Showing 123001 words to 126000 words out of 512766 words
Chapter 42 - Asanadin Makwabtaka Book 3 Hausa Novel Complete
Unknown
27 Dec 2024
1655
d'aure cike da girmamawa Gwaggo ta hau bata hak'uri tace ai hak'uri ya zama dole tunda aikin gama ya riga da ya gama wanda aka cuta an cuce shi" d'an murmushi kawae gwaggon tay Hajiyar tace "Ya jikin Fateemar?" tace mata da Sauk'i bari a kira ta tana d'akinta,
"In tana bacci ne ki rabu da ita",
tace "ban tunanin shi take yi kawae dai tana kwance ne tun bayan da muka dawo sai da dalili take fitowa" tana k'arasawa ta mik'e ta nufi hanyar fita Hajiya na fad'in ai dole tay ta kwanciya wannan uban jini da ta kwararar, lokacin da ta d'aga labulan a kwance ta same ta idanunta a rufe tana sanye da doguwar rigar bacci kanta sanye da hula, nufar ta gwaggo tay ta tsaya a bakin gadon ta kira sunanta jin shiru bata amsa ba yasa ta gane bacci take ta sunkuya ta kai hannu ta d'an bubbuga shoulder d'inta, a hankali ta bud'e idanun suka sauka akan gwaggo tace mata "Sannu ya k'arfin jikin?" hannu ta kai tana muttsike idanun tace mata da Sauk'i gwaggon tace "ba abunda ke maki ciwo?" Kai ta d'aga kafin tace "kawae jikin ne ba k'wari" kai ta jinjina "Wannan dama sai a hankali, ga Hajiya nan tazo ganin ki ki taso" amsa mata tay da to ta fara kokarin saukkowa, a tare suka tafi gwaggon na gaba tana biye da ita suka nufi parlon, bayan gwaggo ta shige da yar sallama itama ta shiga idon Hajiya a kanta ta mik'a hannu tana ce mata tazo ta zauna kusa da ita da yake a saman 2 seater take zaune, a gefenta Fatun ta zauna a hankali ta gaishe da ita ta amsa kafin ta kai hannu ta dafa Shoulder d'inta tana tambayar ta ya jikin tace mata ta samu sauk'i sosae,
"To Ya jinin yana zuba sosae ne?" ta tambaya sunkuyar da kai Fatuu tay tace "a'a kad'an ne kaman zai d'auke" jinjina kai tay tace "ai kin zubar da jini dole yay saurin d'aukewa" shiru Fatun bata ce komae ba Still kanta na k'asa, "Yanzu akwae abunda ke damun ki a jikin?" d'an girgiza kai tay tace "a'a kawae k'arfi ne babu sosae" tace "Wannan sai a hankali zai dawo kina dae cin Abinci sosae ko?" Kai ta d'aga mata alamar eh tace yayi kyau kafin ta sake tambayar tana shan suma magungunan da aka bata tace mata eh, shiru ta d'anyi kafin ta dasa "Fateema ina son tambayar ki kuma gaskiya nike son ki fito ki fad'a man kin ji ko?" d'agowa tay ta kalleta ta d'aga mata kai alamar to,
"Ina son inji shin zaki cigaba da zama da Yayan ki matsayin mijin ki ko kuwa baki so in raba ku?" Dammm! gaban Fatuu yay wani irin bugu ta kasa d'agowa balle tace wani abu ganin haka yasa Hajiya cewa ba shiru zata yi ba ta bud'e baki tay Magana a hankali ta saci kallon gwaggo suka had'a ido tana ganin haka ta juyar da fuskar ta daga barin kallon Fatun ta koma kallon gefe Hajiya tace "ki daina kallon ta ba abunda zata ce maki tunda ai ba ita zata zauna da shi ba dole kece zaki yanke kar Kiji wani abu ki fad'i man ra'ayin ki kan hakan" wani abu Fatuu ta had'iya ta rasa ma wace amsa zata bata duk ta rud'e kanta a k'asa sai zare ido take tana motsa hannuwan ta da bakin ta, da d'an d'aga Murya Hajiya tace mata dare nayi tayi magana d'agowa tay duk ta dabarbarce murya na rawa tace ".....Duk abunda...kuka za6a man yayi man" d'an murmushi Hajiya tay tace "To Fateema in muka za6a maki abunda bai maki ba fa tunda mu ba sanin abunda ranki zai fi so mukai ba kuma dae baso muke mu takura maki ba shiyasa aka baki dama ki fad'i abunda ranki ke so, kinga mu bamu zamu zauna da shi ba don haka kar Kiji komae ki fad'i kina son cigaba da zama dashi matsayin miji ko kuwa a raba ku" k'ara kallon gwaggo tay taga bata kallonta ta maida idon k'asa abu biyu ne suka hanata magana na farko kunya na biyu kuma tana kokonton amincewa ba kamar yanayin da take gani tattare da Haisam d'in,
"Shikenan tunda baza kiyi Magana ba bari in tashi in tafi, ni dae bazan yanke hukunci ba yazo kuma bai maki dad'i ba tunda ai harda irin hakan tasa aka fasa wanccan auren ko an za6a maki wanda baki so duk da harda k'arin halin shi" ganin tana k'ok'arin mik'ewa yasa gwaggo ta canza harshe tay ma Fatun Magana da d'an d'aga murya tace bazata bud'e baki tay magana ba, tana yamutsa fuska kaman zata saka kuka itama ta juya harshen tace mata tana so amman kunya take ji ta fad'i mata hakan, Hajiya da ta fasa mik'ewa ta kya6e baki tana bin su da ido har suka gama sannan tace "wato matsalar ka zauna cikin wad'anda ke yin yaren da baka iya ba kenan har gulmar ka sai ayi a kuma zage ka tass ba tare da ka sani ba k'arshe ma har kai ta washe baki kana tunanin abun kirki ake fad'a kaiga sakarai" murmushi kawae gwaggon tay Hajiya dake kallonta tace to mi suka ce a fad'i mata gwaggo tay mata bayani, wata irin kunya ce ta lullu6e Fatuu kan ta a sadde, d'an murmushi Hajiya tay tace "ina ruwan Fateema to miye abun jin kunya mutumin da dama Mijin ki ne kawae amsa zaki bada, shikenan Allah Ubangiji ya shige mana a Al'amarin tashi kije Allah yay maki Albarka ya k'ara maki lafiya damu baki d'aya, a hankali ta amsa da Amin ta mik'e ta nufi hanyar fita sumi sumi har lokacin bata d'ago fuskar ta ba, Bayan fitar ta Hajiya ta kalli gwaggo tace "Sai ku fara shiri ran Juma'a in Allah ya kaimu zata tare a d'akin mijinta nan part d'in shi" rasss kirjin gwaggo yay bata yi tunanin haka da wuri ba a d'an rud'e tace "to..Amman Hajiya bai yi wuri ba kuwa har a shirya ta tare a ranar?" Hajiya dake kallon ta ta cikin glasses tace "to Dije wane irin shiri ne za'ai da har nan da Juma'a bai isa a gama ba?" Cikin yar inda inda tace "dama wai Saboda kayan d'aki tunda wanccan wanda suka yi su sun fanshe su yanzu dole sai nayi ma Mahaifin nata Magana sai a siya wasu koda anan ne sai kuma sauran dae abubuwa" tana Maganar tare da yin nuni da hannuwan ta har ta k'arasa Hajiya da ta ta6e baki tana saurarar ta tace "To wane kayan d'aki kuma, ina ce a part d'in nashi akwae su kuma ba abunda sukai yanzu in an siya mata wasun su wanccan ya za'ai da su, ki bar zancen wasu kayan d'aki tay amfani da wanda ke akwae acan abunda ma nasan zaman na d'an lokaci ne Saboda karatun ta data gama ai dole ta bi shi inda yake zaune tunda ba yadda za'ai tay zaune nan mijin ta na wata uwa duniya, kuma ko bayan ta taren kina iya ganin ma ya canza mata wasu kayan d'akin tunda wanda ke akwae yanzun ma ai daga can K'asar wajen ya siyo su don haka ki bar zancen su kiyi sauran yan shirye shirye da ba'a rasa ba suma kada kice zaki wani takura kan ki tunda an riga an d'aura ba wani abu da ake buk'ata kawae ki sanar ma makwabta da Abokan Arzik'i don a shaida auren tunda abun surutu bai ma Mutane wuya kuma ma dai wani surutun dole ayi tunda yanzu tazo ta samu ciki kuma tazo daga baya ta haihu duk mutane basu san da auren ba ai kinga dole ayi surutu ko, in da wata matsala kiyi magana ina sauraren ki" godiya gwaggon tay mata daga baya tace "akwai kayan kitchen da ya siya mata na waccan auren suna nan ajiye ban san ko za'a iya kai mata ba tayi amfani dasu" tace "Eh to bai kamata aita ajiye su ba, bari muga tunda akwae d'ayan d'akin da yake aikin injiniyan cin nashi kuma an kwashe komae tunda yanzu ba'a nan yake ba sai abunda ba'a rasa ba inaga sai a jera mata kayan a cikin shi ya zama kaman kitchen dama kuma zagaye yake da table sai a k'ara gyarawa yadda zai yi Sosae, shikenan ko in kuma da wani abun sai ki fad'a don nafi son mu gama Maganar da ta danganci tarewar yanzu" d'an shiru gwaggo tay akwae abunda ke damunta a rai saidae ta rasa ta yadda zata yi mata Maganar Hajiya ta lura hakan yasa tace mata tayi magana inda wani abu ta kalleta cikin yar in ina tace "d...dama wai naga su can sauran dangin nashi da Matar shi basu san da Maganar auren ba shi ne nace...to ba matsala ta taren?" Hannu Hajiya tasa ta ruk'e ha6a "Oni Dije kin fi ni sanin abunda ya dace ne ko kuwa tsoro kike in sun sani za'a cinye maki Fateemar?" da sauri gwaggo ta girgiza kai alamar a'a ta hau bata hak'ura Hajiya ta dasa fad'in "ki bita da Addu'a kawae in sha Allahu komae zai zo da Sauk'i tunda shi ya k'addaro komae nasan hakan duk cikin hikimar sane shiyasa nima na d'auki Al'amarin da Sauk'i" kai gwaggo ta jinjina tay Addu'a tare da k'ara yi mata godiya daga haka ta fara k'ok'arin mik'ewa gwaggo ma ta tashi don tay mata rakiya,
Fatuu na komawa d'aki ta nufi gadonta ta haye can k'arshe ta zauna had'i da jingina bayanta a jikin bango sai zare ido take tama rasa shin murna ya kamata tayi ko mi, canjin da take gani a wurin Haisam duk shi ya Sagar mata da gwuiwa har take jin shakku game da zaman su tare gani take kaman shi bazai so hakan ba saboda in don laifin da ta yi ne ai ta bashi hak'uri, gani take da yana son ta ko yana son cigaba da zama da ita ai da ya hak'uri ya sake mata, tana haka Gwaggo ta shigo bayan ta dawo daga raka Hajiya, gadon ta nufa ta zauna a baki idonta a kan Fatuu da itama ta k'walalo ido tana kallon ta can tay yar ajiyar zuciya ta fara Magana "Sai ki fara shiri ranar Juma'a in Allah ya kaimu zaki koma gidan Hajiya can part d'in Yayan naki" dadamm! k'irjin Fatuu yay wata irin Fad'uwa ta zaro ido kaman zasu Fad'o a razane take kallon gwaggo jin abunda ta fad'a wanda kwata kwata bata zaci jin hakan ba, ko da ta amince ba tay tunanin da wurwuri haka ba, jin bata ce komae ba yasa gwaggo cewa bata ji abunda tace bane ta d'an yamutsa fuska kaman zatai kuka tace "Gwaggo da wuri haka kuma ya za'ai hakan bacin ba wanda ya sani a dangin shi ko ita fa Aunty Fanan bata sani ba" da alamun damuwa akan fuskar gwaggo tace "to nima nayi ma Hajiya Maganar hakan amman tace ayi Addu'a kawae Allah ya shige mana gaba" idanun ta ne suka ciko da k'walla ita tasan hakan ba k'aramar matsala za'a iya samu ba can suka fara zubowa sharr gwaggo dake kallonta tace mata ai ba kuka yakamata tayi ba suyi Addu'a kaman yadda Hajiyan tace komai sai aga yazo da Sauk'i cikin kuka tace "amman gwaggo ni ina tsoron kada azo a samu matsala fa in daga baya suka sani suka ce basu yarda bafa basu son auren tunda kinga Aunty Fanan yar'uwar su ce" shiru gwaggo tay ta sauke idanun ta k'asa ita kanta abunda yafi damunta kenan a cikin rai can ta d'ago tace "Addu'ar dae kawai zamuyi tunda ba abunda yafi k'arfin ta, koda nayi mata magana kan hakan nuna wa tay ban fi ta sanin abunda ya dace ba kin ga ai bazan yi jayayya da ita ba ko" shiru Fatuu tay tana goge kwallan dake zubo mata ana haka Amadu ya d'aga labulan d'akin ganin gwaggo yasa shi shigowa yana fad'in ashe tana nan yaje d'aki bai sameta ba hannun shi ruk'e da k'atuwar leda ya nufo su a bakin gadon ya aje ledar yace gashi nan in ji Ya Haisam yana gaida mai jiki kai gwaggo ta d'aga, ganin yanayin fuskar ta yasa shi tambayar ta lafiya ya juya kan Fatuu dake ta goge k'walla ba shiri ya kai zaune yana tambayar gwaggo jikin nata ne ta girgiza mashi kai alamar a'a,
"To miya ke faruwa ne naga kunyi jugum jugum ga damuwa akan fuskokin ku ita harda kuka don Allah ku fad'a man?" Shima har yanayin fuskar ta shi ya sauya yar ajiyar zuciya gwaggo ta sauke ta fad'a mashi zancen da Hajiya tazo tayi, d'an bud'a ido yay alamar mamaki sai kuma ya washe baki yace "to shine abunda yasa maku damuwa ku da zaku yi farinciki auren zai d'ore wanda mu hakan dama muke fata" d'an murmushin yak'e gwaggon tay tace "ba wai ba'a farincikin bane kawae damuwar tamu game da dangin nashi ne da basu san da zancen auren ba ita gudun ta kar daga baya kuma azo a samu matsala suce basu amince ba" da sauri yace "ku ma cire wannan tunanin in sha Allahu ba wata matsala da za'a samu koda ma an samu Allah zai kawota da Sauk'i don haka mu mik'a komae gare shi ayi Addu'a kaman yadda Hajiyan tace, kuma kun manta ne gaba d'aya dangin na shi da matar ta shi duk tana da iko da su don haka ayi yadda tace kawae" jinjina kai gwaggo tay ya juya kan Fatuu yana murmushi ya d'an kwanta kan gadon ya kai hannu ya kamo hannun Fatuu guda yana fad'in "u should be happy Allah ya amince Romeo ya zama naki ba kuka ba" tura mashi baki tay yasa dariya gwaggo ma murmushi ta bisu da shi, sakin hannun Fatun yay ya koma ya zauna yana kallon gwaggo yace "to yanzu ya za'ai Maganar kayan d'aki gashi an sa k'urarren lokaci ko da yake ai indai da kud'i har a siya ko?" Fad'i mashi yadda sukai da Hajiyar game da hakan tay yace "shikenan ma an hutar da mu naji dad'i wllh in akwai buk'atar ayin ko nan gaba sai ayi matan in kuma zai tafi da Ita can d'in ne bama sai an yin ba" juyawa yay kan Fatuu dake ta bin su da ido yana dariya yace "Waya ga su yar fillo a jirgi za dai asha hauka nasan" k'ara tura mashi baki tay ta d'an harare shi yace "ni kike harara, kifa bar ganin wai ke matar aure ce baki fi k'arfin in kikai man ba daidai ba in zane ki ko da kin bar gidan nan ne zan iya bin ki har can gidan in maki hukunci" gwaggo dake dariya tace "shi kuma mijin nata sai ya bika da ido kai ta dokar mai mata ko",
"Wllh yadda yake tubarkallan nan ma sha Allah yace zai rama mata ai sai ya karairaya ni nasan" ya k'arasa yanata dariya itama gwaggon dariyar take Fatun dai sunkuyar da kai tay tana d'an murmushi yayin da zuciyar ta ke suffanto mata surar Haisam,
"To yanzu shikenan sai dae a jira ranar akaita ko akwae abunda zaki?" Amadu ya tambaya tace "Eh zan bada ayi mata su cin cin tunda za'a sanar da makwabta zancen Auren nasan daga baya za'a shishshiga sai ranar Juma'a d'in ayi Abinci Saboda wanda zasu zo" kai ya jinjina "hakan yayi amman fa kar kiyi su da yawa ayi daidai daidai, to su yan Adamawa fa za'a sanar masu ne naga kaman lokaci ya k'ure ko?" d'an jimm tay kafin tace "zan kira Baffanta in sanar mashi komai amman zance mashi ba sai sun zo ba su bari sai daga baya in an samu natsuwa" kai ya jinjina yace hakan yayi sai kuma yace "Yanzu shikenan haka za'ai bikin Romeo da Juliet d'in lami ba wani d'an cashewa gaskiya yakamata a d'anyi mana ko yar dinner ce mu shaida muna biki" gwaggo dake murmushi tace "aikuwa dai haka zaku yi hak'uri don ba wani abu da za'ai" gyad'a kai yay "shikenan amman fa mun biyo bashi ko daga baya ne dole ayi mana in komae ya daidaita dangin shi sun sani" ta6e baki gwaggo tay "tunda ibada ne ya zama Farilla dole sai an yi ko" k'ok'arin mik'ewa ya fara yi yana fad'in bari ya d'aukko plates su yi shagalin abun farinciki ya nufi hanyar fita, plate guda biyu ya d'aukko babba da k'arami ya duk'a ya bud'e ledar abubuwan daya saba kawo wa ne a ciki ya zuzzuba a plate d'in ya mik'a ma gwaggo ta kar6a shima ya d'auki wanda ya zuba a k'aramin plate ya mik'e idon shi akan Fatuu data takure a guri guda yace "ki saki jiki Amaryarmu dis is worth celebrating don haka ki saki ran ki kici ki k'oshi" ya nufi hanyar fita yana fad'in dole ma ya d'inka sabuwar shaddar kai Amarya daga haka ya fice gwaggo ta d'an girgiza kai da d'an murmushi ta juya kan Fatuu da tay zuru tace ga abu nan taci, girgiza mata kai tay alamar a'a ganin ta damu sosae yasa ta shiga kwantar mata da hankali tace ta saki jiki taci don jikinta na buk'atar su ko kuzarin ta ya dawo cike da tsokana tace mata ko so take a kaita d'akin miji haka sukuku da ita Amarya da ake son ta da kuzari Fatun ta duk'ar da kan ta gwaggon nata murmushi, daga baya ta d'ago suka fara ci tare da gwaggon lokacin take ce mata ta kira Fauzy ta fad'a mata don su fara shirye shiryen su k'unshi da gyaran kai har tana cewa yakamata ma in an gyara kan ai kitso ita dae Fatun shiru tay, bata wani ci sosai ba tace ta k'oshi amman gwaggo ta matsa mata saida ta k'ara ci daga baya ta bar d'akin da sauran da suka