Showing 81001 words to 84000 words out of 512766 words
Chapter 28 - Asanadin Makwabtaka Book 3 Hausa Novel Complete
Unknown
27 Dec 2024
1657
ba",
Fatuu da ta d'ago daga jikinta tace "wace mafita kike tunani data fi wannan Fauzy, in ba hakan muka yi ba duk abunda zamuyi asirinmu tonuwa zai yi ni kuma abunda ban so kenan kar ki manta akwae aminci mai k'arfi tsakanin Gwaggo da Hajiyar su shekaru masu yawa suna zumunci na tabbatar in wannan abun ya bayyana sai zumuncin nan ya lalace abubuwa da yawa Al'amarin nan zai shafa don Allah Fauzy ki bani goyon baya in sha Allahu ba wata matsala da za'a samu kuma Allah zai yafe man tunda yasan ba da son raina hakan ta faru ba sannan cikin kinga k'arami ne ko kwana arba'in bai yi ba duka watan shi guda" shiru kawae Fauzy tay tana bin ta da ido ita dae hakanan hankalin ta bai kwanta da a zubar da cikin ba ba kamar wasu abubuwa da take nazari, magiya Fatuu ta shiga yi mata kan azubar d'in can ta nisa tace "kin gane Zarah ni wllh raina bai kwanta da a zubar da shi ba ba kamar dana yi la'akari da wasu abubuwa shin Ya Haisam ya ta6a kai ki gidan tunda kuke dashi?" a hankali ta girgiza mata kai alamar a'a shiru Fauzy tay tana sake yin nazari tsawon shekara biyar da suka san juna amman bai ta6a kaita gidan ba sai yanzu sannan tace yana yawan ta6a ta ba tare daya ji komae ba wanda a yadda ta bata labari a da sam bai mata haka hasali ma bai son su ke6e su biyu to miyasa yanzu yake mata hakan? wata Zuciyar ta raya mata k'ilan don yanzu ta girma ta zama cikakkar budurwa shiyasa ya fara jin sha'awarta kamar yadda itama Fatun take tunani can kuma nazarinta ya gangaro kan Alkhairin da yake mata wanda harda su wayar miliyan hakanan ba dangin iya bana baba nan ma wata zuciyar ta sake raya mata wannan ai daman ya saba yi mata Alkhairin kuma zai iya yuwuwa ko ya fara son ta ne shiyasa har Yay mata irin kyautar, k'arshe dae kan Fauzy ya k'ulle tamau ta kasa yin tunanin wani kwakkwaran dalili don komae a bud'e yake amman tana jin kaman something is amissing k'arshe dole ta bar ma ranta kawae kaddarar su ce a hakan, kallon Fatuu tay tace "zan amince a zubar kamar yadda kike so amman da sharad'i guda" da sauri Fatuu tace miye sharad'in Fauzy taci gaba "Dole Ya Haisam yasan da cikin nan kafin mu zubar d'in" wani kallo Fatuu tay mata a marairaice tace "miyasa za'a sanar mashi Fauzy abunda shi baima damu da abun da yay man ba kina gani tunda hakan ya faru sau biyu ya kirani ban d'aga ba daga nan fa bai sake kira ba dama shima kiran sai kusan da akai 2 weeks sannan don Allah mu rabu dashi kawae ni nasan ba wani abunda zai yi" d'an girgiza kai Fauzy tay tace "karda idon ki ya rufe Zarah zubda ciki fa ba k'aramin abu bane da za'a ce ayi ba tare da mai shi ya sani ba yanzu ba fata nike ba azo Asiri ya tonu wurin zubarwar taya zamu kare kan mu tunda shi ba sanin da cikin yay ba think about it Zarah" d'an shiru Fatuu tay duk ranta bai so ba tace mata ita tana ganin in sha Allahu ba abunda zai faru ai cikin k'arami ne they should just go ahead and do d abortion ba tare da ya sani ba amman Fauzyn ta kafe kan ita dae a sanar mashi don bata tunanin hakanan yak'i kiranta dole da dalili Fatun tace to taya zata sanar mashi shi da bai nan kuma dae ai bai dace ta kira shi yana can wurin jinyar ba, d'an jimm Fauzy tay sai kuma tace "mi zai hana ki kira Kawu Amadu ki tambayi ko sun dawo baki sani ba" gyad'a kai tay ta juya can kusa da pillow ta d'aukko wayar ta fara k'ok'arin kiran Amadun ringing biyu ya d'aga ta gaishe shi ya amsa ya tambayeta ta dawo gida ne don shi yana Makaranta tace mashi a'a sai anjima d'an shiru tay jin hakan yasa ya tambayeta da wani abu ne tace a'a kawae tana son ta tambaye shi ko Hajiyar Sanata ta dawo ne, yar dariya yay yace "ke dai fad'i gaskia kodae ran ki ne ya baki Romeo d'in ki ya dawo shine kike son ki tabbatar" d'an yamutsa fuska tay tace "kai Kawu Amadu ni don Allah ka fad'a man ai Hajiya dae na tambaye ka ba wani ba ko" tana jiyo dariyar shi kafin yace mata eh ta dawo jiya da yamma harda ma Romeo d'in nata, ko sallama bata yi mashi ba ta katse kiran da ta kalli Fauzy har bata san tayi d'an murmushi ba tace mata ya dawo jiya itama murmushin tayi tace "yauwa kinga Allah ya taimake mu komae zai zo da Sauk'i in sha Allah" cike da farinciki Fatuu ta fad'a jikinta tana Fad'in "Thank u so much Fauzy u'r more like my blood sis than Friend, Nagode ma Allah da yake had'a ni da k'awaye Nagari wanda duk in ina cikin damuwa suma suke shiga damuwa har su bani shawara mai kyau da zata fitar dani" d'agota Fauzy tay tana murmushi tace "What are Friends for, haka yakamata aboki na gaskiya ya kasance wani lokacin in kai dacen aboki sai kaji ma har yafi maka wani dan'uwan naka na jini hakan nake ji a tattare dake Zarah" k'ara fad'awa tay jikinta tana murmushi can taji Fauzyn tace "How I wish ace cikin nan na halak ne lokacin da zamu gama makaranta kuna da d'an yaron ku ko yaranku in twins ne lokacin nasan har sun d'an tasa ma, wai za'a ga ruwan kyau dae wllh amman ba komae komi Allah yay mai kyau ne fatana dae ya shige mana gaba a duk abunda zamu yi" Fatun ta amsa mata da Amin a hankali Fauzyn tace mata to ta tashi tay wanka ta shirya sai taje ita kuma zata jirata har ta dawo bazata tafi weekend ba, sosae Fatuu taji dad'i ta mik'e, ba'a d'au wani lokaci ba tayo wankan ta zura doguwar riga bak'a ta yafa gyalenta Saboda zumud'i har ta ma manta da ita mara lafiya ce, tare suka fito har wajen gate cikin sa'a suka samu Napep da Fatuu zata shiga Fauzy ta kama hannunta tace "kiyi man alk'awari nima zaki same shi kiyi mashi Maganar" kai ta d'aga mata tace "nayi maki Alk'awari kuma in zan dawo zan taho da allurar sai kiyi man" d'an jimm Fauzy tay kafin ta gyad'a mata kai tace shikenan amman dae ta tabbatar sun fara yin Magana da shi daga haka ta shige Fauzy na d'aga mata hannu suka tafi.
Tunda suka shigo Unguwar gabanta ke fad'uwa har d'an rufe fuskarta take don kada gwaggo ko Kawu Amadu wani ya ganta Saboda bazata shiga gidan su ba don kada gwaggon ta gano halin da take ciki ba kamar da ta tuna Maganar data yi mata rannan, har bakin gate mai Napep d'in ya kai ta bayan ta biya shi tana ruk'e da yar purse d'inta ta tunkari gate d'in Office yay mata ya Makaranta ta amsa bayan ta gaishe da shi ta shige, part d'in Hajiya tay tunanin fara zuwa don tayi mata ya mai jiki kuma k'ilan ma ta iske Haisam d'in a can tunda yau Friday, lokacin data shiga Hajiyar na zaune a parlor tayi gayun Juma'a bak'i tayi bayan ta dawo daga Masallaci basu dad'e da tafiya ba ta zauna tana kallo idanunta sanye da medical glasses d'inta, tunda Fatuu tay sallama ta maido idanunta kanta tana kallonta har ta k'araso cikin parlon ta zauna kujerar dake opposite da ita da d'an murmushi tace "Hajiya ina wuni an dawo lafiya" still kallonta take fuska a sake ta amsa mata, Fatun ta sake cewa Ya mai jiki, d'an girgiza kai Hajiya tay tace "mai jiki sai dae mu ce Alhamdulillah don an sha jiki kam amman cikin hukuncin Allah ya warke garas abunda ake gudu Allah ya tak'aita faruwar shi" itama Fatun Alhamdulillah tace kafin tay Addu'ar Allah ya k'ara mashi lafiya Hajiya ta amsa, d'an shiru sukae Fatun ta lura da Hajiyar sai kallonta take hakan yasa tasha jinin jikinta ta sadda kai tana wasa da yatsunta can ta d'ago tace ma Hajiyar Ya Haisam na part d'in shi ne zata mashi ya mai jiki d'an girgiza kai ta k'ara yi tace "bai nan tun jiya da muka dawo yana G.r.a da yake har yanzu shi kaman jikin nashi bai idasa warwarewa ba" shiru Fatuu tay tana maimaita abunda tace a cikin ranta can ta tambaye ta bai lafiya ne, Hajiyar ta ruk'e ha6a tace "ai ciwo yasha shima a can jinya biyu akai wllh dama dae tun da muka bar nan zamu Kano na lura da yanayin shi har na tambaye shi sai yace man fever ke damun shi to da yake mutum ne mai k'arfin hali a hakan har suka fita da Mahaifin na su da yake mu sai daga baya muka bi bayan su Germany d'in, to a can ma bai samu ya huta ba bayan sun je aikuwa sai ciwo ya buge shi wani irin zazza6i mai zafi da ciwon kai suka taru suka rufe shi dama kuma shi yana dad'ewa bai yi ciwo ba, amman fa duk randa ya kwanta yana jin jiki wllh don ni bazan iya tuna ma yaushe yay irin wannan ciwon ba amman dae Alhamdulillah ya samu sauk'i sosae nayi ma tunanin zai wuce can U.s d'in da yake suma su Fanan d'in sun zo nan Germany kusan ita tay jinyar mijin nata har ya samu sauk'i to da zamu dawo ne ita ta wuce can shi kuma muka dawo dashi" duk sai jikin Fatuu yay d'an sanyi a hankali tace Allah ya k'ara basu lafiya Hajiyar ta amsa har zata mik'e taji tace "amman kema dae Fateema kaman baki lafiyar ko?" Damm gabanta ya fadi a dabarbarce tace mata eh itama malaria ke damunta, Hajiyar tace to taga likita ko don fuskarta ta fad'a da yawa gashi tayi fayau kamar mara jini da sauri tace mata eh taje taga likita har test an yi mata an kuma bata magunguna yanzu haka tana cikin sha ma Hajiya tace to Allah ya k'ara lafiya ta amsa da Amin had'i da mik'ewa zata tafi Hajiyar tace ba ta bari taci Abinci tace a'a ta k'oshi taci Abinci daga haka sukai sallama ta nufi hanyar fita, lokacin data fito har saida ta saki yar ajiyar zuciya bayan ta fito wajen gate sai taji dama ta san bai nan da bata bari mai Napep d'in ya tafi ba, ta bayan gidan Hajiyar ta bi saida ta kusa bakin titi sannan ta samu mai Napep ta fad'i mashi G.r.a zai kaita yace to ta hau suka tafi, bayan sun iso ya tambayeta road d'in da zai kaita tace bata san sunan road d'in ba da yake sau d'aya ta ta6a zuwa kuma da daddare ne amman zata rink'a nuna mashi hanya yace to, da yake G.r.a ba kaman geto bace sam Fatuu ta kasa gane gidan sai faman uban zagaye layuka suke a kokarin ta na ta gano, sun d'auki lokaci tana dudduba gidajen Unguwar har dae mai Napep d'in ya gaji ya parker a gefen hanya yace mata gaskiya fa ba lallae su gane gidan ba tunda bata san sunan layin da yake ba k'arshe zasu yi ta yin wahala ne, shiru tay da alamun damuwa bata son ta koma ba tare data gano gidan ba don ta san k'arshe ba lalle Fauzy ta bata goyon baya ba ganin yadda ta damu yasa mai Napep d'in tambayarta bata san sunan mai gidan bane d'an Jim tay ta tuno da Haisam yace ai gidan baban shi ne hakan yasa tace ta sani gidan Senator Alee Adamu Zakee ne yace to bari yaga in za'a samu wanda za'a tambaya da sauri tace to ya fita daga cikin Napep d'in yana duba hanya can saiga wata Mota ta taho ya d'aga ma mai Motar hannu cikin sa'a ya tsaya daga d'an gaban Napep d'in ya nufi Motar da sauri, slowly glass d'in driver side ya sauka wani Alhaji ne a ciki mai Napep d'in ya gaishe da shi bayan ya amsa yace don Allah tambaya suke yace to Allah yasa ya sani mai Napep d'in yace "dama wani gida ne muke ta nema mun kasa ganewa gidan wani Senator Alee....." kakarewa yay yana niyyar d'aga kai ya tambayi Fatuu yaji Alhajin yace gidan Senator Alee Adamu Zakee da sauri mai Napep d'in yace yauwa eh nan, kwatance yay mashi mai Napep d'in ya gane yay mashi godiya yaja Motar shi kuma ya koma Napep d'in Fatuu ta tambaye shi an gane gidan yace eh sosae taji dad'i duk da fargabar da ta cika ta, suna shiga titin layin da aka masu kwatance Fatuu ta hango gidan ta nuna ma mai Napep d'in ya tunkare shi, a gaban tangamemen gate d'in ya parker ta fito su Officer na zaune a saman benci ta nufe su idanun su a kanta har ta k'arasa ta tsaya daga d'an gaban su, bayan ta gaishe dasu tace don Allah ko Ya Haisam na nan d'ayan Officern da tunda ya ganta ya ganeta yace mata eh yana nan, d'an shiru tay ganin haka yasa shi ce mata ba wurin shi tazo bane tace eh yace to ta shiga, juyawa tay ta koma wurin mai Keke Napep d'in tace don Allah ya jirata ba dad'ewa zatay ba sai su koma yace ba matsala hajjaju a fito lafiya harda ce mata wai ta taho mashi da lemu mai sanyi mak'oshin shi ya bushe Saboda yawon da suka sha ta d'aga mashi kai kawae, ta k'aramar kopa ta bi ta shiga gidan tunda ta tunkari ginin gabanta ke fad'uwa abubuwan da suka faru rannan suka shiga dawo mata, saida tay yar tafiya mai d'an tsawo ta isa ginin gidan ta shiga Parlon kafin ta bi ta Corridor ta nufi kopar Bedroom d'in shi.........
_Littafin A Sanadin Makwabtaka part 2 Naira 300 ne za'a tura ma Mutum har part 1 ga mai so zai turo kudin ta wannan Account din, 1509618776, Zainab Bature Access Bank, za'a turo shedar biya ta wad'annan nos din 09013804524 ko 08169856268
[5/8, 19:28] +234 901 700 4868: *ASM Bk2049*
_Destiny may be delayed but cannot be changed...._
*DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI*
.........tsaye tay a bakin kopar k'irjinta na ci gaba da bugawa da sauri da sauri ga tsoro da ya kamata ta d'an d'auki lokaci a haka kafin tay k'arfin halin kai hannu yana d'an rawa ta d'an kwankwasa shiru bata ji an yi magana ba hakan yasa ta k'ara d'an kwankwasawa da d'an k'arfi k'asa k'asa ta jiyo Muryar shi yace "Who is dat" shiru tay har saida ya sake tambaya amman ta kasa bud'e baki tace itace jiyo shi tay yace a shigo kopan a bud'e take da turanci d'an jimm tay kaman bazata shiga ba can ta d'an runtse ido kafin ta bud'e fuska a d'aure slowly ta tura kopar, tana shiga suka had'a ido da shi yana zauna akan kujera 3 seater yana operating system jikin shi sanye da jar armless gabanta anyi bak'in rubutu sai bak'in wando 3-quater abu dae sai dae ace Tubarkallah daga gefen shi c-table ne a saman table d'in kwalin lemu ne aje sai tumbler daga gefe kuma ledar take away ce mai d'auke da tambarin wani Eatery, bin ta da ido yay ya yi matuk'ar mamakin ganinta duk da fuskar shi bata nuna hakan ba itama tsaye tay tana mashi wani irin kallo cike da 6acin rai don bata tsammaci ganin shi haka ba wato dae zargin ta ya tabbata na bai damu da abunda ya aikata mata ba tunda gashi zaune ya warke har yana latse latsen computer ba tare daya nemeta ba tunda suka dawo,
"Come inside" taji cool voice d'in shi ta fad'a kaman bazata shigan ba ta d'aure fuska tamau can dae ta nufi cikin a gefen shiga inda kujerun suke ta ja ta tsaya tana kallon gefe kallonta kawae yake ya lura da yadda ta d'aure Fuska can yace "come and have a seat" banza ta mashi kuma bata kalle shi ba har saida ya k'ara mata magana kan taje ta zauna a d'an fusace ta kalle shi tace "ba shi ya kawo ni ba" still idon shi na a kanta ita kuma ta k'ara juyar da fuskarta can yay sigh yace "am listening miya kawo ki?" d'an yamutsa baki tay alamun mamakin jin yadda ya tambayeta seemed he doesn't care at all aikuwa sosae ranta ya k'ara 6aci idanun ta suka ciko da k'walla ta juya cikin rawar murya ta fara magana "Zuwa nai in fad'a maka ka cuce ni, ka zalunce ni Ya Haisam, an yarda da kai amman kaci Amana kayi man abunda wani ma ban tunanin zai man hakan balle kai, kace ni matsayin k'anwar ka ta jini ka d'auke ni amman abunda kai man ya tabbatar da k'arya ne don in hakan ka d'auke ni baza ka ta6a son wani yayi man hakan ba balle kuma kai da kan ka, kowa nawa ya amince maka amman duk da haka ka ha'ince su kai man abunda na tabbatar ba kuskure bane da niyya ne tunda sai da na rok'e ka amman ka k'i saurare na Saboda dama kana neman dama ne don ka fara nuna alamomin kana son ta6a jikina...." dakatawa tay tana goge kwalla shidae sai kallonta kawae yake bazaka gane yanayin da yake ciki ba, tsayawa tay da goge kwallan cikin muryar kuka tace "..gashi nan sakamakon abunda kai man ka jawo mana abun kunya wanda na tabbatar gwaggo in taji zuciyarta na iya bugawa ta mutu...." dakatawa tay tana sheshsheka sai lokacin yanayin fuskar shi ya canza ya d'an k'ank'ance ido alamar tunani kan abunda ta fad'a kan shi ne ya d'aure gashi tak'i cigaba da Maganar sai kuka take faman yi