Showing 231001 words to 234000 words out of 512766 words
Chapter 78 - Asanadin Makwabtaka Book 3 Hausa Novel Complete
Unknown
27 Dec 2024
1621
Mareeyar ta nufa dama tare suke suna kallo a parlor ta tashi taje ta dawo, a daidai bakin k'opar bedroom d'in nata sukai kacibus don ta jiyo k'wala mata kiran da take, cike da farinciki ta hau bata labarin abunda ya faru tun kafin ta k'arasa ta mik'a hannu ta amshi wayar dama duk Fatun na jin su, tana amsa cike da Farinciki harta kasa rufe baki ta kira sunan Fatun itama tanata murmushi ta amsa mata kafin ta gaishe da ita, Cike da tsantsar farinciki tace "ashe wai haka abu ya kasance, shima bawan Allah ashe ashe yana ta gurzuwa" yar dariya Fatun tay tace mata eh,
"Kai jama'a! Wannan cutar kai har ina kana son abu kuma abun nan ya zama mallakin ka Saboda tsabar cutar miskilanci ka tauye ma kan ka hakki" cike da jin kunya Fatun ta fad'i mata dalilin shi na yana son sai dangin shi sun sani, cikin washe baki tace "duk da yana da dalili amman ai da sai ya maki bayani ko yanzu da yasa zuciyar ki ta buga fa d'an bantan uba da yafi kowa shiga hali kuwa k'ilan ma tashi itama ta buga don na lura irin soyayyar laila da majnun kuke ma juna an sha yan ciwoce ciwoce" dariya Fatuun take ta yi Aunty Mareeyar ta shiga taya ta murna ta kuma yaba ma Fanan tace gaskiya tayi namijin k'ok'arin da ba kowace mace zata iya ba don ita kanta Maganar gaskiya bazata iya ba, daga baya kuma tace to kuma irin haka in har mutum ya fito ya bayyana maka in baka amince ba kai kanka ba samun kwanciyar hankali zaka yi ba, k'arshe kuma tace Allah ma kada ya kawo wacce zata siye mata zuciyar miji haka Fatuu dai sai dariya take, yar Nasiha ta d'an yi mata ta kuma ja hankalinta kan kula da miji dasu kwalliya tace sai sun had'u zata mata karatu sosae,
"Yanzu Zarah nace sai in maido magungunan aro ko, dama shekaran jiya tayi promo jiya aka kawo man wanda na siya" shiru ta d'an yi kafin cikin jin kunya tace mata eh to tunda akwae, dariya Aunty Mareeya tasa tace "ja'ira da ba kince in ma kwashe duka ba, in ce dai na farkon sun yi maki aiki yadda nike ta fata Allah yasa ya magantu iya magantuwa" k'asa k'asa Fatun tace mata eh, kafin da k'yar tace mata harda kuka ma, wani irin ihu da Aunty Mareeya ta saki har saida Fatun ta cire wayar daga kunnanta tana dariya Fauzy ce ta taso da sauri tana tambayar Auntyn wai mi akai tay mata alamun ta tafi da hannu tace mata Maganar manya ce wannan, ce mata tay zata bada in zata je Makaranta gobe sai Fauzy ta tafin mata da su tace eh zata je, daga baya sukai sallama sai farinciki Aunty Mareeya ke yi, bayan Fauzy ta amshi wayar itama sukai sallama tace mata sai sun had'u School gobe, Fauzyn tace ita da ke shan Amarci ta bari ta gama, Fatuu na yar dariya tace yadda in jarabawa tazo zata rubuta hakan ko, duk suka yi dariya nan tayi ma Fauzy godiyar sak'on da ta tura tace dama koda ta nuna bata ji dad'i ba Saboda gudun abun da zaije ya dawo ne, Fauzyn na dariya tace mata haba ba komai ai tun lokacin ta fahimceta tayi mata Addu'ar Allah ya sanya Alkhairi ya basu zaman lpy yasa nan da nine months su sha suna Fatuu dai nata dariya daga baya sukai sallama. Cikin parlon Fauzy ta koma ta zauna kusa da Aunty Mareeya nan suka dasa hirar farinciki Fauzy na fad'in ita wllh dama ranta ya bata shima yana son Zarah bawan Allah ashe ma ya fita shiga hali.
Saida aka gama sallar isha Haisam ya dawo yace mata ta shirya suje part d'in Hajiya suci Abinci tace to, k'ananun kaya skinny jeans da riga wadda ta hau da shi ta fiddo, yana kwance saman gado ya jingina da headboard yana kallonta ta fara shiryawa, tana yi suna sakar ma juna murmushi in tazo kan abunda take jin kunya sai ta duk'e k'asa a haka har ta gama sakawa ta nufi gaban mirror tana gyara parking d'in gashinta, kasa jurewa Haisam yayi ya saukko daga gadon Slowly ya nufe ta, ba zato taji ya rungumota ta baya har saida ta d'an yi firgit, hannu ya kai ya janye gashinta data baza shi tana sharcewa fuskar shi da ya d'aura akan shoulder d'inta ta bayyana, murmushi suka shiga sakar ma juna ya d'an lumshe ido ya furta mata "Baby you're very beautiful" itama Lumshe mashi ido tay itama ta furta "Hubby you're very Handsome man" gaba d'aya sukai murmushi, hannuwan shi yasa yana bin shape d'in jikinta tamkar yana zana ta, d'an runtse ido da mak'e kafad'a Fatuu ta shiga yi, ganin bai da niyyar dainawa yasa tace mashi zai hanata ta gama shiryawa su tafi, juyota yay ya kai hannu ya fara k'ok'arin yi mata parking d'in gashin, suna haka take ce mashi wai a da can da ya fara saninta yana ganin kyaun ta, shiru yay yana d'an murmushi kafin yace bazai iya ganewa ba kawai dai yasan komai nata na burge shi, bayan ya gama d'aure mata gashin d'ago da ita yay ya d'aura ta akan k'afafun shi yadda ta d'an k'ara tsawo hannuwan shi tallafe da waist d'in ta itama ta zagayo da nata hannuwan ta bayan shi, bin juna sukai da wani irin azababben kallo kowa K'ok'arin nuna irin k'aunar dayake ma d'an uwan shi yake ta cikin kallon, As they held each other close, their bodies seemed to melt together like two puzzle pieces that were made for each other, Fatuu ce ta sare ta rufe fuskar ta a jikinshi idonta a lumshe can k'asan mak'oshi taji ya furta yana son ta itace best thing d'aya ta6a faruwa dashi tana mak'ale dashi ta furta mashi itama haka, d'agota yay suna sakar ma juna murmushi yace suje tace bari ta d'aura After dress, bayan ta d'aukko ta saka tayi rolling veil d'in ya kama hannunta suka tafi.
Wuraren k'arfe goma da rabi lokacin basu dad'e da dawowa ba suna zaune a parlorn su suna kallon American film Fatuu ta cire after dress d'in tana mak'ale jikinshi kamar yar mage sai shak'ar k'amshin juna suke, d'aga kai tayi ta kalle shi tace mashi gobe zata je school, shiru ya d'an yi yana kallonta kafin yace bazata bari ta huta ba, a d'an shagwabe tace mashi Exams d'in su ta taho fa Upper week zasu fara bata son ayi wani abun bata nan kuma ma test ake ta masu, jinjina mata kai yay suka cigaba da kallon, bayan wani d'an lokaci taji ya fara magana ta k'ara d'aga kai tana kallon shi, shima kallon ta yake yace mata jibi Fanan zata tafi Lagos yana son zasu rakata, jimm Fatuu tay tana kallon shi ba tare data ce mashi komai ba hakanan sai taji bata son zuwa duk da bazata so ya tafi ya barta ba, ganin tayi shiru yasa shi tambayarta ko bazata rakata ba, da alamun yar damuwa tace ba wai bata son zuwa ba kawae dai bata son wani abu ya faru in taje gidan su, shiru ya d'an yi yana nazarin Maganar tata can yace mata Shikenan sai su sauka a Hotel kawai, bin shi da ido Fatuu tayi don hakan ma bata ji ya kwanta mata ba gani tay in suka yi haka kuma ai kaman ba'a kyauta ma Fanan d'in ba anan suna tare kuma acan ma su ware duk da bata san ya suka tsara da ita ba game da kwanakin da zaiyi da ita ba,
tambayar shi tay kwana nawa zasu yi yace just 2 days, sauke idanunta tayi ta shiga tunanin tunda ba dad'ewa zai yi ba kodai ta k'i bin shi don k'arshen ta hakan ba komai zai k'ara mata ba face bak'in jini a wurin su Hajiya Maryam in dai suka san da ita yaje kuma ya sauka da ita a Hotel tunda dai tasan ai k'ilan duk in suka je da Fanan a gidansu suke sauka, tana haka taji ya tambayi koda wani matsalan ne, kallon shi tay ta d'an girgiza mashi kai kafin a sanyaye tace tana jin saidai yaje ya dawo don a jibin tana da test, shiru ya d'an yi sai kuma yace Ok bari a d'aga tafiyar sai bata da test d'in da sauri tace "Ai Hubby daga jibin fa kusan kullum sai munyi don upper Wednesday zamu fara exam, tunda just 2 days ne ka rakata kawai" shiru yay yana kallonta sai d'an yamutsa fuska take, sam ba haka ya so ba don a yadda ya tsara tare zasu, ganin yanayin shi yasa ta kai hannu tana shafa kwantacciyar sumar sajen shi cikin nuna damuwa tace "You shouldn't worry pls" d'an murmushi yay ya lumshe mata ido, cigaba da shafa beard d'in tayi shi kuma yaci gaba da kallon yana yi yana maido idon kanta, k'arfe 11 na yi yace suje su kwanta tunda zata school suka mik'e a tare yana ruk'e da hannunta sai kace k'anwar shi, bayan ya kashe kayan kallon ya rage hasken Parlon suka nufi Bedroom yana tallafe da ita.
Washe gari bayan ta gama shiryawa tare suka fito da shi zai kaita, saida suka tsaya suka d'auki Mino sannan suka wuce, Mino aka fara ajewa suka wuce, a inda ya saba ajeta nan yayi packing ta kalle shi tana murmushi tayi mashi godiya tana niyyar juyawa ta bud'e kopar taji ya ruk'o hannunta ta juyo ta kalle shi, idanun shi a d'an lumshe ya jingina kanshi jikin headrest, tana kallon shi ta fahimci ruk'on kona miye tay mashi nuni da lip glow d'in da ta shafa ya ida lumshe idon, matsawa tay wurin shi ta kai baki ta manna mashi kiss a kumatun shi tana niyyar janye fuskar ya ruk'o kan, lokacin daya saketa gaba d'aya ba lip glow d'in, komawa tay ta zauna itama ta jingina kanta da kujerar tana breathing rapidly haka shima, bayan sun natsu ya tambayi tana tare da Atm d'inta ta d'aga mashi kai yace ok zai tura mata kud'i ta tabbatar taci Abinci mai kyau ta k'oshi nan ma kai ta d'aga mashi suna kallon cikin idanun juna, har zata juya taji yace ko ya kawo mata Abincin da break, da sauri ta girgiza mashi kai tace a'a ai anan akwae Abinci mai kyau zata ci.
A class ta iske Fauzy don da wuri tazo Saboda zumud'in ganin Fatun, tana shiga ta taso da gudu tazo ta rungume ta cike da Farinciki itama Fatun sai dariya take, bayan sun je sun zauna gaba d'aya Fauzy ta kafeta da ido tana ta washe baki sai kace wadda aka ma Albishir mai dad'i tama kasa Magana, Fatuu na dariya tace "wai sai kallo na kike sai kace yau kika fara ganina" yarfa hannu tay tace "bazaki gane irin farincikin da nike ji ba wllh don abu ne da ban yi zaton shi kusa ba, kinga wai yadda kika canza cikin kwana biyu kacal har fa wani glowing kike wllh ga k'amshin amarci, koda yake dama fa irin su Ya Haisam ba dai iya zuba ruwan love ba wllh kina ganin su shiru shiru sai hum....." dariya kawae Fatuu take ta kasa cewa komai itama Fauzyn dariyar take can tace "k'awata kukan ya Haisam bai damu da ni ba bai sona ya k'are ko" bugu Fatuu ta kai mata tana fad'in "leave me alone Fauzy" gaba d'aya dariya suke a haka malamin su ya shigo, tun bayan da malamin ya fara masu bayani Fauzy na lura da Fatuu sai faman sakin murmushi take da gani ba K'aramin nishad'i take ciki ba, sai da akai break sun fito take ce mata ita wannan Amarcin anya ma zai bari tayi wani karatun Exams Malam na explanation tana sakin murmushi inaga in jarabawar tazo kar ta kai fa in aka tambayi zane ta zana Ya Haisam, sosae Fatuu ke dariya suka nufi inda zasu ci Abinci.
Da yamma wurin sallar la'asar Fatuu ta fito daga wanka, bayan ta zura doguwar riga ta kabbara salla, tana gamawa ta nufi gaban dressing mirror ta fara shirin zuwa part d'in Hajiya, tun bayan daya d'aukkota daga school suna dawowa suka ci Abinci ko wanka bai bari tayi ba suka kwanta bacci, sai da aka fara kiran sallar la'asar ya farka yaje yayi wanka bayan ya fito ya shirya ne ya tasheta ya sanar da ita time d'in salla yayi, tana cikin yin shafan aka yi knocking k'opar Bedroom d'in ta juya ta nufi kopar, tana bud'ewa suka had'a ido da Fanan ta sakar mata murmushi tana sanye da fitted gown ta lace dark blue fuskarta ba wani makeup sai lip glow data shafa a baki sai kuma yanayin fuskar bata rasa shafa powder yar kad'an ta yafa mayafi mahad'in kayan a saman kafad'ar ta, murmushi itama Fatun tayi mata ta kira Sunanta kafin ta gaishe da ita, ce mata tayi ta shigo mana tace a'a bari ta jirata a parlor dama tana son zata rakata wurin gwaggo ne da sauri tace mata to, komawa ray cikin d'akin cike da zumud'i ta d'auki waya ta kira Haisam bayan yayi picking ta sanar dashi zancen fitar yace ai Fanan dama tayi mashi magana sai sun dawo sukai sallama cike da nuna k'auna, ba 6ata lokaci ta k'arasa shiryawa bata canza kaya ba sai kawae ta yafa mayafin rigar jikinta ta d'aukki wayarta ta fita.
A parlor suka zauna gwaggo nata faman sakin murmushin yak'e dama tun lokacin da suka zo tayi arba da Fanan saida gabanta ya fad'i, wani irin nauyi da kunyar Fanan d'in ne suka kamata duk ta bi ta kama kanta a haka suka gaisa tayi mata an zo lafiya da tambayar yan gidan su, lokacin Mino ta tafi islamiyya Amadu kuma yana a shago saida ma suka tsaya ya gaisa da Fanan kafin su shigo, Fatuu ce ta mik'e taje ta d'aukko mata ruwa da lemu don ta lura da yanayin gwaggon, bayan ta zuba mata cup ta mik'a mata ta fara sha, da k'yar gwaggo ta mik'e tace bari a kawo mata Abinci, da sauri Fanan d'in tace "No gwaggo ban dad'e dana ci Abinci bana jin yunwa" still murmushin yak'e gwaggo ke tayi tace "amman d'iyata Fanan ai a d'an ci na zumunci ko Yaya ne tunda yaushe rabon da acin" tana Murmushi tace mata kar ta damu ai tasha ruwa da lemu sai kuma tace "Da dai akwae dambu da na ci"
da sauri gwaggo tace "ah in shi kike so sai in yi maki yanzun nan" girgiza kai Fanan tayi tace ba sai tayi wahala ba tunda babu, da sauri gwaggon ta k'ara cewa "ai ba wani abun wahala tunda komai akwae bari kiga yanzun nan a yi" tana rufe baki ta juya ba tare data jira cewar Fanan d'in ba,
tun bayan data fara aikin girkin dambun take ta faman sambatu ita kad'ai, wani lokacin ta girgiza kai duk ta bi ta damu, Kallo suka cigaba da yi sai dai Fanan ba wani kallon take ba tafi yawan d'aga kai ta kalli sama kaman mai yin tunani sai jefi jefi take sauke idon ta kalli Tv, gaba d'aya Fatuu duk ta damu da yanayin ta don akwae alamun damuwa a tattare da ita hakan yasa bunu bunu sai ta kalleta, suna haka can ta kalli Fanan d'in suka had'a ido ta k'ak'alo d'an murmushi itama Fanan d'in fuskarta a d'an sake tace mata "Sis Zarah kinata kallo na tun d'azun da wani abu ne?" da sauri Fatuu ta girgiza mata kai ta maida idon ta k'asa , kaman daga sama taji tace "ko ina baki tausayi ne?" da sauri ta d'ago ta kalleta idon Fanan d'in akanta da alama amsa take jira da k'yar Fatuu ta d'an d'aga mata kai alamar eh kawai sai gani tay ta mata wani kallo mai kaman harara tace tunda ta k'wace mata miji ba dole taji tausayin ta ba, a rud'e Fatuu tace "a...a Aunty Fanan don Allah ki yi hak'uri.... " idanun ta har sun ciko da k'walla sai kawae gani tay Fanan d'in ta yi dariya tace tana tsokanarta ne, cigaba da kallon sukai saidae duk Fatuu jin ta take wani iri don tasan dama damuwar Fanan d'in bata wuce kan Haisam, ba'a d'au wani dogon lokaci ba gwaggo ta gama yin dambun yasha zogale da gyad'a da albasa sai uban k'amshi ke tashi, saida tazo ta tambayi Fanan d'in da k'uli take so ko yaji tana murmushi tace a kawo duka sai tasa taji wanda yafi dad'i gwaggon tace to, a d'an babban plate ta zubo mata bayan ta aje ta kalli Fatuu da d'an murmushi tace itama zata ci ne ta d'an tura baki tace eh mana, tana niyyar fita Fanan tace ta bari su ci tare in basu k'oshi ba sai a k'aro masu gwaggo ta washe baki tace to, suna cikin cin Abincin Mino ta dawo daga islamiyya ta shigo tana ta fara'a ta duk'a ta gaida Fanan itama tana murmushi ta amsa mata daga baya ta gaishe da Fatuu kafin ta mik'e don taje ta cire Uniform, anan sukai sallar Magrib bayan sun gama suka fara shirin tafiya Fatuu taje ta sanar ma gwaggo zasu tafi, tana sanye da hijab da tayi salla tazo parlon lokacin Fanan na zaune a kan kujera itama ta zauna tana murmushi cike da k'arfin hali ta fara Magana "Y'ata Fanan inata so in baki hak'uri kan yadda abu ya faru tun d'azun nauyin ki yasa na kasa, nasan dole an maki ba daidai ba dole kuma hakan ya jefa ki a halin matsananciyar damuwa, don Allah kiyi hak'uri, duk ta wani bayani ba shi bane tunda mai faruwa ta faru" d'an murmushi tayi tace "No gwaggo ba komai, ni musulma ne na yarda da k'addara mai kyau da mara kyau and I hope wannan ya zama mai kyau, kawae ina son ki ma Zarah magana taci gaba da d'aukana matsayin sister nata ba kishiya