Showing 144001 words to 147000 words out of 512766 words
Chapter 49 - Asanadin Makwabtaka Book 3 Hausa Novel Complete
Unknown
27 Dec 2024
1646
jira fa duk suka mik'e ya d'aga murya yana ma Fatuu sai da safe, yana shirin juyawa Feenah tace don Allah ya taimaka mata da Abdul yadda yay baccin nan ba iya d'aukar shi zatay ba ya k'arasa shigowa cikin d'akin ta kinkimo mashi Abdul d'in ya kar6e shi ya sa6a a Shoulder yana fad'in Allah ma ya taimake su da yayi baccin ai da ba k'aramar rigima za'ai dashi ba don yana iya cewa nan zai kwana ba kamar yana ganin gidan Baban shi da Momy d'in shi ne duk sukai dariya ya juya ya nufi kopa suma suka bi bayan shi Fatuu ta fara k'ok'arin saukkowa daga saman gadon Fauzy dake kallonta tace ina zata, jin haka yasa su Aunty Mareeya juyowa suma suka tambayi inda zata fuskar ta kaman zatai kuka murya na d'an rawa tace raka su zatai, waro ido tay tace a ina ta ta6a ganin Amarya tayi rakiya ta koma ta zauna kafin Angon ta ya zo, ba yadda ta iya dole ta koma ta zauna suka tafi banda Fauzy da tay tsaye ta kasa tafiya yanayin fuskar ta ya sauya itama kaman zata saka kukan, bin juna da ido sukai can k'walla suka zubo ma Fatuu sharrr Fauzy ta d'an girgiza mata kai daga inda take tsaye tace "ki daina kuka Zarah lokacin farinciki ne yanzu, Allah yasa Alkhairi ya baku zaman lafiya sai mun had'u School" da k'yar ta k'arasa Maganar, jin kuka na niyyar k'wace mata yasa ta juya da sauri ta fita, tana fita Fatuu ta d'age k'afafunta ta kife fuskar ta tana kuka a hankali.................
_Littafin A Sanadin Makwabtaka part 2 Naira 300 ne za'a tura ma Mutum har part 1 ga mai so zai turo kudin ta wannan Account din, 1509618776, Zainab Bature Access Bank, za'a turo shedar biya ta wad'annan nos din 09013804524 ko 08169856268
[5/8, 19:28] +234 901 700 4868: *ASM Bk2059*
_Destiny may be delayed but cannot be changed...._
*DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI*
.............Fauzy na zuwa ba 6ata lokaci suka tafi don itama Fatun ta gama shiryawa, sai Magrib ta dawo Fauzy an sauketa a School, daka kalli fuskarta ma zaka gane tasha gyara ga wani k'amshi da jikinta ke fitarwa, lokacin data shiga gidan d'akin gwaggo ta nufa ta isketa ta dawo tana yin salla hakan yasa ta juya ta nufi d'akin ta, a gaban dressing mirror ta tsaya bayan ta cire veil d'in da tayi rolling ta fara k'are ma kanta kallo tana sakin murmushi, hannu ta kai tana shafa kumatun ta da har wani glowing suke, skin d'in ta ta k'ara yin sumul gwanin taushi dama a mulke take Saboda tsadaddun mayukan da take amfani dasu, bayan wani lokaci ta d'auki gyalen ta da ta ajiye a gefen mirror ta fita, d'akin gwaggo ta koma ta iske ta gama Sallar tana zaune kan darduma tana tasbihi, gefen ta Fatuu ta nufa ta zauna suka had'a ido ta sakar mata murmushi saida ta shafa sannan itama ta mayar mata da murmushin tace "Auta ta ta fara fitowa sak Amarya" murmushi kawae Fatun ke yi ta gaishe da ita bayan ta amsa ta tambaye ta Fauzy tace mata an aje ta a Makaranta ta d'aga kai, d'an shiru su kai suna ta yi ma juna murmushi daga baya Fatuu tay mata Maganar kud'in d'azu da aka turo da wanccan da tay mata Maganar su gwaggon ta tambaye ta ta tura ma Aunty Mareeya tace mata eh, tace to ai nata ne ba zatay amfani dasu bane, d'an shiru Fatun tay kafin tace "ni ba abunda zan yi dasu kawae dae ina tunanin zuwa shagon Aunty Zee in siyo wasu kaya" gwaggo dake kallonta ta tambaye ta wane irin kaya ko na sawa tace mata eh, tace "Yanzu duk kayan da ke gare ki sai kin k'ara,wasu ma fa baki ta6a sakawa ba sai aita tara kaya don ma ana bayarwa, duka yaushe Chairman ya baki akwati biyu na kaya ga shima Yayan naki da zai tafi yay maki akwatunan kaya ga wad'anda kike siya duk basu isa ba ki tattara abun ki ki tafi dasu sai kin k'ara wasu" da d'an alamun kunya Fatun tace "d...dama wai ko wanda zan sa ranar Juma'a d'in ne da yan underwear" da k'yar ta k'arasa Maganar had'i da sunkuyar da kai gwaggon tace "ni ina ganin tunda lokaci ya riga ya k'ure kawae ki bar shi yanzu yaushe har aka d'inka ma tunda kina da sababbin kayan da baki ta6a sawa ba ko cikin su ne ki za6i d'aya sai ki saka, nasan ma ko daga bayane zai maki suturar tunda hakanan ma yayi bare kuma yanzu, kawae don lokaci ya k'ure ne amman su underwear d'in zaki iya siyowa" kai ta d'aga mata alamar to, "to wai ma kin had'a kayan naki ko kuwa baki had'a ba?" a hankali ta girgiza mata kai alamar a'a, tace "to har sai yaushe ko sai lokaci ya k'ure kizo Kita faman duminiya" d'an yamutsa fuska Fatuu tayi kaman zatai kuka tace "ni wllh gani nike kaman wasa ba gaske ba wai zan bar gidan nan" yar dariya gwaggo tay tace "ki bari sai ranar zaki shaida in wasa ne ko gaske, in Allah ya kaimu ranar Juma'a kaman yanzu ai ina sa ran kin ma bar gidan nan" cike da shagwaba tace "Wayyo Allah, wllh gwaggo ban jin dad'i zan rabu daku zan koma wani wuri" tana rufe baki k'walla suka zubo mata sharr gwaggo dake ta dariya tace "ni kuma kinga dad'i nike ji..." Katse ta tay da fad'in "kai gwaggo dama ashe kin gaji dani" tace "ai abun farinciki ne yanzu ka ga naka yayi aure ba kamar da auren yay wuya yan mata da dama nata neman mijin aure babu, gashi ke kin samu d'aya tamkar da miliyan don wannan wuce dubu, in na ce banji dad'i ba ai na zama butulu ban gode ma Allah ba daya amsa man Addu'ar da nike maki koda yaushe ta ya baki miji na gari" d'an murmushi Fatun tay ta sunkuyar da kai can ta d'ago tace "nama ji dad'i daba nesa bane zan rink'a zuwa koda yaushe...." Da sauri gwaggo ta tari numfashin ta "ki rink'a zuwa ina? aikuwa dana sa6a maki wllh mi kika d'auki aure ne, abun wasa ko mi to a hir d'in ki kika ce zaki rink'a yin sunturi kina zuwa sai na sa6a maki kuwa, Mutuncin mace ta zauna a d'akinta sai ta kama ta fito" tana ta yamutsa fuska tace "kaman ma ke bazaki missing d'ina ba" tana yar dariya tace "ba kuwa zan yi ba tunda na samu madadin ki, Mino zan d'aukko ta dawo nan dama nayi mata alk'awarin zata dawo" d'an waro ido Fatuu tay ta fara sakin murmushi cike da farinciki tace "Yanzu Mino nan zata dawo kenan?" Kai ta d'aga mata, "amman kuma ai bata gama Secondary d'in ba" gwaggo tace "Eh aji biyar ta shiga in ta dawo nan sai ta k'arasa ai" sosae Fatuu taji dad'i sai faman washe baki take, tana matuk'ar son yan'uwan ta don kuwa mahaifiyar su itama tana son ta suma kuma haka don in ba ka sani bama baka cewa ba uwar su d'aya uban su d'aya ba ba kamar dae Mino d'in bala'en kama take da Fatuu, tana zaune a d'akin akai sallar isha gwaggo ta tashi tayi ita kuma ta koma d'akin ta, bayan gwaggo ta gama d'akin Fatun ta nufa tana shiga ta iske ta a kan gado tana latsa wayarta tace mata ta tashi ta taya ta su had'a kayan nata tace to, saukko da akwatunan ta sukai daga saman wardrobe gwaggo ta bud'e wardrobe d'in ta fara za6o mata wanda zata tafi dasu ita kuma tana jerawa, suna cikin haka taci karo da k'umshin ledar magungunan da Aunty Mareeya ta fara aiko mata ta fiddo tana fad'in miye aciki, d'an zaro ido Fatuu tay ganin gwaggon na kokarin kwancewa yasa gabanta ya hau fad'uwa ta sadda kanta k'asa, bayan ta bud'e k'ura ma abunda ke ciki ido gwaggo tay ta kai hannu ta fiddo da yar kwalbar ciki ta d'aga tana duba takardar jiki lokacin Fatuu ta d'an d'ago gwaggon ta jefa mata wani mugun kallo ba shiri murya na rawa tun ma kafin ta tambaye ta ta hau yi mata bayanin wadda ta bata, har saida gwaggo taji d'an sanyi don da hankalin ta har ya tashi ta maida kwalbar ciki kafin ta kalleta sai yan kame kame take ta tambayeta ta yi amfani dasu ne tace mata a'a gwaggon tace to Saboda mi ba bata akai don tayi amfani da su ba, cikin yar in ina ta ce mata na kwalbar dole sai jinin ya d'auke su kuma sauran wani da nama ake cin shi wani kuma da peak milk tana Maganar tana sussune kai, yar ajiyar zuciya gwaggon tay tace mata taje wurin Amadu ta amso Madarar da sauri tace to ta juya gwaggon ta bita da ido har ta fita, bayan ta amso tasa ta d'aukko Kofi da cokali a Kitchen ta tambayeta yadda aka ce a had'a ta fad'i mata da kanta ta shiga had'a mata bayan ta gama ta bata ta shanye daga baya suka cigaba da abunda suke.
Washe gari wurin Misalin k'arfe sha d'aya saura na safe aka kira Aunty Mareeya daga tasha cewa ga sak'o an kawo mata daga Kano tace to suka fad'i mata tashar da suke, kiran Daddyn su Hanif tay ta sanar dashi zata je ta dawo, ba 6ata lokaci dama tana ta dakon isowar kayan ta tafi, bayan ta amshi sak'on magungunan direct gidan su Fatuu ta nufa lokacin tana Makaranta sai gwaggo ta tarbeta tana ta fara'a suka shiga Parlor, gaisawa suka shiga yi daga baya Aunty Mareeya ta warware kwalin da aka sako sak'on ciki ta shiga firfito dasu tana yi tana ma gwaggo bayanin kowanne ta shiga yabawa tana sa Albarka ita kanta taga sauk'in kayan gasu da yawa, bayan ta gama fiddo su ta nuna mata wanda yakamata a fara ba Fatun zuwa ranar tarewar sauran kuma sai ta tafi dasu taci gaba da amfani dasu a can gwaggon tace to da ta dawo sai a fara batan, sosae tay ma Aunty Mareeya godiya tana Allah ya bar zumunci daga baya ta tambaye ta ko akwae wani abu gwaggon tace ehh kayan k'amshi take so an mata kwatancen in da zata samu to ita kuma ba sanin kan su tay ba Aunty Mareeya tace wannan ba matsala bane akwae inda za'a same su masu kyau jera mata kawai za'ai don already a kwalaben su masu kyau suke nan ma godiya gwaggon tay mata ta tambayi kaman nawa zasu isa ta fad'i mata, bayan sun gama Maganar kayan k'amshin suka shiga Maganar Abinci da za'ai ranar Juma'ar, saida suka gama tsara komae Gwaggon ta bata kud'in abubuwan da zata siyo sannan ta tafi. Tun Aunty Mareeya na kan hanya ta kira Fauzy ta sanar mata zancen isowar sak'on Magungunan taji dad'i sosae ta sanar ma Fatuu ita dae d'an guntun murmushi kawai tay, bayan an tashi Hostel suka wuce Fauzy ta had'a kayanta a cikin d'an trolley zata bi Fatun kaman yadda suka tsara a aji ita da dawowa cikin Makaranta sai bayan ta tare daga baya Haisam yazo d'aukar su, tun bayan da suka shiga Motar suka gaida shi ba wanda ya k'ara cewa uffan har suka isa gida, suna shiga d'akin gwaggo suka wuce tana ta fara'a tay masu sannu da dawowa suka gaishe da ita tace in sun kimtsa su zuba Abinci yana Kitchen suka ce to suka nufi d'akin Fatuu, suna cikin cin Abincin gwaggo ta k'wala ma Fatun kira bayan taje ta bata wasu daga cikin Magungunan da aka kawo kaza da cicci6i da kuma zabuwa duk ta d'ibar mata tace taje ta cinye su duka harda romon su tace mata to ta koma d'aki Fauzy na zaune tana cin Abincin ta shigo ta koma inda ta tashi ta zauna, koda Fauzy taga abunda ta shigo dashi nan take ta gane na maganin ne tunda taga hotunan su jiya ta hau yin murmushi Fatuu ta aje tace su ci Fauzy ta zaro ido tace ta rufa mata Asiri wannan yafi k'arfin ta saidae itan tay d'an murmushi kawae ta kai hannu ta yago naman kazar ta kai baki koda taji taste d'in ta ba Arziki ta d'an yamutsa baki da k'yar ta had'iye na bakinta a tunanin ta ko kazar ce kad'ai haka sai ta d'ibi cicci6i shima tana kaiwa baki taji shi salaf sai kaifin magani bayan ta had'iye ta kalli Fauzy tace don Allah ta ci da dad'i sosae jin haka yasa ta cewa tunda ta matsa mata bari ta d'an ci ta kai hannu ta yagi kazar Fatuu nata gumtse dariya gaba d'aya ta kai naman baki ba Arziki itama ta tsaya cak ta kasa taunawa ta d'an zaro ido Fatuu kau mi zata yi in ba dariya ba, da k'yar Fauzy ta had'iye tana d'an yamutsa fuska ta kai hannu ta d'auki ruwa ta kwankwad'a bayan ta aje tace "tabb, ni fa koda na ganta na zata Normal farfesun kaza ne ashe ashe duk farfesun magani ne wannan dole ma tay aiki a jiki kam" koda Fatuu tace mata ta k'ara don Allah cewa tay wllh in ta ganta a lahira kaita akai hakanan taja ma kanta bala'e ta kasa zaman lafiya ita dae daya zamar ma dole taci Fatuu tay ta mata dariya, daurewa tay taci gaba da ci daga baya ma lafiya lau ta rink'a ci har ta cinye ta shanye romon kaman yadda gwaggon tace, bayan sun gama suka hau shirin tafiya gyaran jiki da wankin kai don gwaggo tace kitso za'a yi mata, da daddare bayan sun dawo sun ci Abinci gwaggo ta kara kiran Fatuu ta bata tsumi kusan kala ukku ta sha harda na magarya mai wanko mara yay maganin sanyi aikuwa sosae yay ma Fatuu aiki don duk wani sauran jini daya rage saida ya fito a daren,
Washe gari Alhamis da safe bayan sun yi breakfast suka hau shirin tafiya Makaranta Haisam ne yazo ya d'auke su, Bayan an tashi ya d'aukko su suna dawowa Abinci kawae suka ci suka hau shirin tafiya k'unshi lokacin da Fatuu ta shiga toilet yin wanka har saida ta d'an yi mamaki ganin Pad d'in data sa da safe Kandas ba jini alamar dae ya d'auke hakan yasa bayan ta gama wanka ta had'a dana tsarki tayi sannan ta fito, tana komawa d'aki ta zura doguwar riga don yin salla Fauzy na ganin haka tay yar shewa ta hau tsokanar ta tana fad'in an yi a daidai abun ya mata dad'i wllh, ita dai d'an murmushi kawai tay ta girgiza kai, bayan duk sun shirya suka tafi, Ana gama sallar la'asar sai ga Saude tare da Tk rike da wasu jakunkuna masu shegen kyau guda ukku Gwaggo ta tarbe su suka shiga cikin parlor, bayan sun gaisa Saude tace mata gashi in ji Hajiya tace Fateema ta fara amfani da kayan ciki gwaggo ta hau godiya Saude ta k'ara cewa da Mota suka zo tace a kwaso kayan kitchen da sauri gwaggo tace to ta mik'e suma suka mik'e gaba d'aya suka fita, saida ta lek'a waje ta kira Amadu ya shigo aka fara kwashe na cikin d'akin shi ana kaiwa cikin Hilux d'in da suka zo da ita daga baya aka kwashe na cikin d'akin Fatuu, sai bayan da suka tafi ne gwaggo ta koma parlor ta bud'e jakunkunan ta fara dubawa, kaya ne ciki dinkakku lace kala biyu atampa kala ukku sai shadda data sha uban aiki itama kala biyu sai lifaya da dogayen riguna suma kala bibbiyu a cikin d'ayar jakar mahad'in sune wato takalma da mayafai harda hijab da jakunkuna sai cikin ta k'arshen underwear ne harda rigunan bacci dasu sark'ok'i da kuma kayan shafa duk da kayan basu da yawa amman fa da ka gani kasan masu kud'ine ba k'ananun kaya bane, bayan gwaggon ta gama dubawa ta hau jinjina kai cikin ranta take raya ita dama ranta ya bata da wuya ba'ai ma Fatun kaya ba, maida komai tay ta mik'e ta fita, d'akin ta ta koma tana zuwa ta kira Hajiyar a waya tay mata godiya ta tambayeta ba wata matsala tace mata eh ta k'ara yin godiya sosae da Addu'oi. Bayan su Tk sun kai kayan ta k'aramar kopa suka rink'a shiga dasu shida Amadu da gwaggo tasa ya bisu Saude ma ta fara d'auka Officer ya taso yace ta barshi ya kama aka rink'a shigar dasu tare da shi ita kuma ta nufi cikin part d'in don ta fara jerawa kaman yadda Hajiya ta bada umarni har aka shigar da komae. Yau ma sai bayan Magrib suka dawo har Fauzy ma anyi mata k'unshi gwaggo na gani ta hau yabawa don ba k'aramin kyau yay ba ya zanu rad'am abun ka da farare kuma gashi ja da bak'i ne yay gwanin burgewa gwaggo ta nuna masu kayan da aka kawo suka fara dubawa Fauzy nata santi ita dae Fatuu murmushi kawai take.
JUMA'AT BABBAN RANA
Washe gari da wani irin yanayi Fatuu ta tashi ta kasa gane farinciki take ko damuwa gaba d'aya kasala ta baibaiye ta har Fauzy ta fahimci hakan ta tambayi Mike damunta tace ita dae gatanan ta rasa Mike mata dad'i ma yar dariya Fauzy tay tace zullumin barin gida ne, Bayan sun yi breakfast suka yi shirin tafiya Makaranta, koda Fatuu taje yima gwaggo sallama cewa tay ai tayi zaton zasu hak'ura da zuwa yau Fatun da tay sukuku tace ai ko sun zauna ba abunda zasu yi gara su tafi gwaggon tace shikenan itama ta lura da yanayin ta har saida ta tambayeta wani abu ke damunta ne tace mata ba Komai ta juya zata fita gwaggon ta bita da kallo tana d'an murmushi, tana komawa d'aki ta jiyo horn d'in Haisam suka fito, Bayan tafiyar su makwabta suka fara shigowa don gwaggo duk ta sanar dasu zancen auren da tarewar kowa yaji sai ya taya ta murna har innar su