Showing 66001 words to 69000 words out of 512766 words

Chapter 23 - Asanadin Makwabtaka Book 3 Hausa Novel Complete

Unknown   

27 Dec 2024

1585

kuka mai sauti tana fad'in ita ya kyaleta yasa a bud'e mata gate ta tafi, fasa d'aukar tata yay ya mik'e tsaye don bai son Officer ya ji har ya zargi wani abu can ya sake duk'awa gabanta a hankali yace "kin ga yanzu dare yayi sosae kiyi hakuri mu koma ciki zan kira Uncle d'in ki sai in sanar mashi dare yayi mana sosae matar Abbas ta wuce dake gidanta in mun shiga ciki zamu yi magana kiyi hak'uri kinga ma baki lafiya sai kisha magani" da ga voice d'in shi zaka fahimce shima a rud'e yake har wani d'an nishi yake don shima zazzabi ne a jikinshi, duk yadda yay da ita su koma ciki tak'i sai ma ta kife kanta tana ta kuka har cikin ran shi yake jin kukan don yasan shine silar shigarta halin da take ciki yama rasa tunanin da zai yi cikin ranshi yanata ayyana miya faru dashi ne ya akai ya aikata wannan d'anyen aikin ina hankalin shi ya tafi ne, yasan tunda ta kafe to bazata koma ban hakan yasa shi ce mata to bari ya maida ita gidan cikin fushi tace ita bata so a bud'e mata gate kawae bai yi mamakin yadda tay mashi Maganar ba don yasan girman shi ya gama fad'uwa a wurin ta rarrashin ta ya shiga yi yana nuna mata illar fitar ta a wannan lokacin in dai bata bari ya kaita ba to saidae su kwana anan ala bashshi sai ya kira Amadun ya fad'a mashi abunda yace zai fad'i mashin, shiru tay saida aka d'an d'auki lokaci sannan tace suje ya kaita ya mik'e da sauri kai kace ba Haisam ba da alama bai ma san ina yake wurga k'afarshi ba dama Motar ba'a parking space take ba yana d'aukko makullin ya shiga ya tada bayan ya juyata ya iso gaban gate d'in ya bud'e ya fito ya koma wurinta yace ta taso suje ganin yadda take kokarin mik'ewa yasa shi kai hannu ya taimaka mata tana ta k'ok'arin kwacewa bai biye mata ba saida ta mik'e sannan ya saketa da k'yar taja k'afa ganin ta nufi kopar baya ya je ya bud'e mata saida dubara ta shiga ya rufe shima ya shige driver seat yay ma Officer horn sai gashi da sauri ya fito yaje ya zuge masu gate d'in Haisam yaja suka fice, bayan officer ya rufe gate d'in tsaye yay da alamun tunani yake saidai ya kasa hasashu komae k'arshe ya gyad'a kai ya koma cikin d'aki, tunda suka taho taci gaba da kukan da take k'asa k'asa tana sheshsheka shiru bai ce mata komai ba tunanin yadda zai maida ta gida acikin wannan halin yake can wata zuciyar ta raya mashi yakamata ma ya kaita Asibiti don da alama akwae matsala Saboda jinin da ya gani duk da first night dinsu da Fanan itama tay shedding blood d'in amman nata d'an kadan ne bai kai yawan na Fatuu ba da wannan tunanin ya yanke wucewa da ita Asibiti kawai, kanta na duk'e har suka iso jin an tsaya yasa ta d'ago lokaci guda ta gane Asibiti ne bayan ya kashe Motar ya bud'e ya fita saida ya rufe ta da Makulli sannan ya nufi ciki Fatun na mashi wani kallo ta cikin glass wa zai yi tunanin zai iya aikata mata haka ta raya a ranta, yana shiga reception sai ga wata Nurse zata wuce da sauri yay mata magana ta dakata baiwar Allah har saida ta saci kallon k'afafun shi don taga in ba kofato bayan yay mata ya aiki tace Alhamdulillah yace don Allah Doctor mace yake son gani tace mashi gaskiya ba mace duk maza ne shiru yay kawai yana tunanin bai kamata ace namiji ne zai duba ta ba ganin haka yasa tace mashi dole sai mace yace eh yafi son haka har zai juya tace "Yalla6ai akwae wata Mama tsohuwar nurse ce ba likita ba amman kusan ma kamar likitan ake d'aukarta don ta san abubuwa sosae in kana so tana nan sai ka ganta" da sauri ya kalle ta yace Ok tana ina tace suje ta juya hanyar da ta fito yana biye da ita har suka isa wata kwana a bakin wata k'opa ta tsaya ta juya tace mashi tana zuwa ya d'aga mata kai, lokacin data shiga mamar wadda dattijuwa ce tana kwance a saman gadon da ake duba mara lafiya ta d'age kai baki bud'e tana bacci ga gilashin fuskarta ya zame a gabanta nurse d'in ta tsaya ta kira sunanta har sau biyu bata farka ba hakan yasa ta d'an matsa ta kai hannu ta d'an bubbuga gefen kanta aikuwa sai gashi ta bud'e ido kaman an latsa mata remote ta k'ura ma nurse d'in ido ita kuma tana mata murmushi can ta yunk'ura ta tada kanta cikin fushi tace "Nurse Bilki ke wace irin muguwa ce ne?" D'an bud'a ido bilkin tay tace "Mama nice muguwa kuma" tsuke fuska tay tace "eh mana in ba mugunta da rashin tausayi ba duka fa ban dad'e dana samu na kwanta ba bayan gama kacaniyar Labour room shine kuma zaki zo ki katse man bacci?" Sanin halin ta na mita yasa bilkin cewa "to yi hakuri Mama dama bak'o kika yi ne shiyasa na tashe ki" d'an yamutsa baki tay tace bak'o kuma da tsakan daren nan waye shi bilkin ta fad'i mata yadda sukai da Haisam wata uwar harara ta zabga mata tace "to in banda iskanci baki ji likiciya yake son gani ba zaki tada ni ni likita ce?" d'an murmushi bilki tay tace "ai kema mama kaman likitan kike kuma don naga kaman yana cikin tashin hankali ne yasa nace bari in maki Magana k'ila wata matsalar ce yake son fad'i maki" cigaba da harararta tay kafin can ta yunk'ura ta saukko tana d'aure da zanin Atamfa saman farar doguwar rigar aikinta tambayarta tay yana ina tace yana nan bakin kopa ta nufi kopar tana mita bilkin na dariya a ranta tana ayyana dama ina ma'aikacin Asibiti yaga wata damar yin bacci mai yawa, Mama na bud'e kopar idonta suka sauka kan Haisam dake jingine da bangon dake opposite da Office d'in har saida tasa hannu ta gyara gilashin ta yadda zata gan shi da kyau ta bishi da kallo tun daga sama har k'asa ganin yana kallonta yasa tace shine mai neman ta yace eh yana kokarin matsowa gabanta tace tana d'an zuwa to yace Ok ta koma ciki suka had'a ido da bilki dake murmushi tace "Ke kin tabbatar wannan mutum ne kuwa ba Aljani ba nifa ban yarda da shi ba don kwanakin nan dama ina yan gane gane" Bilki mi zatayi ba dariya ba ganin yadda mama tayi zuru zuru da alama dae ta tsorata da Haisam d'in cikin dariya tace "Wllh mama nima dana gan shi har saida na kalli k'afafun shi dama banga lokacin da ya shigo ba sai dae naji anyi man Magana kawae ga abu na dare" turo baki Mama tay tace mata yanzu ya zasu yi bilkin tace ita tana ganin lafiya lou Mutum ne in ba haka ba mi zai sa yazo wurin su har yace yana son ganin likita Mama tace "Bilki raba kan ki da sharrin Mutanen 6oye" juyawa tay tace suje tare koma mi zai faru ya faru dasu duka bilkin ta bita tana fad'in kai Mama kefa dama kin tsufa ni kuma yanzu nike kuruciya ta a tare suka fita bawan Allah Haisam yana jingine da bango duk yayi zuru zuru bayan ta fito tace mashi tana ji miye matsalar yake son ganinta ba tare daya ji komae ba ya shiga yi mata bayani bayan ya d'an daidaita natsuwar shi tana ta jinjina kai ta d'an ta6e baki har ya gama saidae a yadda yay mata bayanin nuna mata yay matarshi ce, tambayar shi tay yanzu ina take yace tana Mota ta tambaye shi tana iya tafiya yace eh amman ba sosae ba ta kalli Bilki tace taje ta d'auki Wheelchair ta taho da ita su fara tsayawa Nurses room a turo ta tace to ta kalli Haisam tace suje, da taimakon Bilki Fatuu ta fito ta taimaka mata ta hau wheelchair d'in kafin ta tura ta tana biye da ita suka shiga saida ta tsaya aka tura sunanta ta computer sannan suka wuce wurin Mamar da zasu shiga tace ma Haisam ya jira ta nuna mashi waiting seats dake gefe alamar ya zauna yace ok, bayan an shiga da ita tare da Mamar aka taimaka mata ta hau gadon ta sanya hand gloves ta fara dubata tana yi tana yamutsa baki can ta fara mita tana fad'in "ni wllh irin wannan duk nafi ganin laifin iyayen ku su same ku suyi ta yi maku banke banken magungunan mata to su mazajen naku duwatsu ne da bazasu rikice har suyi maku aika aika ba, kamar ke yanzu ai baki wani bukatan magunguna iya lafiyayyen Abinci ma ya Wadatar kuma da gani ana ci sai abu ya faru kuzo kuyi ta ma Mutane jan ido" bilki dai na tsaye daga can gefe tana k'umshe dariya sosae ta duba ta bayan wani lokaci ta gama ta fara cire safar ta jefar a cikin dust bin kafin ta juyo ta kalli Fatuu tace "Allah ya taimaka baki buk'atar stitches kin samu rauni ne a farko wurin shiga da alamu ansa ma wurin k'arfi ne halan hana shi hakkin shi kika so yi ya nuna maki k'arfi haka?" sunnar da kai Fatuu tay idanunta suka ciko da k'walla da tasan halin da take ciki da batai mata wannan Maganar ba kallon bilki tay tace ta kamata su shiga toilet d'in cikin Office d'in ta taimaka mata da ruwan zafi ta zauna ta d'an samu relieve tace to ita kuma ta juya ta fita Haisam na ganin ta lek'o ya mik'e yaje gabanta tayi mashi bayanin komae tace yanzu dole ta dage da zauna ruwan zafi amman ba mai zafi ba sosae da d'an gishiri sai magungunan da za'a bata ta rink'a sha in tana haka zata samu sauki yace to d'an zare mashi ido tay tace "Amman fa ka k'yaleta ta huta sosae har ta warke garas kafin ka k'ara tunanin yin wani abu" jinjina mata kai kawae yay tace ya jira zata tura magani yaje Pharmacy yace to tana niyyar juyawa ya dakatar da ita ta hanyar rok'on ta ko ya samo mata wani abu a bata taci sai in ya amso magungunan a bata ta fara sha daga nan d'an kya6e baki Mama tayi tace halan fushi take dashi yasan in ya bata bazata ci ba d'an guntun murmushi kawae yay tace yaje ya kawo ya amsa da Ok ya wuce, bada jimawa ba ya dawo Cake da lemu ya samo a shop d'in cikin Asibitin su kadae ne yake tunanin zata d'an ci don ba Abinci a wurin bayan ya kwankwasa Nurse Bilki ce ta fito ta amsa kafin ya juya ya nufi Pharmacy d'in aka tura kud'in yaje ya biya kafin ya amsa magungunan suma ya kai masu ya koma ya zauna, saida Mama ta matsa mata ta cinye duka har lemun tana yamutsa fuska alamar bata so bayan ta gama suka rakota waje ba laifi tafiyarta ta d'an k'ara warwarewa yana ganin ta fito ya mik'e ta kauda kai gefe Mama tace to gatanan sai a kiyaye ya amsa da Ok yay mata godiya kafin ya rok'eta ta d'an bashi Account details nata farko kaman bazata bashi ba tace ai ba sai ya bata wani abu ba ai aikinta ne yace ya sani just kyauta ce sannan ta fad'i mashi nan take yay mata transfer d'in 70k yace taba Nurse Bilki 20k suka hau godiya har tana zolayar shi tana in Amarya ta haihu a sanar masu ya d'an dai yi murmushin yak'e kawae suka tafi yana ruk'e da ledan magungunan da bilki ta bashi, a hankali take tafiyar yana biye da ita a haka har suka fito shi ya bud'e mata back door d'in kaman bazata shiga ba yanata kallon ta ita kuma ta juyar da fuskarta gefe saida ta ga dama sannan ta shiga ya rufe kopar koda ya zagaya maimakon ya shiga driver seat d'in sai shima ya bud'e bayan ya shiga tana ganin ya shigo ta juya mashi k'eya shiru yay yana kallon bayan kan nata Magana yake so suyi saidae ya rasa ta inama zai fara can ya nisa yace "Zaraah" shiru bata amsa ba balle ta kalle shi cigaba yay "I know i ave wronged u dat sorry isn't enough to make u forgive me but I will still use it to apologize for what I have done am very sorry Zaraah" banza ta mashi yaci gaba "nasan na cutar dake saidae billahi bada nufi hakan ya faru ba ni kaina I don't know what came over me da har hakan ya faru amman koma miye laifi na ne cos am the one who took u there" nan ma dae tsit tay sai yar sheshsheka da take yi a hankali shiru yay yana ta kallonta a cikin ranshi kuwa bai mamakin duk abunda tay mashi ba don yasan dole ma girman shi ya fad'i a idonta sigh yay yace "in sha Allah zan gyara laifin da na aikata gobe zamu yi Magana da ke but before then pls don't disclose what happened to anyone" cikin fushi ta juyo fuskarta jage jage da hawaye tace "ai in ban fad'a ma kowa ba Allah shi ya sani miyasa zaka man haka ka cutar dani bayan laifin da kasa muka aikata hakan bai isa ba har sai ka cutar da rayuwata....." Fashewa tay da matsanancin kuka still yay yana kallon ta komae ya gama kwance mashi ya rasa ta ina zai taro matsalan ta gyaru gashi shi kanshi ba lafiya gareshi ba don zazza6i tuni ya gama rufe shi k'arfin hali kawae yake k'arshe dai hak'urin yaci gaba da bata yana zasu yi Magana gobe da k'yar ya samu ta d'an tsagaita da kukan ya bud'e Motar ya fita bayan ya rufe ya bud'e driver seat ya zauna kafin ya rufe yaja suka tafi...........



_Littafin A Sanadin Makwabtaka part 2 Naira 300 ne za'a tura ma Mutum har part 1 ga mai so zai turo kudin ta wannan Account din, 1509618776, Zainab Bature Access Bank, za'a turo shedar biya ta wad'annan nos din 09013804524 ko 08169856268
[5/8, 19:28] +234 901 700 4868: *ASM Bk2046*

_Destiny may be delayed but cannot be changed...._


*DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI*





..........Tana d'aga labulan d'akin ta sauke idanunta akan gadon dake wayam ba kowa da d'an mamaki ta k'arasa shiga don ta tabbatar da abunda take gani, tabbas ba Fatuu kwance tsaye tay ta fara ayyana ina taje ne acikin ranta can tace ko tana band'aki ne, sai kuma ta raya anya dae tana can tun d'azu fa tana kitchen kuma bata ga fitowar ta ba in ba dai tun kafin ta fara aikin girkin ta shiga ba to amman mi zai sa ta dad'e har haka ta jefa ma kanta tambaya, can dae ta juya ta fita daga d'akin ta nufi hanyar toilet don ta tabbatar tun ma kafin ta k'arasa ta hango kopar shi a bud'e alamar ba mutum d'an tsayawa tay sai kuma ta juya ta nufi hanyar fita daga gida, a bakin k'opa ta tsaya ta fara k'wala ma Amadu dake cikin shago kira ya bud'e ya lek'o ganin itace yasa shi k'arasa fitowa ya nufo inda take ya tsaya yana kallonta yace gashi tambayar shi tay ina Fatuu da d'an mamaki yace "bata ciki ne?" Gwaggon ta d'aga kai tace mashi bata nan ta duba har toilet d'an jimm yay kafin yace "gaskiya ni banga ta fito ba tunda na bud'e shagon" shiru gwaggon tay tana tunanin to ina ta shiga Amadu ya katseta da tambayar ta kira wayar ta ta girgiza mashi kai alamar a'a yace to bari ya kirata ya juya ya koma shagon, bayan ya fito ruk'e da wayar ya dawo gaban gwaggon ya fara k'ok'arin kiran Fatuu lokacin da kiran ya shiga tana ta sharar bacci har kiran ya yanke bata ji ba sai da ya k'ara kira ne can a cikin bacci ringing d'in ya kai mata ta fara motsi a hankali ta fara bud'e idanunta jin wayan nata k'ara yasa ta yunk'ura ta tashi zaune tana kai hannu zata d'auka kiran ya katse, bayan ta d'auka ta duba mai kiran nata har saida gabanta ya fad'i ganin sunan Kawu Amadu tana haka sai gashi ya sake kira tay shiru kaman bazata d'aga ba can dai tay picking ta kara ta a kunne daga can bangaren Amadun ya kira sunanta ta amsa a hankali ya tambaye ta tana ina ne tace mashi ta tafi Makaranta ya maimata abunda tace jin haka yasa ya mik'a ma gwaggo ta amsa ta kara a kunne ta kira sunanta itama ta amsa mata had'i da gaishe da ita tace "naji kin ce kina Makaranta lafiya kika tafi baki fad'a ma kowa ba?" Had'iyar abu tay ta fara tunanin k'aryar da zata mata cikin yar rawar murya tace "d..dama na manta ban fad'a maki ba da yake jiya baki nan na dawo akwae wani malamin mu to ba'a cika gane abunda yake koyawa ba ana ta mashi complaining shine ya ware mana lokaci a cikin wannan weekend d'in da safe yace zai yi mana lesson tunda lokacin da yake dashi cikin ranakun aiki bai isar shi ya rink'a yin bayani sosae yadda za'a gane" gwaggo dake sauraronta tace "to yanzu sai yaushe zaki dawo?" shiru Fatuu ta d'anyi kafin tace "sai Allah ya kaimu Juma'a"

"Har sai Juma'a kuma ba da safe zaku rink'a yin lesson d'in ba in aka gama ai sai ki taho gida ko?" Fatuu tace "eh amman da yamma ma zamu yi group Assignment" sauke yar ajiyar zuciya gwaggon tay tace "to amman shi yayan ki fa daya maido ki yace zai rink'a kaiki baki tunanin zaiga kaman kin k'i jin Maganar shi ko baki gode ba" d'an runtse ido Fatuu

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login