Showing 99001 words to 102000 words out of 512766 words
Chapter 34 - Asanadin Makwabtaka Book 3 Hausa Novel Complete
Unknown
27 Dec 2024
1635
yasa ya d'an d'ago don duk kunya ta rufe shi ya shiga bata hak'uri yana fadin sun yi kuskure ta ta6e baki tace su dae suka sani ita dae ai yanzu jiran Fateema take sumi sumi ya juya ya nufi hanyar fita bayan ya fito ya nufi Lab duk ran shi ba dad'i, sosae baiji dad'in yadda Al'amarin ya kasance ba kamar cikin da ya zube, lokacin da ya isa d'akin da Haisam yake a lab yana shiga suka had'a ido dashi ya jingina da bango hannun shi ruk'e da abubuwan da Dr ya kawo mashi yana ci a hankali Abbas ya shiga da yar sallama can k'asan mak'oshi ya amsa mashi ya nufi inda yake ya zauna daga bakin gadon yana kallon shi da yar damuwa yace mashi sannu kai kawai Haisam d'in ya d'aga mashi suka d'an yi shiru idon Abbas akan shi shi kuma ya maida nashi k'asa can Abbas yace "ashe haka abu ya faru ba dad'i yanzu Hajiya ta tutsiye ni tana ta fad'a" ido kawae Haisam ya bi shi dashi Abbas dake kallon shi yace "to wai ya akai hakan ta faru ba tare da ka warware mata komae ba, nasan da kayi mata bayani duk hakan bazata faru ba" still idon ya bishi dashi ba alamar zai tanka mashi wata yar dariya Abbas yay yace "look dude ba fa wata fuska da zaka man bayan ka aikata 6arna ka cuci yar mutane kaja har muma ta shafe mu" shigar da lip d'in shi na k'asa yay ya d'an ciza suka bi juna da ido Abbas nata sakin murmushin iskanci can ido a d'an lumshe slowly yace "What do u want me to say Abbas? It was intentionally or what?" Abbas dake murmushi yace "kusan hakan mana in ba da niyya ba mi zai sa ka aikata?" Still idon shi na akan shi ya d'an ta6e baki kafin yace "isn't as u think, it was mistake" Abbas yace "to ya akai har kai irin wannan kuskuren, ni mamaki na a ina hakan ya faru ko a part d'in naka" ya k'arasa yana yar dariyar iskanci d'an langa6ar da kai Haisam yay kaman bazai tanka shi ba ganin haka yasa Abbas gumtse Dariyar yace ya bari don Allah ya fad'a mashi don kan shi ya daure sai da yay d'an Jim kafin a nutse ya soma bashi labari tun daga barin su wurin dinner d'in Prince da dalilin kaita G.r.a d'in har zuwa yadda Al'amarin ya fara cike da damuwa bayan yazo nan a bayanin yace "I don't know what came over me and how everything happen dat way, i completely lost control as if my life depends on it dat moment...." dakatawa yay ran shi a 6ace Abbas nata girgiza kai had'i da d'an murmushi Haisam d'in ya cigaba "She said she was pleading me then I dont even heard her" yar Dariya Abbas yay mai d'an sauti Haisam d'in ya jefa mashi wani kallo mai kaman Harara cikin dariyar yace "Da alama akwae bambanci kenan?" Ya d'age ma Haisam d'in gira d'an guntun tsoki yay sai kuma yay d'an murmushin gefe had'i da juyar da kan shi, hannu Abbas ya kai ya dafa k'afar shi guda da ya mik'ar a saman gadon yace "Wllh H,Zakee ba wani abu bane face rabo Allah ya k'addara a wannan ranar a kuma daidai wannan lokaci Mom Zarah sai ta samu cikin ka shine kawae kuma Allah ya kaddaro dama can ita matar ka ce shiyasa wata kil hakan ya faru don asiri ya tonu" shiru bai ce komae ba dae Abbas ya dasa "amman miyasa daga baya ba kai mata bayani ba har abun ta kasance haka" sigh yay yace "ranar da hakan ya faru naso in mata hakan but tana cikin mawuyacin hali gashi ta matsa sai ta tafi gida don ni bamma san lokacin da ta je gate ba saida security yazo ya sanar dani bayan na fita naso mu koma ciki a lokacin I intend to explain myself but sai tak'i and banso muyi jayayya don dare yayi sosae ga security zai iya tunani na daban shiyasa nai mata yadda take so sai ma dana fara kaita hospital don tay shedding blood sosae" d'an bud'a ido Abbas yay fuskar shi tay yanayin tausayi ya hau girgiza kai can yace "to amman daga baya fa, da kai mata bayani ko kuma ni kayi man magana nayi mata na tabbatar da bata yi tunanin yin abortion ba in shi d'in tayi" hannu yasa ya d'an shafo forehead d'in shi kafin yace "a ranar nima kwana nay ban lafiya dama tun da abun ya faru naji ni abnormal daga baya fever mai tsanani ya rufe ni wurin Asuba sai ga kira daga Mom ta sanar dani halin da Dad ke ciki so I have no option dole in tafi muna zuwa can nima ciwo ya rufe ni kuma harda abunda nay ma yarinyar ke damuna duk da nasan mata ta ce amman nasan ban kyauta mata ba hakan ya k'ara worsen condition d'ina bayan na d'an samu sauk'i na Kirata amman tak'i picking dama ko ranar da abun ya faru na kira bata yi picking ba, a lokacin da ina can da ta d'auki wayan zan mata bayani ne in ma bata yarda ba zance taje ta tambayi grandma d'inta so ganin bata d'auka ba I just decided in rabu da ita in na dawo sai in mata bayanin komae" Abbas dake ta kallon shi jin ya dakata yasa shi cewa "to amman data gane tana da cikin bata sanar da kai bane?" Yanayin face d'in shi ne ya k'ara canzawa yace "Yau d'in nan nasan da Maganan Abbas, ta same ni can G.r.a lately anan take sanar man tana ta ciwo a School har an fara rumours d'in ciki ne da ita shine ya ja hankalinta......" Nan ya kwashe yadda sukai da ita d'azun ya sanar mashi Abbas sai girgiza kai yake har ya gama sannan cike da damuwa yace "Wllh harda rashin rabo Allah ya k'addaro dama ba za'a haife shi ba saidae Al'amarin ya bayyana kawae" shima Haisam d'in ran shi a d'an 6ace yace "with her stubbornness also, if she had listened to me this wouldn't hv happened......" Shiru yay bai k'arasa ba ya juyar da fuskar shi ganin yanayin shi yasa Abbas cewa "Kayi hak'uri nasan dole kaji ba dad'i kaga tak'i jin Maganar ka amman na tabbatar in ma zubar da shi d'in tay tayi hakan ne don Saboda ku duka bazata so sunan ku ya 6aci ba tunda kallon da take ma cikin bana halal bane" shiru bai ce mashi komae ba kafin Abbas ya k'ara cewa wani abu Dr Habeeb ya shigo ya nufo su da d'an murmushi kallon Haisam yay da shima ya kalle shi yace ya gama ya d'ibi d'ayan kai ya d'aga mashi Abbas yay saurin tambayar wani jinin za'a d'iba yace mashi eh cewa yay a d'ibi nashi in zai yi Dr yay yar dariya yace "Malam bari dae a diba nashi d'in tunda akwae don na tabbatar ko naka yayi sai an samu Malaria a ciki" dariya sukae gaba d'aya shidae Haisam d'an guntun murmushi kawae yay, bayan an fara d'ibar jinin Dr ke tambayar Abbas wai mara lafiyan matar H,Zakee ce yace mashi eh ya sake cewa amman yaga kaman ba itace suka je bikinta ba Abuja yace mashi eh wannan Amaryar shi ce da d'an murmushi yace "ai da yake su manya ne shiyasa har ya k'ara, itama wanccan din ai Amaryar ce tunda duka yaushe akai bikin" Murmushi kawae Abbas yayi bayan an gama d'iba saida ya zauna ya huta sosae lokacin Dr ya tafi daga baya suma suka mik'e Abbas nata mashi sannu saidae ya d'aga kai kawae bayan ya tashi tsaye Abbas ke ce mashi yakamata yaje yay wanka ya canza kaya don jini ya 6ata mashi gefen hannun shi da gefen rigar shi saima lokacin shi Haisam d'in ya lura yace suje Office d'in Dr ya wanke hannun zuwa anjima yaje yayi wankan Abbas yace to yasan in ba don ta kama dole ba ba yadda za'ai Haisam ya zauna da rigar nan, bayan sunje ya wanke suka nufi d'akin da Fatuu take lokacin da suka shiga jinin da aka saka mata nata shiga jikinta tunda Hajiya ta kalle su sau d'aya ta kauda kai Gwaggo ce tai mashi sannu ta mik'e tace suzo su zauna har yace tay zamanta tace zata shiga toilet ne lokacin Magrib ya yi ta nufi toilet d'in su kuma suka zauna yana ta kallon Fatun can suka had'a ido da Hajiya tana hararar shi ya sunkuyar da kan shi k'asa Abbas dae sai d'an murmushi yake, fitowa gwaggo tay tana gyara hijab d'in jikinta bayan ta daidaita ta kalli Abbas tace suje suyi salla kar lokaci ya shige ya amsa mata da to hannun shi ruk'e dana Haisam suka mik'e suka tafi gwaggo ta kalli Hajiya tana son yi mata magana amman tana jin shakka can dae ta tay k'arfin halin ce mata an fara kiran salla a fad'ace tace tana ji ai d'an murmushi gwaggo tay ta k'ara ce mata ga Hijab nan a jikin kujera ta d'aukko mata tace bata so ai batasa ta ta d'aukko mata ba yadda take Maganar ta d'aure fuska irin tayi fushin nan kwantar da Murya gwaggo tay ta shiga bata hak'uri har saida taga ta d'an saki Fuska ta fara k'ok'arin mik'ewa sannan gwaggon ta nufi gefe ta kwanto kallabinta ta shimfid'a ta kabbara salla, suna fita yace ma Abbas ya tsaya nan yay salla shi bari yaje yayi wanka sai ya dawo Abbas d'in yace to suje tare mana yace No ya tsaya koda za'a buk'aci wani abu sannan yace Ok sukae sallama ya tafi, ana gama sallar Abbas ya koma d'akin nan gwaggo tasa shi ya kira mata Amadu don ta baro wayarta a gida har Hajiya ma bata zo da waya ba a gida ta baro ta tun lokacin da Haisam ya sanar mata zancen cikin Fatuu, bayan ya kira ta fara ringing ya mik'a mata yana d'auka yaji muryar gwaggo ya hau tambayar ta ya Fatuu ko gaida ita bay ba dama tunda suka tafi hankalin shi ba kwance yake ba k'arshe ma kulle shagon yay ya koma gida bayan ya shiga kuma hankalin shi ya k'ara tashi haik'am ganin d'igo d'igon jini a tsakar gidan har zuwa cikin Parlor, saida ya gyara duk inda ya 6aci sannan ya shige d'akin shi ya kwanta cike da zullumi gashi duk yaga wayoyin su a Parlor balle ya kira yaji halin da ake ciki, jin yanayin muryar tashi tace mashi ya kwantar da hankalin shi da Sauk'i sosae ana mata k'arin jini ne cike da damuwa yace mata zasu iya yin Magana tace ai bata kaiga farkawa ba tukun, nan tace mashi ya zubo Abinci a Warmer da plates ya kawo da ruwa sannan ya d'aukko abun salla da buta da kayanta kala d'aya sai bargo ya tambayi Asibitin da suke sai lokacin ta tuna da bai sani ba ta fad'a mashi yace to, Haisam na barin Asibitin G.r.a ya nufa bayan ya shiga Bedroom d'in shi dole wanka ya fara ya zura jallabiya kafin yay sallar Magrib anan cikin dakin don lokacin ta ya shige, bayan ya sallame zaune yay jigum duk ya rasa mike mashi dad'i daka kalle shi zaka fahimci yana cikin damuwa don fuskar shi ta nuna, ya d'an d'auki lokaci a haka kafin yay Addu'a ya mik'e ya nufi cikin Corridor, sanye cikin wasu k'ananan kayan ya fito fess da shi ya d'auki Car key da wayarshi ya fita, saida ya tsaya yay sayayya mai yawa su lemu da ruwan roba katan katan da uban fruit harda gasassun kaji da balango mai yawa sannan ya wuce Asibitin, bayan ya isa ya parker Motar ya fara d'aukar lemu da ruwan ya shiga dasu lokacin Amadu har ya k'araso yana zaune cikin d'akin yay zugudum sai kallon Fatuu yake Haisam na shigowa ya mik'e da sauri yaje zai amshi abunda ya shigo dashi yana gaishe shi amsawa yay yace ya bashshi yaje Mota akwae wasu ya d'aukko ya amsa da to da sauri ya juya ya fita shima ya k'arasa ciki gwaggo na mashi sannu da zuwa cikin cool voice d'in shi ya amsa ya gaishe da ita kafin ya gaishe da Hajiya dake zaune akan Carpet d'in da Amadu ya kawo gwaggo ta mik'e ta koma gefen gado tace ya zauna, bayan ya zauna d'akin yay tsit Amadu ya dawo ruk'e da manyan ledoji ya aje a gefen inda sauran kayan suke ganin yay tsaye Haisam yace yazo ya zauna mana ya nufi gefen shi ya zauna shiru ta sake biyo baya har aka fara kiran sallar isha lokacin Haisam yace ma gwaggo ga kaya nan nasu ne tay mashi godiya ya mik'e ya fita Amadu ma ya bi bayan shi, bayan sun gama sallar isha ta bud'e ledojin ta d'aukko plate ta fara zuba ma Hajiya koda ta mik'a mata cewa tay bata ci da alama dae ran ta ya 6aci sosae hak'uri ta shiga bata suna haka suka dawo daga Masallaci harda Abbas nan fa ya sa baki aka cigaba da ba Hajiyar hak'uri sannan tace taji zata ci, k'ara zuba wani tay taba Amadu ya kai ma su Abbas harda Fruit d'in shima Amadun ta zuba ma shi kowa ya fara ci banda Haisam da tunda aka kai masu Abbas ya aje a tsakiyar su yay mashi magana sai yace ya fara ci yay zaune shiru idon shi na kallon floor gwaggo ta lura da bai ci hakan yasa tay mashi magana tana lallashin shi kan yaci kar yunwa tay mashi illa dama gashi bai warware sosae ba ga kuma jinin shi an d'iba da yawa jin haka yasa Hajiya ta ta6e baki tace "ai itama wadda ya kwantar bata ci ba waya san ma ko duk yau bata ci komae ba don haka ki rabu dashi" shiru gwaggo tayi shi kuma ya d'aga ido ya kalleta suka had'a ido tana ta tura baki yanayin fuskar shi ne ya d'an canza kamar zai yi murmushi amman bai bayyana ba sai daga baya ya fara ci a hankali don yana jin yunwa sosae kuma d'akin fess yake tamkar ba Asibiti ba ko d'azun gab da Magrib saida aka shigo akai Mopping tiles d'in kasan da bazai ma ci ba, wurin k'arfe tara Dr Habeeb ya shigo ya duba ta ya sanar masu da ta farfad'o don numfashin ta ya dawo bacci take yi yanzu ko wane lokaci zata iya farkawa shi lokacin tashin shi yayi amman akwae Doctor da yazo in da wani abu sai ai mashi Magana ga Nurse nan zata cigaba da kula da ita sukae mashi godiya Abbas da Haisam suka raka shi ita kuma Nurse d'in ta gaishe dasu tay masu ya mai jiki duk suka amsa tace zata tafi amman zata rink'a lek'owa in kuma da wani abu sai ai mata magana tana a Nurses station gwaggo ta amsa da to ta juya ta tafi, bayan wasu mintuna Haisam ya dawo shi kadae ya tsaya a gefe cikin girmamawa yace ma gwaggo su je Abbas na waje zai maida su gida tana jin haka tace mashi a'a Don Allah suje su ita zata tsaya ta kwana tun kan ta rufe baki a harzuk'e Hajiya tace "Yau naga ikon Allah ni Hauwa, shin wai shi d'in ba mijinta bane kuma shine sanadin kwanciyar ta to waya kamata yay jinyar ta dama bashi ba ko kuwa ya ja ma yar Mutane wahala sai kuma yaje yay share share akan gado yana bacci to kuwa bai isa ba shi zai zauna yay jinyar ta duk da kema bai kamata kiyi baccin ba shima Abbas d'in muje ya kaimun dole ya dawo nan ai jinyar ta dashi" tana gama Magana ta fara k'ok'arin mik'ewa duk gwaggo bata ji dad'i ba wllh don Haisam d'in na buk'atar isasshen bacci saidae ba yadda ta iya dole tabi Maganar Hajiyan itama ta mik'e ta d'auki kayan da Amadu ya kawo mata na sawa amman banda su bargon dama Amadu a tsaye yake sukai mashi sallama yana tsaye ya d'aga masu kai sai da ya raka su bakin k'opa yay tsaye har suka bar wurin sannan ya koma ciki, bakin gadon ya nufa ya tsaya hannuwan shi zube cikin Aljihun jeans d'in shi yanata kallonta bazaka iya karantar yanayin fuskar shi ba ya d'an d'auki lokaci a haka kafin yay yar ajiyar zuciya ya kai hannu ya shafi forehead d'in shi kafin ya juya walking slowly ya koma kan kujera ya zauna, suna hawa hanya Hajiya ta amshi wayar Amadu ta kira saude bayan ta d'aga ta gaishe da ita tace mata taga bata ganta a gida ba ko abu ne na gaggawa ya taso shiyasa batai mata ko sallama ba ta fita Sauden tay Addu'ar Allah ya maido ta lafiya tace ai gata nan ma a kan hanya so take tay sauri ta feraye dankali tay Faten shi yaji Alaiyahu sai kuma ta d'ibi yan ciki tay d'an ferfesu karta 6ata lokaci don Allah da sauri ta amsa mata da to ta kashe wayar, su gwaggo aka fara ajewa kopar gida sukai ma Hajiyar saida safe ta amsa ba yabo babu fallasa aka wuce da ita su kuma jiki a sanyaye suka nufi cikin gida gwaggo taso taga tashin Fatun, bayan sun isa gidan Hajiyan sawa tay dole Abbas ya tsaya har aka gama Abincin don ma ba me d'aukar lokaci bane aka zuba a k'ayatattun Warmers Saude ta bi shi dasu har zai fita daga parlon Hajiya ta tsaida shi tace ma Saude ta je ta daukko mosquito spray bayan ta kawo ta ba Abbas d'in tace gashi nan a fesa a d'akin kar sauro ya ciji Fateema ya k'ara mata wata cutar banda wadda suka jaza mata shi dae d'an murmushi kawae yay yasan harda don Haisam ta bada shi yay mata saida safe ya tafi Saude na biye dashi