Showing 501001 words to 504000 words out of 512766 words

Chapter 168 - Asanadin Makwabtaka Book 3 Hausa Novel Complete

Unknown   

27 Dec 2024

1547

da hannu tunda ai shiya biya mashi yaje yayi karatun fasahar da yake samun kuɗi duk akayi dariya harda Security dake biye dasu, itama Mom yaba ma Jidderh tayi tace bata san kamfaninta sun ƙware haka ba sai yanzu gaba ɗayan kayan da aka zuba ma gidan sun hau kuma sunyi kyau nan fa duk aka shiga yaba mata tanata dariyar jin daɗi haka mijinta Sadeeq shima yaji daɗin yabon nata da ake Dad ɗin su har yana cewa zai bata kwangilar zuba ma gidan su kaya in ya sauka zasu koma, cike da jin daɗi tayi mashi godiya Aunty ma tace zata rinƙa samo mata kwangila kuwa tunda sun ƙware haka Hajiya Zainab ma itama tace zata rinƙa samo mata dama harda ita aka zo don yanzu sunfi zama a Abuja bayan an ba Dad ɗinsu Sameer Minister, Fauzy dai basu ƙasar kuma har yanzu bata sake haihuwa ba itama don Sameer yace sai ta huta sosae ba kamar daya ga Cs aka yi mata, ganin Dad ɗinsu na niyyar tafiya yasa Haisam ce mashi please ya bari suci abinci ya ɗan buɗa mashi ido kafin yace ai baya jin yunwa Jidderh dake murmushi tace ai na murnar sabon gida ne ya kamata yaci yana murmushi yace to tunda hakane a bashi ya tafi da abunshi duk akayi dariya dama ya iya barkwanci, Fanan ce ta nufi cikin gidan da sauri dama sunyi Order ɗin abinciccika saboda masu rako su sabon gidan, bada jimawa ba ta fito ruƙe da manyan ledoji guda biyu ta nufo shi dasu, har rige rigen amsa muƙarrabanshi daya zo dasu suke amman sai yace masu su bari shi zai ruƙe abunshi don kada wani ya cinye mashi aikuwa mi za'ai ba dariya ba kuma shi ɗin ya kar6i abun shi anata ya kawo don Allah a ruƙe ya ƙi badawa, Addu'o'i yayi masu na Allah ya sanya alkhairi yasa sun dawo a sa'a ya karesu daga dukkan sharri anata amsawa daga baya sukai sallama aka buɗe mashi mota duk sauran abokan tafiyar nashi suma suka shiga motocin saida aka ga tafiyar su sannan suka koma cikin gidan harda su Mom, a falo aka zazzauna zaman cin abincin abun gwanin sha'awa su Mom sai kace ba First lady ba sun saki jiki cikin yan uwa ana ta cin abinci ana hirar nishaɗi. Sai gab da Magrib Fatuu ta iso Haisam yaje ɗaukkota tasha gayun doguwar rigar shadda, tun a bakin gate ɗin gidan ta fara sakin baki don itama ba sanin gidan tayi ba ta dai san shi a hoto, lokacin su Mom duk sun tafi sai su Mino da Aysha da kuma Jidderh da suka tsaya su tarbeta, sosae aka nuna farincikin dawowarta bama kamar su twins, Esha tana ganinta ta ƙanƙameta tana mata welcome tare da nuna mata sabon gidan su, sam Fatuu ta kasa 6oye al'ajabinta da kuma farincikin gidan sai faman bin gidan take da kallo idanu waje tana kuma sakin murmushi duk a lokaci guda, zagayawa suka shiga yi da ita harda Fanan Haisam kuma ya tafi Masallaci, bayan sun gama ganin ko ina ciki suka dawo don yin salla, sosae Fatuu tayi godiya ga Allah da yadda yake ta mata ni'imomi da bata ta6a zaton samu ba a rayuwarta, harda kukan daɗinta sannan tayi ma Mijinta Addu'o'i sosae shima, bayan sallar isha aka zo ɗaukar su Mino anata mata Addu'ar Allah ya raba ta da cikinta lafiya haka Aysha amarya ma ba'a daɗe da ɗaukar Mino ba itama angonta Na'eem yazo ya ɗauketa, Jidderh ce ta ƙarshe da aka ɗauka duk saida mazajen nasu sukai ma Fatuu Allah ya sanya alkhairi kafin su tafi don ɗazun da suka zo bata nan, bayan Haisam ya dawo a tare gaba ɗaya suka zauna cin abinci a dining area fuskokin kowannensu cike take da annuri, bayan sun gama cin abincin ne Haisam yace suyi alwala suyi Nafila duk suka ce to harda yaran, anan babban falon sukayi sallar raka'a biyu ta godiya ga Allah bayan sun gama kowa yayi addu'a Esha tana yi tana dariya tana leƙen fuskokin su twins, a falo suka zauna nan Fatuu tayi ma Haisam ɗin godiya da Addu'oin Allah ya ƙara mashi lafiya da arzuƙi mai amfani harda su Fanan dasu Esha ake amsawa, kallo suka yi zuwa ƙarfe tara da rabi Haisam yace ma su twins suje ya rakasu su kwanta aikuwa Esha na jin haka ta fara tura baki tana ƙunƙunin ita ba'a yi mata ɗaki ba a saka mata ɗan gadonta itama duk sukai dariya Fatuu tace ita dake da ma ɗakuna har biyu ga ɗayan na part ɗinta ga kuma na Momynta sai inda take so zata kwana ta tura baki tace ai duk gadon sun mata ƙato ita kalar nasu twins take so, Haisam dake a tsaye yana murmushi yace mata tayi haƙuri in ta samu sister sai ayi masu ɗakinsu suma su biyu ta wani yarfa hannu tace to ba Aunty da Momyn suƙi su haihu ba tayi ƙanwa duk sukai dariya, jawota Fanan tayi jikinta tana bata haƙuri tace bada daɗewa ba zata yi ƙanwa da Aunty ta gama karatu,

"To Momy ke ki haihun man younger sister tunda ita sai ta gama karatun" ta faɗa a shagwa6e, murmushi Fanan ɗin ta shiga yi tana ɗan kikkifta ido ta kasa ce mata komai, hannu Fatuu ta kai ta dafa kafaɗar Esha ɗin tace "Momy zata haifar maki sister in sha Allahu, daga yanzu duk kikai salla pray for her, kuma su twins ku rinƙa yi ma Momynku Addu'ar Allah yasa ta haiho mana Baby mai kyau" ta ƙarasa tana murmushi duk suka ce to Haisam nata murmushi bai ce komai ba ya kama hannuwansu bayan sun yi masu saida safe suka tafi yadda ya ruƙe su abun gwanin sha'awa, bayan sun haye bene Fanan ta miƙe tana ruƙe da hannun Esha tace suje itama ta kwanta ta ɗaga hannu tana ce ma Fatuu "Good night, Aunty" itama hannun ta ɗaga mata tace "Goodnight, Esha Darling" ta saki dariyarta mai kyau suka tafi, bin su da ido Fatuu tay har suka shige ta ɗan girgiza kai wani irin tausayin Fanan take ji game da rashin haihuwarta don ta san dole tana tsananin son ta haihun, lokacin da su twins suka fara girma duk sun ɗauka Fanan ɗin ce ta haife su saboda yawan jan su a jiki da take, koda ta fahimci hakan don sun fi sakewa da ita da kanta ta sanar masu da cewa Fatuu ce ta haife su Adam har saida yaje ya tambayi Fatun wai da gaske ba Momy bace ta haife su ta tambayeshi waya faɗi mashi hakan yace ita, jin haka yasa taje tayi mata magana kan miyasa zata yi masu wannan Maganar tana murmushi tace yakamata su sani ne don uwa ba wasa bace in bata faɗi masu ba zasu iya ƙin bata muhimmancin daya kamata lokacin har saida su duka sukai ƙwalla, daga baya ne Fatun tace masu suci gaba da ɗaukar Fanan matsayin Momyn su ita kuma su rinƙa ce mata Aunty, miƙewa tayi ta nufi Bedroom ɗinta inda keda royal bed, bayan ta shiga shirin yin wanka tayi dama duk kayan sawarsu an riga an kawo su tun kafin su dawo har ta ware wasu masu yawa zata aika ma Gwaggo a bada su sadaka a Foundation ɗinsu wanda yanzu sosae ya cigaba ana tallafa ma marasa ƙarfi ba kamar yan gudun hijira da akwae su sosae a yankin Katsina, su twins ma da Esha duk an ware kayan su da yawa za'a bada Fanan ma haka, a cikin laundary ta cire kayan jikinta ta ɗaukko rigar wanka ta saka tana ta kallon kanta ta cikin ƙaton madubin wurin, gaba ɗaya ganin komai take kamar a mafarki gashi sai take ganin komai ya faru da wuri wato dai ashe cin ribar haƙuri haka yake da daɗi, lafiyayyan wanka tayi lokacin data fito sai faman sakin wani irin ƙamshi take, Bedroom ta shiga ta zauna akan kujerar gaban madubi tana kallon kanta tana goge lemar ruwan jikinta data kanta, tana haka Haisam ya shigo cikin ɗakin da sallama ta juya tana kallonshi suna haɗa ido ta fara sakar mashi ƙayataccen murmushi shima ya shiga maido mata, tun kafin ya ƙaraso gareta ƙamshin turarenshi ya rigashi isowa yana sanye da kayan bacci riga da wando farare masu taushi wanda da gani sababbi ne, wurinta ya nufo yana zuwa ya tsaya yana kallonta suna sakar ma juna murmushi can ya miƙa hannu ya amshi towel ɗin da take goge jikin ya cigaba da goge mata sai dai nashi da wani irin salo mai tsuma zuciya yake yi suna yi suna kallon juna ta cikin madubin suna cigaba da sakin ƙayataccen murmushi mai tattare da tsantsar ƙaunar juna, bayan ya gama goge mata da kanshi ya shafa mata man da yasan tana amfani dashi da daddare, gaba ɗaya shi yayi mata shafe shafe da goge gogen da take yi da daddare da yake gashinta bai jiƙe ba sosae iya baki baki ne hakan yasa bai busar mata dashi ba, bayan ya gama miƙewa tayi da niyyar taje ta saka kaya kawai sai ji tayi ya janyota ya haɗe jikinsu kafin ya haɗe fuskokinsu suka shiga shaƙar numfashi da ƙamshin juna, slowly ya kai lips ɗinshi ya haɗe da nata ya shiga bata deep and hot french kiss, tun ƙafafunta na ɗaukarta har suka kasa gaba ɗaya ta ƙanƙame shi, ya ɗan ɗauki lokaci kafin ya saketa ai da ƙyar take iya kallonshi hakan yasa shi yin ɗan murmushi mai sauti ya kai hannu ya ɗauketa gaba ɗaya, yana ɗauke da ita ya nufi switch ya kashe hasken ɗakin kafin ya nufi haɗaɗɗan royal bed ɗinta daya sha lafiyayyan zanin gadon da ko mutum bai yi niyyar bacci ba ya kwanta sai ya ɗauke shi, sosae Fatuu tayi ma Haisam godiya ta hanyar faranta mashi daren ranar ya shiga cikin tarihinta, Washe gari da safe ita da Fanan suka shiga Kitchen don yin Breakfast sai mai aikinsu ta wancen gidan da suka taho da ita ita kuma tana gyara gidan duk da bai wani 6aci ba, suna cikin aiki ne Fanan take ce ma Fatuu yakamata a ƙara masu aiki don yanzu aikin dole zai yi yawa ba kamar wanccan gidan ba tunda shi iya inda suke amfani ake gyarawa Fatun tace mata tana ganin a ƙara guda ɗaya tunda in ta gama karatunta zata dawo da Asabe mai aikinta ta can
Zaria nan,

"Allah sarki, har na tuna da Aunty Saude mace mai kirki gashi sam bata da son jiki, in mutum ya samu mai aiki kamarta ya more don tana da amana" Fatuu dake juya dankalin turawa cikin mai ta faɗa, Fanan na jin abunda tace itama tace gashi ta iya girki kamar me Fatuu tace wllh,

"To ko ayi mata magana in tana da wadda zata turo mana, dama ni ban cika son irin wanda agent ke turowa ba don baka san mutum ba wasu mutanen are evil" kai Fatuu ta jinjina tace to zata mata magana dama basu daɗe da sukai waya ba tayi mata barka don ta haihu, ɗan buɗa ido Fanan tayi "Don Allah fa!" Fatuu tace mata wllh,

"Amman ban samu labari ba ai da nayi mata barka kuwa, ikon Allah, itama tunda tayi aure bata haihu ba sai yanzu duk da bansan ko tana Family planning bane tunda ance tana da wasu yara" Fatuu tace mata eh tana da yara da tsohon mijinta kafin ta ƙara cewa "kema in sha Allahu Aunty Fanan zaki haihu" tana murmushi tace to Amin in tana da rabo in kuma bata da rabo already Allah ya bata ta wata hanyar Fatuu tay murmushi,

"Amman fa in kin mata Maganar mai aiki kada a samo yarinya ko budurwa babba kamarta zaki ce" Fanan ta faɗa tana motsa farfesu, cikin rashin fahimta Fatuu tace to dama aikin gidan nan babbar zata fi, yar dariya Fanan tayi don ta fahimci bata gane dalilin da yasa ta faɗi haka ba tace mata ita saboda kada a ƙwace masu miji ta faɗi haka don tana jin labarun faruwar irin haka, dariya sosae Fatuu tay harda ɗage kai Fanan dake dariya itama tace Allah, bayan Fatuu ta tsagaita da yin dariyar tace ai Hubby bazai yi hakan ba,

"Uhmm, wani lokacin suna ba mutum mamaki fa ba kamar shi da ya cika tausayi hakan na iya saka shi ya auri mai aiki",

shiru Fatuu ta ɗan yi tana ɗan murmushi, jin tayi shiru yasa Fanan ɗin kallonta nan take ta fahimci yanayin fuskarta ya canza da sauri ta kai hannu ta dafata tace "Zarah bafa nayi Maganar saboda ke bane wllh, i just said it as an example, Babe wani irin mutum ne shi yana da kirki sosae, inda kirki yana yin yawa to zance kirkin shi har yayi yawa abunda baka tunanin zai iya yi sai kiga ya yi, kamar yadda ya aure ki da niyyar taimako nima haka ne, gara ke ma don na tabbatar yana son ki kawai bai sani bane, amman ni na tabbatar baya sona lokacin daya aure ni kawai yayi ne don ya faranta man ganin na shiga mawuyacin hali saboda shi, amman saboda kirkin shi tunda nike dashi bai ta6a wulaƙanta ni ba daidai da rana ɗaya gashi ko haihuwa bana yi, Babe na musamman ne" ta ƙarasa idonta a sama tana murmushi, itama Fatuu murmushin ta shiga yi tana tunano tun daga farkon haɗuwar su,

"Amman Aunty Fanan nace mi zai hana mu ɗan hada mashi surprised party matsayin godiya da wannan sabon gidan" Fatuu ta faɗa tana kallon ta, da sauri Fanan tace wannan shawara ce mai kyau ya take gani za'ai Fatun tace ayi mashi cake sai ai decorating falonta, Jidderh suka yanke zasu kira kan tazo ta shirya falon Fanan ɗin in zasu yi mashi partyn bazatar, waya Fatuu ta ɗauka bayan ta kira Jidderh ta ɗauka sun gaisa take faɗi mata abunda suke son yi, tambayar ta tayi yaushe suke son yin partyn Fatuu ta kalli Fanan ta tambayeta tay ɗan jimm alamar tunani kafin tace ko gobe ko Fatun tace to ai kuma ita gobe zata koma, ce ma Jidderh sukai in zai yuwuwa zuwa da yamma kamar wurin ƙarfe biyar tace Ok lafiya lau zata masu ƙoƙarin hakan,

Misalin ƙarfe huɗu Jidderh ta iso gidan a Motarta, saida ta fara kiran Fatuu ta tambayi in Haisam bai a babban falo tace mata eh yana Masallaci, tare da wata abokiyar aikinta yare suka zo, bayan sun fito daga cikin Motar suka fara kwasar kayan da suka zo suna shiga dasu, bayan sun kai wasu Fanan da Fatuu suka biyo su suma suka taya su ɗaukar wasu, ba 6ata lokaci Jidderh da abokiyar aikinta suka fara shirya falon, bayan sunyi nisa ne Fanan da Fatuu suka tafi su shirya,

wuraren ƙarfe biyar Fanan ta kira Haisam a waya ta tambayi yana ina ya bata amsa da yana a sama suna yin lesson dasu twins tace pls in ba damuwa ya zo part ɗinta tana son ganin shi ya furta Ok, ba'a ɗau lokaci ba ya turo ƙopar yana sanye da ƙananun kaya da suka amshi jikinshi, yana niyyar yin sallama ya dakata sakamakon wani ƙyalƙyali daya zubo mashi har saida ya ɗan runtse ido, bayan ya tsagaita da zubo mashi yasa hannu yana kakka6e wanda ya maƙale mashi a jiki da saman sumar shi, yana ɗagowa ya kalli gaban shi idanunshi suka sauka akan wata yar banner da aka yi rubutu mai walwali an rubuta _"Thank you for our new home, We really love you our Husband"_ ƙayataccen murmushi ya saki ganin rubutun kafin ya juya ya kalli cikin falon wanda aka ƙawata shi da baloons wato balo kala kala sannan an aje manyan hotunan bikinsu shida Fanan da kuma wanda akayi mashi da Fatuu a Dinner ɗin su da akai a Abuja sannan an aje wanda sukai su duka da yaran su harda babban cake mai hawa biyu anyi decoration da hotunan Haisam da zasu kai biyar sannan an yi rubutu in icing an rubuta "Home sweet home" sannan daga saman baki bakin cake ɗin anyi topping da fresh fruit da suka ƙara ƙawata shi, nufo shi Fatuu da Fanan sukayi sun sha gayun ƙananun kaya riga da wando da suka bayyanar da dirin su gashin kan su gaba ɗaya sun sake shi kai kace hausa bazata fito daga bakunansu ba, ko a iya matan da Allah ya ba Haisam za'a iya cewa ba ƙaramin dacewa yay ba don mata ne da suka amsa sunan mata uwa uba gasu da hali na gari, a gabanshi suka tsaya suna sakin murmushi tare da ƙara yi mashi godiyar yanata murmushi ya ware masu hannuwanshi a tare suka faɗa jikinshi suna ta yar dariya Jidderh da abokiyar aikinta ma dariyar suke ta shiga yi masu Vedio, bayan sun ɗago daga jikinshi kamo hannuwansu yayi suka nufo ciki, a saman doguwar kujera suka zauna dama a gabanta aka aje cake ɗin, bayan zaman su Jidderh tace yakamata a kira su twins suzo a yanka cake tare dasu Fanan ta miƙe ta nufi inda wayar landline take ta kira part ɗin Haisam, Esha ce ta ɗauka cikin zazzaƙar muryarta tace waye ne ke kiran Dad to bayanan da turanci tayi Maganar Fanan na murmushi tace to Momynsu ce, waro ido Eshar tayi sai kuma tayi dariya ta kira sunanta ta amsa tare da tambayarta ina su twins tace mata gasu nan tace to suzo part ɗinta yanzun nan akwae surprise da sauri Esha ta maimaita abunda tace tare da waro ido Fanan ɗin tace mata eh, kife kan telephone ɗin tayi cike da zumuɗi ta faɗi ma su twins abunda Momy tace ta nufi hanyar fita da gudu, Esha ce ta fara shigowa da gudu tana sanye da ɗan skirt na jeans da farar t-shart bayan ta shigo su twins suka biyo bayanta suma ƙananun kaya ne a jikinsu, koda Esha taga yadda akai ma Falon da tsananin

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login