Showing 252001 words to 255000 words out of 512766 words

Chapter 85 - Asanadin Makwabtaka Book 3 Hausa Novel Complete

Unknown   

27 Dec 2024

1568

ganinta ta tashi zaune sosae tana mata murmushi, a bakin gadon kusa da Jidderh ta zauna itama fuskar ta d'auke da Murmushi Fatuu ta gaishe da ita ta amsa, kallon Jidderh tayi tace "nazo ki ban aron Yayar ki" yanayin face d'inta ne ya canza tace "aro kuma Mom, mi zata maki da daddaren nan" har saida tay yar dariya jin wata tambaya ta Jidderh tace to zasu je d'akinta ta kwanta ne, da sauri tana yamutsa fuska tace "gaskiya Mom a'a bacin gashi har ta kwanta anan lafiya lou" still Murmushi take tace mata ai ba lalle taji dad'in kwanciya anan ba gadon zai iya masu kad'an shiyasa, a hak'ik'an ce tace "No mom ba wani kad'an da zai mana yana fa da d'an girma in ma yayi kad'an d'in ni zan yi shimfid'a a k'asa", d'an bud'a ido Mom d'in tayi ta hau jinjina kai Fatuu dai sai faman murmushi take, kallonta Mom d'in tayi tace mata lafiya lou taji dad'in kwanciya anan da sauri tace mata eh harda ce mata ta tabbata ta k'ara cewa eh, mik'ewa tayi tana fad'in ai tasan Jidderh bazata bari ta fad'i mata gaskiya ba Saboda ta faranta mata duk sukai yar dariya tayi masu sai da Safe ta juya, tana fita wayar Fatuu ta fara ringing Jidderh ta d'aukko mata akan bedside drawer tana kallon screen d'in ta gane Haisam ne mai kiran kallon Fatuu tay ba tare data bata ba tace "Ya Haisam ne yanzu haka shima yana iya cewa kije part d'in shi ki kwana wllh, don Allah bari in ce mashi kin yi bacci" shiru Fatun tay don tana son jin muryar mijin nata Jidderh tace "pls is just for today gobe Kya je can in ma so yake ki kwana acan d'in" kunya ce ta kama Fatuu a dabarbarce tace mata a'a wllh ba haka bane lafiya lou tace mashi tayi baccin kiran na gabda yankewa ta d'aga tun kafin yayi Magana Jidderh tace mashi tayi bacci tun d'azun yay d'an shiru kafin ya furta Ok ya katse kiran Jidderh nata Murmushin jin dad'i.

Washe gari da Asuba suka tashi don yin salla, bayan Fatuu ta yo Alwala ta d'aura doguwar rigar bacci asaman kayan Jidderh ta shimfid'a masu prayer mat suka kabbara a tare, bayan sun gama kowa ya cire Hijab d'in jikin shi ya linke Jidderh ta maida su cikin wardrobe, gaida Fatuu dake tsaye Jidderh tayi tana murmushi Fatun tay shiru itama murmushin take duk sai taji nauyin gaidatan da tayi don ta girme mata, ta fahimci dalilin k'in amsawar tata tace mata ita fa yanzu Yayar suce har Yaya Laila ma, ganin tayi tsaye yasa tace mata ta hau gadon mana su k'ara yin bacci kafin lokacin breakfast don malamin su mai masu karatun safe yayi tafiya, harda tambayar Fatuu wai ko tana jin yunwa ta had'o mata wani abun Fatun ta girgiza mata kai, suna kwanciya bada jimawa ba wayar Jidderh ta hau ringing ta kai hannu kan side drawer ta d'aukko, saida ta duba mai kiran nata kafin tay picking shiru tay tana sauraren abunda ake fad'i mata kafin ta furta "a'a" sai kuma ta k'ara cewa "Okey" daga haka ta cire wayar daga kunnanta bayan ta maida ta inda ta d'aukko ta juya ta kalli Fatuu data juya mata baya ta kira Sunanta, amsa mata tayi ta juyo tana kallonta da d'an murmushi tace "dama Ya Haisam ne wai yana main parlor yace in raka ki wurin shi" d'an jimm Fatun tay ta rasa mi zata ce Jidderh na murmushi ta tashi ta zura k'afafunta k'asa, mik'ewa tay tana kallon Fatuu ganin bata saukko ba tace mata yana jira fa, saukkowa tayi tace ma Jidderh ta bata Hijab d'in data cire tana murmushi tace sai tasa wata Hijab suje haka mana Fatun tace a'a ta bata dai, bayan ta d'aukko mata ta saka Jidderh tayi gaba tana biye da ita suka nufi k'opar fita, lokacin da suka iso cikin parlon yana zaune akan Royal sofa 2 seater dake kusa da tagwayen benayen da zasu kai ka sama ya d'aura kafa d'aya akan d'aya jikin shi sanye da farar jallabiya, basu dad'e da dawowa daga Masallaci ba suda Dad d'in su da sauran Mazan gidan kowa ya wuce d'akin shi, idon shi akan Fatuu har suka k'araso Jidderh ta zauna akan 1 seater Fatuu ma ta zauna akan d'ayar one seater d'in, gaida shi Jidderh tay ya amsa fuskar shi a sake tana murmushi tace "gata nan ko sauro d'aya ban bari ya cije ta ba in ma akwae shi" d'an murmushi yay ya furta mata thanks, gaida shi Fatuu tay ya bita da ido kawae ganin kallon da yake mata yasa taji kunya ta sadda kanta k'asa Jidderh dai sai murmushi take saki, ce mata yay taje tace zata jirata ne su koma yay mata wani kallo kafin yace zata 6ace ne, dariya tayi ta girgiza mashi kai alamar a'a ta mik'e ta nufi hanyar barin wurin, jin ta bar wurin yasa ta d'ago suka had'a ido dashi k'ara gaishe da shi tay kawae sai taga ya mik'e ya nufo wurinta, yana zuwa ya kamo hannunta ya mik'ar da ita Slowly yace suje inda ya kamata ta gaida shi, hanyar bene ya nufa da ita yana ruk'e da hannunta sai d'an waige waige take gudun kada wani ya gansu, sosae cikin ranta take jinjina tsaruwar ko ina na gidan don shima saman benen ba K'aramin had'uwa yay ba, part d'in shi ya nufa da ita bayan ya tura k'opar ta bud'e ya shige da ita, daddad'an k'amshi mai had'e da sanyin Ac ne suka tarbeta bayan sun shiga bin d'akin tay da kallo sosae ya burgeta, maido idon tay kan shi ya jawota jikinshi suka tsaya suna kallon juna da murmushi can tace mashi ina kwana Slowly ya amsa tare da d'an lumshe ido, had'e foreheads d'in su yay k'asa k'asa ya furta "I didn't sleep well last night because u weren't by myside" rufe idanunta tay tana shak'ar k'amshin shi daya cika mata hanci, ganin abun na neman yin yawa yasa ta fara k'ok'arin raba jikin su, k'in sakinta yay ya bita da kallo idanunshi a d'an lumshe har sun fara canza yanayin su tana yamutsa fuska tace "Hubby kar wani ya shigo" shiru yay yana kallonta kaman bazai tanka ba can kuma ya d'age mata gira yace "d'akin wani ne da zai shigo?" da yanayin damuwa tace "naga ai ba gidan mu bane nan d'in" d'an guntun murmushin gefe yay yace "gidan su waye?" rasa amsar da zata bashi tay sai yamutsa fuska take, sakin ta yay yace "i'm sorry ina damun ki, u can go" waro ido tay da sauri ta kama shi da d'an rawar murya tace "a'a Hubby ba haka nike nufi ba fa, kawai dai naga kaman ni matsayin bak'uwa ce ina jin kunya ne a ganni anan" shiru yay yana kallon ta kawae ta d'an jijjiga shi tace yayi Magana mana, still bai tanka mata ba sai kallonta kawae da yake shi kanshi yana mamakin kanshi yadda yake mata wanda sam ba haka ya saba yi ma Fanan ba mafi yawancin lokutta ma ita ke neman shi yanzu kuma sai abun ya juye duk in ya kasance da ita wata irin natsuwa ta daban yake samu, har idanunta sun ciko da k'walla kawae zai gani yay sun zubo mata sharr ta fad'a jikin shi tana fad'in don Allah kada yay fushi da ita sigh yay ya kai hannu ya d'agota Fuskar shi a sake yace mata waya fad'i mata zai iya hakan kawai dai bai son yana takura mata, da sauri tace "ni baka wani takura man hubby kawae ina jin kunya ne" murmushi yay yace to miye abun kunya nan fa d'akin mijinta ne dama ai anan yakamata ta zauna ba wani wuri ba, kai ta jinjina mashi ya kama hannunta suka nufi hanyar Bedroom yana fad'in har yanzu kuka bai mata wuya ko tay murmushi ta d'an fad'a jikinshi ya tallabo ta,

Bayan tayi wanka zaune tayi jikinta sanye da bathrobe tana son ta koma d'akin Jidderh amman kunya ta hanata don ta d'auki lokaci anan, bin Haisam dake gaban mirror yana gyara sumar shi jikin shi sanye da k'ananun kaya jeans da t-shirt tay, bayan ya gama nufo inda take zaune yay ya tsaya a gabanta yace tazo ya rakata sai ta sa kaya, mak'e mashi kafad'a tay tana yamutsa fuska tace Allah ita kunya take ji tun d'azu fa take nan murmushi yayi sai kuma yay moving wurin side drawer ya kai hannu ya d'aukko wayar shi dake ajiye asama, Jidderh ya kirawo tana fara yin ringing ta d'aukka don lokacin itama ta tashi daga baccin data koma ta fito wanka tana cikin shiryawa, ce mata yay ta d'aukko ma Fatuu kaya a cikin trolley d'inta tace to, bayan ya gama wayar komawa yay wurin ta ya zauna daga gefen ta ta kai kanta ta kwantar a saman shoulder d'in shi k'asa k'asa da murya yace "Yunwa ko?" girgiza mashi kai tay alamar a'a yana murmushi yace yasan zuwa yanzu dole taji yunwa, ba'a jima ba Jidderh ta kawo kayan ta tsaya a bakin k'opa tana knocking, mik'ewa yay ya nufi kopar yana bud'ewa ta sakar mashi murmushi tana sanye da riga da wando skin tight sai rigar ta saukko mata zuwa rabin cinyoyin ta, mik'a mashi kayan tayi ya amsa ya furta mata thanks har zata juya sai kuma ta dakata lokacin shima har zai koma ciki tace mashi ko ta jirata su tafi tare d'an shiru yay sai kuma yace ta zauna a parlon ta jira ta fito tana murmushi tace to ta juya ta nufi wurin kujeru, bayan ya kai mata kayan waro ido tay tana kallon su ganin skinny jeans ne da riga wanda in tasa kayan sosae suke kamata, da alamun damuwa ta kalle shi tace gaskiya bazata saka su ba yace Saboda me, nuna mashi kayan tay tace baiga wanda ta d'aukko mata bane,

"Ai weekend ne irin su ake sawa yau" ya fad'a yana murmushi k'ara waro ido tay a d'an rud'e tace "amman ni ai ba yar gidan bace bak'uwa ce kawae sai in saka wannan kayan in fita ai wllh cewa ma za'ai banda kunya" yar dariya yay jin Maganan da tayi wai ita ba yar gidan bace, tambayar ta yay to miyasa ta taho da su in bazata saka ba tace "ai dama ko zan sa zan d'aura after dress ne a sama ba hakanan ba sai dai in kasa a d'aukko man after dress d'in sai in d'aura" shiru yay yana bin ta da kallo kawae har saida ta k'ara ce mashi "ka ji hubby k'asa a d'aukko man tana nan acikin kayan" sigh yay ya tambayi ba wasu ne sai wannan da sauri tace mashi akwae mana su atampa da lace duk akwae lumshe ido yay ya d'an girgiza kai yace mata ba irin su yake nufi ba irin wanda aka d'aukko mata tace eh akwae wasu, mik'ewa yay daga zaunen da yake a gefen ta ya nufi hanyar fita daga cikin d'akin ta bi shi da kallo har ya fita sannan ta maido idon ta kan kayan ta fara imagining kanta sanye da su a fili tace "tabb wayaga mara kunya", yana fita parlor yace ma Jidderh suje ta mik'e, d'akinta suka nufa bayan sun shiga daga bakin k'opa ya tsaya yace ta d'aukko mashi trolley d'in Fatuu tace to, bayan ta d'aukko mashi ya amsa yace ta jirata anan zata dawo yanzu tace to, part d'in shi ya koma tana zaune ya shigo da akwatin ya nufi inda take, a saman gadon ya d'aura shi ya bud'e da kanshi ya hau duba mata wanda zata saka dama k'ananun kayan ba su da yawa basu fi ukku ba koda aka fiddo sauran biyun suma duk saida tayi k'orafin sun kamata yace dole ta saka d'aya ciki, k'arshe wani bakin pencil skirt da bakar riga v-neck mai dogon hannu tasa sai faman yamutsa fuska take tana fad'in ita gaskiya after dress zata saka yace da yake unguwa zata je ko, shi ya taimaka mata ta gyara fuskarta da gashinta bayan sun gama yace ta saka hula su tafi lokacin breakfast yayi kar a jira su rigima ta fara mashi tana fad'in wai ya za'ai ta fita haka don Allah dama gashi tazo d'akin shi kuma duk ansan ba anan ta sauka ba, still yay yana kallonta ya goya hannuwan shi a chest, suna haka akayi knocking k'opar har saida Fatuu ta d'an tsorata, nufar k'opar yay ya bud'e ganin Mom d'in shi yasa shi sakin k'ayataccen murmushi ya ambaci sunanta tana sanye da jar polo shirt ta mata da dogon bakin skirt kanta sanye da bakar hula abun sai dai ace Tubarkallah, k'arasa fitowa yay ya rungumota jikinshi yana gaishe da ita ta amsa tana murmushi, bayan ya saketa tace "nazo tafiya da wadda kaje ka d'aukko, in kai baka jin yunwa ita ce maka akai bata ji da zaka ruk'eta ka hana tazo tayi breakfast har kiran ka akai ta landline baka d'auka ba" tana d'an hararar shi ta k'arasa Maganar yana murmushi ya bata hak'uri yace dama yanzu zasu fito tace Ok su kad'ai ake jira, har zata juya yace bari ya kirata sai su tafi tare tace Ok, juyawa yay ya koma d'akin Fatuu dake zaune a bakin gado ta d'aga ido ta kalleshi ya nufa ta, a gabanta ya tsaya yace ta tashi ga Mom nan tazo tafiya da ita yamutsa fuska ta fara yi ya d'aure mata tashi kawae sai ta fara ta6e baki bud'a ido yay alamar mamaki sai kuma yay murmushi yace bari yay ma Mom d'in magana sai ta shigo ta tafi da ita tana jin Haka ta mik'e da sauri, zuciyar tace ta bata ta d'aukko gyale tay rolling da sauri ta juya wurin kayan ta, bayan ta d'aukko ta nad'a duk da haka bai rufeta sosae ba amman dai taji gwara hakan, tare suka fito tana biye dashi Mom d'in har ta zauna akan kujera, suna had'a ido da Fatuu ta sakar mata murmushi, wurinta ta nufa a kunyace tana zuwa ta fara k'ok'arin zama a k'asa Mom d'in ta kamo hannunta ta zaunar da ita akan kujera kusa da ita, cikin jin kunya Fatuu ta gaishe da ita ta amsa mata tayi mata ta tashi lpy tace lafiya lau, mik'ewa tay ta kamo hannun Fatun tana fad'in suje tayi breakfast Habiby ya ruk'eta kuma tasan bata rasa jin yunya gaba d'aya kunya ce ta rufe Fatun, bayan sun saukko k'asan kasa d'aga ido tay ta kalli Mutanen dake a Dining area d'in wata irin kunya ta lullube ta, Haisam ne yaja seat yace ta zauna Mom ta koma gefen Senator ta zauna bayan ta zauna shima yaja kujerar gefen ta ya zauna, da k'yar ta d'ago ta gaishe da Senator idon shi akanta yana murmushi ya amsa yace "My Daughter how was ur night, hope u slept well" kai ta d'aga mashi yace haka yake so, juyawa tay ta gaishe da Hajiya itama ta amsa tana d'an murmushi, kallon Aunty tay ta gaishe da ita tana murmushi itama ta amsa tayi mata ta tashi lpy bayan ta amsa tana niyyar gaishe da Laila ta riga gaishe da ita a kunyace itama Fatun ta maida mata gaisuwar ta amsa tana mata murmushi komai nata burgeta yake bama ita kad'ai ba kusan kowa ma, dama akwae mutanen da zaka ga suna da farinjini sosae kowa son su yake sai wad'anda ba'a rasa ba tunda ance Abincin wani dama gubar wani ne amman dai Fatuu tana burge mutane sosae, sauran yaran ma duk suka gaishe da ita harda su twins Nameer k'in gaishe da ita yayi saidae ita ta gaida shi saida ya ga dama sannan ya amsa har Senator na ce mashi shi bai gaishe da ita ba tana Yayar shi kuma ta gaishe shi sai ya mula zai amsa ya kalli Dad d'in yana murmushi Hajiya tace wannan ya k'yale su kawai sun saba Senator d'in yace oh to ya gane duk akayi murmushi, Fatuu Senator yasa tayi masu Addu'a bayan ta gama suka fara cin Abincin a nutse tun Fatuu bata saki jiki ba har sai ta washe taci gaba da cin Abincin ta.

Bayan sun gama Jidderh ta ja ta d'akinta Mom d'in Haisam tace mashi tana son zasu yi magana suka nufi cikin parlon , a saman doguwar kujera suka zauna suna kallon juna tace mashi dama Maganar dangin ita Daughter ne bata san ko anyi Magana ba yakamata suzo yace mata eh sunyi Magana da Dad jiya za'a tura Mota a d'aukko su tace hakan yayi amman a tura da wuri ba sai lokaci ya k'ure ba Saboda su kar6i lefen ta yace Ok, bayan sun gama Maganar sama ya haye ya koma part d'in shi, a parlor ya zauna ya fara k'ok'arin kiran Abbas, bayan yayi picking sun gaisa yayi mashi Maganar Alhaji Lawal kaman yadda sukai da Dad d'in shi Abbas d'in yace Ok zai kira shi da sun gama wayar sai aji in zai samu zuwa, Maganar dangin su Fatun ya k'ara yi mashi nan ma yace in suka gama zai kira gwaggo sai aji yadda za'ai Haisam d'in ya tambaye shi su yaushe zai taho da su yace yana tunanin ran Wednesday, hiran yadda abubuwa zasu kasance suka shiga yi kafin daga baya sukai sallama,

Suna gama wayar ya kira Alhaji Lawal d'in bayan sun gaisa a mutunce Abbas ya fara mashi bayani game da bikin, sosae ya nuna jin dad'in shi yace ai wannan ba wani abu bane, shi a wurin shi ma girmama shi akai dama kuma lokacin yana a Abujar, nan yake sanar ma Abbas d'in yana shirin tsayawa takarar d'an majalissar tarayya ne a zabe mai zuwa Abbas d'in yayi mashi fatan Alkhairi yace in sha Allahu yana nan zuwa daga baya sukai sallama, Gwaggo ya kira bayan ta d'aga sun gaisa yayi mata Maganar zuwa d'aukko yan Adamawan cike da Farinciki

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login