Showing 213001 words to 216000 words out of 512766 words
Chapter 72 - Asanadin Makwabtaka Book 3 Hausa Novel Complete
Unknown
27 Dec 2024
1635
Annabi salati (SAW), bayan sun gama ta fara masu Nasiha gaba d'aya kan zaman tare da kuma hak'uri da juna daga baya ta fara ma Haisam shi kadae kan rike amanar matan shi da kuma yin Adalci a tsakanin su, bayan ta gama dashi ta koma kan Fanan ta nuna mata kada ta dauki duk abunda ake fad'a akan kishiya ta d'auka ita d'in Alkhairi ce sai taga ta zame mata Alkhairin ta rufe idanunta ta kuma toshe kunnuwan ta daga dukkan wata zuga da za'ai mata kan Fateema, kada ta goyi bayan a cutar da ita domin tasan Allah baya barin cuta, tace ta ci gaba da yi mata kallon k'anwarta kamar yadda take yi mata a da, a matsayinta na babba ta zamo mai hak'uri sosae akan komai in taga tayi ba daidai ba ta nusar da ita...Sosae tayi mata Nasiha itama Fanan d'in dake jingina da kujera tana ta d'an jinjina mata kai, a k'arshe ta yaba mata sosae akan Namijin kokarin da tayi wurin yak'i da zuciyarta ta danne kishinta don Farincikin su ta nuna samun matan da zasu iya yin hakan yanada matuk'ar wahala ta nuna mata kar ta d'auki hakan gazawa face jarumta wurin yin abunda yake daidai, ta nuna more ma rayuwa shine ka sanya farinciki a zukatan mutane ba ka za6i ka saka kanka kad'ai ba hakan zai saya maka soyayya da k'ima a idon mutane, haka kuma ko bayan ba ranka za'a ji rashin ka baza kuma a manta da kai ba riba biyu kenan sa6anin ka za6i Farincikin kanka kai kad'ai ka cuta ma mutane su rink'a k'in ka k'arshe ka mutu aita murna tunawa ma da kai yayi wuya,
Kallon Haisam tay dake kishingid'e yana sauraran ta tace "ina son ka sani Fanan masoyiyar ka ce ta hak'ika tunda har ta za6i Farincikin ka fiye da nata don haka indai ka wulakanta ta wllh sai Allah ya saka mata duk da bani da haufi a kan ka kawai tuni nake maka" jinjina mata kai yay a lokacin Fanan tasa hannu ta d'an dafe goshinta jin kuka na niyyar taho mata ita kad'ai tasan abunda take going through don ma tana ta yin Addu'oi a cikin ranta, komawa Hajiya tayi kan Fatuu da kanta ke a sadde tace ta dawo gareta, farko maraba da shigowa cikin Family d'in su ta k'ara yi mata tace tasan halinta itama bata da shakku a kanta don haka kada ta sake ta canza daga yadda ta santa ga Fanan nan taci gaba da d'aukar ta matsayin Yayarta kar ta sake daidai da rana d'aya tace zata mata kallon kishiya, in tana da matsala ta sanar da ita tana da yak'inin zata bata shawarar kirki sannan ta taimaka ma mijin su wurin ganin yayi masu Adalci hakan shine son gaskiya, in Fanan tana yi mata abunda bata jin dad'i ta fad'i mata idan bata gyara ba ita ta fad'i mata duk da tasan in sha Allahu hakan bazata faru ba, daga k'arshe bayan ta gama yi masu nasihohin da suka tsuma masu jiki sosae tayi masu Addu'oi tasa Haisam shima yayi duk suka d'aga hannuwa suna amsawa har ya gama gaba d'aya suka shafa, shiru ta biyo baya duk suka cigaba da yin kallo saidai kowa da abunda ke kai kawo cikin Zuciyar shi, gaba d'aya Fatuu ta kasa sakewa don jikinta na bata Haisam kallon ta yake hakan yasa duk ta takura ga kuma yanayin Fanan data lura tana a cikin damuwa k'arfin hali kawai take hakan yasa duk ta sha jinin jikinta, kiran sallar Magrib da aka fara yi yasa Haisam mik'ewa hannunshi ruk'e da rigar shi ta sama daya d'auka yace ma Hajiya zai je salla tai mashi a dawo lpy, d'an d'aga ido Fatuu tayi tana kallon bayan shi har ya kusa fita sannan ta maido shi k'asa, zuciyarta ce ta shiga raya mata wani abu game da shi, bayan fitar shi Hajiya ta mik'e tace masu suje suyi salla, Fanan ce ta fara mik'ewa da d'an murmushi ta kalli Fatuu data d'ago tana kallonta ta mik'a mata hannu, a sanyaye ta kama hannun ta mik'e suka nufi ciki.
Yadda hakan ta faru, bayan Haisam sun gama Magana da Fanan kan zuwa Nigeria ranar talata, da yamma Hajiya Maryam ta kirata don ta ji halin da ake ciki game da tahowarta nan take sanar mata yadda sukai da Haisam kan zuwa Nigeria ta yi ma Hajiyar Magana da kanta, nan Hajiya Maryam taji dad'i sosae don tasan da wuya in Hajiyar bata bari an saki Fatun ba Saboda su duka sun nuna basu so kuma tasan yadda take ji dasu gaba d'aya, hakan ne yasa washe gari da Hajiya ta kira Hajiya Maryam game da zancen dawowar Farha da Maganar data yi mata sam bata damu ba, tun bayan da suka yanke zuwa Nigeria Haisam ya kasa samun natsuwa, damuwa tayi mashi yawa don yasan shi dae ba iya sakin Zaraah zai yi ba yadai biye mata ne don ya kwantar mata da hankali k'arshe kuma yasan indae suka zo Nigeria yak'i sakin Fatuu to abun zai k'ara kwa6ewa ne, hakan yasa ya yanke tunkararta akan hakan, Ranar Alhamis da daddare ya isketa a d'aki lokacin tana zaune akan gado tana latsa wayarta, tana ganin shi ta d'ago tana mashi dariya ya nufi bakin gadon ya zauna shima yana mata murmushi, aje wayar tayi ta matso inda yake ta kwanta a bayan shi ta yadda yay kaman ya goyata ta sak'alo hannuwanta a wuyan shi nan ta shiga fad'a mashi kalaman soyayya, sosae yaji fargabar sanar da ita abunda ya kawo shi k'arshe dai yay k'arfin hali yace mata magana yake so zasu yi, tana jin hakan ta sake shi ta dawo daga gefe tana kallon shi, d'an jimm yay ta kafe shi da ido daga baya ya fara magana gently, ce mata yay Alfarma yake son ya nema a wurinta for the first time a zaman su, jinjina mashi kai tay gaba d'aya ta maida hankalinta akan shi, ce mata yay ya zauna yayi dogon tunani gaskiya idan ya saki Zarah bai mata Adalci ba zai zama ya cuce ta ne Saboda shi ya fara saninta sannan tayi k'arama ace ta zama bazawara, wani kallo take bin shi dashi yanayin fuskar ta ya canza da alamun d'aurewar kai tace to mi yake nufi kenan, kauda idon shi yay tana ta kallon shi can ya juyo ya kalleta yace "I can't divorce her......" waro ido tay hankali tashe take kallon shi, hannu ya kai zai kama hannunta da sauri ta janye ta fara k'ok'arin nufar can d'ayan 6angaren gadon ta sauka, da sauri ya idasa hayewa saman gadon ya cafkota, rungume ta yay k'am ta fara kokowar kwacewa amman ta kasa kawae sai ta fashe da matsanancin kuka ta fara fad'in ita zai yaudara bacin sun gama Magana shine zai zo yace bazai saketa ba dama tasan yana sonta ne shiyasa ya aureta yanzu kuma daya san ita tana haihuwa shine zai ce bai iya rabuwa da ita to indai ya za6i zama da ita ita Allah bazata cigaba da zama da shi ba, sosae ta tashi hankalin ta sai k'ok'arin k'wace kanta take k'arshe kawai sai ya had'e bakunan su ya fara kissing d'inta deeply don yasan hakan zai iya calming nata, ya d'an d'auki lokaci yana mata hakan kafin ya saki bakin nata jikinta sai kerma yake tana sheshsheka, kwantar da kanshi yay saman kanta cikin sigar rarrashi ya fara magana yace mata yasan ita ba mai son kai bace tayi tunani, in ya saki Zarah zai cuceta ne yasan bazata so hakan gareta ba ko kuma sister d'inta Farha tayi aiki da Hadisin manzo SAW da yace love for ur brother what you love for urself, a yadda yasani tana son Zarah sosae miyasa bazata tausaya mata ba, sai huci take ta hau girgiza mashi kai tace ita dai bazata iya zama da ita matsayin kishiya ba, miyasa zai saka mata rai yayi mata alk'awarin zasu zauna su biyu, ce mata yay ya gaya mata already da aure a tsakanin su amman yanzu zai iya yi mata wani daga Zarah bazai k'ara Auren wata ba su biyu zasu zama matan shi har k'arshen rayuwar shi, shiru tay kaman mai nazarin wani abu can ta d'ago ta kalle shi idanunta sharkaf da hawaye tace "Tell me the truth, do you love Zarah?" Shiru ya d'an yi yana kallonta can ya jinjina mata kai kawai sai ta fashe da kuka ta fad'a jikin shi tana fad'in ita daman tasan son Zarah yake shiyasa tun farko ya auretan in ba haka ba miyasa bai sa Abbas ya aureta ba daga baya ya saketa sai shi daga baya kuma yazo ya kwanta da ita, tasan itace First love d'in shi dama ita ba son ta yake ba kawai tausayinta ne yasa ya aureta don haka zata bar shi sai suji dad'in zama da juna, sosae take kuka yana rungume da ita cikin kwantar da murya yace mata wayace mata bai sonta, da farko da akai mashi Maganar aurenta Saboda yasan ba soyayya suke ba shiyasa ya nuna bazai aureta ba don bai d'auka Maganar da ta yi mashi ta zai aureta ba da gaske take Saboda lokacin a wurin shi tayi k'arama da wannan Maganar, amman daga baya daya nuna ya amince Saboda yana son ta ne, kuma da bai sonta a zaman da sukai ai ya isa ta gane, tambayarta yay a zaman su tare ya ta6a cutar da ita ko hantarar ta ko dai yi mata wani abu na rashin so, d'an girgiza mashi kai tay yace to ta daina cewa haka he truly loves her kuma yana rokonta tayi mashi wannan alfarmar Saboda son da take mashi koda kuwa daga ita bazata k'ara mashi wata ba har k'arshen rayuwar su ya amince, gaba d'aya ya kashe mata jiki ganin haka yasa yaci gaba da rarrashinta, wai akace tsakanin mata da miji sai Allah d'agowa tay tace "Shikenan na Amince but don't break the promise u have made now kuma kayi man Alk'awarin zaka yi mana Adalci" sosae ta bashi tausayi don yasan Saboda son da take mashi ne yasa tayi saurin Amincewa, ce mata yay in sha Allahu zai yi masu Adalci tace ita bata yarda ba sai yayi mata Alk'awari da d'an murmushi yace to ya yi mata. Koda suna a jirgi saida ta jaddada mashi ya dai ce zaiyi Adalci a tsakanin su ko yana murmushi yace mata eh, Bayan sun iso a Bedroom d'in Hajiya suka sauka dama tun kafin su zo Haisam d'in ya fad'i mata game da amincewar da tayi itama Hajiya taji dad'i sosae, bayan sun gama gaisawa tayi masu Maganar Abinci duk suka ce mata basu jin yunwa a lokacin nan ta k'ara yi ma Fanan Nasiha sosae ta nuna mata ta d'auki abun a matsayin Alkhairi ta shiga bata misalai kan irin hakan sosae Fanan ta d'auki Nasihar Hajiyar daga baya ta tambayi Fatun Hajiya tace bata dad'e da barin Part d'in ba, ita da kanta ta tambayi Hajiya takarda ta rubuta abun ciki taba Haisam d'in tace zata mata wasa ne Hajiya na dariya tace ta dai tada mata hankali dama yar'uwarta da Mahaifiyarta sun gama nasu da alamun rashin fahimta Fanan d'in ta tambayi mi sukai mata nan Hajiya ta kwashe komai da Hajiya Maryam da Farha sukai ma Fatun, sosae ta bata tausayi har fuskarta ta bayyana, daga baya suka koma Parlor nan Hajiya ta kirata saidae ita bata san da Maganar sak'on da Fatuu ta tura ma Haisam ba saida tazo Fanan na mata Maganar ta fahimci ita ta tura mashi sak'o Fanan d'in ta gani.
Sai bayan da aka yi isha sannan Haisam ya dawo lokacin suma sun dawo cikin parlon, Fatuu na ganin shi ta gane yaje part d'in su don har ya canzo kaya, har ya k'araso idon shi na akan Fatuu da tunda ta kalle shi ta maida idon ta akan Tv, Fanan ce tay mashi sannu da zuwa da murmushi ya amsa mata Fatuu tay d'an jimm zuciyar ta ta raya mata itama tace mashi mana, da k'yar ta d'an kalle shi da yake Facing d'in su yake murya na d'an rawa tace mashi sannu da zuwan ya jinjina mata kai kawae ya zuba mata ido da sauri ta maida nata kan Tv, wani abu take ji mai kamar haushin shi a ranta, bai dad'e da zama ba Saude tazo ta sanar dasu ta shirya Table, Hajiya ce ta fara mik'ewa tace masu su taso, bayan duk sun zauna Saude na niyyar Serving nasu bayan ta gama da Hajiya tace mata taje kawae, kallon Fatuu tay tace ta tashi tay Serving bak'inta ta d'aga mata kai, Haisam ta fara zuba mawa tana yi tana tambayar shi in yayi ya kafeta da kaifafan idanuwan shi da suke a d'an lumshe dasu yake bata amsa ko da kai gaba d'aya yana neman rikita ta, bayan ta gama ta juya kan Fanan itama ta zuba mata saidae d'an kad'an tasa ta zuba mata, zubawa itama tayi bada yawa sosae ba duk suka fara ci a nutse, baka jin komai sai k'arar cokulla, duk in ta saci kallon Haisam sai taga ita yake kallo yanayin fuskarta kamar a d'aure, tana lura da Fanan sam bata wani cin Abincin juya cokali ya fi yawa sai an d'auki lokaci take d'an d'iba ta kai baki tay ta taunar shi sai kaga kaman tana ci, duk Fatuu sai taji ba dad'i don gani take itace silar damuwar ta, can dae tay k'arfin hali murya na d'an rawa tace "A...unty Fanan baki ci sosae" da sauri Fanan d'in ta kalleta tay mata murmushi murya k'asa k'asa tace mata tana ci mana, Hajiya da ta d'ago ta kalli Fanan d'in da d'an murmushi tace an sha tafiya ko gajiya ce tasa ta kasa ci sosae in tana son wani abu ta fad'i sai a had'a mata, d'an girgiza ma Hajiyar kai tay tace wannan ma lafiya lou, kad'an ta k'ara ta mik'e duk suka kalleta tana murmushi tace ta k'oshi bata da appetite ne zata k'ara da tea daga haka ta fita daga cikin Kujerar ta nufi hanyar Bedroom idon Haisam a kanta ita kuma Fatuu lokacin ta samu damar kallonshi sosae bata Ankara ba ya juyo suka had'a ido, kayataccen murmushi taga ya sakar mata ta bishi da ido kawae, kaman daga sama suka ji muryar Hajiya tana fad'in suyi sauri su gama ba sai suje suji dad'in kallon Junan ba, sosae kunya ta kama Fatuu ta sunkuyar da kai, da k'yar ta cinye Abincin ta mik'e tace ma Hajiya saida safe ta kalleta tace to Allah ya basu Alkhairi,
bayan ta fita daga cikin Kujerun Hajiya ta tsaida ita tace taje suyi sallama da Yayar ta tace to ta nufi hanyar Corridor tana tafiya kamar wadda k'wai ya fashe mawa a ciki, d'an jimm tay a bakin kopar visitor room d'in gabanta na d'an fad'uwa hakanan fargabar shiga take ji, can dai ta tura kopar a hankali tare da yin yar sallama, a kwance ta hangota ta kife fuska a jikin pillow kai da gani kasan da wuya in ba kuka take ba, bugun k'irjin Fatuu ne ya k'aru da sauri ta juya zata fita don ta lura kaman bata ji sallamar data yi ba, har zata fita taji Muryar ta ta kira Sunanta, juyowa Fatuu tay ta kalle ta taga ta tashi zaune, a sanyaye ta nufi gadon ta nuna mata gefen ta alamar ta zauna Fatuu na kallon idonta ta gane kuka take duk da goge idon da ta yi, shiru suka d'an yi kafin Fanan d'in tace mata har ta gama cin Abincin ta d'aga mata kai ta jinjina nata itama, shiru suka k'ara yi idanun Fatuu a k'asa wani irin tausayin Fanan d'in take ji can ta d'ago ta kalleta idanunta sun ciko da k'walla cikin karyayyar murya tace "Aunty Fanan don Allah kiyi hak'uri wllh ban ta6a nuna mashi ina son shi ba, ko wannan sak'on da kika gani bani na tura mashi ba wllh k'awata ce kuma sai da na nuna mata ban ji dad'i ba daga baya ma na goge shi ko tambayar shi zaki ko ki duba zaki ga an goge" idanun Fanan d'in suma cike tabb da k'walla take kallon ta harda Murmushin k'arfin hali har ta gama sannan ta kai hannu ta janyota ta kwantar da kanta a saman shoulder d'inta cikin sanyin murya tace 'its okey Zaraah I understand everything, kema bake kika d'aura ma kan ki ba, komai da yake Faruwa akan mutum was already written, Allah ya bamu ikon ruk'e Amanar juna and am sorry for what u'r going through itama Friend d'in tak'i taga kina wahala ne yasa ta yanke turo sak'on" shiru Fatuu tay wani irin tausayin Fanan ya mamaye mata zuciya, can ta d'ago daga kan kafad'ar tata ta kalleta a sanyaye tace mata to don Allah ta daina yin kuka bata jin dad'in ganin ta haka sai taita ganin kaman Saboda ita ne, da sauri ta girgiza mata kai tace ta bar sama ranta hakan kawai abunne gaba d'aya yazo mata a bazata so dole sai a hankali zata washe nan ta sanar mata da bata san komai ba sai da aka turo sak'on ita ta fara gani, sosae Fatuu taji ba dad'i Fuskarta a yamutse take kallonta can Fanan d'in tace mata ta k'ara girma sosae tana murmushi harda tambayar ta ta kai 20yrs ne yanzu, Fatun tace mata a'a 19 take ta jinjina kai tace tana da jiki mai kyau ita dai d'an murmushi kawai tayi sai kuma tace mata itama ai tana da kyaun jiki ga tsawo ita kuwa gajera ce har saida tasa Fanan d'in yar dariya,
tambayarta karatun ta tayi tace ta kusa gamawa ko, ta bata amsa da yanzu zasu kama nursing 2 sai su shiga 3 daga nan zasu gama, jinjina kai tayi tace Allah ya basu sa'a bayan Fatuu ta amsa tace "in kika gama nasan U.S zaki dawo sai kiyi Medicine