Showing 120001 words to 123000 words out of 512766 words
Chapter 41 - Asanadin Makwabtaka Book 3 Hausa Novel Complete
Unknown
27 Dec 2024
1548
ciki Amadu ya d'auki wasu ya nufi gida Haisam d'in na niyyar d'auka gwaggo tace mashi don Allah ya barshi za'a kwashe hakan yasa ya dakata, godiya ta shiga yi mashi had'i da Addu'oi a hankali yake amsawa ta d'auki wasu kayan ta juya Fatuu dake tsaye ta bita suka nufi gidan tana tafiya a hankali har ta kusa shiga ta juyo ta kalle shi suka had'a ido har lokacin yana tsaye a bakin boot d'in jiki a sanyaye ta juya ta shige, suna shiga gidan tsaf da gani ma da safen nan an share shi anyi Mopping dama Amadu baida ganda ya iya komai na cikin gida, d'aki Fatuu ta nufa gwaggo tace ta shiga parlor bari ta canza mata zanin gado tace to, bayan ta d'aukko wankakke a d'akinta ta shiga ta canza mata sannan Fatun ta koma d'akin tana shiga ta nufi gado ta hau ta kwanta, bayan gwaggo ta koma d'akinta ta kira Hajiya a waya ta sanar mata an sallamo su tay mata barka tace sai ta shigo tare da tambayar jikin Fatun suna gama wayar gwaggo ta cire kayan jikinta ta fito don yin wanka dama ita bata yi ba a Asibitin sosae taji dad'in sallamo sun da akai don komi dad'in wuri naka yafi ba kamar kuma wuri irin Asibiti da sam baida dad'in zama sai dole, tana kwance lamo can ta tuna da bata fad'i ma Fauzy an sallamo su ba kuma tasan yanzu an isa yin break hakan yasa ta kai hannu ta d'aukko wayarta dake a gabanta ta kira ta, sosae taji dad'in jin an sallame su tace in aka tashi tana nan zuwa sukai sallama, bayan ta gama wayar ta aje shiru tay tana tunanin Mijinta ta rasa gane mashi yanzu ada in tayi mashi abu ba daidai ba da ta bashi hak'uri yake hak'ura amman yanzu ta lura kaman bai hak'ura ba koda ta bashi hakurin gashi kuma ita a ganinta in ma tana da laifi ai shima yana da shi miyasa tun da abun ya faru bai sanar mata shi mijinta bane koda lokacin da suka je Asibiti ne bayan an gama dubata da suka dawo Mota ya shigo baya yana bata hak'uri har yana fadin zai gyara laifin shi ai tun lokacin ya kamata ya sanar mata, sannan ko da bai K'asar da ya turo mata kud'i har ya kirata daga baya da bata d'auka ba ai ko message ba sai ya turo mata ba yayi mata bayani haka tay ta raya abubuwa a ranta har bacci ya kwasheta, gwaggo na fitowa daga wankan ta sa yar doguwar rigar shan iska ta haye gado don tana da bashin bacci aikuwa nan da nan ya kwasheta, ba ita ta farka ba sai wurin sha biyu ta fito don d'aura girki ta lek'a d'akin Fatuu da har lokacin bacci take sakin labulan tay tana niyyar shiga kitchen ta jiyo wayarta na ringing ta koma d'aki ganin Hajiya ce yasa ta d'aga da sauri bayan ta gaishe da ita tace mata ba sai sun yi Abinci ba gashi nan Saude nayi ta kira d'azun ba'a d'aga ba tasan bai wuce bacci suke gwaggon tace eh wllh tay mata godiya bayan sun gama wayar sosae ta ji dad'in hakan a ranta dama baccin bai ishe ta ba ta koma ta kwanta cikin ranta tana jinjina kirki irin nasu shiyasa sam bata ji dad'in Al'amarin nan da ya faru ba don gaba d'ayan su sun shiga tashin hankali ba kamar Hajiya data sha kuka,
Bayan sallar Azahar Saude ta kawo Abincin lokacin Fatuu ta farka saida ta shiga d'akin tay mata ya jiki sannan ta tafi gwaggo ta zubo ma Fatuu Abincin da aka kawo wanda lafiyayyar sakwara ce miyar egusi da tasha ganyen ugu ga ganda da kuma nama sai farfesun yan ciki wanda hanta tafi yawa a ciki sai uban k'amshi ke tashi ta kai mata d'aki itama Abincin ya burgeta tun bata ci ba, saida ta wanko bakin ta sannan ta fara ci, bayan gwaggo ta zuba ma Amadu ta mik'a mashi itama ta zuba ta koma d'akin Fatun ta zauna kan Carpet tana ci suna d'an yin fira da Fatun dake zaune a bakin gado tana cin Abincin, wurin la'asar Fauzy tazo harda Abinci ta kawo masu bayan ta shiga sun gaisa da gwaggo ta aje mata basket d'in tana ta mata godiya ita kuma tana murmushi tana cewa ba komai ta fito ta nufi d'akin Fatuu lokacin tana kwance tayi wanka ta canza kaya zuwa doguwar rigar material itama Fauzy ita ce a jikinta tayi rolling veil tana rataye da side bag suna had'a ido suka sakar ma juna murmushi ta nufi gadon Fatuu ma ta tashi zaune, hayewa gadon Fauzy tay ta yadda suke facing juna tace "sannu Amaryar mu ya k'arfin jiki?" Yar harararta Fatuu tay Fauzyn tana dariya tace "ai dai ba k'arya nayi ba ko kuma wasa da gaske amaryar ce ke, kinsan kuwa a Makaranta dana fad'a cewa ke matar aure ce akaita mamaki" Fatun tace miyasa ta fad'a tace "to ai kinga dama anata gulma gashi yau baki je ba sai tambayata ake wai badai jikin naki bane yay tsanani shine nace masu miscarriage ki kai dama ke matar aure ce mijin naki ne ba zaune yake a K'asar ba yana dai zuwa, aikuwa kinga yadda akaita mamaki kuma wllh nan da nan suka yarda har wasu na cewa wai shiyasa wani lokacin kike zama hostel wani lokacin kuma kiyi day nace masu eh har na bud'e pictute d'in ki wanda kikae tare dashi na nuna masu wasu suka ce sun ta6a gani ya kawo ki wasu kuma ya zo d'aukar ki Zainab Muhammadu ma cewa tay tabbas ta ta6a ganin shi har sukai ta yaba kyawun shi ita da su Sa'adatu nan fa ta hau shela harda hawa saman Desk tana fad'in to masu gulmar Fatima Ard'o na da ciki tabbas tana da shi kuma na halal ne don da auren ta kuma gashi nan sun ja sakamakon gulmar da suke cikin ya zube sai Allah ya saka mata bak'in k'azafin da akai tay mata, sosae ta bani dariya wllh" d'an murmushi Fatuu tay ta d'an ta6e baki tace "Auran dake lilo" da sauri Fauzy tace "in sha Allahu ba wani lilon da yake komai zai daidaita mu sha biki...." Katseta Fatuu tay "har yanzu fa Fauzy fushi yake" Fauzy tace "zai yi ya gama ne amman ni na tabbatar ya riga ya gama shigowa hannu tunda abunnan ya faru kin ma tuna man ga sak'o Aunty Mareeya ta bani in kawo maki" tana kai Maganar tasa hannu ta ciro side bag d'inta ta bud'e wata kullin bak'ar leda ta fiddo bayan ta bud'e ta ciro wata yar kwalba madaidaiciya ta mik'a ma Fatun ta amsa ta fara karanta sunan maganin da bayanin yadda ake amfani dashi ba Arzik'i tasa hannu ta rufe baki Fauzy ta kyalkyace da dariya tace "Wllh nima sunan maganin ya ban dariya lokacin da zata bani sak'on fa hana ni tay in duba aikuwa ina hawa Napep na bud'e nima saida na rufe baki nace Ya Haisam ya bani ana shirya mashi makaman da zasu tarwatsa miskilancin shi" yar dariya Fatuu tay tare da d'an girgiza kai Fauzy ta shiga fiddo sauran tana mata bayani wani da Madara zata sha wani da nama haka tay ta mata bayani ita dae tayi zuru saida ta gama sannan tace "Dama sana'ar kika fara yi kinga yadda kike bayani sai kace kece mai maganin" Fauzy ta kyalkyace da dariya Fatun ta k'ara cewa "kema yakamata Fauzy ki manta da abunda ya faru ki fara saurarar samari ko Kya samu miji kema kiyi auranki, lokaci tafiya yake muna k'ara shekaru gashi mutuwa ake yakamata muyi auren ko don mu samu masu yi mana Addu'a" idanun Fauzy ne suka ciko da k'walla cikin raunanniyar murya tace "Wllh Zarah na kasa mantawa da Mujaheed duk da irin abunda yay man ba kuma wai ace in ya dawo gare ni zan iya auran shi ba wllh tllh ko da ace misali dole sai shi zan aura to saidai in mutu ban auren ba, kawae zuciyata ce sam bata man Adalci data kasa cire man shi a rai",
Fatuu tace "matsalar daga wurin ki ne Fauzy kin k'i ba wani namiji dama da zaki daure ki ba wani da yake son ki dama a hankali zaki ga kin fara cire shi a ran ki, ki daure Pls" ta kai hannu ta kama hannunta guda, d'an murmushin yak'e Fauzy tay tace "zan jaraba in sha Allahu duk da a yanzu ba wani da zan ba damar amman k'ilan ko da bikin ki kinsan ance a bikin wata wata ke samun miji" ta k'arasa tana d'an murmushi haka Fatun ma tace "wai wane biki abunda an riga da an d'aura tuni" da sauri tace "aikuwa dole in komae ya daidaita mu sha shagali sai kace wani auren mak'iya za'a yi shi lami dole musha anko mu cashe bikin d'an Senator guda" dan ta6e baki Fatun tay can tace "Don Kawu Amadu bai had'u ba dana had'a ku" yar harara Fauzy ta wurga mata "Kawu Amadun ne zaki ce bai had'u ba santalelen saurayi dashi ga tsawo gashi fari ga kyau daidai gwargwado" dariya Fatuu tay tace "ai ba wannan had'uwar nike nufi ba ta kud'i nike nufi shi baida kud'i ke kuma na fi son ki auri wanda Mujaheed zai girgiza in yaji" d'an murmushi Fauzyn tay "Allah ya za6a mana abunda yafi zama Alkhairi a gare mu" Fatuu ta amsa da Amin suka cigaba da hira har Fauzy na ce mata ta tashi ta 6oye magungunan kada gwaggo ta shigo ta gani tace to tana k'ok'arin sauka daga gadon.
Tun bayan da Haisam ya maido su G.r.a ya wuce don yin wani aiki a computer sai da akai Azahar sannan ya dawo gidan Hajiya ya kwanta bacci, saida aka fara kiran sallar la'asar sannan ya tashi yay wanka ya shirya ya wuce Masallaci, bayan ya fito daga Masallacin parlon Hajiya ya wuce lokacin da ya shiga ba kowa ya nufi ciki ya zauna kan 2 seater ya d'auki remote yana canza channel, bai dad'e da zama ba Hajiya ta fito jikinta sanye da doguwar riga da mayafinta hannunta ruke da sandar ta haka idanunta na saye cikin medical glasses d'inta hango shi da tay yasa ta nufi cikin parlon don da gidan su Fatuu ta fito zata, tana zuwa cikin parlon ya d'aga ido yana bin ta da kallo har ta zauna a kan one seater d'in dake gefen shi itama kallon shi take bayan ta zauna tace "ashe ka tashi" kai ya d'aga mata,
"ai tun d'azu nike dakon ka bansan ma ka dawo gidan ba saida Saude ta dawo daga gidan su Fateema
nike tambayarta ko taga Motar ka a parking space tace man eh" shiru kaman bazai ce komae ba sai kuma yace "ba sai ki kira ba" d'an ta6e baki tay tace ai na kira ka sau biyu ko, farko landline na kira ba'a d'aga ba na kira wayar ka itama baka d'aga ba nan nagane bacci kake" yana ta kallonta har ta gama sannan ya d'an d'age gira yace "Wani abu?" tace "kaci Abinci ne?" Kai ya girgiza mata alamar a'a, "to sai kai zaune da yunwa baka iya shiga kaman magana" tay Maganar tana d'an hararar shi d'an guntun murmushi yay "ban jin shi sosae ne" tace "uhmm kai dai ka sani wa zai zauna yay ta fama da kai kan abunda amfanin kan ka ne alhali kai ba damuwa kai da halin da mutum zai shiga ba ya mutu ko yay rai ba abunda ya dame ka" d'an murmushi yay kawae ya fahimci kan zancen ciki daya zo yay mata take Magana da alama dae abun yay mata zafi,
"Am all ears da wani abu ne?" Fuska a kwa6e tace ya ci Abinci tukun ta juya tana k'wala ma Saude kira bayan ta fito ta bata umarnin kawo mashi Abincin, akan c-table ta d'aura tray d'in kayan Abincin tana kokarin yin serving nashi ya d'aga mata hannu alamar ta bashshi ta mik'e tace aci lafiya ya jinjina mata kai, a nutse ya fara cin Abincin yana yi yana kallon channel d'in daya kamo Hajiya ma idonta na akan Tv d'in tana kallon American film d'in da ake yi tana yi tana d'age kai had'i da yamutsa fuska wani lokacin har hannu take d'an d'agawa in anyi abun tashin hankali, bai d'auki lokaci mai tsawo ba ya gama ya yago tissue yana goge baki, kallon Hajiya yay bayan ya gama yace mata "am done" ta maido idonta kan shi saida ta gyara zama ta fara magana "dama game da Fateema ne tunda an sallamo ta ina son in ji miye matsayin ta tunda bai yuwuwa a barta tay ta zama da aure a kanta ba kamar yanzu da tasan da shi" shiru yay yana kallon gaban shi har saida tace mashi kar ya 6ata mata lokaci ya bud'e baki yay mata magana don fita take son yi, sigh yay ba tare da ya kalleta ba yace "I will divorce her" wani kallo Hajiya ta bishi da shi jin bata ce komae ba yasa ya juya ya kalleta ganin kallon da take mashi yace "dama haka aka tsara ai ba Abbas ya fad'a maki ba?" a k'ufule tace "eh ya fad'a man hakan aka tsara amman bai ce acikin tsarin anyi da kai zaka rabata da budurcin ta ba" yana jin haka ya juyar da fuskar shi daga barin kallon ta taci gaba "Yanzu kai irin Adalcin ka kenan? Sai da ka raba yarinya da pride d'inta sannan zaka ce ka saketa wato k'aramar bazawara kake son mayar da ita kenan, idan k'anwar ka ce zaka so ai mata haka?" Shiru bai ce komai ba bai kuma kalleta ba a fad'ace tace "ba tambayar ka nike ba Haisam! idan Jidderh ce Fateema zaka so ai mata haka?" Sai lokacin ya d'an juyo slowly ya furta "am sorry for dat" daga haka yay shiru itama bata k'ara cewa komae ba sai da aka d'an d'auki lokaci sannan ta dasa fad'in "ko kusa ban amince wai kace zaka saketa ba yanzu ta riga ta zama Matar ka dole kaci gaba da zama da ita don haka yanzu dole ta baro gidan su akawo ta part d'in ka nan zata cigaba da zama kafin muga abunda Allah zai yi sai kasan yadda in ka koma zaka sanar ma Matar ka ni kuma daga baya zan kira iyayenka su zo harda ita ta Lagos din sai in sanar masu su kuma ganta ko don Saboda halin rayuwa bai kamata ace duk basu san da Maganar ba auren ba" shiru yay can ya kalleta yace "is dat all?" Kai ta d'aga mashi ganin yana K'ok'arin mik'ewa yasa da alamun mamaki tace "au tashi za kai bazaka ce komae ba?" Dakatawa yay yace "So What do you want me to say ba kin tsara komae ba kiyi yadda yay maki" wannan karon bud'e baki tay galala tana kallon shi ganin hakan yasa shi d'an d'age gira "ba haka ya yi maki ba so just go ahead do as u wish" ta6e baki tay tana mashi wani kallo tace "to yalla6ai shikenan" mik'ewa yay ya nufi hanyar barin parlon walking majestically Hajiya ta saki baki tana bin bayan shi da kallo har ya fuce, hannu ta kai ta ruk'e ha6a a fili tace "tabbas Yau na shaida Miskili yafi mahaukaci ban haushi kaji fa yaron nan don Allah wai ni zai ma duniyanci, in da farko ya aure ta don ya taimaketa wannan na yarda don zai iya yin hakan amman na tabbatar yana son zama da Fateema shiyasa bai saketa ba kamar yadda suka tsara" ta kai Maganar tana ta6e baki had'i da yin k'wafa tana niyyar mik'ewa Saude ta kawo mata wayarta data baro d'aki tace anata kira ta amsa ta duba mai kiran kafin ta d'aga suka hau yin wayar, sun d'auki lokaci suna wayar kafin sukai sallama ganin yamma tayi sosae yasa ta yanke barin zuwa gidan su Fatun sai da daddare.............
_Littafin A Sanadin Makwabtaka part 2 Naira 300 ne za'a tura ma Mutum har part 1 ga mai so zai turo kudin ta wannan Account din, 1509618776, Zainab Bature Access Bank, za'a turo shedar biya ta wad'annan nos din 09013804524 ko 08169856268
[5/8, 19:28] +234 901 700 4868: *ASM Bk2057*
_Destiny may be delayed but cannot be changed...._
*DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI*
............. Bayan gama sallar Magrib Hajiya ta nufi gidan su Fatuu lokacin da ta zo daidai shagon Amadu ta d'an d'aga Murya tace "Ahmad ya kasuwa" jin haka yasa ya kallo wajen yana ganinta da yake akwae wuta da sauri ya fito lokacin har ta karya kwanar shiga suka had'e da fara'a ya gaishe da ita ta amsa ta k'ara ce mashi ya kasuwa yace Alhamdulillah, ganin yana k'ok'arin bin ta su shiga gidan tace ya koma wurin sana'ar shi ta gode yay mata a fito lafiya ya juya, tana shiga cikin gidan tay sallama jin ba'a amsa ba yasa ta k'arasa wurin kopar parlon ta k'ara yin wata sallamar da d'an d'aga murya lokacin gwaggo dake cikin d'aki ta ji ta amsa, tana lek'owa ganin mai yin sallamar yasa ta k'arasa fitowa da sauri ta nufeta jikinta sanye da hijab tun bayan da ta gama sallar Magrib bata Mik'e ba zaune take tana yin tasbih ta jiyo sallamar, sannu da zuwa tay mata ta gaishe da ita tana d'an murmushi Hajiyar ta amsa ta nufi cikin parlon tun ma kafin gwaggon tace mata ta shiga, bayan ta shige tabi bayanta daga d'an can gefen kujerar da Hajiya ta zauna itama ta zauna tana k'ara gaishe da ita bayan ta amsa tace "Barka an dawo" gwaggo tace "Yauwa eh wllh",
"to Allah ya kyauta gaba ya k'ara mata lafiya, ai kun auna Arziki da Allah ya tashi k'afadun ta ba tare da wata matsala ba" yadda tay Maganar fuskar ta a d'an