Showing 495001 words to 498000 words out of 512766 words
Chapter 166 - Asanadin Makwabtaka Book 3 Hausa Novel Complete
Unknown
27 Dec 2024
1551
ce mata kada taji komai in taji bata son shi ta faɗi mashi bazai ji komai ba kuma ko Yayanta bazai faɗi ma yadda sukai da ita ba, motsa baki ta fara da ƙyar tace mashi shikenan idan Yaya Haisam ya amince to ta yarda, ɗan girgiza mata kai yayi yace mata aure ba abu bane da wani zai amince maka tunda bashine zai zauna maka ba sannan aure ana yin shi in ana son juna don haka ita zata amince mashi in taji tana son shi, shiru tayi tana yi tana maida idonta ƙasa ya ɗan ɗage mata gira yana murmushi, sai faman yan kame kame take don taji itama yayi mata don Na'eem ba irin mazan da suke furta ma mace so taƙi amincewa bane kawai dai abun ne taji yayi mata girma ba kamar da yake wannan ne karo na farko da tayi Magana irin haka da Namiji,
"Amman...ita Matarka to zata amince ka aure ni ne?" da ƙyar ta furta mashi hakan, gyara zama yay kafin yace "Ayshat ba kowace mace bace ke son a ƙara mata abokiyar zama ba saidai inada kyakkyawar fahimta da mata na nasan zata amince koda hakan bai mata dadi ba amman tasan inada ikon ƙara wata matar kuma dama ban ta6a mata alƙawarin zan kasance da ita kaɗai ba don haka nasan bazata bani matsala ba in kin amince zaki aure ni" kai ta ɗaga mashi kafin tace shikenan,
"Kin amince zaki aure ni kenan?" kai ta ƙara ɗaga mashi ya sake cewa "ina fata dai ba saboda wani dalili ko don ni abokin yayanki bane yasa kika amince man, nafi son ki amince man don kema kinji kina sona" kai ta jinjina mashi yana mata wani kallo yace "nayi maki kina so na?" kan dai ta sake ɗaga mashi,
"Ok in dai da gaske kike kema kamata yay ki faɗi man da bakinki kamar yadda na faɗa maki" ɗan murmushi ta shiga yi tana motsa baki ya ɗage mata gira alamar ta bashi amsa, da kyar ta furta "nima ina son...ka" tana yin Maganar da sauri tasa duka hannuwanta masu ɗauke da dogayen yatsu ta rufe fuskarta Na'eem ɗin ya shiga yin yar dariya, da yake wayayye ne sai gashi yasa ta saki dashi sun shiga yin firar soyayya, suna haka Hajiya Fatuu ta shigo cikin falon tana sanye da riga da skirt na lace da suka amshi jikinta tare da gyale mahadinsu, tana nan yadda take bata ƙara ƙiba ba saidai ta ƙara cikowa tay dumdum fatar nan tata har wani sheki take hutu ya zauna mata sosae, ƙafafunta na sanye da wasu takalma masu tsini mai ɗan gwa6i har yanzu halinta nason takalma masu tudu nan, ta bangaren hips dinta kuwa abun saidai ace tubarkalla don suna nan sai ma ƙara cika da sukai duk da gyalen jikinta babba ne amman kana kallonta zaka san tana dasu, hannunta na hagu na rataye da yar babbar jaka da take ɗauke da kayan karatunta sai kuma ɗayan hannunta na hagu ta ruƙo Lab coat dashi, tana ganin Na'eem ta fara yin murmushi hakan ya bayyanar sa fararen haƙoranta kamar auduga masu ɗauke da haƙorin makka daya ƙara ƙawata fuskar tata, cikin falon ta nufa sam bata yi mamakin ganin Na'eem ɗin ba don da sukayi waya da Haisam ya sanar mata tare suka zo, a saman kujera dake gefen wadda suke ta zauna Na'eem daya maido idonshi kanta yana murmushi shima yay mata sannu da dawowa ta amsa tare da gaishe dashi da yi mashi anzo lafiya, bayan ya amsa ya tambayi karatunta tace mashi Alhamdulillah itama ta tambayi matar shi Fadeela da yaransu duk yace mata lafiya lou suke, saida suka gama gaisawa sannan Aysha tayi mata sannu da zuwa ta maida idonta kanta tana murmushi ta amsa ta tambayi ya School tace mata lafiya lou, yar hira sukai da Na'eem kafin ta miƙe tace bari ta ɗan shiga ciki yace Ok. Sai bayan sallar Magrib sun dawo daga masallaci suka zauna cin abinci gaba ɗayan su Na'eem da Aysha sai satar kallon juna suke suna murmushi, bayan sun dawo daga sallar isha gaba daya a falo suka zauna suna kallo, wuraren ƙarfe tara Haisam ya miƙe yace ma Na'eem bacci yake ji ya taso suje ya kai shi ɗakin da zai kwanta yana murmushi yace shi da Aysha basu gama yin kallon ba yace Ok yazo suje ya nuna mashi in ya gama sai yaje ya kwanta ya miƙe, bayan tafiyar su ne Fatuu ma ta miƙe tayi ma Ayshar saida safe dama duk in Haisam yazo a ɗayan bedroom ɗin dake part ɗin Fatuu take kwana tare da mai aikin su Asabe, bada jimawa ba Na'eem ya dawo a saman kujera mai mazaunin mutum ukku ya zauna yace ma Aysha ta dawo nan, a can gefe kamar ɗazu ta zauna ya jingina kanshi da jikin kujerar ya shiga sakar mata kallon love da alama dai shima gwani ne ta bangaren soyayya, hirar soyayyarsu suka shiga yi ba laifi ta saki jiki sun ɗan ɗauki lokaci wurin ƙarfe goma saura yace bari ya barta taje tayi bacci kadda ya gajiyar da amaryarshi tayi dariya suka miƙe a tare.
Washe gari bayan Haisam ya dawo daga sallar Asuba itama Fatun tayi sun koma sun kwanta ta tada kanta a saman jikinshi yake mata zancen son auren Aysha da Na'eem keyi ya faɗi mata yace mashi ya nemi amincewarta to har sunyi magana kuma ta amince, sosae Fatuu ta jinjina abun don ita koda ta gansu tare bata kawo komai a ranta ba saboda tasan Ayshar nada saurin sakin jiki da mutane ba kamar Mino ba, da alamun damuwa tace mashi amman bai ganin hakan zai iya haifar da matsala tsakaninsu da matar shi taga anyi mata ba daidai ba tunda sun san juna suna gaisawa, yana ɗan murmushi yace itama ba sun san juna ba da Fanan kuma ta aureshi, juyawa tay tayi mashi wani kallo tare da ɗan tura mashi baki tace to ai ita bata san da Auren ba ko ya ɗage mata gira yace data sani bazata amince ba kenan tay shiru tana kallon shi yace ta bashi amsa, yamutsa fuska tay ta sigar shagwa6a tace to tunda dai an riga anyi ya wuce miye na maido maganar, yana murmushi yace Ok tunda itama ya aureta kuma sun san juna da Fanan itama Ayshar ba wani abu bane don ta auri Na'eem, shiru Fatuu ta ɗan yi kafin tace ya sani fa Aunty Fanan daban take a cikin mata don da wuya a samu wadda zata iya jarumtar da tayi, shiru yay yana sakin murmushi yayin da zuciyarshi ta shiga dawo mashi da fuskar Fanan. Wuraren ƙarfe goma na safe suka zauna yin breakfast, kowa cikinsu yayi wanka Haisam da Na'eem na sanye da ƙananun kaya wando da riga Fatuu kuma da Aysha suna sanye da dogayen riguna masu taushi suna da gajerun hannuwa kowa ya saka hula a kanshi daga bayan hular yay tudu sosae saboda gashin su, bayan sun zauna a kujerun dining ɗin suka shiga gaishe da juna kafin Fatuu ta shiga yin serving nasu, bayan ta gama a nutse suka fara ci baka jin komai sai ƙarar cokulla sai kuma Ac dake a wurin tana ta aiki, bayan sun gama gaba ɗaya a falo suka zazzauna suna yin hira wadda Haisam da Na'eem sai Fatuu ne ke yi ita dai Aysha tayi shiru tana saurararsu akai akai kuma suke haɗa ido da Na'eem su sakar ma juna murmushi, suna cikin yin firar Na'eem yace ma Fatuu "Madam ko in ce Yayata, ina fatan Yalla6ai ya isar maki da saƙona na naga ƙanwarmu tayi man ina neman iri pls, yace man in nemi amincewarta da yake mu indai ta wannan bangaren ne bamu failing tuni har an amince man ance ana sona" ya kai idon shi kan Aysha yace "Ayshanah hakane ko, kin amince zaki aure ni ai ko?" ai tana jin abunda ya faɗa tay zumbur ta miƙe da gudu ta nufi hanyar bedroom duk suka bita da ido suna yar dariya, bayan barinta wurin ne Fatuu tace mashi sunyi Maganar da Hubby taji daɗi saidai tana gudun hakan ya haifar da matsala tsakaninsu da Fadeela tana iya ganin an yi mata ba daidai ba, yana murmushi yace mata kar ta damu zai faɗi mata shi yaga Aysha yaji yana sonta kuma akai sa'a itama tana son shi ba wanda ya haɗa su in sha Allah ba wata matsala da zata faru tsakaninsu Fatun tace Allah yasa, tambayar ta yay lokacin da zata gama School Fatun ta faɗi mashi yace Ok nan da sati ɗaya in sha Allah zaije Yola ya gaida Parents ɗin su Haisam yay mashi wani kallo kafin slowly yace mashi saurin mi yake ne tunda ta amince mashi yabi komai a hankali da sauri Na'eem ɗin yace ai ba mata irinsu ake bi a hankali ba wurin neman aurensu nan tana gama Secondary zaiga masu son ta suna ta kunno kai ƙarshe asamu wani yayi mashi overtaking shiyasa yake son tana gama School ɗin yayi wuff da ita duk sukai yar dariya, hira suka cigaba da yi bayan wani lokaci Haisam ya tambaye shi yaushe zai je gaida relatives ɗin nashi Na'eem ɗin ya duba agogon hannunshi kafin ya bashi amsa da zuwa ƙarfe sha biyu zai tafi Haisam yace Ok in lokacin ya ƙarasa sai suje ya raka shi,
"No, kai zaman ka kaida kazo Weekend Madam na buƙatar ka a kusa da ita koda yaushe ka ƙyale ni in je ni kaɗai, ko kuma tunda nima ga Amaryata sai ta rakani kawai kaga ma sai inyi amfani da daman in fara introducing nata ga Family na" Na'eem ya faɗa yana murmushi suma duk murmushin sukai basu ce komai ba, ganin lokacin fitar nashi ya ƙarato yasashi ce ma Fatuu pls yana neman alfarmar fita da Aysha tana murmushi tace an mashi yay mata godiya kafin yace to ta taimaka tayi ma Amaryar tashi mai kunya magana ta shirya tace to tana dariya tare da miƙewa shima Na'eem ɗin ya miƙe yace ma Haisam bari ya shirya ya ɗaga mashi kai, a bedroom ta iske Aysha kwance saman gado ta nufeta tana faɗin kwanciya tayi kenan Ayshar ta ɗago tana kallonta, a bakin gadon ta zauna tana kallonta da murmushi tace mata Amaryar Na'eem Ayshar tayi murmushi kawai, shiru Fatun ta ɗan yi kafin tace mata ta tabbatar da yayi mata tana son shi don shi da gaske yake aurenta zaiyi tana gama School, shiru Ayshar tayi tana kifce kifcen idanu Fatuu tace mata ta buɗe baki tayi mata magana, a hankali tace mata eh in dai baida wata matsala Fatun tace gaskiya Na'eem bata tunanin yanada wata matsala a yadda ita ta sanshi mutumin kirki ne kuma tasan da yanada matsala ma tun Farko Haisam bazai bashi damar ya nemi soyayyarta ba kawai inda take tunanin matsala wurin matarshi ne duk da itama tana da kirki to amman wata baka gane rashin kirkinta sai za'a mata kishiya kawai dai suyi addu'a Allah yasa ta fahimta ta kuma kar6i abun kamar yadda Aunty Fanan tayi Ayshar ta amsa da Amin kafin tace "amman fa Adda Fatuu wllh Aunty Fanan ta daban ce" murmushi Fatun tay tace ta sani samun irinta cikin mata da wuya in ma akwae duk da tasan akwai mata da yawa wanda in mijinsu yaje masu da zancen ƙara aure duk da basu so amman suna karbar abun a matsayin ƙaddararsu tunda sun san Allah ne ya halarta masu yin jayayya da hakan kuma wahalar da kai ne ƙarshe mutum ya jefa kan shi a halaka, faɗi ma Ayshar tayi zasu fita da Na'eem ɗin yana son zuwa da ita wurin danginshi ya gabatar masu da ita, tana jin haka ta ɗan zaro ido kafin tace amman da wuri haka, miƙewa Fatuu tay tana yar dariya tace shifa da gaske yake yace ma nan da sati ɗaya zaije Yola gaishe dasu Baffa don haka ta fara shiri don ita amarya ce,
"Amman Adda Fatuu ban yi ƙarama ba da yin aure" Aysha ta faɗa da yar damuwa, Fatuu dake tsaye a gaban wardrobe ɗin bango tana ƙoƙarin za6o mata kaya ta bata amsa da "ba wata ƙarama da kikai Aysha, ke ai gara kema akan Mino, ita fa ko gama Secondary bata yi ba akayi mata aure gashi ko a jiki ma kin ɗan fita kauri lokacin" ta ƙarasa Maganar tana dawowa wurin gadon hannunta ruƙe da riga da skirt na lace kalar blue da ratsin golden brown, ita ta taimaka ma Ayshar ta shirya cikin kayan ta saka mata yan kunnan zinari da zobe sai kuma agogo golden mai kyau, yar light make up tayi mata ta ɗaura mata kallabi sai gashi ta fito tayi wani irin kyau, bayan an gama saka kayan ta yafa gyale mahadinsu haka jaka da takalmanta suma duk kalar kwalliyar lace ɗinne takalman masu dan tudu ne kadan don tana da tsawo don bata cika saka takalma masu tsini ba, lokacin da suka fito falon Na'eem din har ya gama shiryawa ya dawo suna zaune da Haisam, shima shadda ce ya saka brown wadda ta hau da kwalliyar lace ɗin jikin Ayshar sai baza ƙamshi yake, Na'eem na ganin shigarta yana murmushi yace ko daga yanayin shigar su hakan ya tabbatar da sun dace da juna duk akayi yar dariya Aysha ta sunnar da kai, har bakin galleliyar baƙar Motar Haisam da suka zo da ita suka rako su bayan sun shiga sukai masu sai sun dawo, yana driving suna hira irin ta masoya haka suka shiga zaga gidajen yan'uwan su Na'eem wanda duk mawadata ne, duk inda suka je sai ya gabatar da ita matsayin matar shi ta biyu da zai aura nan bada jimawa ba anata yabata tare da fatan alkhairi, lokacin da suka je gidan Kakarshi wadda ta haifi Mom ɗinshi shima haɗaɗɗan gidane mai girma don yana da parts da yan'uwan mahaifiyarshi maza ke zaune da matansu haka itama kakar 6angarenta daban an ƙawata shi ai kace ba sashen tsohuwa ba, lokacin daya gabatar mata da Aysha matsayin wadda zai ƙara mata cike da zolaya irinta Kaka ta yamutsa fuska tace in baya ga rigima irinta namiji mi zai ci da wannan yar ƙaramar bafullatanar bayan yana da mata ƙaƙƙarfa kamar ita, ita dai Aysha murmushi kawai take kanta a ƙasa haka shima Na'eem ɗin yar dariya yake yace ina wani ƙarfi a tare da ita, sosae ta sake ma Aysha tana ta mata tambayoyi game da ita tana bata amsa da yake tasan Haisam sosae ta yaba da al'amarin tayi Addu'ar Allah ya sanya alkhairi, duk sauran parts ɗin gidan saida ya kai ta ko ina an yi mata tarba mai kyau, daga baya bangaren Kakar suka koma sai bayan sallar La'asar ya dawo daga Masallaci yace mata zasu tafi tace ma Aysha tunda a garin take zaune ta rinƙa zuwa gaishe da ita tana kama ƙafa in tana son ta amince ta aurar mata miji in ba haka ba ita dashi saidai kallo, tana murmushi tace mata in sha Allahu zata riƙa zuwa sukai mata sallama cike da tsokana Na'eem yace tunda ita mai ƙarfi ce sai ta taso ta raka su bakin mota ko, wurga mashi harara tayi tace Allah ya kyauta tayi ma kishiyarta rakiya duk sukai dariya, bayan sun baro gidan Shopping ya wuce da ita, koda yace mata ta ɗauki duk abunda take so cikin marairaicewa tace mashi ai ita tana da komai yana mata wani kallo yace duk da haka ta ƙara so yake daga yau ta fara amfani da kayan mijinta, ba yadda ta iya haka ta fara ɗaukar yan abubuwa tana sakawa a cart da ya ɗaukko mata, ganin bata ɗaukar kayan sosae yasa shi fara za6ar mata da kanshi yana yi yana tambayar wanda take amfani dasu, bayan sun gama da wurin kayan shafa wurin dogayen riguna suka nufa tana ta roƙon ya barsu tana da su da yawa amman duk da haka saida ya daukar mata guda biyar da takalma guda ukku bayan sun gama da nan bangaren undies suka nufa duk yadda take jin kunya saida ya sakata ta ɗauka, abunda bata sani ba yana amfani da hakan ne wurin sanin size ɗinta saboda in zai yi mata lefe, saida ya cika Shopping cart ɗin taff da kaya sannan suka nufi wurin biya aka saka masu kayan a ledoji bayan an saka a Mota suka tafi.
Kamar yadda Na'eem yace wani ƙarshen satin na zagayowa suka shirya zuwa Yola da Haisam, ranar asabar da safe suka bi jirgi zuwa Yola bayan sun isa aka tura Mota ta ɗauke su zuwa garin su Fatuu, bayan sun isa sun samu kyakkyawar tarba daga mutan gidan aka sauke su a part ɗin su Yadikko nan aka shiga zuwa gaishe da su kan kace mi an jere masu kwanonin abinci iri iri koda Yadikko tayi masu Maganar cin abinci cewa sukai a ƙoshe suke Baffa dake zaune yana murmushi yace duk da haka yakamata su ci tunda tafiya suka yo, ba wani mai yawa suka ci ba saidai sun sha fura ba laifi, bayan sun gama ne Haisam ya gabatar masu da Na'eem matsayin shine mai son auren Aysha in ta gama School, dama an riga an sanar masu game da zuwansu, sosae suka nuna farinciki da Addu'ar Allah ya sanya alkhairi bayan sun amsa Haisam ya sake cewa yana son a faɗi mashi lokacin da zasu turo a saka rana Baffa na murmushi cikin Maganar shi mai tattare da natsuwa yace ai tunda ga shi Haisam ɗin shima matsayin Mahaifi yake wurin Aysha don haka a nemi aurenta a wurinshi duk yadda ya yanke yayi lafiya lou tunda ba abu bane na kusa kada aita wahalar yin zarya, hakan ba ƙaramin daɗi yayi ma Na'eem ba shima Haisam yaji daɗin yadda ya girmamashi yay mashi godiya da Addu'ar Allah ya ƙara girma da lafiya yana murmushi ya amsa shima yay mashi godiyar abubuwan alkhairi da ake ta