Showing 471001 words to 474000 words out of 512766 words
Chapter 158 - Asanadin Makwabtaka Book 3 Hausa Novel Complete
Unknown
27 Dec 2024
1573
Dad ɗin
a fusace tace "tsabar kin raina mu yasa kike dubar idanun mu kina faɗin Mutumin daji zaki kawo mana mu aura maki!!!!" idanun Farhar ne suka ciko da ƙwalla tana tura baki tace ai ba a daji yake ba ko yana nan gidan kakar shi a Katsina kuma yanzu haka yana cikin yin Degree ɗin shi a Umyuk,
"Over my dead body.....!!! Wllh bazaki auri wannan dangin ƙarnin ba, anya ma kuwa kina cikin hankali ki...Not at all, Farha dana sani bazata ta6a son wani ɗan wannan Family ɗin ba so kuma na aure there must to be something behind all this..." har huci take tana Maganar cikin kuka Farhar tace ita Wllh itace kuma shi take so ai talaka da mai kuɗi duk ɗaya ne a wurin Allah aikuwa tun kafin ta rufe baki Hajiya Maryam ɗin ta yunƙura tare da kai hannu zata maketa da sauri ta goce tare da miƙewa ta nufi Dad ɗinsu ta faɗa jikinshi tare da ƙanƙame shi tana kuka tana faɗin ita Allah she will not marry Emran don bata son shi Kamal take so shi zata aura, aikuwa Mom ɗin ta ƙara yin kukan kura zata kai mata bugu Dad ɗin ya tare ta yana girgiza mata kai yace abi komai a hankali kada ta ji mata ciwo a fusace tace ai gara ta lahanta ta tunda ta raina mutane bata da hankali har su zata zo ma da wannan Maganar to in ma bata cikin hankalinta ne gara tun wuri ta dawo cikin shi don matuƙar tana raye bazata ta6a auren shi ba har taya ma aure zai yuwu tsakaninsu ai kalar zaren ba kalar yadin bane, ɗago kan Farhar Dad ɗin su yay yana kallon fuskarta da tayi jage jage da hawaye ta sigar lallashi yace mata ba gara ta auri Emran ba shida ya gina rayuwar shi yana da komai wannan da take so tace yanzu yake cikin yin karatu yaushe ya gama har ya samu aiki tunda ba yadda za'ai suyi auri bai da hanyar samun kuɗi, cikin muryar kuka tace ai yana yin business Dad ɗin ya tambayi wani irin Business tace suna da provision store a jikin gidansu tun kafin ta rufe baki cike da takaici Hajiya maryam ta kai hannu ta ciro hular kanta ta jefa mata a fuska Farha ta fashe da kuka tare da miƙewa ta nufi hanyar Bedroom tana tafiya tana bubbuga ƙafa tana faɗin ita Wllh shi zata aura itama Sis Fanan ba wanda take so aka bata ba cikin zafin nama Hajiya Maryam ta yunkura zata bi bayanta da sauri Dr ya riƙo hannunta ta juyo ta kalleshi tana huci kamar zakanya ya girgiza mata kai tare da yi mata alamar ta zauna, bayan ta koma ta zauna cikin kwantar da murya ya fara lallashinta tare da nuna mata komai a hankali yakamata a bi shi yaro ɗan lallashi ne in ta kwantar da hankalinta cikin rarrashi da kalamai sai taga tayi nasara akanta, haka ya dingi kwatanta mata har ta ɗan saukko ta miƙe tace bari ta sameta shima ya miƙe suka nufi ɗakin Farhar, lokacin da suka shiga tana saman gado ta kife fuskarta sai rizgar kuka take kai kace an faɗi mata saƙon uwarta ta mutu ne, a bakin gado duk suka zauna cikin kwantar da murya Hajiya Maryam ɗin ta kira sunanta shiru bata amsa ba saida ta ƙara sannan cikin kuka ta amsa tace ta tashi zasu yi magana ta fara ƙoƙarin ɗagowa idanunta har sunyi ja, zama tayi tana cigaba da yin kukan Mom ɗin tasu ta kai hannu tana goge mata tana faɗin ya isa, bayan ta ɗan tsagaita ne ta tambayeta yadda akai suka haɗu da Kamal ɗin cikin disashshiyar murya tace mata a wurin bikin Ya Nameer ne ta taho zata je yin liƙi shine ya bugeta bai gani ba har purse ɗinta ta faɗi ya bata haƙuri ya ɗaukko mata to tun daga nan taji ya burgeta daga baya ne tasan shi Yayan Fatuu ne har suka yi exchanging phone number suka fara gaisawa daga haka suka shaƙu shine ma dalilin daya sa taje bautar ƙasa Katsina, wani murmushin takaici Mom ɗin tayi tace "i know, wannan ba yin kan ki bane asiri ne" wani kallo Farhar tayi mata Hajiya Maryam ɗin ta ɗaga mata gira cike da tabbatarwa tace yess asiri ne ke ɗawainiya da ita Farhar tace amman shi ai bai santa ba ko sai ranar suka fara haɗuwa taya zata ce asiri yay mata tana murmushi tace mata ai su dama mutanen daji irinsu da an haifi yaro ake tsafe jikinshi don ya kasance yadda ake so to su tana jin na asirin nasara akai masu wannan dalilin ne yasa har Ƙanwarshi tayi nasarar auran Haisam ba don ta kai matsayin ya aureta ba kuma ya kasa sakinta haka Nameer ma shima abun ya faɗa kanshi yana ganin ƙanwarsu yaji yana sonta to itama kusan hakan ne, shiru Farha tay da alamun maganar ta ɗan yi tasiri a zuciyarta ta shiga tunanin ko shiyasa lokacin daya bugeta ta kasa yi mashi faɗa sai ma ji tay ya burgeta ko asirin ne ya shigeta can kuma wani bangare na zuciyarta ya shiga raya mata amman da asirin ne miyasa tunda suka haɗun bata ji tana son shi ba sai daga baya kuma koda ta furta mashi tana son shi farko bai amince ba kuma yan gidan su ma basu amince ba, koda ta faɗi ma Hajiya Maryam cewa itace fa ta fara cewa tana son shi kuma yangidan su da suka ji basu amince ba cewa sukai su haƙura gudun matsala sai cewa tay ai duk dubara ce sun san cewa sun riga sun asirce ta dole bazata iya haƙura dashi ba, shiru Farha tayi tana nazarin maganar a cikin ranta wani bangare na zuciyarta ya ƙi gasgata zancen asirin wani bangare kuma na son gasgatawa, lokaci guda ta fara ganin fuskar Kamalu ɗauke da ƙayataccen murmushin shi da maganarshi mai daɗi wata zuciyar ta raya mata yanzu shikenan sai ta haƙura dashi ƙilan ma Mom ɗin nata duk daɗin baki ne tayi mata ba wani abu ba, kamo hannunta Hajiya Maryam tay tace kada ta bari asirinsu yay tasiri akanta tazo taƙi mai sonta da gaskiya wanda zai treating ɗinta kamar Queen wanda zai mata duk abunda take so wannan kuma ƙarshe zata yi dana sani ne don ba iya ruƙeta zai yi ba kawai zai yi auren jari ne da ita don haka ta cire shi a ranta, shiru Farhar tayi tana kallonta yayin da zuciyarta ke ƙara tabbatar mata da wayau ne Mom ɗin nasu ke mata in ta rabu da Kamal kanta tayi mawa dama danginshi ba so suke ba dama, wani irin son Kamal ɗin ne taji ya taso mata cikin yamutsa fuska tace ma Mom ɗin ita ta tabbatar ba Asiri bane Allah ne ya saka mata son shi ita dai shi take so Wllh yanzu bata jin son Emran, wata uwar harara Mom ɗin ta wurga mata tare da sakin hannunta a fusace tace to tunda ita keda kanta ai sai ta aureshi ta gani daga haka ta tashi fuuu ta nufi hanyar barin ɗakin Farhar ta fashe da sabon kuka tana buga katifa Dad ɗinta ya matsa tare da jawota jikinshi ya rungumeta yana faɗin shikenan tayi shiru kada taja ma kanta ciwo cikin kuka take faɗin "Dad i love him, help me marry him pls" shiru yay yana shafa bayanta shi in don tashi ne indai har yaron yana da hali mai kyau to zai amince ta aure shi don mutum ne mai tsananin son yaranshi dama kuma haka turawa suke da son yara gashi suna ba yaran su yanci sam bai son abunda zai tada masu hankali ko ya 6ata masu rai shiyasa duk abunda suke so to yana son shi, jin ta ɗan lafa da yin kuka yasashi ɗagota yace ta kwantar da hankalinta indai har yaron baida matsala to yana tare da ita zai yi bakin ƙoƙarinshi ya ga ya taimaka mata ta samu abunda take so da sauri tace mashi wllh baida matsala ya kira Hajiya ya tambayeta yana da ilimin addini kuma yana da ƙokari gashi yana da ƙoƙarin neman na kan shi sam baida kwaɗayi don ko abu tayi mashi da ƙyar yake amsa, murmushi Dad ɗin yayi yace yayi kyau ya tambayi tana da hoton shi ya gani da sauri tace eh ta juya tana laluban wayarta, bayan ta ɗaukko ta shiga gallery ta dawo jikin Dad ɗin ta shiga nuna mashi hotunan Kamal wasu tare sukai wasu kuma shi kaɗai yana murmushi yace yana da kyau ta ɗaga kai ya sake cewa amman kamar ta girmeshi a shekaru tace a'a ya ɗan girmeta yace Ok yana son ta kwantar da hankalinta duk abunda Allah ya ƙaddaro shine zai faru ta ɗaga mashi kai,
Hajiya Maryam na fita ɗakinta ta nufa a zuciye tana shiga ta nufi bakin gado ta zauna ta shiga cize baki abun ya matuƙar daure mata kai wai ace Farha data sani itace zata ce tana son yaron wannan dangin tabbas bata tunanin yin kanta ne, a fusace ta kai hannu ta rarumo wayarta ta shiga kiran Hajiya bayan tayi ringing Hajiyar ta ɗauka murya ciki ciki ta gaishe da ita ta amsa daga haka tayi shiru Hajiyar tace ya akai ne taji muryarta wani iri ai kaman tana jira ta miƙe tsaye yadda zata ji daɗin kora bayani ta shiga faɗin wai Farha ce tazo masu da wani banzan zance na bata son wanda ke sonta ɗan dangin shanun nan take so ashe ma dalilin zuwan ta wurinta kenan yin service duk saboda shi ne, Murmushi Hajiya tayi tace ai tasan da Maganar suna son junansu, da tsananin mamaki Hajiya Maryam ɗin tace amman shine kuma ta ƙyale su bata hana abun ba,
"To akan mi zan hana Maryam, yara suna son junansu",
"Saboda bai kai yayi soyayya da ita ba Hajjaju", yar dariya Hajiya tayi "saboda shi ba mutum bane ko mi?",
"Mutum ne amman wanda bai kai yayi soyayya da ita ba" ɗan ta6e baki Hajiya tayi tace "to ni a wurina ya akai shiyasa ban dakatar da abun ba" yarfa hannu Hajiya Maryam tayi muryarta har tana sarƙewa wurin faɗin "Wai Hajjaju miyasa a koda yaushe kike goyon bayan bare ne taya za'ace wai kamar Farha ta auri wannan dangin ƙarnin" faɗaɗa dariya Hajiya tayi tace "A'a Maryam banda sharri, anan ai ba bare na goyi baya ba tamun na goya ma baya tunda ita ta fara nuna tana son shi hasali ma su dangin yaron ba so suke ba don kakarshi har nan ta same ni tayi man magana kan hakan kinga da bare na goya ma baya to zan ƙi abun ne", cikin huci tace ai duk wannan munafurci ne don sun san sun asirce Farhar Hajiya ta shiga girgiza kai tace "anya Maryam, taya akai wai kike neman barin imanin ki yay rauni ne, komai kice anyi asiri",
Murya kamar zata yi kuka tace to in ba asirin ba taya Farha zata kamu da son wannan yaron Hajiyar tace ta in Allah ya ƙaddaro hakan don haka tana bata shawara tabi komai a hankali in har Allah ya ƙaddaro aure tsakanin su to dole zasu yi, ai kamar Hajiyar ta watsa mata garwashin wuta a cikin zuciya cike da cin alwashi tace Wllh bazata bari Farha ta auri wannan yaron ba Hajiya tace ai shikenan ɗiyarta ce tayi duk abunda take ganin yayi mata Hajiya Maryam ɗin tace zatayi kuma ta faɗi ma kakar yaron in ma wani abu sukai ma ɗiyarta suyi gaggawar warware shi in ba haka ba duk abunda ya faru dasu to su suka siya ma kansu Hajiya tace tsakaninsu ne tazo da kanta sai ta faɗi masu,
tana niyyar kashe wayar Hajiya tace "Maryam ina son ki sani yadda kike uwar zamani haka Farha take ɗiyar zamani sannan yin jayyaya da ikon Allah tamkar ɗaukar dutsen Dala ba gammo ne don haka ina mai baki shawara da ki bi komai a hankali sannan kibar ikon Allah yay aikin shi, ki gaida man da kowa" daga haka ta yanke wayar,
komawa Hajiya Maryam tay ta zauna da6as saman gado ta shiga juya Maganar Hajiya ta ƙarshe nan take ta yanke wani abu a ranta, gaba ɗaya yinin ranar a cikin ɗaki Farha ta wuni koda lokacin cin abinci yay aka aiko kiranta ƙin fita tayi ƙarshe saidai Dad ɗin su yazo ya fito da ita suna zuwa Dining ɗin Hajiya Maryam ta miƙe ta bar wurin hakan yasa Farhar fashewa da kuka Dad ɗinta ya shiga rarrashinta, ganin abunda ya faru yasa da daddare Dad ɗin bai matsa ma Farhar ta fito ba bayan sun gama cin abincin ya ɗauki nata ya kai mata ɗaki saida ya zauna taci sannan ya baro ɗakin, a daren ta kira Fanan tana kuka ta faɗi mata abunda ke faruwa itama rarrashinta ta shiga yi tace tunda Dad ya nuna zai taimaka mata ta kwantar da hankalinta tasan Momynsu nada zuciya dole bazata goyi bayan abun ba ta cikin sauƙi amman itama tana goyon bayan abunda take so don haka zata tayata da Addu'a itama ta dage da yi tace to tare da yi mata godiya, suna gama yin wayar Fanan ta kira Mom ɗin nasu ko daga yanayin muryarta ta fahimci tana cikin 6acin rai, bayan sun gaisa cikin kwantar da murya Fanan ɗin ta fara lallashinta tana nuna mata ba aibu bane don Farha ta auri Kamal tasan kawai don basu da arzuƙi ne matsalansu kuma shi na Allah ne a duk lokacin daya so sai ya azurta bawa haka mai kuɗin ma duk yawan kuɗinshi cikin few seconds sai ya maida mutum talaka don haka suyi fatan alkhairi a gare su kawai, har ta gama maganarta Mom ɗin bata katseta ba saida ta gama tace mata ta gama Fanan ɗin tace eh kawai sai ta kashe wayar tare da buga uban tsoki, gaba ɗaya Farha ta koma rayuwar ɗaki washe gari lahadi da yamma Hajiya Maryam ta shirya komawa Abuja taci gayu cikin jigunannan lace ta soke kallabi bayan ta fito ne ta nufi ɗakin Farha lokacin data shiga tana kwance kan gado kamar mara lafiya tana ganin Mom ɗin nasu ta shigo ta yunƙura ta tashi zaune tana kallonta can ta gaishe da ita a hankali Mom ɗin ta ta6e baki tace ta ruƙe gaisuwarta bata so ai yanzu bata da daraja a wurinta saboda dangin shanu shiyasa bata iya zuwa ta gaishe da ita, idanun Farhar ne suka ciko da ƙwalla tace mata tayi haƙuri Hajiya Maryam ɗin ta ƙara ta6e baki tace ita ai zata ba haƙuri don tazo ne ta sanar mata nan da sati biyu za'a ɗaura auranta da Emran don haka gara ta tsaida hankalinta wuri ɗaya tana gama faɗin hakan ta juya ta tafi Farhar tasa wani irin kuka tana faɗin Wllh bazata aure shi ba Kamal zata aura in ba haka ba mutuwa zatai, daidai Hajiya Maryam ta kai bakin ƙopa ta watsa mata hannu daga haka ta fuce. Gaba ɗaya hankalin Dr ya tashi ganin halin da Farhar take ciki kullum cikin kuka ta daina cin abinci sai ya rarrasheta dole hankalinshi ya kasu biyu wurin aiki da kuma gida a haka har sati ya ƙare Hajiya Maryam ɗin ta dawo ya sameta don suyi magana ya nuna mata gara a bar Farhar ta auri wanda take so don tana niyyar lahanta kanta Hajiya Maryam ɗin tace ya rabu da ita duk tana yi ne don a saduda a goyi bayanta da an ɗaura masu aure da Emran ya tafi da ita America zata koma daidai, bayan ta gama Weekend ta koma an shiga wani satin ganin yana niyyar rasa ɗiyarshi yasa ya kirawo Hajiya ya sanar mata halin da Farhar ke ciki da hukuncin da Hajiya Maryam ta yanke na ɗaura masu aure da Emran a satin Hajiya na jin haka ta saka salati tace Maryam badai taurin kai ba ai ita bata san da ta yanke wannan hukuncin ba tace ma Dr ɗin abunda za'ai yasa Farha ta rubuta takarda cewa tunda an hanata wanda take so to ta shiga duniya kuma kada a nemeta don baza'a sameta ba in ta rubuta sai ya turo mata ita amman kada ta hawo jirgin Katsina ta hawo na Kano in ta sauka sai ta hau Motar haya ta ƙaraso Katsina sannan kada ya bari kowa yasan da wannan plan ɗin daga shi sai Farhar kuma ya siya mata sabon layin waya sannan itama wayar ya siya mata ƙarama tata ta baro ta nan gida, bayan sun gama wayar tasa ya kai ma Farha wayarshi ta sanar da ita yadda sukai da Mahaifinta tace mata ta kwantar da hankalinta ta samu niƙab in ta isa kano ta saka shi a fuskarta har ta iso Katsina sannan kuma tayi dubara ta saka dogon Hijab a park ɗin data iso Katsina sai ta kirata ta sanar mata zata sa azo a ɗauketa da sauri tace to, kamar yadda suka tsara haka sukai ya sakata ta siya ticket ta online washe gari ya kama talata lokacin duk ƙannanta sun tafi School shima Dad ɗin ya fito daga gidan matsayin ya tafi aiki bayan wani lokaci ya kirata ta sabon layinta yace ta fito daga gidan koda wani zai tambayi ina zata tace zata je Abuja ne wurin Mom ɗinta, tana janye da madaidaicin trolley ta fito cikin sa'a har ta fito daga gidan ba wanda ya ganta sai Security dake gadin gate da suka gaisa suka tambayi unguwa zata je ne tace eh zata Abuja wurin Mom ɗinta har wani yace to ina driver ta fito ita kaɗai tace bai dawo daga kai su Noor School ba tana sauri zata hau taxi kawai sukai mata Allah ya kiyaye, bayan sun haɗu da Dad ɗin nata inda ya tsaya tace ya bari ta hau taxi tunda in ya kaita Airport za'a iya gane plan