Showing 240001 words to 243000 words out of 512766 words
Chapter 81 - Asanadin Makwabtaka Book 3 Hausa Novel Complete
Unknown
27 Dec 2024
1658
bayan ya gama Jidderh tace to yanzu ai sai a kawo Fatuu nan ayi shagulgulan biki ko, shiru Haisam d'in yay kawae Fuskar shi a sake ganin baice komai ba yasa a shagwabe Jidderh tace "Big bro talk pls, yaushe zaka kawo ta sai mu tsara programs da zamu yi" d'an murmushi yay ya girgiza mata kai kafin slowly ya furta ba sai anyi wannan ba tunda an wuce wurin, tura baki tay a shagwabe tace gaskiya basu yarda ba su suna so ya za'a ce ayi Auren ba wani celebration, Aunty ce itama tace gaskiya ya kamata ayi koda bada yawa ba Saboda she needs to be introduced as one of the Family tunda duk ba'a san da Auren ba, Mom d'in shi ma ta goyi bayan ayin ba yadda Haisam ya iya don an fi k'arfin shi yace su tsara abunda suke son yi, nan suka shiga tattauna abunda yakamata ayi Jidderh sai lissafo abubuwa take cike da zumud'i, Senator ne yasa baki yace tunda ba yanzu aka yi Auren ba yana ganin ba sai an yi abubuwa ba sosae dama ya lura Angon kamar bai so ko don kar a kalle mashi mata ne ko kuma kar a wahalar da ita oho gaba d'aya sukai dariya shima Haisam d'in murmushi yayi, k'arshe dai abu biyu suka yanke zasu yi Walima wadda zata kama ranar Friday ayi kaman yinin biki sai washe gari ayi Dinner party, ita Jidderh hakan bai isheta ba sai yamutsa fuska take tana shagwabar gaskiya a k'ara ita kenan Sis Zarah d'in baza ayi Ethiopian Night ba dasu Arabian Mom d'in su na yar dariya tace tayi hak'uri a barshi hakan,
"Yanzu sai Maganar lefe ko, shi banji anyi Maganar shi ba" Senator ne yayi Maganar, Aunty tace "Eh nima ina niyyar yin Maganar shi" Mom d'in su ce ta kalli Haisam tace ya za'ayi lefen, yana a d'an kishingid'e yace suyi yadda ya kamata, Aunty tace "dama k'awata Hajiya Sakeena yanzu haka tana Dubai ina ganin duk abunda ake so za'a iya tura mata in sha Allahu nasan zata yi komai yadda ake so ta aiko batare da 6ata lokaci ba in ma ba yanzu zata dawo ba, sannan ga Zee Collections ma itama za'a iya yi mata magana sai a za6i abubuwan da ake so ta aiko da su" sosae hakan yayi ma kowa nan suka shiga tattaunawa kan yawan akwatunan da za'ayi kowa na fad'in yadda yake ganin yakamata Jidderh tafi kowa fad'in masu yawa a hakikance take fad'in Sis Fatun fa big girl ce gaskiya ayi mata masu yawa har saida Senator yasa baki yana yar dariya yace ya lura dai tana ji da wannan sabuwar Yayar tata, bayan sun gama yanke yawan akwatunan da za'ayi Aunty ta tambayi Haisam lokacin da zai kawota don ai fixing date da za'ai programs d'in, sanar dasu yay zata fara Exams ne next week kuma bai san date d'in da zasu gama ba sai dai ya tambaye ta tace Ok, daga baya suka shiga tattauna ankon da zasu yi Jidderh tace yakamata a kira Aunty Laila ta za6a tunda tasan takan gayu sosae duk suka yi dariya su Yasmeen da twins sai murna suke za'a sake yin biki a gidan, Haisam ne ya tambayi Shikenan ko akwae wani abu Mom d'in shi tace in aka gama tsara komai za'a mashi magana ya furta Ok daga haka ya mik'e yay masu saida safe Senator na dariya yace "halan Amarya tayi kira" faffad'an murmushi Haisam d'in yay ya mik'a mashi hannu Senator d'in ya dunkule na shi ya buga mashi ya wuce ya nufi upstairs yana murmushi duk suka bi shi da ido su Mom d'in suma dariya suke, gaba d'aya sun lura da canzawar da Haisam d'in yayi tun bayan da yazo yayi wani irin Fresh daka gan shi kasan yana cikin nishad'i, yana shiga part d'in nashi bedroom ya wuce har zai kira Fatuu sai kuma yayi tunanin ya fara yin wanka sai ya kwanta gaba d'aya ya nufi toilet, within 30 minutes ya gama shiryawa cikin sleeping dress, a bakin gado ya zauna ya kai hannu ya d'aukko wayarshi dake ajiye a gefe, Fatuu ya kira lokacin suna a parlor ita da Mino suna yin kallo basu dad'e da dawowa daga part d'in Hajiya ba, bayan tayi picking ya sanar da ita zasu yi Video call cike da Farinciki tace mashi to, dama tunda ya tafi sau d'aya sukai Vedio call d'in sai dai suna yin waya akai akai, mik'ewa tayi tace ma Mino in ta gama ta kashe kayan kallon ta nufi hanyar Bedroom da sauri...
Next Day......
Washe gari Friday bayan sun gama shirin Makaranta harda Mino ma anan ta shirya suka nufi parking space. Lokacin da akai ma su Fatuu break ganin tayi zaune yasa Fauzy ce mata ta taso suje su yi break kawae sai ta fad'a jikinta a shagwabe tace "Wayyo Fauzy miji na, don Allah ya dawo wllh ina kewar shi" dariya Fauzy ta sa dama kullum sai tayi mata magana akan mijin nata tace "to mai miji kiyi hakuri zai dawo ai" d'agowa Fatuu tay tana dariya itama, Fauzyn ta k'ara cewa "da alama dai Magana ta zata tabbata in exams tazo inaga labarin mijin ki zaki rink'a rubutawa banda zana shi dana ce" lumshe ido Fatuu tay tare da langa6ar da kai hannunta dafe da k'irji Fauzy ta kai hannu ta 6aka mata bugu a shoulder, bud'e idon Fatuu tay tana dariya tace "Fauzy ina rok'on Allah ya baki miji wanda ya iya buga love irin Ya Haisam wato gaba d'aya jin ki zaki rink'a yi a wata duniya ta daban kina rayuwa mai cike da nishad'i" sosae Fauzy ke dariya tace "na lura dai giyar soyayyar Ya Haisam na bugar dake sosae da alama Maganar Aunty Mareeya akan ki ta faru wato ke kika zaucen kullum baki da magana sai ta mijin ki" cigaba da dariya Fatun tayi Fauzy ta k'ara cewa "Wai ni anya ma kina karatun jarabawa kuwa sosae a gida?" Kashe mata ido tay a hankali ta furta soyayya bata bari, jinjina kai Fauzy tay tana dariya tay yar k'wafa tace sai ki rinka rubuta hakan ai a jarabawar, da kuwa an kad'a k'eyar ki, murmura idanu tay tace "ba Shikenan bama sai inje in ta shan soyayya ta da hujja in muka gama soyewa har muka kone bayan mun koma US sai in yi karatun" dariya sosae Fauzy ta saka tana fad'in ina Magana kuma in aka k'one itama Fatun dariyar take Fauzy ta mik'e tana fad'in ta taso suyi sauri su dawo su k'ara duba book kafin a shigo yi masu Test d'in da zasu yi tace to ta mik'e.
Wuraren k'arfe d'aya suka tashi da yake ranar juma'a ne, duk suka goya jakunkunan su suka nufi hanyar fita daga class d'in, suna fitowa wayar Fatuu ta fara ringing ta kai hannu cikin aljihun rigarta ta d'aukko ta, tana dubawa taga sunan Hubby ya bayyana ta kalli Fauzy dake kallonta ta kashe mata ido tace mijinta ne ke kira Fauzyn ta d'an yi murmushi kawae, picking tay ta kara wayar a kunne a shagwabe ta kira sunan shi shima kiran sunanta yay taji yace yana a inda yake tsayawa, cikin rashin fahimta ta tambayi inda yake tsayawa a ina yace a School d'in su, waro ido tay with surprise written boldly all over her face tace "Are u serious Hubby!" tana jiyo sautin murmushin shi yace mata ai tasan bazai mata irin wannan wasan ba, cire wayar tayi cike da murna ta kalli Fauzy tace mata mijinta ya dawo gashi ma har yazo d'aukarta, itama Fauzyn tayi mamaki da sauri ta kamo hannunta tace tazo suje su gaisa sai faman washe baki take ta kasa 6oye murnar ta, sosae take sauri tana ruk'e da hannun Fauzy itama dole ta rink'a yin saurin tana fad'in kar tasa su fad'i don Allah, tana hango Motar ta saki hannun Fauzy ta nufeta da sauri sauri gudu gudu Fauzy nata dariya tana girgiza kai, k'opar gaba ta bud'e tana sa kai wani fitinannan k'amshi tare da ni'imtaccen sanyin Ac suka tarbeta, had'a ido sukai dashi yana sanye da farar shadda sumar nan tasha gyara, k'ayataccen murmushi ya sakar mata itama murmushin take mashi ta matsa kusa dashi ta kai duka hannuwanta ta tallabo fuskar shi batai wata wata ba ta had'e lips d'in su, da k'yar suka raba fuskokin nasu breathing rapidly sai murmushi suke ma juna, saida ta samu natsuwa sannan ta tuna da Fauzy da sauri ta lek'a ta hango ta daga d'an can nesa ta tsaya, da hannu tay mata alamar tazo ta nufo Motar tana d'an hararar Fatun had'i da d'an murmushi, a bakin kopar ta tsaya Fatun ta juya tace mashi ga Fauzy zasu gaisa ya jinjina kai, da hannu tay ma Fauzyn alamar tazo ta duk'o da kanta tace mashi ina wuni fuska a sake ya amsa ta sake ce mashi an dawo lafiya nan ma ya amsa, janye kan tay Fatuu na murmushi tace mata sai Monday wani kallo Fauzyn tay mata itama tana murmushin kafin tace to sai sun yi magana, tana maida kai cikin Motar zata rufe Haisam d'in ya mik'o mata kud'i yan dubu dubu sabbi dal yace ta bata, da sauri ta lek'o lokacin Fauzyn har ta tafi Fatun ta fito daga cikin Motar tare da kiran sunanta da d'an k'arfi, tsayawa tay ta juyo Fatun ta nufota, tana zuwa gabanta ta mik'a mata kud'in tace gashi inji Mijinta har saida Fauzyn ta d'an bud'e ido ganin kud'in nada d'an yawa sai kuma ta amsa tana murmushi tace "tukuicin tura sako ne aka bani kenan" gaba d'aya sukai dariya daga baya tace tay mashi godiya, har Fatun zata juya Fauzy tace mata kar dai ta manta ran Wednesday zasu fara Exams sosae Fatuu ta saki dariya kafin ta juya ta tafi, Motar ta koma ta shiga bayan ta rufe ya ja suka tafi hannun shi d'aya ruk'e da nata nan fa ta shiga zabga mashi shagwaba tana fad'in miyasa bai fad'i mata yau zai dawo ba kuma ko yau da safe ba saida sukai waya ba, yana ta murmushi idon shi akan hanya, d'an kallon ta yay yace kawae yana son bata Surprise ne, tura baki tay tace amman daya fad'i mata ai ta shirya, tambayarta yay wane irin shiri tace tayi gayu mana harda kitso da lalle har saida yay yar dariya, ganin ta d'an d'aure fuska ita ala dole fushi take yasa shi d'an matsa hannunta ta kalle shi shima kallon ta yay yace kada ta damu ko bata yi su ba a koda yaushe k'ara mashi kyau take har bata san lokacin data saki murmushi ba ta d'ago hannunshi dake ruk'e da nata tay pecking d'in shi ya d'an lumshe ido tare da furta "Day's my Baby", A wani babban Eatery ya tsaya yace mata yana zuwa ta d'aga mashi kai, tana ta kallon shi ta glass har ya shiga cikin wurin, after some minutes ya fito hannun shi ruk'e da yan manyan ledoji masu d'auke da tambarin wurin, back door ya bud'e ya saka bayan ya rufe ya koma cikin Motar yaja suka tafi. bin hanyar da suka bi tay da kallon ganin ba wadda suke bi bace, sai daga baya ta fahimci G.r.a suka nufa........
*ASM 078*
~_*✊💋BOSS LADIES WRITERS💋✊*_~
*DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI*
........Ganin inda zasu yasa ta fara k'ok'arin raba hannun su tana fad'in bari ta kira Tk ta fad'i mashi ba sai yaje d'aukota ba ya d'aukko Mino kawae, ba tare daya saki hannun ba yace mata sun yi magana dashi tace Ok, suna isa Officer ya bud'e masu Gate ya shiga da Motar, a bakin entrance ya parker Motar Fatuu ta juya suka had'a ido a tare suka sakar ma juna murmushi har lokacin yana ruk'e da hannun nata, jingina kan shi yay da headrest idanun shi a d'an lumshe ya furta mata zaije Masallaci ya dawo ta jinjina mashi kai, cewa yay bari ya kama mata ledojin Abincin tace ya barshi zata d'auka still da murmushi akan Face d'in shi ya tambayi zata iya, yar dariya Fatun tay tace to abunda ba wani nauyi ne da su ba kuma ko suna da nauyin ai zata iya d'auka ya jinjina kai yace ya manta Babyn shi mai k'arfi ta iya bugun mutane Fatun tasa dariya, saida yay pecking hannunta sannan ya saki tace mashi sai ya dawo, bud'e Motar tayi ta fito shima fitowa yayi ya zagayo side d'in da take har ta bud'e kopar bayan ya duk'a ya fiddo mata ledojin ta amsa tana murmushi ta furta "Thanks My Hubby" jawota yay jikinshi suka kafe juna da ido suna d'an murmushi can Fatuu ta hura mashi iska a fuska ya d'an kikkafta ido tasa dariya tace yaje kar ya makara a gama sallar bai samu ba, sakin ta yay ya ce mata sai ya dawo ta d'aga mashi kai, har ya juya tace yayi masu Addu'a sosae ya d'an juyo ya jinjina mata kai kafin ya cigaba da tafiya, tsaye tay hannunta d'aya ruk'e da ledojin ta d'aga d'ayan tana mashi bye bye, bayan ya juya Motar ta kalli gate tsayawa yay ya sauke glass da hannu yay mata alamar ta shiga ciki tana murmushi ta juya tana yi tana waiwayen shi har ta shige sannan ya ja Motar,
Tana shiga ciki corridor d'in da zai kaita Bedroom d'in shi ta nufa, tura k'opar tay ta bud'e ta shiga, tana shiga ta tsaya tana k'are ma Bedroom d'in kallo tsaf tsaf da shi ga wani sanyi mai had'e da daddad'an k'amshi sun karad'e shi gadon ya sha lallausan bedsheet kai kace ba d'akin namiji bane, wurin kujeru ta nufa ta d'aura ledojin akan c-table kafin ta sauke bag pack d'inta ta aje a k'asa gaban kujera itama ta zauna akan kujerar fuskarta a sake tana k'ara bin d'akin da kallo, tunanin abunda ya kamata tayi ta shiga yi zuciyarta ta bata ta yi salla itama, mik'ewa tay ta nufi hanyar corridor d'in da toilet yake, bayan ta shiga cikin toilet d'in sai kuma ta canza ra'ayi ta yanke tayi wanka kawae, after some minutes ta fito cikin Bedroom sanye da bathrobe d'in Haisam har ta kusa kai mata k'asa ta nufi gaban mirror, kallon kanta ta shiga yi tana d'an murmushi ita kanta taga canzawar da ita fuskarta tayi wani sumul tayi wani Fresh, mai ta fara shafawa bayan ta gama ta fesa turarurruka ta goga roll on, tunanin to wane kaya ma zata sa ta shiga yi don bai kamata ta zauna da bathrobe d'in ba, zuciyarta ce ta raya mata taje ta duba cikin kayan shi k'ilan ta samu wanda zata iya sakawa, laudary room inda press d'in shi take ta nufa, bayan ta bud'e ta fara bin kayan ciki da ido ganin wurin su shadda ne yasa ta rufe ta bud'e d'ayan side d'in anan taga k'ananun kaya suke, hannu ta sa ta fara d'add'agawa idanunta ne suka kallo wata jar riga a linke ta raya bari ta duba k'ilan babbar t-shirt ce in zata d'an saukko mata sai ta saka ta kawae, bayan ta d'aukko tana warware ta ba shiri ta waro ido da sauri ta kai hannu ta rufe bakinta alamar Al'ajabin ganinta, cire hannun tay ta fara murmushi ganin jar rigar data sa ranar da suka je dinner party d'in abokin shi har suka wuto nan, tun lokacin da abun ya faru bata bi ta kan rigar ba tasa jallabiyar ta kawae da yake mai zip ce ta tafi, rigar sai sakin k'amshi take ta yanke bari ta saka ta ma kawai, cikin Bedroom d'in ta dawo ta tsaya a gaban mirror ta fara kiciniyar sakata dama ko wanccan lokacin da k'yar ta shige ta don ma tana roba, yanzu ma ta shigeta saidae ta kamata kaman lokacin data sakata da farko, sosae shape d'inta ya fita ita dad'in hakan taji don dama tana son kaya su kamata, bayan ta gama d'aukar bathrobe d'in tayi taje ta bazata a laundry kafin ta dawo gaban mirror ta fara gyara gashinta, tana cikin sharce shi a cikin ranta ta shiga raya yakamata tayi kitso duk da ba son kitson take ba amman ko rannan saida gwaggo tayi mata Maganar kitson har tace zata yi mata k'arshe ta zille ba'ayi ba, tana haka taji an turo k'opar da sauri ta kai idon ta, shine ya dawo aikuwa da gudu ta nufe shi kafin ta isa ya bud'a mata hannuwan shi tana isa ya kamata ya d'aga ta sama, sosae hakan ya burge ta sai dariya take shima dariyar yake fararen hak'oran shi har sun bayyana, sauke ta yay ya rungumota jikinshi ta d'aga kai tana kallon shi suna sakar ma juna murmushi a shagwabe tayi mashi sannu da zuwa cikin cool voice d'in shi yace yauwa, tambayar shi tay yayi masu Addu'ar ya d'aga mata kai alamar eh tace to wace iri, d'an jimm yay yana mata murmushi sai kuma ya rankwafo da kanshi ya kai bakin shi saitin kunnanta ya rad'a mata wadda yayi masu ba shiri ta kife fuskarta a jikinshi tana dariya, d'ago Fuskar tata yay sai d'an runtse ido take alamun kunya, bin fuskar yay da kallo yana jin wata irin sabuwar k'aunarta acikin zuciyar shi, bayan ta bud'e idanun tambayar ta yay taci Abincin ko ta girgiza mashi kai alamar a'a tace shi take jira ya bata a baki yace Ok, kama hannun ta yay suka nufi ciki anan take ce mashi bai ga rigar data saka ba yay murmushi ya had'eta da jikin shi yace ya gani tayi kyau, wurin kujerun suka nufa ya saketa, matso da c-table d'in yayi a gaban kujera bayan ya zauna ya mik'a ma Fatun hannu ya ruk'ota, a saman jikin shi ya d'aurata tana ta murmushi ya kai hannu ya fara bud'e ledojin Abincin, tambayar shi tay a ina kitchen yake ta d'aukko plates slowly yace ta barshi ai zasu iya ci haka, Fried rice suka fara ci shi yake bata a baki tace ya barshi