Showing 174001 words to 177000 words out of 512766 words

Chapter 59 - Asanadin Makwabtaka Book 3 Hausa Novel Complete

Unknown   

27 Dec 2024

1668

ganin lokaci nata tafiya don 4:30 jirgin su zai tashi yasa shi kai hannu ya d'auki wayar shi, kiran Fatun yay bayan tayi picking yace tazo yana jiranta a part d'in su a sanyaye ta amsa da to, bada jimawa ba ta turo kopar parlon ganin shi zaune yasa tayi yar sallama ya amsa idon shi a kanta har ta k'arasa shigowa ta zauna daga d'ayan 6angaren, ganin yadda ya kafeta da ido yasa ta juyar da face d'inta gefe tana haka taji yay sigh ya fara magana, ce mata yay yanzu zai tafi duk abunda take buk'ata tayi ma Abbas Magana, jin yayi shiru yasa ta d'an juyo suka had'a ido da k'yar murya na rawa tace mashi to ta maida kanta k'asa, wani irin kuka ne ke taho mata sai k'ok'arin maida shi take tana haka taji yace taje Bedroom ta d'aukko mashi trolley d'in shi ta mik'e ba tare data ce komai ba ta nufi hanyar corridor yana ta kallon ta har lokacin hannun shi na ruk'e da beard d'in nashi, janye da trolley d'in ta fito yana ganin ta ya mik'e tsaye, daga gaban shi ta tsaya ta mik'a mashi a hankali tace gashi bai amsa ba ya kafeta da ido kawae, jin yayi shiru yasa ta d'ago idanunta cike da k'walla ta kalle shi suka had'a ido da sauri ta juyar da fuskarta, k'ara ce mashi tay gashi ba tare data kalle shi ba taji yace "Won't u accompany me to the Airport?" Shiru bata bashi amsa ba don tasan tana bud'e baki zata saki kuka sai yamutsa fuska take ta gumtse baki, hannu ya kai ya kamo hannun ta ya matso da ita har lokacin Fuskar ta na gefe, kiran sunanta yay aikuwa kaman tana jira ta k'wace hannun nata ta juya da gudu ta nufi hanyar corridor, tana shiga ta nufi gado ta fad'a ta fashe da kuka mai cin rai, ta d'auki lokaci tana ta rizgar kukan, ganin bai biyo ta ba yasa ta gane ya tafi hakan ya k'ara tunzura ta, tashi tay zaune kallabin ta ya kwance fuskar ta jage jage da hawaye idanunta sun yi ja a fusace ta fara magana cikin kuka "Yanzu na tabbatar baka sona Ya Haisam baka kaunata, kawae ka amince kaci gaba da zama dani ne hakanan ba don kai rayuwar Aure dani ba Saboda ni ban kai matsayin da zan zama matar ka ba, da kana sona na tabbatar bazaka tafi yanzu ka barni ba, shiyasa ka tafi wurin matar ka da kake so ka bar ni, hada cewa duk abunda nike so in ma Ya Abbas Magana wato Saboda baka son in rink'a ma magana ko, to shikenan bazan kira ka ba kasha soyayya da matar ka lafiya zan ma fita daga rayuwar ka kwata kwata sai ka huta" tana kaiwa nan ta sake fashewa da kuka ta fad'a saman gadon, ta jima haka har idanunta sun d'an kumbura can ta mik'e ta nufi mirror ta d'auki wayarta dama da ta shigo d'aukar mashi trolley ta d'aura ta anan, call log ta shiga ta kira lambar Fauzy tana fara ringing ta d'aga tace "Amaryar mu ya kika koma gida" fashe mata da kuka Fatuu tay a rud'e Fauzy ta saki salati ta hau tambayarta lafiya cikin kuka tace "Fauzy na gaya maki ya Haisam bai sona gashi nan har ya tafi ya barni" a kid'ime ta hau tambayar ta ina ya tafi ya barta tace mata ya koma Us, cike da mamaki Fauzy ta maimaita abunda tace Aunty Mareeya dake gefen ta tana sauraron su ta kai hannu da Sauri tana fad'in ta bata wayar, bayan ta amsa ta kira sunan Fatun cikin muryar kuka ta amsa tace "naji kina cewa ya koma?" Tace "Eh Aunty Mareeya yanzun nan ya tafi kuma bansan da zai tafin ba sai jiya da daddare yake fad'i man" salati Aunty Mareeya ta rafka ta kai hannu ta ruk'e ha6arta cikin bacin rai tace "Amman wannan anyi d'an jakar uba wllh....ke yi hak'uri na zagar maki miji raina ne ya 6aci, to wai miyasa zai tafi duka sati guda da kai mashi Amarya, mi ya koma yi ne yaushe yace maki zai dawo" cikin kuka tace "nifa Aunty Mareeya ce man yay kawae zai tafi bai fad'i man ko wani dalili ne yasa zai koma d'in ba kuma bai ce man ga ranar da zai dawo ba" salati ta k'ara sakawa sai faman fad'in kai take,

"amman Zarah wani abu bai shiga tsakanin ku bane?" Ta jefa mata tambaya, ta fahimci abunda take nufi tace mata eh, da tsantsar mamaki tace "Yanzu kina nufin tsawon sati gudan da kikai kallon ki kawai yake ba abunda ya wakana" k'ara amsa mata tay da eh, cike da takaici da har muryarta ta nuna tace "Amman dai wannan anyi sak'ago wllh, sai kace ba jini a jikin shi, to ko dai bai lafiya....Amman ma ai mu shaida ne in ma bai lafiyan tsabar iskanci ne ba wani abu ba, haka suke dama irin Mutanen nan akwae ban haushin tsiya wllh..." Dakatawa tay tana numfasawa can ta d'aura "Yanzu ina magungunan da aka siyo maki kina ta amfani da su ne?" tace "a'a, tun bayan da aka kawo ni na daina sha dana ga......" Shiru tay ta kasa k'arasa Maganar Aunty Mareeya tace "Yauwa Nagode ma Allah kin yi kyaun kai gara da kika daina amfani dasu duk da haka nasan kin k'waru, don Allah kiyi hak'uri Zarah kin ji, nasan dole ki shiga wani hali komai anyi maki ne don a nema maki k'ima" amsa mata tayi da to, taci gaba "bari mu zuba mashi ido muga iya gudun ruwan shi, ki k'ara hak'uri kinji in sha Allahu zaki ci ribar hakurin da kikai, ina nan dake sai reshe ya juye da mujiya a lokacin kuma zaki murza kambun sarautar ki sai yadda kika so zaki yi, in dai bada wani kwakkwaran dalili yay maki hakan ba bi'iznillahi ta'ala shima sai ya yi kuka share share" sosae ta shiga kwantar mata da hankali har saida taji ta d'an saukko sannan su kai sallama Fauzy ma ta rarrashe ta tace mata tana nan zuwa daga baya sukai sallama, tana niyyar aje wayar taji kira ya shigo ta kai idonta taga sunan da ta sa ma Abbas ya bayyana, d'an jimm tay kaman bazata d'aga ba can ta kusa yankewa tay picking ta kara a kunne, tun kafin tace wani abu ya tambayi tana ina tace mashi tana cikin d'aki yace yana a parlor ta fito a hankali ta amsa mashi da to, gyalen ta dake saman gado ta d'auka ta yafa ta nufi k'opa, dan jimm tay a bakin k'opar a ranta ta shiga raya komi ya kawo shi can dai ta kai hannu ta bud'e kopar ta fita........



_Littafin A Sanadin Makwabtaka part 2 Naira 300 ne za'a tura ma Mutum har part 1 ga mai so zai turo kudin ta wannan Account din, 1509618776, Zainab Bature Access Bank, za'a turo shedar biya ta wad'annan nos din 09013804524 ko 08169856268
[5/8, 19:28] +234 901 700 4868: *ASM Bk2065*

_Destiny may be delayed but cannot be changed...._


*DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI*


........... Kissing d'in ta ya shiga yi deeply a nutse hannun shi duka biyun talla6e da kanta da ba kallabi gashinta dake fake yayi k'asa, Fatuu kam tuni ta k'ame ta kasa ko d'aga hannunta don abun yazo mata unexpected sai numfashin ta da ke fita rapidly kirjinta na hawa da sauka da sauri da sauri, sun d'auki lokaci a haka kafin slowly ya kwantar da ita akan kujeran tayi Flat still idanunta na a rufe, had'e fuskokin su yayi ta yadda tsinin hancin shi ya had'e da nata inhaling each other's breathe wanda gaba d'aya yake fita da k'arfi, sun d'an d'auki lokaci a haka kafin slowly ya janye fuskar ya fara Moving dinta around her neck yana inhaling scent d'in jikinta, a wannan lokacin a wata irin duniya ta daban Fatuu take jinta the world around her faded away, sai faman sakin nishi take ta kai har saida ta d'an bud'e bakinta don ji take numfashin ta na neman katsewa, wani irin salo yake mata mai rikita kwakwalwa a nutse cike da gwanancewa, suna cikin haka ya kai hannu ta k'asa a hankali ya fara tattare rigar ta, Fatuu na jin haka bugun zuciyar ta ya k'aru, dakatawa yay da shak'ar K'amshin wuyan ta da yake ya fara jawo fuskar k'asa har ta sauka kan flat tummy d'in ta daya bayyana sakamakon dama iya rigar baccin ce ta rufe shi, har saida Fatuu ta d'an gantsare lokacin da taji ya kai nan jikinta ya fara d'an rawa ta fara mommotsa k'afafun ta, bin cikin nata ya fara yi yana cigaba da shak'ar Scent d'in da jikinta ke saki giving her soft kisses at the same time, she's savoring every touch and every kiss ji take tamkar zata suk'e, cigaba da moving face d'in shi yay yana yi mata abunda yake mata, a haka har ya rage da ya k'ara janye rigar boobs d'in ta zasu bayyana a lokacin numfashin Fatuu kusan d'aukewa yay, yana k'ok'arin k'ara janye rigar hannun shi ya gogi boob d'in ta, dakatawa yay da abunda yake matan tamkar an latsa mashi pause yay d'an jimm can kuma sai ya d'ago daga jikin nata, dakatawar da yay yasa da k'yar ta d'an bud'e idanun ta da sukai mata wani irin nauyi ta hango shi zaune daga gefe kan shi a k'asa yasa hannu guda ya dafe gefen fuskar tashi, k'arasa bud'e idanun ta da tuni sun canza daga ainihin kalar su da yanayin su tayi ta bi shi da kallo har lokacin numfashin ta da d'an k'arfi yake fita, sun d'an d'auki lokaci a haka can wata zuciyar ta raya mata zaman me take ta tashi ta tafi d'aki, da k'yar ta yunk'ura ta tashi zaune ta saukko da k'afafawun ta k'asa kafin ta mik'e, ko ta kan littafin ta da laptop d'in bata bi ba ta nufi hanyar corridor tana tafiya a harhard'e gaba d'aya jikinta jin shi take kaman ba nata ba sai kace na wadda ta tashi daga ciwo sam ba k'arfi a jikin nata kwata kwata, Slowly ya d'aga idon shi da suka sauya daga yanayin su yana kallon ta har ta shige d'aki sannan ya maida kan nashi k'asa yasa dukkan hannuwan shi ya talla6e shi, tana shiga ta nufi bakin gado ta zauna dabas ta kankame jikinta da har lokacin yana d'an yin rawa, gaba d'aya ji take kamar har lokacin yana cigaba da yi mata abubuwan da suka wakana tsakanin su, gaba d'aya ya tado mata da urge d'in ta dama kuma a tsume take a yadda take ji ma sai tayi wanka, ta d'an d'auki lokaci a haka can ta kai kwance k'afafunta na a k'asa tay tsuru tana ta imagination hakan ya k'ara kashe mata jiki sosae, zuciyar ta ce ta fara raya mata anya Ya Haisam na son ta kuwa, inda yana son ta bata tunanin yadda suka kai wani mataki haka zai k'yale ta, wata zuciyar ta k'ara raya mata da bai son ta zai yi mata abubuwan da yayi mata ne sai kuma ta sake raya ai k'ilan bada niyya bane kaman yadda ya faru a G.r.a dalili ne ya sa komai ya faru to k'ilan yanzu ma haka ne tunda ita ta fad'a mashi, idanunta ne suka ciko da k'walla ita kad'ai tasan abunda take ji a jikinta can ta runtse idanun ta suka fara gangaro mata, ta d'an d'auki lokaci a haka saida taji ta d'an samu sassaucin abunda take ji a jikinta sannan ta yunk'ura ta tashi zaune sai kuma ta mik'e tana tafiya a hankali ta nufi wurin kayanta ta d'aukko hula tasa, gaban dressing mirror ta tsaya tana kallon kanta kwalla na ci gaba da zubo mata daga baya ta sa hannu ta goge ta juya ta nufi hanyar laundry, d'aure da towel ta fito ta koma wurin kayanta ta curo doguwar riga ta zumbula daga haka ta nufo gado ta kwanta ta ja duvet ta lullube har kanta. Tun bayan da ta shige yake zaune a yadda yake tsawon lokaci sai daga baya ya mik'e ya nufi hanyar fita daga cikin parlon walking slowly, not too long da fitar shi ya dawo hannun shi ruk'e da wani abu har ya zauna sai kuma ya mik'e bayan ya aje abunda ya d'aukko a kan kujerar ya nufi hanyar Dining, bottle water ya d'aukko daga cikin freezer ya dawo, zaunawa yayi ya shiga bud'e ruwan bayan ya bud'e ya aje shi akan c-table ya kai hannu gefen shi ya d'aukko abunda ya aje wanda d'an kwali ne kamar na magani ya bud'e, ciro abunda ke ciki yay ya 6allo guda d'aya ya saka cikin bakin shi ya kai hannu ya d'aukko robar ruwan, bayan ya shanye ya rufe robar ya aje ya maida abun cikin kwalin wanda kaman magani ne, bayan ya rufe kwalin ya sake mikewa ya nufi hanyar fita, bada jimawa ba ya dawo ya nufi wurin Switch ya kashe hasken Parlon ya bar na wasu k'ananun fitilu kaman yadda yake yi ya koma wurin Kujerar, Zaune yay idon shi akan Corridor kaman mai tunanin wani abu, ya d'an d'auki lokaci a haka kafin ya kwanta yau ko pillow d'in babu saidae ya tada kan shi da hannun kujera yasa tafin hannun shi d'aya ya rufe fuskar shi, ta dad'e bacci bai d'auke ta ba sai tunane tunane take tana juye juye har dare ya yi sosae tana a haka, har Addu'a tay a cikin ranta kan Allah yasa tayi baccin, sai bayan wani lokaci sannan baccin ya d'auketa cike da mafarkan abunda ya faru.

Sai da gari ya fara wayewa sannan ta farka lokacin har anyi sallar Asuba tuni, bayan tayo Alwala tazo ta kabbara salla, zaune tay da ta gama cikin ranta tana ayyana Ya Haisam bai shigo bane yin Alwala da bai tashe ta ba, haka tay ta zancen zuci ita kad'ai sai bayan wani lokaci sannan ta mik'e ta cire Hijab d'in data yi sallar ta ninke ta d'auke prayer mat duk ta maida su wurin da suke, komawa tay gado ta kwanta ta kudundune taci gaba da yin sak'e sak'e a ranta, tsawon lokaci tana a hakan bacci yak'i d'aukar ta har taji ta gaji da kwanciyar ta mik'e don ta gyara d'akin, bayan ta gama gyaran d'akin tasa turaren wuta toilet ta wuce tayo wanka, bata canza kaya ba doguwar rigar jikinta ta bari haka jikinta ma iya mai kawai ta shafa sai turare data fesa ta koma bakin gado ta zauna, hakanan rashin shigowar Haisam d'in ta tsaya mata ta raya k'ilan don abunda ya faru ne k'ilan kuma ya shigo tana bacci, gaba d'aya ta rasa mike mata dad'i har wayarta ta daukka don tayi ko chatting ne amman k'arshe sai dai ta aje ta ta haye gado tay shiru, tana kwancen taji anyi knocking kopar d'akin ta tashi zaune da alamun mamaki, jin an k'ara kwankwasawa yasa ta mik'e ta nufi kopar, tana bud'ewa taga Saude ce tayi mata murmushi itama ta d'an yi mata ta gaishe da ita, bayan ta amsa tace mata dama Breakfast ne ta kawo to bata iske kowa a parlon ba kar ta aje ta tafi kuma ba'a san ta kawo ba yasa tace bari tayi mata magana, Fatuu ta d'an yi mamakin jin tace ba kowa a parlon kenan ma baya nan godiya tay mata har Sauden zata juya ta tafi sai kuma ta dakata idon ta akan Fatun tace "amman ko baki lafiya ne?" d'an fad'uwa gaban ta yay tayi d'an murmushi tace mata a'a lafiyar ta lau, Sauden tace "amman Fateema naga idanunki sun canza kaman ma kuka kikai ko?" da sauri ta girgiza mata kai "a'a Aunty Saude" tana kai Maganar ta sunkuyar da kanta k'asa don sai taji idanunta na tara k'walla, hakan da tayi yasa Saude zargin da wani abu ta kai hannu ta dafa Shoulder d'inta tace "in wani abu ke damun ki Fateema ki fad'a man in da taimakon da zan maki, barin damuwa ba abunda yake ma mutum sai haddasa mashi ciwo" da k'yar ta maida k'wallan ta kalle ta da d'an murmushin yak'e ta girgiza mata kai tace "ba abunda ke damuna Aunty Saude kawai na tashi da ciwon kai ne" kai Sauden ta jinjina ta yarda da abunda tace ta tambayi to tasha magani tace mata eh tun jiya da daddare,

"to yanzu ai yakamata ki k'ara sha tunda ga Abinci nan na kawo ki zo ki ci sai ki sha maganin in kuma kinji bai daina ba gara kiyi magana akai ki Asibiti, kinsan yanzu haka malaria ke sa mutane suyi ta ciwon kai mai tsanani" kai ta d'aga mata tace ta zo tayi breakfast d'in, ba musu ta fito suka shigo parlon tare Sauden tace suje tay serving nata da sauri tana murmushi tace mata lafiya lau zata yi ai ba wani ciwo yake mata sosae ba tay mata godiya ita kuma tay mata Allah ya sawak'e ta tafi, zaune tay a dining d'in ta kasa yin Breakfast sai tunanin inda Haisam d'in ya tafi take wata zuciyar ta raya mata k'ilan ma ba gidan ya kwana ba k'arshe ta yanke watak'il yana G.r.a, ta d'auki lokaci a haka kafin ta fara yin Breakfast din, bata wani ci da yawa ba ta mik'e ta koma d'aki, ji tay duk zaman bai mata dad'i ta yanke tafiya part d'in Hajiya bayan ta d'aukko gyale ta yafa ta fita, tana kaiwa bakin k'opar parlon zata bud'e taga an turo ta kalli mai shigowar da sauri, Haisam ne ya shigo jikin shi sanye da k'ananun kaya da gani wanka yayi sai sakin uban k'amshi yake, suna had'a ido ta sadda kanta k'asa da sauri, k'arasa shigowa yay idon shi a kanta ya tsaya daga gefe, kirjinta ne ya fara bugu da sauri sauri da k'yar ta bud'e baki ta gaishe dashi ba tare data kalle shi ba ya amsa, shiru ba wanda

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login