Showing 3001 words to 6000 words out of 512766 words
Chapter 2 - Asanadin Makwabtaka Book 3 Hausa Novel Complete
Unknown
27 Dec 2024
1529
wani kalan fad'uwa gabanta yay ta amsa suna Kallon juna ita da Haulat har taje d'akin gwaggon tace ta kira Haulat itama ta dawo ta kirata, duk a k'asa suka zauna idon gwaggo a kansu sai da ta nisa sannan ta fara Magana,
"Miya faru kuka dawo?" Shiru sukai suna kallon juna kafin Fatuu ta sauke idanunta kan gwaggo murya na rawa tace "b..ban son Auren ne" zuba mata ido kawae gwaggo tay ganin kallon da take mata yasa Fatuu d'an sunnar da kai can taji tace "Baki son auren, kenan gudowa ki kai?" a hankali ta d'aga mata kai still gwaggo tay tana kallonta kawae da alama tama rasa mi zata ce mata ne,
"Saura kwana nawa a d'aura maki Auren?" a sanyaye Fatuu ta bata amsa da hud'u, kya6e baki gwaggo tay tace "Saura kwana hud'u shine zaki ce baki son auren to yanzu da kika zo man nan ni mi zan maki??" Idonta akan gwaggo idanunta sun kawo kwalla tace "Don Allah gwaggo kar ki bari ayi man Auran nan" d'an murmushin takaici gwaggon tay kafin ta d'aure fuska a kausashe tace "ni ba abunda zan iya yi maki yanzu, lokacin da nike tunanin inada yadda zanyi nuna wa ki kai baki son hakan don haka yanzu bakin Alk'alami ya riga da ya bushe dole ki koma ai maki Auren, kuma ke da kika amince don ki taimaki Mahaifinki ki fitar dashi daga halin da yake ciki shine yanzu zaki za6i k'ara jefa shi a wani halin saura kwana hud'u bikin ki kice wai baki so kina da hankali kuwa!" tuni Fatuu ta fara kuka gwaggon ta juya kan Haulat rai 6ace tace "Ke Haulat ke kika bata shawarar ta gudo ne da kuka taho tare?" Da sauri murya na rawa Haulat tace "a..a gwaggo jiya bayan munje ne shine da tsakar dare ta tashe ni tace man gida zata taho lokacin nima na nuna mata had'arin dake tattare da hakan nace tayi hak'uri amman sai tay man bayanin irin mijin da ake so a aura Matan tace dama kema baki so in ta dawo zaki taimaka mata a fasa, to da ita kad'ai ma zata taho daga baya nace bari mu taho tare" d'an ta6e baki gwaggon tay tace "to ni kam yanzu ba abunda zan iya yi kan hakan don haka sai ku tattara ku sake komawa tayi hakuri taje a d'aura mata Auren kaman yadda tun farko ta amince...." Kuka sosae Fatuu take yi ta fara mata Magiya tana fad'in "Don Allah gwaggo ki taimaka man wllh ban iya rayuwar Aure da shi in aka aura man shi mutuwa zan yi d'an iska ne mai neman mata kuma mashayi...." Nan Fatuu ta kashe komae duk abunda ya ta6a yi mata ta fad'i ma gwaggon, a zahiri sai kace abun bai dake ta ba amman a bad'ini ba k'aramar kad'uwa gwaggo tay ba da jin hakan ba kamar gidan gonar da ta ce ya kaita har ya zuba mata maganin bacci ya ta6a ta duk da haka fuskarta ta nuna tashin hankalinta rai 6ace ta tambayi Fatun ta fad'a ma wani cikin iyayenta wannan zancen da sauri tace eh ta fad'a ma Yadikko amman sai ta bata hak'uri tace lokaci ya k'ure kuma wai itama tana ganin don ya biya sadaki ne yasa yay mata hakan kamar yadda yace, a fusace gwaggo tace "Zancen banza kenan! a ina biyan sadaki ya zama aure da har zai samu damar ta6a ki???" Shessheka kawae Fatuu ke yi gwaggo taci gaba da fad'in "ni dama tun farko abunda na guda kenan don Kamalu ya fad'a ma Amadu yaron ba nutsattse bane in ba don haka ba wllh bazan tsani yi maki aure ba, tabbas nasan zan ji ba dad'i don ina son ki yi karatu amman kuma nasan darajar kowace yarinya d'akin mijinta ne ba kamar zamanin nan da mazajen aure ke wuya sai kaga yarinya ta gama karatun kuma sai mijin aure ya gagara shiyasa iyaye masu dubara da yarinya ta gama secondary suka ga tana da tsayayye sai kiga sunyi mata aure sun ce taci gaba da yin karatun a d'akin mijinta don kar a rasa damar da aka samu, to ke kanki da ace naji an yaba da yaron wllh zan goyi baya ne in kin je can Kya yi karatun amman Kika watsa man k'asa a ido kika nuna ke kin amince, nasan da niyya mai kyau kikai hakan amman yanzu baka cewa zaka kashe kan ka don ka raya wani ba kaman akan abunda ansan da matsala yanzu in akai maki Auren matsala ta biyo baya ke ce a ciki shi kan shi mahaifin naki ba samun kwanciyar hankali zai yi ba kina cikin matsala shiyasa maganin kada ayi to kada a fara da kin ban dama da nayi duk yadda zan yi inga an fasan in dae Allah ya nufi hakan in kuma nayi bakin k'ok'ari na naga na kasa sai abar ma Allah, Yanzu ni gaskiya bansan ya zanyi in tsaida Al'amarin nan ba lokaci ya k'ure" rai a tsananin 6ace take Maganar ta k'arasa tana girgiza kai Fatuu ta matsa gabanta ta kamo hannuwanta tana cigaba da rok'onta Haulat sai matsar k'walla take to itama dae gwaggo kasa jurewa tay saida kwallan suka zubo mata Fatuu nata mata Magiya tana fad'in ita bata san ashe dalilin da ya sa bata son ai mata Auren ba kenan can gwaggo ta nisa tace mata abar ma Allah komae tayi Addu'a ya tabbatar da abunda yafi zama Alkhairi ta jinjina kai, mik'ewa gwaggo tay ta fita bada jimawa sosae ba ta dawo hannunta ruke da tray ta aje masu tace ga Abinci nan su ci ta sake fita sai gata ta dawo da ruwa da lemu ta aje masu kafin ta nufi bakin gado ta zauna hannunta dafe da ha6arta gaba d'aya kanta ya gama k'ullewa ta rasa tunanin ma da zata yi, a hankali suke cin Abincin jikin kowannan su ya gama yin sanyi ba laifi sun ci sosae bayan sun gama atare suka fitar da kayan gwaggo tace suje suyi wanka tunda Magrib bata k'arasa yi ba suka amsa da to ta bi su da ido gwanin tausayi, Haulat ce ta fara yo wanka sannan Fatuu gaba d'aya sun ji dad'in jikin su saidae kowa da fargaba a cikin ran shi ba kamar Fatuu, bayan sun canza kaya zaune su kae a cikin d'akin jigum saida akai sallar Magrib suka fito bayan sun gama sallar gaba d'aya suka 6ingire a kan abun salla suna baccin gajiya lokacin da akai Isha da k'yar Gwaggo ta tashe su suka yi salla tayi masu Maganar Abinci duk suka ce basu jin yunwa tace to su hau gado dama Haulat bata ma yi tunanin tafiya gida ba tunda tsugunne bata k'are ba, Allah sarki gwaggo sam ta kasa ma kwanciya sai kai da kawowa take a cikin d'akinta wani lokacin ta zauna a bakin gado abun duniya duk ya isheta ba k'aramin k'una ranta ke mata ba can ta d'auki waya ta kira Mahaifin Fatuu bayan ya d'aga sun gaisa ne take ce mashi yanzu ashe sun san halin wanda za'a aura ma Fatuu amman suka amince a jefa rayuwar yarinya a cikin matsala kamar zai kuka ya fara mata rantsuwa yana fad'in harda k'arin hakan yasa shi kwanciya ciwo lokacin da Ard'o ya fad'i mashi hakan kuma har wurin mahaifin yaron yaje don ya rok'eshi a kan a fasa harda Maganar halin yaron nashi yay mashi amman sai ya tabbatar mashi da cewa ya kwantar da hakalinshi yaron ya canza hali ya shiryu shiyasa ma ya nema mashi aurenta ya kuma tabbatar mashi da ko bayan bikin yaci gaba da yin hali mara kyau shi da kan shi zai d'auki mataki gwaggon ta tambaye shi yaji abubuwan da yay ma Fatun yace eh Yadikko ta fad'a mashi tace to yanzu ina canza hali anan yace babu kam, tambayar shi tay yanzu wane mataki zai d'auka ko kuwa a hakan za'a aura mata shi cikin karewar murya yace shi wllh ya rasa mafita amman har ga Allah bai son ayi mata auran gwaggo na jiyo sheshshekar shi sake tambayar shi tay an san Fatun ta gudo yace ba wanda ya sani iya su ne tace to abunda za'ai in Allah ya kaimu yaje ya fad'i ma Ard'o harda dalilin da yasa ta gudon kar ya rufe komae, d'an jimm yay kafin ya amsa mata da to sukae sallama, koda suka gama wayar cigaba da tunanin mafita tay gashi Hajiya bata nan bare taje neman shawara jiya da yamma Senator yasa aka tafi da ita Abuja Saboda ciwon kafar da ya taso ta gaba, k'arshe dai Alwala taje tayo tazo ta kabbara salla don neman mafita wurin Allah, Washe gari bayan da su Fatuu sukae salla komawa sukai sai da gwaggo ta gama breakfast taje ta tashe su sukai breakfast d'in bayan sun gama suka gyara gidan tsaff gwaggo na d'aki bata je aiki ba dama kwana biyu tana gida Saboda bata jin dad'in jikinta sai jiya ta koma yau kam gaba d'aya bata jin dad'i damuwa tay mata yawa hakan yasa ta kira ta fad'a bazata samu zuwa ba, har d'akin ta suka je don su gyara tace su bar shi in ta tashi sai a gyara, Wanka su kai Fatuu ta tsuke cikin jeans da t-shirt har ta jita ta dawo Fatunta ta da duk da da sauran rina a kaba ta ba Haulat doguwar rigar Material don kayanta masu nauyi ne duk na cin biki ne ta tafi da su, tsaye Fatuu tay gaban dressing mirror tana kallon kanta tana ce ma Haulat wai kaman yadda fuskarta ta rame hips d'in ta ma sun rame don ita ji take kaman sun rage girma dariya kawae Haulat d'in ke yi can ta tuno da abunda Khalid yay mata ta d'aure fuska ta dawo gefen gado ta zauna Haulat na ganin yanayinta ya canja ta fara tambayar ta abunda ya faru idanun Fatuu cike da kwalla tace ta tuna abun da Khalid yay mata ne yanzu shikenan ya gane mata jiki Haulat ta dafata tace "ki daina damuwa k'awata yaje don kan shi kuma bi'iznillahi ta'ala ya yi mashi ganin farko kuma na k'arshe" a sanyaye Fatuu tace Allah ya sa suna haka wayarta ta fara ringing ta d'aukko tana duba mai kiran ganin Abbas ne yasa tay picking bayan sun gaisa yace "Mom Zarah Amarya kwana biyu inata jira baki turo man invitation card ba shiyasa nace bari in kira in ji Date d'in" shiru ta d'anyi sai kuma tace mashi "ai na dawo gida fa" da alamar mamaki yace "wane gida?" Tace "Nan Katsina" still da mamakin yace "ba dae har an d'aura Auren ba anan zaku zauna ne?" Har saida Fatun tay yar guntuwar dariya jin abunda yace kafin tana tura baki tace "a'a ba'a d'aura ba banson auren ne shine na gudo jiya" Abbas yace "What! Kin gudo?" kaman zatai kuka tace "Eh Ya Abbas ni ban son Auren" tana jin yadda ya sauke nannauyar ajiyar zuciya yayi d'an shiru kafin ya tambaye ta yanzu haka tana gidan su tace eh yace Ok gashi nan zuwa yanzu.................
_Littafin A Sanadin Makwabtaka part 2 Naira 300 ne za'a tura ma Mutum har part 1 ga mai so zai turo kudin ta wannan Account din, 1509618776, Zainab Bature Access Bank, za'a turo shedar biya ta wad'annan nos din 09013804524 ko 08169856268._
[5/8, 19:28] +234 901 700 4868: *ASM Bk2033*
_Destiny may be delayed but cannot be changed...._
*DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI*
.........After some minutes sai gashi ya kira yace mata yana waje tace to, babban gyale ta d'aukko a cikin wardrobe ta d'aura saman kayan jikinta tace ma Haulat tana zuwa ta d'aga mata kai, bayan ta fito daga d'akin saida ta shiga d'akin gwaggo har sannan tana kwance saman gado ta fad'i mata ga Ya Abbas nan yazo zata je gwaggon ta d'ago da kai ta kalleta tace kiran shi tay ta fad'i mashi ne Fatun tace "a'a d'azun ya kirani wai ban tura mashi Iv ba har yanzu shine nace mashi ai na dawo ya tambaye ni yadda akai shine nace ban son Auren ne na gudo" ta k'arasa tana d'an sunnar da kai, shiru gwaggo ta d'an yi kamar mai tunanin wani abu sai kuma ta d'aga kai tace taje, tana fitowa daga cikin gidan Abbas ya bud'e kopar Motar ya fito idon shi akanta har ta k'araso ta tsaya d'an gaban shi tana ta kikkafta ido ta gaishe da shi, da alamun mamaki yace "Mom Zarah so u'r serious kin gudo d'in dae kenan" d'an tura baki tay bata ce komae ba yace "Amman miyasa kikai hakan ba kince man kin amince bane Saboda Daddy en ki yanzu da kika gudo baki tunanin zaki k'ara jefa shi a wata matsalar da ta fi wanccan?" Yamutsa fuska ta fara nan da nan idanunta suka kawo kwalla cikin rawar murya tace "Ya Abbas ban son wanda za'a aura man d'in ne....." Katseta yay "ai nasan hakan Zarah kuma dama ai ba don kina son nashi kika amince ba why saida aka kusa zaki hakan" ya kafeta da ido rasa abun ce mashi tay kawae sai ta saka mashi kuka tana fad'in "Ya Abbas mai neman mata kuma mashayi ake son aura man fa" waro ido Abbas yay da alamun ya d'an razana da jin Maganar tata ita kuma sai kuka take, nuna mata other side en Motar yay yace su shiga ciki ta juya tana matsar k'walla shima ya juya ya shiga, bayan ta shiga cigaba da kukan tay Abbas da shima ya shigo yace mata is ok ta daina kuka, d'an tsagaitawa tay yanata kallonta yace "Mom Zarah ya akai kika san abunda kika fad'a game da shi" shiru tay tana tunanin ko ta fad'a mashi shima tunda ta ga da ta fad'i gwaggo hakan ta saukko Abbas d'in ya lura kaman tana 6oye wani abu hakan yasa yace mata kar taji komae ta fad'a mashi yankewa tay gwara ta fad'i mashi kawai ta d'aga kai ta kalli gefen shi cikin muryar kuka ta fara fad'i mashi tiryan tiryan tun farko abunda ya fara mata har zuwa gidan gonar da ya kaita da washe gari da suka dawo daga wurin gyaran jiki tana kai wa k'arshe ta sake fashewa da kuka mai cin rai, iya girgiza Abbas ya girgiza da jin abunda ta fad'an fuskar shi har ta nuna yama kasa Magana sai kawae ya maida kan shi jikin heardrest ya d'age sama wani irin bak'in ciki ne ya turnuk'e shi, ya d'an d'auki lokaci a hakan kafin ya sauke kan yana kallonta sai kuka take hannu ya kai ya bud'e glove box ya curo tissue ya yagi mai d'an yawa bayan ya maida ya mik'a mata yace tayi shiru ta daina kukan hakanan, amsa tay ta fara goge fuskar saida ta gama ta ruk'e tissue d'in a hannu sannan ya fara mata magana cikin murya mai tattare da 6acin rai yace "But Mom Zarah are sure daga hakan bai cutar dake ba?" ta fahimci mi yake nufi hakan yasa ta fara girgiza kai tace "Wllh daga hakan bai man komae ba, ko lokacin da na gane yasa man maganin bacci ina mashi Masifa har nace mashi Mazinaci shine ya fara man fad'a har yana cewa da shi Mazinaci ne ai da bai k'yale ni ba duk da damar da ya samu" tana kai k'arshe ta d'ukar da kanta d'an yamutsa baki kawai Abbas yay cike da takaici, suna cikin hakan sai ga Haulat ta fito ta zagayo side d'in da Fatuu take ta d'an kwankwasa glass tana ganinta ta bud'e kopar ta d'an duk'a kan ta ta gaida Abbas da k'yar ya amsa mata tace mashi dama gwaggo ce tace tana Magana yace Ok gashi nan zuwa daga haka ta juya ta koma, kallon Fatuu yay suka had'a ido yace su je a tare suka fito daga cikin Motar, lokacin da suka shiga Parlon gwaggon na zaune tayi mashi sannu da zuwa ya amsa yana kokarin zama, nuna ma Fatuu wuri tay tace ta shiga ta zauna ta kalli Abbas cike da damuwa tace "d'ana Abbas tayi maka bayanin abunda ke faruwa ne?" d'aga mata kai yay alamar eh ta sauke Ajiyar zuciya taci gaba "abun dae sam ba dad'in ji gashi ni na rasa mafita shiyasa nace a kira man kai koda shawarar da kake ganin zaka bani, na so ace Hajiya na nan to kuma bata nan gashi lokaci ya riga ya k'ure amman sam bai kamata ta auri Mutumin nan ba tunda daga ji baida hali" girgiza kai Abbas yay yace "tabbas bai dace ta aure shi ba gaskiya, amman su can yanzu da ta taho mi suka ce ne?" d'an yarfa hannu tay tace "to jiya dae da daddare munyi Magana da Babanta yace Matar tashi ta fad'a mashi dalilin tahowar Fatuun ya nuna shima bai son ta auri Mutumin saidae baisan taya zai dakatar da Al'amarin ba, anan nake tambayar shi ko mutan gidan nasu sun san Maganar tahowar tata yace ba wanda ya sani to dae nace ya je ya sanar da Ard'on komae dake faruwa, har yanzu dae bai kira ni ba balle in san halin da ake ciki" sigh Abbas yay yana d'an jinjina kai kafin yace "Yanzu za'a jira shi ne aji ko akwae abunda kike ganin za'a yi?" a sanyaye tace "eh to ni da na yanke shawarar zan tafi can garin ne gobe gwara ayi wacce za'ai tun kafin ranar d'aurin auren tunda su can dangin Angon bama su san ita Fatuun ta taho ba" d'an biting lower lip d'in shi yay ya k'ura ma carpet d'in k'asan parlon ido da alama yana tunanin wani abu ne can ya d'ago yace mata shikenan ta shirya gobe idan Allah ya kaimu zai zo da Asuba sai suje can garin tare gwaggon tace "a'a d'ana Abbas ai ba'ayi haka ba kaima ai kana da hidindimun ka da za'a k'ara d'aura maka nauyin tafiya dama dae shawara nike