Showing 414001 words to 417000 words out of 512766 words
Chapter 139 - Asanadin Makwabtaka Book 3 Hausa Novel Complete
Unknown
27 Dec 2024
1613
Yalla6ai Sameer ne yace ta kawo ma Amarya Aunty tace to ta tashi tsaye ta kar6a, kafin matar ta tafi ta nuna mata magunguna dake ciki basket d'in tace hada su aka ce ta kawo ta sake cewa sai kuma wannan ta Mik'o mata wayar Fauzyn, amsa tayi tay mata godiya Matar ta tambayi da wani abu Aunty tace mata a'a ta k'ara mata godiya ta juya ta tafi, nufar side drawer tayi ta d'aura kwandon kafin ta shiga bud'e had'add'un Warmers d'in dake ciki, d'aya farfesun kaza ne yaji kayan k'amshi gwanin kyau a ido, bayan ta rufe ta bud'e d'ayar soyayyen dankalin turawa ne da dafaffun k'wai sai kuma Flask wanda da gani set ne da Warmers d'in nan tea ne da yaji kayan k'amshi daga gefe akwae plates da cup sai cokulla sai Madara da milo da kwalin sugar, Murmushi Aunty ta shiga yi a fili ta furta "Su surukina kenan tunda fa an cuci yar mutane dole aita nan nan da ita" a ranta kuwa dad'i ne ya kamata don da alama komai ya kasance yadda take so, tashin Fauzy ta shiga yi bayan ta bud'e ido tace mata ta tashi ga Abinci nan Angonta ya aiko mata ta kamata ta tashi zaune, Fauzy taji dad'in Abincin dama a lokacin ta fara jin yunwar sosae, ba laifi ta ci sosae ba kamar kazar Aunty tasata tasha romon sosae, ganin tana ta ci yasa ta kalleta cikin d'an disashewar murya tace mata itama ta ci mana Aunty Mareeya tayi d'an murmushi tace ita dai ta ci ta k'oshi tukun don ta fita buk'ata, tana cikin ci sai ga kiran Sameer ya shigo Aunty ta d'auki wayar ganin shine tay d'an murmushi, picking tayi ta kara ma Fauzy a kunne shiru tay ta dakata da cin Abincin taji ya kirata da Babes d'an kallon Aunty tay data ruk'e mata wayar kafin can k'asan mak'oshi ta amsa, tambayar ta yay jikin a hankali tace mashi da Sauk'i yace ya manta bai sata ta zauna ruwan ba ta bashi amsa da tayi anan yace Ok sai kuma ya tambayi taci Abincin da aka kawo tace eh gashi nan tana ci yace Ok bari ya barta taci amman pls taci sosae sai tasha magani ta amsa da to ya katse kiran, bayan ta k'oshi ta bata magungunan tasha kafin ta koma ta kwanta sannan Aunty Mareeya itama ta zuba tana cikin ci Yaya Fareeda ta farka wai k'amshin abincin ne ya kai mata cikin bacci tama yi zaton Mafarki take Aunty tay dariya tace ango ne ya aiko ma amaryar shi shine take cin saura itama ta wanko baki tazo taci tace to. Wuraren k'arfe tara da rabi aka kawo masu breakfast lokacin Fauzy nata shan bacci tun bayan data ci Abinci, sanin ba yunwa take ji ba yasa Aunty bata tashe ta ba su Gwaggo nata tambayarta aka ce masu bacci take, bayan sun gama zama sukai anan falo suna kallo kafin zuwa k'arfe sha biyu suka fara shirin Walima don ana gama sallar Azahar za'ayi Saboda masu tafiya don gobe Monday, sosae Fauzy tasha bacci don saida Aunty ta tasheta Saboda shirin Walima kaman zata yi kuka tace ita dama an k'yaleta tayi kwanciyarta a d'aki Aunty tace ai tasan hakan bazai yuwuwa ba ta dai daure da anyi angama ai shikenan. Zuwa bayan Azahar kowa ya shirya Amarya Fauzy ansha rantsattsiyar shadda da ta sha ubansun aiki wuyanta da hannunta duk diamond ne, ba tare da 6ata lokaci ba aka shiga gudanar da Walimar data samu halartar manyan mata k'awayen su Her Excellency kowacce ka gani hamshakiyar kanta ce tsadaddun sutturu kawai kake gani kowa tayi shiga mai sunan shiga ansha gwalalai abundai sai wanda ya gani suma su Aunty ba laifi sun yi shiga mai kyau daidai k'arfin su, sai la'asar aka gama an ci an sha an kuma ba Fauzy kyaututtuka, ana gama Walimar su Mom sukai shirin tafiya harda yan Ethiopia zasu tafi can Abuja tare suma su Gwaggo suka ce tunda dai an gama mi suke jira akace Aunty tayi ma Her Excellency magana, koda tayi mata cewa tayi a'a yamma tayi su bari sai gobe da safe za'a maida su, sosae Fauzy taji dad'i da har ta shiga damuwa da suka ce zasu tafi, Fatuu ma da zata bi su Mom Aunty Mareeya ta rok'eta ta tsaya sai in zasu tafi koda ta kira Haisam ta sanar mashi cewa yay ba komai Allah ya kaimu, bayan gama Walimar ne aka kawo masu sauran akwatunan lefen Fauzy set biyu suma guda goma an narka uban kaya su Aunty suna ta jinjina yawan akwatunan har guda ashirin, bayan sun natsu ne Fauzy tace ma Aunty ta d'aukar masu kaya cikin lefen tunda dama wanda aka fara kaiwa ba'a d'auki komai ba don kayan duk a d'inke suke Fatuu ma tace mata ta d'auki abunda take so tace mata a'a ta bar shi aikuwa Fauzy tace in dai bata d'auka ba to tasan zaman da zata yi da ita wato ita ta amshi nata sai itace zata k'i amsar nata Fatuu na dariya tace to ai abun ba gasa bane ko kuma ita duka yaushe akai sunan su twins ta samu kaya sosae, duk da haka matsa mata Fauzy tayi sai ta d'auka k'arshe dai sai Aunty Mareeya ce ta d'aukar mata wasu abubuwan. Da daddare bayan sun yi shirin kwanciya Aunty tace ma Fauzy ta tafi wurin mijinta ta kwa6e fuska tace bazata je ba su Fatuu nata dariya ganin abun ya zamar masu drama Yaya Fareeda k'asa ta kwanta kan Carpet ganin gadon bazai ishe su ba don ga su twins. Washe gari bayan sunyi breakfast suka hau shirin tafiya gaba d'aya Fauzy duk tayi sukuku da ita, Misalin k'arfe sha d'aya na safe duk suka fito don tafiya Fauzy nata k'walla suna ta bata hak'uri Hajiya Zainab data rako su tana murmushi tace ma Fauzy nan ma ai gida ne ko, sha tara ta Arziki akai masu harda kud'i aka babbasu ganin da gaske tafiya zasu yi yasa Fauzy yin kuka sosae har ta karya ma Aunty Mareeya zuciya itama saida tayi k'wallan, aure kenan mai raba Y'a da uwa mai kuma raba dan'uwa da dan'uwa dole Aunty Mareeya taji kewar Fauzy don sun saba sosae, tana ji tana gani suka tafi suka barta sai fatan Allah ya kiyaye hanya ya kai su lafiya. Bayan tafiyar su Aunty part d'in Hajiya Zainab aka tafi da Fauzy anan Sameer ya sameta tana zaune a parlor ita kad'ai tana kallo saidai hankalin ta ba'a kan tv d'in yake ba damuwar tafiyar su Aunty ce a ranta yaran gidan duk sun tafi Makaranta da Amal ta zauna suna d'an yin hira jefi jefi don basu saba ba daga baya ta tashi don itama shirin barin K'asar take ta koma Makaranta dama bikin ne yasa ta zo, yana sanye cikin sabuwar farar shadda sai baza k'amshi yake ya zauna a kujerar gefenta, a sanyaye ta gaishe shi ya amsa yanata kallonta ganin yanayinta yasa a hankali ya tambayi ko har yanzu jikin nata su tafi hospital ta d'an girgiza mashi kai yace to ya ya ganta haka kaman abu na damunta tace mashi ba komai, shiru yay yana mata wani kallon ta kauda idonta can ya mik'e tare da kama hannunta yace suje, marairaice mashi tayi tace Momy ce ta taho da ita nan ya za'ai su tafi yace to sai ta zauna ita kadai tace ai tasan zata dawo sai kuma ta sameta bata nan, ce mata yay zai kirata ya sanar mata shi ya tafi da ita tana niyyar k'ara magana ya d'an d'aure fuska yace bai son gardama dole tayi shiru yana ruk'e da ita suka nufi barin falon, bayan sun fito ne ganin bata iya tafiyar sosae yasa hannu ya d'auketa gabanta sai fad'uwa yake kar wani ya gansu ahaka cikin sa'a har suka isa part d'in nashi basu had'u da kowa ba, bayan sunje a bakin gado ya d'aurata shima ya zauna ya kai hannu ya kamo nata yace ta fad'i mashi Mike damunta in ba ciwon bane, k'walla ne suka ciko mata cikin karyayyar murya tace mashi ba wani abu bane kawai ta damu da tafiyar da su Auntyn ta sukai ne tana yin Maganar k'wallan suka zubo mata sharr, jawota yay jikinshi ya sa hannu yana shafa bayanta alamar rarrashi can ya kai bakin shi saitin kunnanta yace mata ba gashi tare da ita ba miyasa zata damu, lamo tayi tana ta shak'ar daddad'an k'amshin shi mai narkar da zuciya, sun d'an d'auki lokaci a haka kafin ya d'ago fuskar ta suka had'a ido nata sun d'an lumshe, tambayar ta yay jikin yana sauk'i ta d'aga mashi kai ya k'ara tambayarta ta zauna ruwan zafin yanzu tace mashi eh lokacin da tayi wanka da safe yace Ok bari a bari zuwa anjima sai ta k'ara a hankali tace to, bin juna sukai da kallo yanayin fuskar shi da d'an murmushi haka itama sun d'an d'auki lokaci haka jin bata iya jurewa yasa ta fad'a jikin shi tana d'an murmushi, kai bakin shi yay saitin kunnanta ya rad'a mata wata magana sai gashi ta d'ago da sauri tana kallon shi idanunta a d'an waje ya d'age mata gira, yamutsa fuska tayi idanunta sukai raurau alamar zata saka kuka kawai sai gani tay yay yar dariya har fararen hak'oran shi sun bayyana, maidota yay jikinshi ya rad'a mata he won't do it again until she've healed, murmushi ta shiga yi idanunta a rufe tana jin wani irin son shi na ratsa zuciyar ta.
Ana gama bikin Fauzy aka tsaida lokacin da za'a yi nasu Nameer da Aunty Laila nan da wata ukku lokacin sun gama duk wani abu daya danganci karatun su, Fatuu bata koma Katsina ba dama hada karatu ke zaunar da ita can yanzu kuma ta gama k'arshe ma Haisam yanke tafiya da ita Us yay ta shiga yin shiri, ta bangaren Amarya Fauzy ma itama barin K'asar zasu yi bayan bikin da sati d'aya don har anyi mata passport, ana saura kwana biyu su tafi ranar laraba suka zo Abuja zo kaga murna wurin Fatuu su Mom ma sun yi farinciki da zuwansu suka tarbi Fauzy hannu bibbiyu, bayan sun ke6e da Fatuu a part d'in su ne ta shiga yaba canzawar da tayi cikin d'an lokaci har tana fad'in lalle Sameer ya iya tarairaiya Fauzy dai sai dariya take itama tace ma Fatun ai itace za'a ce ta canza don gaba d'aya yanzu ta koma kalar hajiyoyi haka dai sukai ta hirar nishad'i tsakanin su, anan suka wuni sai k'arfe biyar na yamma suka tafi Fauzy harda ce ma Fatuu in taje Us d'in zata sa Sameer ya kawota wurinta. Ranar Friday Jirginsu ya tashi zuwa England sai fatan a sauka lafiya. Washe gari Asabar Haisam da Fatuu suka tafi Katsina don yin sallama dasu Gwaggo ta kuma d'aukko kayan da take son tafiya dasu, har gidan Aunty Mareeya taje dama tasa tayi mata tanadin kayan gyara ta amso suka yi bankwana haka gidansu Haulat ma taje sunyi bankwana harda abun Arzik'in da ta saba tayi mata, washe gari Lahadi wuraren Azahar suka komo Abuja ta ci gaba da yin shiri don gobe in Allah ya kaimu suma jirginsu zai tashi zuwa Us, da yamma bayan anyi La'asar suka tafi inda za'a mata k'unshi da gyaran kai, Washe gari da Safe sukai bankwana wad'anda ke a gidan sukai masu rakiya zuwa Airport Jidderh kaman zata yi kuka wai zata yi missing yaranta Abie da Grandpa kaman yadda suke ce masu Mom na dariya tace koda su basu tafi ba ai itama tafiyar zata yi Dubai ta barsu ko tunda a cikin satin zata tafi itama. Tuni jirginsu Fatuu ya d'aga sai Fatan a sauka lafiya Fanan na can tana shirya masu kyakkyawar tarba sai faman farinciki take yaranta su Twins zasu zo gareta.
Satin su Fauzy d'aya da zuwa lokacin tuni ta warke suna ta shan Amarci na gaske har yanzu ko ruwa bata ta6a dafawa ba bayan sunyi aure don anan d'in ma akwai mai aiki namiji da dama shi yake ma Sameer d'in Abinci da gyaran gida, koda tayi mashi magana kan ya sallame shi ta rink'a yi sai cewa yayi ba buk'atar sai tayi Abinci a marairaice ta nuna mashi ita dai tana son ta rink'a mashi girkin sai yace to ba yanzu ba, saidai ta ci ta sha ta ji da Sameer d'in, Washe gari ya kama Asabar ta kira Aunty lokacin bayan Azahar ne Sameer ya fita, Aunty na kwance tana bacci kiran ya shigo, saida ta kusa katsewa sannan ta farka ta duba tana ganin Fauzy ce ta saki murmushi tare da yin picking, bayan sun gaisa ta tambayi yadda suke ta bata amsa daga haka tay shiru, Aunty ta fahimci kaman akwae abunda take son fadi hakan yasa ta ce mata ya akai ne, ai kamar tana jira cikin murya kamar zata yi kuka tace "gaskiya Aunty wllh akwae Matsala" jin haka yasa Aunty Mareeya yunk'urin tashi zaune tana fad'in "Matsala kuma!, Allah ya rabamu da ita" bayan ta zauna sosae da alamun d'an tashin hankali tace mata wace matsala ce,
Shiru tay kaman bazata yi magana ba saida Aunty ta k'ara tambayarta tace bazata fad'i mata ba ko so take hankalinta ya tashi ne sannan tace "Aunty kwanaki ba cewa kikai in dai matsalata yace yana sona ba ke zaki sa shi ya rink'a fad'i man hakan kaman cin Abincin shi safe da rana da dare ba" da sauri Aunty tace "eh hakane, bai fad'i maki hakanne?" Da sauri tace "a'a yana yi amman fa....Ke ba wai kina nufin zai rink'a ce man hakan ba?" ta canza Maganar zuwa tambaya Auntyn tace mata eh mana haka take nufi,
"To nidai wllh ba ta yadda kika ce ba yake fad'i man Allah" da alamun rashin fahimta Aunty tace to taya yake fad'i mata, shiru tayi kaman bazata yi magana ba Aunty tace tana jinta taya yake fad'i mata, yar in ina ta shiga yi "n..ni Aunty bansan ya zance maki ba amman gaskiya abun yayi yawa wllh" yadda tayi Maganar kamar zata saka kuka lokaci guda Aunty ta gane mi take nufi ta shiga yin dariya jin haka yasa Fauzy ce mata yanzu dariya zata yi mata don Allah, tana yin dariyar tace mata "to Yar gidan Hajiya kece da wani abun dariya wllh, dama kawai sai ya zaune yay ta faman ce maki I love you Fauziyya kamar wani zautacce, yadda yake maki dama ta hakan nake nufi kuma wllh naji dad'i sosae k'ok'arina bai tashi a banza ba kenan kema farinciki ya kamata kiyi ba k'orafi ba" tura baki tayi tana yamutsa fuska tace to ai gaskiya abun yayi yawa bata iyawa, ta6e baki Aunty tay tana faffad'an murmushi tace "ba wani yawa, kowacce mace da kika gani da kalar mijinta haka kowa take hak'uri, bai kamata ace tun yanzu kin fara k'orafi ba yayi wuri da yawa yar gidan Aunty, kiyi hakuri a hankali zaki saba kada ki sare ko ki nuna gazawa ta wannan hanyar ake kama miji a hannu ni wllh baki ji dad'in da naji ba don hakan ya tabbatar da kwalliya ta biya kudin sabulu, ina son in ja hankalin ki dole sai kin jajirce in ba haka ba to kuwa zaki ja ma kan ki matsala ne tun ba'a je ko ina ba don yadda yanzu yasan takan abun to kuwa in baki wasa ba zai iya zarta halin shi da aka fad'i don haka kiyi hak'uri kada ki bari ki zama raguwa kawai ki dage da gyara kan ki kinji yar gidan Aunty Mareeya" kai Fauzyn ta d'aga kafin tace to don ta tsorata da Maganar Aunty da tace zai iya zarta ta6a matan da aka ce yana yi wanda shi kanshi k'ok'ari take ta saka shi ya daina kwata kwata duk da bata san ko har yanzu yana hakan ba, cigaba da kwatanta mata Aunty tay tana fad'in wannan dama ce a gareta da zata maido gaba d'aya hankalinshi a kanta Fauzyn nata fad'in to, bayan ta gama ne tace mata dama tana ta son tayi mata magana game da Motarta da suka dawo da ita nan tana ganin da aita ajiyeta mi zai hana a kai mata ita can Nasarawa in suka zo sai taci gaba da yin amfani da abunta Fauzyn tace to zata yi mashi magana kan hakan daga baya sukai sallama Aunty nata yar dariya. Sai bayan da akayi la'asar ya dawo gidan lokacin har tayi wanka ta canza kaya zuwa skinny jeans da yar top kanta tayi parking gashinta ba kallabi da yake da kanshi ya nuna mata irin kayan da yafi so tana sakawa kenan shiyasa ko da yaushe cikin k'ananun kaya take ko fita zasu yi da yake yana yawan fita da ita zaga gari a haka suke fita saidai in kaman zasu fita daga Mota ne ko siyan wani abu sai ta d'aura After dress, tana zaune a parlon su mai kyau mara hayaniya mai d'auke da lafiyayyun kujeru leathers ya shigo hannunshi ruk'e da wata yar jaka yana sanye da k'ananun kaya shima, juyawa tay ta kalle shi yana cire takalma a bakin kopa a wurin da aka tanada don yin hakan in mutum ya cire wanda ya shigo dasu sai ya saka wasu kaman slippers su kuma na shigowa cikin parlon ne, mik'ewa tay tana murmushi ta nufo shi tana zuwa daf da shi ya d'an wara mata hannuwa ta fad'a jikinshi ya rungumeta gaba dayansu sai sakin kamshi suke, d'ago kai tayi tace mashi welcome back ya d'aga mata kai fuskar shi da d'an murmushi yay sunkuyo yay pecking goshinta, nufo cikin parlon suka yi yana tallafe da ita suka nufi kujera 2 seater ya zauna tare da ita, k'ok'arin raba jikinsu ta shiga yi tana fad'in bari ta kawo mashi ruwa yak'i sakinta tare da girgiza mata kai alamar ba zai sha ba tana mashi wani kallo tace to bari ta kawo mashi lemu sai