Showing 372001 words to 375000 words out of 512766 words
Chapter 125 - Asanadin Makwabtaka Book 3 Hausa Novel Complete
Unknown
27 Dec 2024
1557
kwanta bayan ta d'auka cikin girmamawa ya gaida ta tare da tambayar yadda take tace mashi Alhamdulillah kafin ta ce kiran sassafe mai tattare da abu biyu Alkhairi ko akasin haka tana fatan Alkhairin ne yasa aka kirata Dad dake dariyar Maganar tata yace eh Alkhairi ne dama zai sanar mata ne tayi Ya'ya yan samari amman d'aya a ciki kuma miji ne Daughter tayi mata tana jin haka ta fahimci zancen, cikin washe baki ta hau fad'in ma sha Allah Fateema Allah yayi an sauka kenan, tambayar lokacin da akai haihuwar tayi ya fad'i mata yace gasu ma a Asibitin ko sallamarta ba'a kai ga yi ba ta kara tambayar to ya jikinta nan ma yace lafiya lou take bari ya bata ya mik'a ma Fatun cikin murmushi ta gaishe da Hajiya tace "Fateema yau ai ni ya kamata in yi gaisuwa nida aka Haifa ma sabon miji, to barka, barkanmu da Arzik'i Fateema, sannu da k'ok'ari Allah ya k'ara maki lafiya ya raya mana ya kuma Albarkaci rayuwarsu" kaman bazata amsa ba sai kuma can k'asan mak'oshi ta amsa Kafin ta tambayi yaushe zata taho tace ai don yau ta riga tayi da ta taho amman gobe in sha Allahu tana nan tafe ai bata zauna ba wannan abun Arzik'in ya samu, bayan sun gama wayar tana niyyar mik'a ma Dad Jidderh tayi karaf ta amsa ko gaida Hajiyar bata yi ba ta hau zuzuta mata kyaun jariran da kuma girman su Hajiyar nata fad'in Ma sha Allah Tubarkallah kafin a k'agare tace mata tayo mata Vedion su yanzun nan ta gani da sauri tace to, bayan Hajiya ta gama wayar Gwaggo ta shiga kira lokacin itama bata dad'e da komawa ta kwanta ba wayar ta fara ringing koda ta d'aukko ganin mai kiran saida gabanta ya d'an fad'i, d'auka tayi da sallama Hajiya ta amsa tun kafin gwaggon ta k'ara cewa wani abu tace "to barkan mu da Arzuki Fateema dai Allah yayi ta sauka lafiya an samu yan samari" ba shiri gwaggo ta tashi zaune cikin washe baki take ta fad'in Alhamdulillah daga baya tayi Addu'ar Allah ya raya ya Albarkace su Hajiya ta amsa tace ai ita gobe in Allah ya kaimu ma zata tafi don harda maigida a ciki ta fad'i mata sunayen su Gwaggo tace ah lallai yakamata ta tafi da wuri ta tarbi sabon maigida tayi Maganar tana dariya, suna gama wayar ta fito ta nufi d'akin Mino har ta koma bacci tsabar farinciki ta tasheta ta fad'i mata zo kaga murna don wani kalan wuntsilowa tayi daga kan gado ta duk'a k'asa tayi sujjadar godiya ga Allah don kullum damuwarta itace yadda Adda Fatuu zata haihu, da gudu ta fito ta nufi d'akin Kawu Amadu shima har ya koma bacci ta fad'a d'akin tana faman kwad'a mashi kira aikuwa a fusace ya farka don tunda ta fara kiran nashi yana ji yayi shiru sai daga baya ya farka har zai rufeta da fad'a dama suna yawan haka duk aka aikota ta tashe shi ko kuma wata buk'ata tata kamar in tana son yayi mata Assignment, da sauri ta tari hanzarin shi cikin tsananin murna ta fad'i mashi Adda Fatuu ta haihu yan biyu duk maza nan take ya waro ido sai kuma ya washe baki, Bayan Hajiya ta kira gwaggo Hajiya Maryam ta shiga kira bayan ta d'aga ta gaishe da ita ta amsa kafin tace to tayi Ya'ya harda sabon maigida a ciki da rashin fahimta ta tambayi wani ya'ya ta fad'i mata itama ta nuna farincikinta ta yi Allah ya raya masu, lokacin da Haisam ya kira Fanan ya sanar mata Kusan suk'ewa tayi don dad'i tace miyasa da ana labour d'in bai kirata ba sunyi tare yace mata ya rud'e ne, sawa tayi ya maida kiran Vedio call lokacin da taga yaran sai kawai ta fashe da kukan dadi baiwar Allah bata da burin daya wuce ta haifi yaro mai kama da Haisam ashe ba itace mai rabon hakan ba ta raya a ranta saidai sosae take farinciki don tana da yak'inin yaran zasu zama tamkar nata, gaba d'aya saida su Dad sukai mata barka ta cikin wayar tana ta washe baki take amsawa, kan kace mi duk an kira yan'uwa da Abokan Arzik'i an sanar dasu game da haihuwar anata ba Fatuu suna mata barka a haka ma don Wayarta bata a hannun ta, lokacin da gwaggo ta kira Aunty Mareeya ta sanar mata Fauzy na cikin yin shirin Makaranta Aunty tazo d'akin nata cikin tsananin farinciki ta sanar mata har saida ta daka wani uban tsallan murna tana ta faman fad'in Wayyo Allah da Alhamdulillah, kiran layin Fatun suka shiga yi ba'a d'aga ba Aunty tace k'ilan bata tare da wayar ne gaba d'aya Fauzy a k'agare take da suyi magana Haisam ya fad'o mata a rai gashi kuma bata da lambar wayarta shi tunowa tayi da tana da Lambar Jidderh to itama data kira ba'a d'aga ba don ta bar wayarta a gida,, zuciyar ta ce ta bata ta kira Sameer sai ta tambaye shi lambar Haisam d'in, bayan ta kira saida ta yanke sannan ya kirata, gaida shi tayi kafin tace mashi don Allah lambar Haisam take so farko shiru ya d'an yi sai kuma taji ya tambayi mi zatai da shi a tunanin ta yasan da haihuwar tace mashi tanata kiran layin matar shi ne tayi mata barka to bai shiga shine take son ta kira shi sai ya bata, tambayarta yayi barkan mi zata ma wife en nashi nan ta gane bai san da haihuwar ba ta fad'i mashi yace bai sani ba Allah ya raya, karanto mata lambar yay tayi mashi godiya suna gama wayar ya kira Haisam d'in bayan ya d'aga sun gaisa Sameer d'in yace mashi tunda shi bai so yasan sun yi babies yaji wani wuri Haisam d'in na dariya ya bashi hak'uri yace baya tare da wayarshi ne bai dad'e da ya d'aukko ta daga gida ba ya tambayi ina yaje ya sanar mashi suna hospital ne yace Ok, tambayar lafiyar yaran da Mom d'in su yay Haisam d'in yace mashi duk suna cikin k'oshin lafiya bari ya maida Vedio call ya ga babies d'in nan ma Ok yace, bayan ya maida kiran Vedio nuna mashi yaran ya shiga yi Sameer na kallon shi yanayin fuskar shi da d'an murmushi daga baya yaba Fatuu suka gaisa yay mata barka, bayan Haisam ya amsa Sameer d'in na wani murmushin gefen baki yace Babies d'in sun bayyana he's very active shiyasa sukai Kamannin shi Haisam d'in yay murmushi kawai don su Mom na wurin gudun kada ya k'ara fad'in wata Maganar yasa shi saurin ce mashi ga su Mom yayi masu barka, suna gama yin wayar da Sameer kiran Fauzy na shigowa Haisam ne ya d'auka bayan sun gaisa tayi mashi barka sannan ta fad'i mashi ko wacece ya mik'a ma Fatuu, cikin tsananin farinciki suka yi mata barka harda Aunty suma harda Vedio call suka ga yaran lokacin da Fauzy ta gansu murna kamar kamar me, haka dai akaita yin waya dasu ta wayar Haisam d'in har su gwaggo suma ta nan suka kira, bayan kiraye kirayen wayar sun lafa Dad yace ma su Yasmeen su tashi ya tafi dasu suyi shirin School tun kafin ya rufe baki Mubeen da Mubeena suka tur6une fuska cikin shagwaba suka hau rok'on a k'yale su yau ba sai sunje ba suna Welcoming Babies d'in su Mom tace to ba Babies na nan ba ko sun dawo zasu gansu, da k'yar suka tashi zasu bi shi Jidderh ma ta mik'e zata bi su don akwae abunda take son yi a gidan kafin a sallamo Fatuu, bayan tafiyar su Mom tace bari ta kira Iya a d'aura ruwa Aunty tace a'a tana ganin ba sai anyi wannan ba don bp d'in Fatun ya d'an hau so bata buk'atar ruwan zafi sosae yanzu lafiya lou in sun koma zata iya amfani da na heater zuwa bp d'in ya daidai ta duk da haka ba ruwa masu zafi zata rink'a amfani dasu ba Mom tace Ok kafin cike da kulawa ta kalli Fatuu tace maijego mi take son a dafa mata ne Fatun tayi murmushi kawai gaba d'aya idanunsu na akanta harda Haisam wani irin son ta ne ke mashi yawa a jini jiki, Aunty ce tace a yanzu dai ai tasan zata fi buk'atar farfesu tace ma Fatun hakane ko Daughter ta d'aga mata kai still da murmushi a fuskar tata, masu aikin girkin gidan Mom ta kira ta basu umarnin kalolin farfesun da zasu yi..........
_Littafin A Sanadin Makwabtaka part 2 Naira 300 ne za'a tura ma Mutum har part 1 ga mai so zai turo kudin ta wannan Account din, 1509618776, Zainab Bature Access Bank, za'a turo shedar biya ta wad'annan nos din 09013804524 ko 08169856268
94
~_*✊💋BOSS LADIES WRITERS💋✊*_~
...........Wuraren k'arfe sha d'aya na safe aka sallami Fatuu saida Haisam yay ma su Nurse Haleema kyautar kowa dubu hamsin, a bayan Mota ta zauna ita da Aunty sai Mom ta zauna a gaba tana ruk'e da Adam Aunty kuma tana ruk'e da Aliyu, lokacin da suka iso gidan a bakin Entry Hall ya parker Motar duk suka bubbud'a kopopin suka fito, suna fitowa Iya ta fito daga cikin gidan ta nufo su cikin washe baki tana masu sannu da zuwa ta nufi Fatuu ta rungume ta tana fad'in "Barkan mu, Barkan mu yar gidan Iya, barka da Arzik'i" dariya Fatuu ke yi ta d'agota tana k'ara mata sannu da tambayar jikinta tace mata Alhamdulillah, juyawa tay kan Haisam daya zagayo hannun shi ruk'e da Jaka tayi mashi barka shima fuskar shi a sake ya amsa ta juya kan su Mom suma tana masu barkan duk suka amsa ta amshi jaririn hannun Aunty duk suka nufi shiga cikin gidan lokacin Dad ya fito cikin Fara'a yake masu sannu da zuwa shima ya amshi jaririn hannun Mom suka wuce, parlon tsaf dashi yasha gyara sai k'amshi ke tashi suka nufi part d'in su Fatuu, suna shiga cikin parlon Jidderh ta tarbesu cikin washe baki ta rungumo Fatuu tana k'ara mata sannu itama murmushi take mata, bayan sun shiga cikin parlon shima dai yasha gyara hatta labulaye an canza sai k'amshi yake tashi, ganin zasu zauna a cikin parlon yasa da sauri Jidderh tace ba anan zasu zauna ba pls su shiga ciki Mom ta tambayi Saboda mi tace Saboda Sis Fatuu ta kwanta ta huta suma babies d'in ta gyara masu gadon su a kwantar dasu suji d'umi duk sukai murmushi suka nufi cikin harda Dad da Haisam ta matsa mawa saida suka shiga, a tare duk sukai tsaye cakk bayan sun shiga suna k'are ma d'akin kallo daya canza suffa yasha decorations daya danganci jarirai irin su Baby photo frames da wall decals an mammanna su a wurare daban daban masu k'ayatarwa wasu hotunan bishiyu ne wasu flowers suna ta sakin k'yalli harda masu yin haske kala daban daban hatta gadon d'akin ma yasha gyara an shimfida sabon bedsheet milk a saman shi an watsa jajayen Flowers suma labulayen d'akin an canza su, daga jikin bangon da kan gadon yake wani Wall decal ne mai kaman d'an allo anyi mashi shape mai kyau jikin shi na d'auke da rubutu kamar haka _"Welcome to the world, little ones. May your life be filled with love, laughter and light. We love you"_ gaba d'aya yanayin d'akin yayi kaman nursery sai dai komai ya tsaru ba'a cika ba, gaban su Jidderh tazo tana murmushi tace ya suka ga decorations d'in gaba d'ayansu suka hau yabawa fuskokin su d'auke da faffad'an murmushi kowa ya hau yaba mata ana fad'in tayi k'ok'ari Dad yace Saboda wannan abun da tayi ko gaba da Dubai take son zuwa K'arin Karatu zai kai ta, jin haka da sauri ta nufo shi tay mashi side hug Saboda jaririn da yake ruk'e da shi tace "That's why I'm always proud of you lovely Dad, You're a Father like no other" fad'ad'a murmushin shi yay yayi pecking saman kanta tare da Fad'in shima yana Alfahari da ita a koda yaushe, sakin shi tay ta koma kan Haisam tana fad'in big brother ya kaga decorations d'in shima yaba mata yay ya jawota yay hugging nata, Aunty ce ta tambayi zasu iya zama a kan gadon ko su kwashe flowers d'in duk akai dariya Jidderh tace a'a a haka zasu hau su zauna Mom tace ma Fatuu ta hau suma duk suka zauna a baki, Addu'a Dad ya k'ara yi masu yayi ma Fatuu sannu Fuskar shi cike da annuri ya mik'a ma Mom shi kafin ya tafi Haisam kuma ya nufi kan bedside ya zauna, Iya dake ta faman washe baki ta mik'a ma Aunty na hannunta tana fad'in bari taje ta kwaso ruwan wanka dama tunda su Jidderh suka dawo taji an haihun ta d'aura tuni ma ya tafasa Aunty ta kar6i babyn tana fad'in anya wankan nan bata buk'atar ruwa masu zafi sosae Iya tace to lafiya lou sai a bari su sha iska sosae tunda akwae magunguna da zasu k'ara mata lafiya da ruwan nono a ciki yakamata tayi wankan dasu Auntyn tace mata to ta juya da sauri ta nufi hanyar fita, gaba d'aya Mom da Aunty da Jidderh idanun su na akan Babies suna ta kallon su suna sakin murmushin dadi yayin da Haisam da Fatuu keta kallon juna suna murmushi can Mom ta d'ago ta kalle shi tace "New Dad ya gajiyan labour" murmushi kawai yayi Aunty da itama ta d'ago tana murmushin tace "aikuwa kam ansha labour harda su Kuka" waro ido Mom tayi "kice labour d'in koke koke akai kenan",
yar dariya Aunty tay "eh to ba sosae ba ya d'an yi hawayen tsoron kada ya rasa Babyn shi" dariya Mom ta saka haka Auntyn da Jidderh ma Haisam d'in ma ya d'an fad'ad'a murmushin shi Fatuu kuwa da sauri ta sunnar da kanta tana murmushin jin kunya, kallonta Mom tayi tana fad'in ai gaskiya tayi kokari sosae wllh angode ma Allah daya sauketa lafiya ba wata matsala gaba d'aya suka jinjina kai Mom d'in ta tambayeta bata jin wani ciwo sai lokacin ta d'ago da murmushi akan Fuskar ta tace mata eh kawai jikinne take jin shi wani iri tace mata ai wannan dama dole ne tunda yara fa har biyu suka fita daga jikin nata a hankali zata ji ta koma normal ta d'aga mata kai, masu aikin Abincin gidanne mutum biyu suka shigo kowanne na sanye da apron bayan sun gaishe da su suka yi masu barka Aunty ta nuna masu bakin gado tace su zauna, bayan sun zauna aka basu jariran nan fa suka shiga yabawa fuskar kowannen su d'auke da Murmushi, tambayar su Mom tayi sun gama aikin data sasu a tare suka amsa da eh tace Ok in sun koma sai su kawo shi nan cikin girmamawa suka amsa mata da to, Iya ce ta fara shigowa da ruwan wankan ta wuce toilet, bayan ta gama ta tambayi Mom ta fara yi ma jariran ne tace a'a bari ita tayi masu ta kawo mata ruwan tace to, bayan ta kawo tace ma Aunty ga ruwan Fatuu can ta kai toilet tace to suje sai ta taimaka mata tayi wankan ta amsa da to, tambayar dami za'ai wankan tayi Aunty tace mata towel Jidderh ta mik'e da sauri tana fad'in bari ta d'aukko mata Mom ma tace ta had'o da kayan wankan babies d'in, kallon Fatuu Iya tayi tace to suje ayi wankan tace to ta fara k'ok'arin saukkowa daga saman gadon lokacin Jidderh ta kawo towel d'in k'arami da babba Iya ta amsa suka wuce toilet. Gaba d'aya idanun su harda Haisam na akan Babyn da Mom ta fara yi ma wanka sai tsanyara kuka yake Aunty na fad'in "haba grandpa yada kukan wanka kai fa babba ne" gaba d'aya suna ta dariya kawai sai ji sukai Fatuu ta saki k'ara itama daga cikin toilet d'in da sauri suka kai idanunsu kan kopar toilet d'in dake a rufe cikin d'an d'aga murya Aunty ta k'wala ma Iya kira daga ciki ta amsa tace mata Lafiya, bud'e kopar tayi ta lek'o tana yar dariya Aunty tace badai cika mata ruwan zafin akai ba ko Iya tace "Wllh Aunty basu da wani zafi daidai daidai ne tunda kince kar a cika" kai ta jinjina mata tace Ok hakan yayi kafin ta k'ara cewa asata ta zauna ruwan sosae tace to ta koma ciki, Mom dake yar dariya tace sai a k'yale grandpa yay kukan shi tunda ga maman shi can itama tana yi duk sukai dariya, mik'ewa Haisam yayi yana murmushi yace bari yaje Aunty dake kallon shi tace shima tunda Angon jegon ne ya tsaya yay wankan, yar dariya yay har hak'oran shi suka bayyana Mom tace "gaskiya kam haka yakamata tunda ya taya nak'uda wankan ma sai ayi tayi" still dariyar yake bai dai ce komai ba yay masu sallama ya tafi, bayan angama ma Fatuu tana d'aure da Towel ta fito ta yafo gyalen rigar ta a kai duk su Aunty suka kalleta suna mata sannu tana d'an murmushi ta amsa ta nufi gadon ta zauna Jidderh ta mik'e don ta d'aukko mata kayan shafa, bayan Mom ta gama yima jariran wanka Iya ta fidda ruwan ta dawo da garwashin gashin cibiya Aunty tace ai tayi zaton za'a basu magani ne kawai Iya tace gashin yafi, bayan Fatuu ta gama shafa mai tasa Jidderh ta d'aukko mata kayan da zata saka sabuwar doguwar rigar lace ce Jidderh tace bari tayi mata makeup tunda ita amaryar jego ce duk aka yi murmushi, yar light makeup tayi mata ta d'aura mata kallabi sai gata ta fito a Amaryar jego sosae tayi kyau tana ta sakin kamshi su Mom ma duk suka yaba kwalliyar lokacin Iya ta gama gashin Aunty ta fara shirya jariran, Mom da kanta ta zuba ma Fatuu Farfesun da aka kawo Kusan kala hud'u akwae na yan ciki dana kaza sai na kifi da kuma na nama mai had'e da ganda gaba d'aya sunyi gwanin kyau a