan za'a iya samun 6araka kuma shi kan shi yafi sabawa da nan tunda anan ya taso yace taba Haisam haƙuri kuma tayi mashi godiya kan kudirin nashi tace to, koda ta sanar ma Haisam ɗin ya fahimci Baffan ya nuna mata bakomai, da yamma ta shirya komawa Zaria ta jirgi Esha ta saka rigimar sai ta bita Fanan ta shiga rarrashinta tace ta bari in akayi hutun School sai suje mata hutu kamar yadda suke yi sannan ta haƙura suka yi mata rakiya gaba ɗayansu harda Haisam Airport tabi charter flight zuwa Kaduna daga can driver zai wuce da ita Zaria.

Cikin sa'a Mino ta fara yin bautar ƙasarta a Asibiti, wata biyu da farawa kwatsam sai ga ciki ta samu, zo kuga farinciki a wurin Mino duk yadda take da kunya saida ta kasa 6oye murnarta haka kowa ma yayi farincikin samun cikin karma dai Fatuu sosae tayi murnar samun cikin na Mino, ta bangaren Nameer shima yayi farinciki don duk yadda yake nuna bai damu ba yana son yaga ɗanshi na cikin shi, bayan samun cikin sai kuma ta fara yin laulayi sosae ta yadda har saida ta daina zuwa Asibitin da take bautar ƙasan nata ƙarshe ma saida ta kai Nameer ya maidata wurin Mom ɗin su don bata iya cin komai duk abunda kuma ta samu ta ɗan ci sai ta amayar dashi tun lokacin ta gane ciki ba wasa bane, saida tayi wata biyu a Villa kafin ta dawo gidanta lokacin cikin ya kai wata ukku kuma ba laifi ta ɗan rage yawan laulayin amman bautar ƙasan da take yi saidai aka tsaida shi daga baya tayi, cikin na wata biyar akayi bikin Aysha da Na'eem anan Abuja, a gidansu Haisam akayi hidiman bikin don Haisam su Baffa suka amince mawa ya bada aurenta, yan Katsina da yan Adamawa duk nan suka zo ranar ɗaurin auren ya kama Juma'a kafin lokacin yin salla su Baffa suka iso, ana gama salla aka ɗaura masu auren akan sadaki naira dubu ɗari ukku sai fatan Allah ya sanya alkhairi ya basu zuri'a ɗayyiba, ana gama sallar Magrib jerin motoci suka zo ɗaukar yan kai Amarya zuwa gidanta dake a Garki, ba'a gida ɗaya zasu zauna da kishiyarta ba ita tana a gidajen manyan ma'aikatan bankin da yake aiki wato CBN, gidan da aka kai Ayshar babban Flat ne mai kyau, ba laifi anyi mata kaya daidai gwargwado wanda da yawa Haisam ne yayi mata su Fatuu ma da Kamalu dasu Gwaggo sun taka rawa wurin yin kayan ɗakin, shi kanshi angon Na'eem ya siya wasu abubuwan na gidan kafin a kawota kamar labulaye dasu carpets sannan part ɗin shi ya zuba komai, tun kafin ayi bikin Fatuu ta fahimtar da ita komai game da aure gudun kada a maimaita na Mino sai gashi a yadda ta fahimta Ayshar tasan miye auren wanda bata yi mamakin hakan ba don tafi Mino wayewar kai lokacin da aka yi mata aure, an kai amarya ɗakinta lafiya tana ta kuka aka barota sai fatan Allah ya basu lafiya.


Ana gama yin bikin Aysha su Haisam suka fara shirye shiryen komawa gidanshi na Asokoro, ƙara sawa a gyara gidan Haisam yayi duk da sabo ne ba'a ta6a shigar shi ba amman za'a ƙara ƙawata shi, Jidderh na jin zancen shirin komawar tasu ta roƙi Haisam kan ya bata kwangilar shirya gidan in an gama gyaran sai gashi ya bata aikuwa sosae taji daɗi dama yanzu ta ƙware ta fannin shirya wuri har ta buɗe Company Hajiya Maryam ma na taimaka mata wurin gudanar da kamfanin harda hannun jari ta zuba kuma da yake ita babbar yar kasuwa ce tana yo mata Order ɗin kaya daga wasu ƙasashen, kafin tayi Odar kayan gidan saida ta fara zuwa ta gano shi don bata ta6a zuwa ba ta dai san da Haisam nada gida, bayan ta gano gidan ta tuntu6i Fatuu da Fanan don taji irin kalar kayan ɗakin da suke so duk suka faɗi mata sannan ta fara ƙoƙarin yo Order ɗin kayan da taimakon Hajiya Maryam. Saida aka ɗauki wata ukku wurin ƙara gyara gidan da kuma shirya shi kafin aka gama, ranar da zasu koma ya kama Friday bayan an gama sallar Juma'a akai convoy harda President da Mom da sauran yan uwa da abokan arzuƙi aka raka su lokacin Fatuu na kan Hanyar dawowa daga Zaria, lokacin da suka iso tun daga bakin gate ɗin gidan abun kallo ya fara, dakakken electric gate ne wanda ake amfani da remote wurin buɗe shi idan kuma ba wuta akwai inda ake dannawa sannan a zuge shi saidai sai mutum ya iya sannan zai iya buɗewa haka saman katangar gidan da aka tsarata nan ma zagaye take da electric fence, daga bakin gate din akwae Security guda ukku ruƙe da bindigu, bayan an buɗe masu gate ɗin duk suka kutsa Motocin cikin harabar gidan wadda take mai girman gaske, to Salamu alaikum mun shigo daular su Fatuu, tsaye nan ina kallon ƙasan harabar gidan wadda na kasa gane glass ne a ƙasanta ko kuwa wani kalar tiles ne da ban sani ba don gaba ɗaya harabar wani irin salƙi take kai kace in Mota ta taka ƙasan zai fashe saidai abun mamaki ko gezo bata yi ba, bayan duk an parker motocin wasu a parking space ɗin gidan guda biyu dake a 6angaren hagu da dama da zasu ɗauki motoci shidda shidda wasu kuma a gaban danƙareren ginin gidan duk aka parker su, akwae shukokin fulawoyi masu ban sha'awa su kansu an tsara su ta yadda sun ƙara ƙawata farfajiyar gidan, bayan duk an firfito harabar aka fara tsayawa ana kallo kafin aka nufi shiga cikin ginin wanda yake ƙaton ginin bene ne, koda nayi arba da ƙopar shiga shiru nayi na shiga tunanin ta yadda za'a buɗeta ban gama tunanin ba naga Haisam ya nufi ƙopar a wani ɗan rami mai glass ya ɗaura saman babban yatsan shi sai gashi ta buɗe ashe ƙopar mai fingerprint sensor ce, ganin yadda ya buɗe yasa Hajiya dake bayan shi tace yanzu wannan in mutum na gaggawa sai ya tsaya yan ta6e ta6e kuma su yara in tsawon su bai kai ba taya zasu ta6a har ta buɗe duk akai murmushi Haisam ya bata amsa da ana cire fingerprint ɗin a buɗe lafiya lou ko kuma in cajin ƙopar ya ƙare Hajiyar ta jinjina kai, bayan ƙopar ta buɗe aka fara shiga ciki, wata yar hanya ce zaka fara shigowa tun anan zaka ji wani ni'imtaccen sanyi ya ratsa sassan jikin ka, saman wurin na ɗauke da wata irin babbar fitila mai sarƙoƙi da suka zubo ni dai har saida na ɗaura hannuwana a saman kai don sai naga kamar zata faɗo man, ta cikin wurin matattakalar bene take ta wani lanƙwaya daga bangon dake kallon mutum kuma nan ma wata dakakkar ƙopa ce ita Haisam ya buɗe aka bi bayan shi nima na saka kai, a wani irin haɗaɗɗan falo mai sunan falon masu arziki na tsinci kaina, gaba ɗaya na ruɗe na rasa ma ta ina zan fara, falon nada girma ba laifi gaba daya fentin cikinshi fari ne sai walwali yake haka ƙasan shi malale yake da tiles, akwae set na jajayen kujeru royal masu ratsin golden brown haka lallausan carpet ɗin dake tsakiyan kujerun shima kalar kujerun ne, komai na falon mai daukar hankali ne tun daga kan inda kayan kallo suke da sound systems haka Dining area ɗin dake a can gefe nan ma abun mutum ya tsaya kallo ne akwae dining table da kujeru suma royal kalar na falon da gani mahaɗinsu ne akwae glass door deep freezer wadda marfinta na gilas ne kana hango abubuwan dake a cikinta sannan akwae display Carbinet ta glass mai ɗauke da cups da dishes da wasu kayan ƙawa dake ta walainiya, sosae wurin ya ƙawatu harda flower vases masu ɗauke da fulawoyi masu ban sha'awa a jikin bangon wurin daga gefe ƙatuwar ƙopar shiga Kitchen take, babban Kitchen ne U-shape gaba ɗaya kayan cikinshi kalar ja da fari ne hatta cabinet ɗin sama da ƙasa katakon fentin ja da fari ne sosae Kitchen ɗin ya tsaru ya sha tsadaddun kayan amfani kama daga masu amfani da wuta zuwa wanda basu amfani da wuta a cikin shi ƙopar store take shima shaƙe yake da kayan abinci, a jikin bangon falon ba'a liƙa komai ba don irin tsarin bangon ba'a fasa shi sai daga wurin adon gidajen da aka saka kayan kallo ne aka aje manyan hotunan masu gidan dana sauran Family ɗinsu su Dad da Mom da Hajiya da dai sauran su, daga wurin bangaren cin abinci wato dining area akwae wata matattakalar benen da itama zata kai ka sama wato daga nan falon zaka iya bi ka hau sama ka sauka ta ɗayan matattakalar dake a waje ko kuma daga ta wajen ka hawo ka saukko ta cikin falon, daga bangaren dama na falon part ɗin Fanan yake sai na Fatuu na a bangaren hagu, a kowane part ɗin nasu akwae madaidaicin falo sai ɗakuna guda biyu, a falon Fanan komai na ciki blue ne kama daga lumbutsa lumbutsan kujerun ciki wadda suke na fata wato leather chairs zuwa carpet da labulaye duk suma kalar kujerun ne akwae kayan kallo da kuma kayan ƙawata falo harda wani haɗaɗdan console wato madubin falo mai hade da table ɗin shi anyi masu design masu ban sha'awa, sosae falon ya haɗu ba kamar da fentin cikinshi ya kasance fari sai ya ƙara mashi kyau sosae, a Bedroom ɗaya gadon ciki italian royal ne shima blue da Wardrobe ɗinshi bango guda sai side drawers da dressing mirror, a ɗayan bedroom ɗin shima gadon italian ne amman mara hayaniya katakon irin mai salƙi ne komai na cikin shi fari da ratsin baƙi ne, a cikin kowanne ɗaki akwae toilet kalar na zamani komai na cikinshi fari da silver ne, a cikin toilet ɗin da Royal bed yake har da laundary room wato wurin yin wanki mai ɗauke da injin wanki da kuma cabinet mai marfin glass anan tawul suke da rigunan wanka, in muka koma bangaren Hajiya Fatuu itama kamar yadda bangaren Fanan yake haka nata yake wato falo da kuma ɗakuna biyu, a falonta itama leather chairs ne maroon sai dai nata L-shape ne, tun daga kan Carpet da labulayen ɗakin suma duk marron ne akwae tabur ɗin tsakiyar falo wato center table na glass haka daga can ƙarshen kujerar akwae wani madaidaici an ɗaura ɗan madaidaicin abun saka fulawa shima kalar maroon cikinshi ɗauke da fulawoyi green da ja wanda ya ciza yay kamar maroon sai kuma farare, itama akwae kayan kallo kamar na falon Fanan, a Bedroom ɗin farko itama italian royal bed ne kalar maroon da sauran mahaɗinshi sai dayan ɗakin simple modern italian ne wato itama mara hayaniya kamar na Fanan amman nata kalar ruwan toka ne suma sai salƙi suke jikinsu nada sul6i, a kowane ɗaki akwae toilet itama komai na ciki fari ne da silver sosae aka kashe mashi kuɗi ba abunda babu na banɗakin masu kuɗi da suka amsa sunan masu kuɗi harda shower cubicle wato ke6antaccen wurin yin wanka na glass, bayan an gama da ƙasan benen sama aka hau saidai Hajiya bata hau ba tace suyo mata Vedio Haisam harda cewa bari ya ɗauketa ta watsa mashi harara, Mino ma an hanata hawa don cikinta ya tsufa ya shiga wata na takwas itama a falon ƙasa ta zauna tare da Hajiya, saman benen 6angaren Oga Haisam ne akwae ɗan babban falo mai ɗauke da kujeru leathers kalar ruwan madara suma L-shape ne haka carpet da labulayen duk ruwan madara ne akwae kayan kallo daga inda suke anyi adon gidaje an saka hotuna haka daga gefen kujerar an aje ɗan tebur na glass an ɗaura fitila mai kyau haka a tsakiya ma an aje wani tebur ɗin, akwae bedroom guda biyu a bangaren dama da hagu, a bangaren dama Bedroom ɗin Haisam yake yana ɗauke da saitin italian bed shima mara hayaniya ruwan madara a ciki akwae laundary room da kuma toilet, ɗayan ɗakin ake kusa dashi nan kuma ɗakin daya danganci aikin Haisam ne duk kayan aikin fasaha ne a ciki, daga ɗayan bangaren falon nan ma wasu ɗakunan ne ɗaya nasu Twins ne yana da ɗan girma an saka yan gadajen katako guda biyu iri ɗaya harda drawers ɗinsu sannan akwai wardrobe ɗin bango daga can gefe kuma wurin karatu ne aka ware masu akwae ɗan babban tebur da kujerunshi guda biyu sai kuma daga gefe yar kanta ce mai ɗauke da littattafai harda toilet ke akwae a cikin ɗakin, a ɗayan ɗakin kuma nan ma akwae gado kalar coffe brown da drawers ɗinshi da madubi sai wardrobe ɗin bango itama kalar coffe brown nan kuma matsayin ɗakin baƙin Haisam ne, abun saidai ace Masha Allah kawai komai yayi an narka dukiya ba kaɗan ba a wannan gida gashi akwae free internet access wato damar hawa yanar gizo da mutum ya buɗe wi-fi shikenan sai yay ta browsing da chat basai kana da Data ba, bayan an gama da ciki bayan gidan aka nufa wanda gaba ɗayan shi malale yake da grass carpet, akwae swimming pool wanda aka ƙawata tsarin shi gwanin burgewa ruwa har ta sama yake zubowa sannan ta ƙasa ma akwae wasu haɗaɗɗun kan famfuna dake zubo da wani ruwan, daga gaban shi wani wuri ne da aka zagaye da waya ciki kayan wasan yara ne kamar dai park, akwae wurin wasanni guda biyu na ƙwallon kwando wato basketball da kuma ƙwallon raga wato Volley ball sai wasu rumfuna biyu na shaƙatawa ne sai ɗayar wadda ta gini ce ita kuma anyi tane don yi ma yara lesson, daga jikin gidan ta baya akwae ƙopar fitowa sannan akwai wani ɗaki mai babbar ƙopa cikinshi ma yana da girma nan kuma Gym ne wato ɗakin motsa jiki mai ɗauke da kayan motsa jikin iri iri harda treadmill irin wanda Fatuu ta ta6a hawa ya wujijjigata har ta suma...

105



~_*✊💋BOSS LADIES WRITERS💋✊*_~



......... Alhamdulillah Allah yayi mun gama zagaya ko ina sai yaba gidan ake ana an dai kashe kuɗi, cike da tsokana Dad ɗin su Haisam wato Mr President yace mashi anya bazai sa EFCC su bincike shi ba don an kashe ma gidan kuɗi da yawa duk akai dariya Hajiya tace in an tashi bincikar tashi sai a haɗa dashi tunda ai shine ƙarfin nashi, Dad ɗin na yar dariya yace shi ai gida kawai yasan ya bashi amman ba hannunshi a wannan uban kayan daya zuba ma gidan Hajiyar tace aikuwa shike

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login