Showing 273001 words to 276000 words out of 512766 words

Chapter 92 - Asanadin Makwabtaka Book 3 Hausa Novel Complete

Unknown   

27 Dec 2024

1641

ya d'an haska cikin Motar fuskar shi ba d'igon annuri ya mik'a mata hannu yace ta bashi wayoyin hannunta, da sauri ta mik'a mashi saida ya kashe su gaba d'aya sannan ya bude glove box ya saka su, ba tare da ya kalleta ba ya juya ya bud'e Motar bayan ya fita ya maido k'opar ya rufe, zuru tay tana kallon shi dishi dishi ta glass d'in kopar daya fita har saida ta daina hango shi sakamakon wasu da suka zo wurin shi suka tafi bata san ina sukai ba ta dai daina ganin su, maida kanta tay jikin headrest tay shiru ta shiga tunanin k'ilan ana can anata nemanta tunda ba wanda yasan ta fito sai Ya Haisam kuma shi tasan ba lalle in zai fad'i ma Fatuu ba cewa bata gidan ba kaman yadda ta sanar mashi, shiru shiru har kusan bayan mintuna talatin bai dawo ba gaba d'aya Fauzy ta gama gajiya ga wata bak'ar yunwa da take ji sakamakon bata ci Abincin dare ba ga zafi ya ishe ta don ma ta bud'e glass d'in gefenta, gaba d'aya ta rasa mike mata dad'i sai yamutsa fuska take tana yan kalle kalle ta cikin Motar can ta kai hannuta a d'arare ta bud'e k'opar Motar, zuro kanta tayi tana k'are ma wurin kallo ba K'aramin had'uwa yay ba iya fitilun dake sakin haske a wurin abun kallo ne, kai idonta tay cikin wata had'add'iyar rumfa mai girma wadda mutane da d'an yawa ke acikinta, bazata iya gane Mutanen Musulmai bane ko Christians daga yanayin shigar su, wasu cikin su na tsaye suna buga snooker mata da maza yayin da wasu ke a zaune saman k'ayatattun kujeru zagaye da table suna kallon su yayin da saman table d'in ke d'auke da abubuwan ciye ciye dana sha wanda bazata iya gane ko su miye ba, daga gefen su kuma wasu ne ke yin ludu wasu kuma na yin wasan chess, ta d'an d'auki lokaci tana kallon su don yanayin wurin akwai d'aukar hankali can ta idasa fitowa daga cikin motar a tsorace gaba d'aya tayi kalar rashin gaskiya, jingina da kopar Motar tay ta na kallon cikin wurin Mutane sai kai da kawowa suke suma dai duk kalar irin shigar na cikin rumfar gare su wasu na fitowa daga cikin ginin wurin wasu kuma na shiga daga can gefen wurin wani irin k'aton swimming pool ne an k'awata shi mutane sai wanka suke mata da maza, daga inda take ta fara k'ok'arin ganin sunan wurin dake a sama yana ta sakin walwali saidae ta kasa gane mi aka rubuta dama bata gani ba da zasu shigo, gajiya tay da tsayuwar ta koma cikin Motar taja kopar ta rufe, shiru tay tana ta yamutse yamutsen fuska don Allah kad'ai yasan irin yunwar da take ji, wasa wasa ta shafe fin awa amman bai fito ba lokacin tuni ta fara yin k'walla abun har ya kai ta fashe da kuka a fili ta shiga fad'in "Wllh wannan mutumin mugu ne, in ya yafe man ba sai ya maida ni gida ba amman ya jibge ni a cikin Mota sai kace ba Mutum ba" haka tay ta sambatu. Sai wuraren k'arfe d'aya saura yan mintuna ya dawo, yana shiga cikin Motar idanun shi suka sauka akan Fauzy data langa6ar da kai, hannu ya kai ya kunna fitilar Motar haske ya gauraye cikin Motar ya bi ta da kallo, shi gaba d'aya ya manta ma da ya barta a Motar, da ganin fuskarta ta sha kuka da alama ma tana cikin yi baccin ya d'auketa don fuskarta duk jirwayen hawaye kallabinta data yafa ya zame, bayan wani lokaci ya fara k'ok'arin tada ita da fad'in "Hey...." Shiru bata ko yi motsi ba ya k'ara cewa hakan nan ma bata Motsa ba, hannu ya kai ya fara d'an bubbuga shoulder d'in ta lokacin ta fara motsi, a hankali ta fara bud'e idanuwanta tana yi tana k'ara rufe su cikin husky voice d'in shi ya furta "Wake up" aikuwa da sauri ta bud'e idanun gaba d'aya ai koda tay arba da Fuskar shi ba shiri ta shiga gyara zaman ta, bin juna sukai da kallo duk tayi wuri wuri da ita can k'walla suka zubo mata sharr da sauri ta juyar da fuskar ta daga barin kallon shi tana d'an yi sheshsheka a hankali,

"da wa ya buge ki?" taji ya furta, shiru bata bashi amsa ba bata kuma kalle shi ba, ya k'ara furta "am I not asking you?" Sai lokacin ta juyo ta girgiza mashi kai alamar ba kowa, d'age gira yay ya furta "shi wannan d'in na miye?" ta gane kuka yake nufi ta fara motsa baki ta kasa yin magana, ce mata yay kar ta k'ara sa shi ya maimaita mata magana ya k'ara tamke fuska da sauri cikin rawar murya tace mashi yunwa take ji, bin ta yay da wani kallo ganin haka yasa cikin yar in ina tace mashi bata ci Abincin dare ba, ta6e baki ya d'an yi ya janye idanunshi daga barin kallon ta ya koma kallon gaban shi, bin gefen fuskar shi mai d'auke da kwantaccen saje sumar tayi luff tayi da kallo, juyawa yay dama bai datse kopar ba ya fita tana ta kallon shi ya maido kopar ya rufe, maida kanta tayi jikin kujera tay shiru ba abunda take gani sai fuskar shi, bayan wasu yan mintuna taji za'a bud'e Motar da sauri ta kai idonta, shine ya bud'e ya shigo hannun shi ruk'e da abu, bayan ya zauna ya mik'a mata d'an babban cake ne nad'e a leda sai lemu irin na cikin kaman d'an cup da straw manne a jikinshi, a hankali tayi mashi godiya bai ko kalle ta ba ya maida kan shi jikin headrest, ruk'e su tay a hannu bata da niyyar fara sha sai yan kame kame take tana haka taji yace zasu kwana ana ne, abu ta had'iya kafin ta fara k'ok'arin ciro straw d'in jiki, bayan ta saka a cikin lemun ta bud'e cake d'in ta fara ci tana yi tana satar kallon shi, bayan ta d'an ci da yawa ta rage sauran duka a hankali ta juya ta kalle shi ya d'age kan shi idanun shi a rufe, bin fuskar shi tay da kallo Idan tace ga wani abu da bai yi ba a fuskar tashi to kuwa ta shirga babbar k'arya, tana cikin kallon nashi ba tare data ankara ba ya bud'e idanun ya kallo ta, in ina ta kama yi tace mashi ta gama ya kallo sauran data rage a hannunta ba tare da ya d'ago ba kawai sai gani tay ya maida idanun ya rufe, bayan d'an lokaci taji yace "Don't waste my time, else zan barki anan ne" ai tana jin Haka da sauri ta kai lemun baki taci gaba da sha, saida ta cinye komai sannan ta kalle shi tace ta gama shiru kaman bai jita ba ta k'ara d'an d'aga murya ta maimaita ta gama, slowly ya fara bud'e idon ya d'ago daga jikin kujerar ya fara k'ok'arin tashin Motar yana haka yace mata wannan d'in wani zata kai mawa ta d'an girgiza kai kafin tace bata san ina ake aje wa ba ya juyo yay mata wani kallo da sauri ta juya ta bud'e kopar ta wurga ledar da d'an cup d'in, rufe kopar yay daga haka ya fara yin reverse bayan ya fita daga wurin ya shiga juya kan Motar Fauzyn nata kallon wurin har lokacin da mutane kusan ma yafi cika yanzu.

Lokacin da suka iso gidan kusan k'arfe d'aya da rabi, a bakin Entry Hall ya parker Motar Fauzy ta bi shi da ido gudun kada tayi wani laifin, shiru kaman ba zai tanka ba can yace "Get out of my car" juyawa tay zata fita sai kuma ta dakata ta juya a d'arare tace mashi don Allah ya bata wayar kawar tata ta kai mata, sai da ya mula sannan ya kai hannu ya bud'e wurin da ya saka ba tare daya kalleta ba yace ta d'aukko, hannunta har d'an rawa yake ta kai shi ta d'aukko ta Fatun kawae a fusace yace waye ta bar ma d'ayar ta sake kai hannu ta d'aukko, d'an kallon shi tay tayi mashi godiya yay banza da ita jiki a sanyaye ta juya zata bud'e k'opar kaman daga sama taji yace ta sani dole zata biya shi damage d'in da tay ma wayar shi, juyowa tay fuska a yamutse tace "Don Allah kayi hakuri...Na fad'i maka wllh Allah ba zan iya biyan ka ba, d'age shoulder yay alamar bai dame shi ba kafin yace ta fita, bud'e k'opar tay bayan ta fita ta juyo idonta a kanshi ta kai hannu ta rufe mashi, nufar shiga cikin gidan tay tana yi tana waiwayen shi har saida ta kusa shigewa sannan taga ya ja Motar,

Lokacin da ta shiga main parlor d'in tsit kowa yayi bacci, kopar baya ta nufa tana waige waige tsoron ta kar wani ya ganta ta dawo a lokacin duk da bata san k'arfe nawa ba amman daga yanayin da ta ga garin ta fahimci dare yayi sosae, har ta fita baya ko motsin mutum bata ji ba ta nufi part d'in da suke, lokacin data shiga cikin parlon kwalam yake da sauri ta nufi d'akin su, sai da tay d'an jimm kafin ta sa hannu a hankali ta d'an tura kopar, d'an lek'awa tay ta hango kowa yayi bacci sannan ta k'arasa tura kopar ta shiga, cikin tafiya mai kaman sand'a don kar tayi sauti wani ya tashi ta nufi cikin d'akin, a bakin gado ta zauna tana kallon su Haulat dake ta shan bacci, maido idon ta tay tana kallon gabanta tayi shiru zuciyarta ta shiga tunano mata dukkan abun da ya faru tsakanin ta da Sameer, tunano lokacin da yake mata magana gab da ita ta shiga yi yadda hucin bakin shi mai had'e da k'amshi ya rink'a bugun fuskarta, kokonton kodai ba giya bace ya sha ta shiga yi wata zuciyar ta raya mata to ita tasan yadda giyar take ne ai k'ilan kala kala ce akwae mai kamshi, tunano lokacin da ya kawo fuskar shi ya had'e da tata tayi har bata san lokacin data rufe ido ba sai kuma ta bud'e da sauri kawae sai ta saki murmushi, wasi wasi ta shiga yi na inda ta amince mashin da gaske zai yi mata wani abu ko kuwa, wata zuciyar ta k'ara raya mata kawai dae k'ilan hakanan yay mata hakan amman ai bata kai yayi hakan da ita ba in ma yana yin, har saida ta d'an ta6e baki, tunanin ko mi yaje yi a wannan wurin ta shiga yi tana raya wurin kaman Club a yadda ta fahimta kuma dai tasan ana cewa ba abun arzik'i ake ba a can, a hankali a fili ta furta "ko ma ina ruwa na" ajiyar zuciya ta sauke ita kanta tasan ba K'aramin firgici ya sata ba, tunanin ko ya yafe mata ko kuwa da gasken yake sai ta biya shin kamar yadda ya fad'a mata yanzu da suka dawo ta shiga yi can ta ta6e baki a fili ta furta "ni dai ai na fad'a mashi gaskiya bansan taya zan biya shi ba kuma" shiru tay tana kallon wuri guda can tay murmushi tunowa da abubuwan daya kawo mata taci ta raya ashe yana da kirki, kunna wayoyin tayi gaba d'aya nan taga ashe a fly mode yasa wayarta ta raya k'ilan ma Aunty Mareeya ta sake kiran ta, ta d'an d'auki lokaci a zaunen can ta tuna da ko sallar isha bata yi ba ta mik'e ta nufi hanyar toilet bayan ta aje wayoyin, saida tayi wanka ta d'auro alwala ta fito d'aure da kallabin ta, wurin akwatin kayanta ta nufa, doguwar rigar bacci ta fiddo bayan ta saka ta d'aukko Hijab ta wuce inda abun salla yake ta d'aukko ta shimfid'a, bayan ta gama sallar tayi Addu'a anan ta kwanta ba tare data cire Hijab d'in ba, gaba d'aya bacci ya k'aurace ma idanunta tay shiru tana kallon wuri guda can ta rufe su nan take zuciyata ta shiga tunano mata sufar Sameer a haka har bacci ya kwashe ta.

Washe gari bayan sun tashi sallar Asuba kowa ya ganta sai ya tambayi ina taje ne jiya ba'a kwanta da ita ba cikin kama kai take basu amsa da sun fita ne bayan sun dawo kuma ta tsaya d'akin Jidderh fira, bayan ta gama sallar ta d'auki wayar Fatuu don ta kai mata, lokacin data je d'akin su Jidderh ma basu dad'e da gama sallar ba sun koma gado bayan sun gaisa ta tambaye ta Fatuu nan ta sanar mata ba a gidan ta kwana ba, bayan ta fito zata koma part d'in su a ranta ta shiga raya dama dalilin kiran da Ya Haisam ke ta mata kenan tay d'an murmushi, tana shiga cikin parlon suka had'e da Aunty Mareeya tana sanye da doguwar rigar bacci kanta sanye da hula har saida gaban ta ya fad'i, tana ganinta ta tsaya Fauzyn ta tunkareta tana k'ak'alallen murmushi, gaishe da ita tayi ta amsa tana mata wani kallo tace mata ina taje jiya, rasa amsar da zata bata tayi ta fara yan kame kame, tunanin ko tace mata tare suka fita da Zarah tay sai kuma ta tuna da har yanzu ita bata gidan k'ilan kuma Aunty Mareeyar tasan ba gidan zata kwana ba, hannu ta kai ta kama kunnanta tace "fad'i man ina kika je jiya har aka kwanta baki dawo ba, kuma na kira wayar ki baki d'aga ba k'arshe ma dana sake kira sai kika kashe" yamutsa fuska Fauzy tay alamar tana jin zafin kama kunnanta da tayi, hakanan taji bata son fad'i mata abunda ya faru don bata san ya zata d'auki zancen kai ta wani gida da Sameer yayi ba, k'ara murd'e kunnan tayi ta saki yar k'ara tace zata fad'i mata don Allah kar ta tsinka mata kunne, cikin yar in ina tace mata dama da wani abokin Ya Haisam ne suka fita, waro ido Aunty Mareeya tayi ta saki kunnan nata da alamun Mamaki tace "kuka fita ku ka je ina?" tana kikkafta ido tace gari suka fita ya zagaya da ita, hannu Aunty Mareeya ta hau tafawa da alamun d'an tashin hankali tace zaga gari shine har wurin sha biyu bata dawo ba don ma taji Zarah itama bata nan shiyasa hankalinta ya d'an kwanta tayi tunanin suna tare, abu Fauzy ta had'iya a ranta ta raya don ma bata san k'arfe nawa ta dawo ba, daga Maganar da Aunty Mareeya d'in tayi ta samu k'aryar da zata mata tace ai daga zaga garin wurin su Zarah d'in suka wuce, tambayar ta ina Zarah d'in taje tayi tace suna tare da Ya Haisam a wani gidan su, gaba d'aya tayi kalar rashin gaskiya don hakanan ta fad'i hakan bata san ina Fatun suka je ba, murmushi Aunty Mareeya tay tace "Uhm su Malam miskili kenan gaba d'aya yana neman takura ma Yarinyar Mutane" murmushi Fauzy tay cikin alamun kunya tace "to Aunty Mareeya ba duk ke ce ba" hannu ta kai zata kai mata bugu tana fad'in ita uban mi tayi Fauzy ta goce tana dariya, tambayar ta tay shi wanda suka fitan cewa yay yana son ta Fauzyn ta d'an girgiza kai tace a'a kawae dai sun fita ne, harara ta wurga mata tace ita kuma ga mara aji kawai sai ta bishi zararai zararai Fauzyn tay dariya,

"Amman gaskiya Fauziyya yakamata kiyi saurayi ko kema Kya zo kiyi aure don Allah Zarah bata burge ki ba" tana murmushi tace "ta burge ni sosae Aunty, kuma dama tun lokacin data tare naji nima ina son in yi auren to amman ni fa har yanzu banda saurayi...." A hasale Aunty Mareeya ta katse ta "ta gidan uban wa zaki saurayin bacin har yanzu kin kasa cire wanccan shashashan mayaudarin daga cikin Zuciyar ki" yanayin fuskar Fauzyn ne ya canza cikin karyayyar murya tace "Aunty dole fa Mujaheed ya tsaya man a rai ko ya ya ne, kar ki manta bansan soyayyar kowa ba sai tashi, tun bansan kai na ba nasan miye soyayya ya koya man son shi daga shi kuma ban k'ara son wani abu, tsawon lokaci muna tare" idanunta har sun ciko tab da k'walla, ta6e baki Aunty Mareeya tay tace "Shikenan kada Allah yasa ki cire shi daga ran naki kiyi ta zama kar ki yi aure har mahadi ya bayyana" tana gama Maganar ta juya zata tafi da sauri Fauzy ta k'ank'ameta ta baya ta saki kuka tana fad'in don Allah tayi hak'uri wllh a yanzu a shirye take da tayi Aure indai ta samu mai son ta tsakani da Allah kuma itama taji tana son shi, juyowa tay ta rungume ta ta kai hannu tana goge mata hawayen tana fad'in ya isa, bayan ta yi shiru tace "Yanzu shi wanda kuka fita d'in da gaske bai ce yana son ki ba?" Kai ta d'aga mata ta sake cewa "to in yace yana son ki zaki amince" shiru Fauzy tay a ranta ta shiga tunanin to waima ita waye zai ce yana son nata Sameer dai tasan ko fad'uwa zatai a gaban shi tana mashi magiyar ya so ta ba son ta zai ba balle har ayi Maganar aure shiyasa ma bata sa ma ranta wai taji ko tana son shi ba, ganin ta kafeta da ido yasa tayi d'an murmushi ta jinjina mata kai alamar eh, sakinta Aunty Mareeya tayi ta d'aga hannuwa ta fara fad'in,

"Ya Ubangiji ina rok'on ka da sunayen ka tsarkaka da suffofinka mad'aukaka, ga kanwata nan ka bata miji nagari wanda zai so ta Saboda kai, Ya Allah Idan wanda suka fita tare Alkhairi ne a tattare da ita kasa mashi son ta da k'aunar ta a zuciya ta yadda har Al'amarin zai kai su da Aure Alfarmar Annabin rahama SAW" a hankali Fauzy itama ta fad'i S.w.a ganin Aunty Mareeyar ta shafa itama ta shafa tana d'an murmushi ita tausayi ma Aunty Mareeyar ta bata wllh ganin ta shirga mata

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login