Showing 90001 words to 93000 words out of 512766 words

Chapter 31 - Asanadin Makwabtaka Book 3 Hausa Novel Complete

Unknown   

27 Dec 2024

1607

d'aga ba kema kuma baki d'aga mata ba?" A rud'e Fauzy tace "a....a'a banji kiran ba k'ilan ko wayar bata a tare da ita don ban ganta ba tun d'azun"

"To ki tasheta ki bata wayar taki ina son magana ne da ita" Fauzy ta amsa da to da sauri tana k'ok'arin sauka daga kan gadonta ta nufi Fatuu ta sunkuya ta kai hannu tana tashin ta a hankali ta bud'e idanunta da sauri don kada ta fad'i wani abun Fauzy ta kanga mata wayar a kunne tace "gwaggo ce ke son magana da ke kiyi magana" waro ido Fatuu tay saida ta had'iya miyau Kutt kafin tayi sallama gwaggon bata amsa mata sallamar ba tace "ina kika jefa wayar ki ne anata kira tana shiga amman ba'a d'agawa?" Kikkafta ido ta fara yi a d'an razane jin yanayin voice d'in gwaggon tace mata wayar na a silent ne shiyasa ita kuma bacci ya d'auketa cike da bada umarni tace "to duk abunda kike yi ki bari yanzu yanzun nan ki taho gida ina jiran ki" zaro ido Fatuu tay sosae gabanta ya hau fad'uwa cikin inda inda tace "s..sai anjima da daddare zan taho gwaggo zamu yi wani group......" Bata samu damar k'arasawa ba sakamakon tsawar da gwaggon tayi mata tace yanzu take son ta taho ba sai anjima ba da sauri Fatun tace mata to gata nan tahowa daga haka ta kashe kiran, kallon Fauzy Fatuu tay idanu waje itama kallon nata take a d'an kid'ime ta tambaye ta abunda ke faruwa Fatun ta yarfa hannu tace "nima ban sani ba tace dai komi nake yi in bari in tafi gida yanzu gashi a muryar ta kaman akwae alamun tashin hankali" wani kuka cikin Fauzy yay tace "to kodae tasan da Maganar cikin ne?" tay Maganar hannunta guda ruk'e da ha6arta Fatuu dake kallonta tace "taya za'ai ta sani baccin daga ni sai ke muka sani...." da sauri Fauzy tace "sai kuma Ya Haisam ba" wani kallo Fatun tay mata tace "kina nufin shi zaije ya gaya mata?" Fauzy tace "Eh mana shiyasa nace da kin d'auki kiran shi kin ji mi zai ce maki yana iya yin tunanin kar kije ki samu matsala wurin yin abortion d'in ya yanke gwara yaje ya gaya ma gwaggon" wani kallon anya kina da hankali Fatun ke bin Fauzy dashi tace "Saboda tsabar baida hankali ya aikata man hakan sannan yaje ya fad'i mata haba da Allah kema Fauzy ai baya ma fara ba wllh k'ilan dae akwae abunda ya faru kawae ba wannan ba" uhmm kawai Fauzyn tace,

"Ni tsoro na ma kada sai ina gidan cikin ya zube tunda har yanzu shiru, koda yake tunda ba wani babba bane nasan ba wani jini zan zubda ba in sha Allahu in ma ta fuskanci wani abu sai in ce mata period d'ina ne ya zo yau" tana k'arasawa tay d'an murmushin jin dad'in samun mafita ta mik'e Fauzy dae nata bin ta da ido gaba d'aya a tsorace take, bayan ta had'a duk abunda zata d'auka a jakar goyonta ta yafa mayafin jallabiyar jikinta tace ma Fauzy ta tafi jiki a mace tace bari ta rakata ta hau Napep, bayan sun fito daga Hostel d'in sun nufi gate Fatuu ke tambayar ta sai yaushe zata tafi weekend d'in Fauzyn tace sai d'an anjima bayan Magrib in ta gama kimtsawa, bayan sun fito suka samu Keke Napep Fatun ta shige Fauzy tace mata duk abunda ake ciki don Allah ta kirata don a tsorace take wllh Fatun tace ta kwantar da hankalin ta in sha Allahu ba game da wannan abun bane ta d'aga mata kai kawae suka tafi Fauzy ta juyo sukuku da ita ta koma Hostel,

lokacin da suka iso layin gidan nasu tun kafin su tsaya a kopar gidan ta hango Motar Haisam dake fake wani irin bugu k'irjinta ya shiga yi har Mai Napep d'in ya tsaya a gaban Motar ta fito da tsananin mamaki take kallon Motar, bayan ta biya shi ta juya suka had'a ido da Kawu Amadu dake kallonta ta cikin shago nan da nan ta sha jinin jikinta da k'yar ta d'aga k'afarta ta nufi wurin shi ta tsaya a gaban Shagon ta gaishe da shi duk ta kame kanta ya amsa yanata kallonta don shi kan shi ya lura da canzawar da tayi kafin yace mata ta shiga gwaggo na jiranta, a kid'ime ta tambaye shi Ya Haisam na ciki ne yace mata eh tay jimm kaman bazata wuce ba har saida yay mata magana sannan ta nufi hanyar shiga gidan k'irjin ta tamkar ana mata luguden ta6are kanta ya gama d'aurewa ta tabbata dae Ya Haisam d'in zuwa yay gidan su ya fad'a, tunanin abunda yazo yace ta shiga yi ba kamar yadda taji gwaggon na mata Magana da ta kira waya "ba dai kaina aka d'aura laifin ba!!!" ta raya a cikin zuciyar ta, lokacin data shiga zauren gidan d'an jimm tay kaman bazata shiga ba can dae ta shiga cike da fargaba ta nufi Parlor ganin takalman su anan tana zuwa bakin kopar parlon taja ta tsaya ido waje ganin Hajiya a zaune ita bata ma ganta ba saida gwaggo tace mata ta shigo ciki sannan Hajiyar ta juya ta kalleta, a d'arare ta shiga ta k'ara togewa a bakin kopar tana ta zare ido wani irin kallo gwaggo ke bin ta da shi Lokaci guda jikinta yay lakwas don ko ba'a fad'a mata ba ta gane mike faruwa da Fatun Hajiya ce ta nuna mata gefenta tace tazo ta zauna ta nufi wurin jikinta tamkar ana zare mata lakka, bayan ta zauna murya na rawa ta gaishe da ita kafin ta d'an saci kallon Haisam da idanun shi ke akan Carpet itama ta sunkuyar da kan nata tana kallon yatsun hannunta dake yin rawa ji take inama ta 6ace bat daga wurin Hajiya ce ta katse shirun da fad'in "Dije ga Fateema ta zo yanzu zan sanar dake abunda ke faruwa amman kaman yadda na rok'e ki kafin yanzu ina sake rok'on ki don girman Allah kiyi hakuri kiyi hakuri dije duk da wannan yayi kad'an ya hana zuciyar ki girgiza amman dai ina rok'on ki kar ki tashi hankalin ki sosae ta yarda zaki cutu don aikin gama ya riga da ya gama sai ayi tunanin mafita kawae tunda ko an tashi hankalin ba abunda zai canza...." d'agowa gwaggo tay ta kalli Hajiyar fuska a kwa6e ta jinjina mata kai kawae, d'an jimm Hajiya tay ita kanta bazata iya tuna ranar da taji fargabar sanar da wani abu irin yau ba gani take kamar zuciyar gwaggo zata iya bugawa ita kanta Fatuu tuni kwalla sun fara gangaro mata tasa hannu ta rufe bakinta ji take kamar kar a sanar ma da gwaggon don in dai wani abu ya sameta to bazata ta6a yafe na kan ta da kuma Haisam ba, sosae kuma tay mamakin k'arfin halin shi da har ya iya zuwa ya sanar da abu irin wannan, jin Hajiyar tak'i cigaba yasa gwaggo ce mata karta ji komae ta sanar mata kawae ita ai musulma ce ta yarda da k'addara mai kyau da kuma Maras kyau jin haka yasa Hajiya d'an gyara zama ido cike da k'walla tace "Dije Fateema dai.....CIKI ne da ita, kuma ba kowa ne yay mata ba sai wannan k'aton kawai d'in da bai dubi girman zumunci ba bai dubi girman yarda ba ya iya cin Amana har haka ta hanyar biye ma son zuciya...." Fashewa tay da matsanancin kuka Fatuu ma haka ita kuwa Gwaggo ta sadda kanta ta yadda bazaka iya gane halin da take ciki ba can Hajiya ta d'ago taci gaba "Don girman Allah dije kiyi hak'uri a taru a rufa ma juna Asiri tunda abun nan duk na gida ne iya cuta dae nasan an cuceku shiyasa ma ake baku hakuri......." kallabin ta ta kwanto taci gaba da share hawaye da shi, duk da kasancewar ta tsufa kan cike yake da gashi wanda rabin shi duk hurhura ce anyi mata kitso all back, duk abun nan sai yanzu Haisam ya d'ago da kan shi ya kalli Hajiya kafin ya maida idon kan Fatuu da sadda kai tana ta kuka slowly ya maido kallon kan Gwaggo cikin sa'a ta d'ago da fuskarta suka had'a ido d'an jinjina mata kai yay had'i da d'an lumshe ido kafin ya mayar da kallon k'asa nan take ta fahimci abunda yake nufi, d'agowa Hajiya tay ta kalli Fatuu dake ta kuka tace "Fateema ya akai kika biye mashi, ki ka bari ya cutar da ke har haka keda nike ganin ki mai hankali da wayau baki tunanin ke zaki fi cutuwa ba a matsayin ki na yarinyar budurwa shi kuwa yayi auren shi!" d'agowa Fatuu tay cikin kuka tace "Wllh Hajiya ba laifi na bane shine yace zan raka shi dinner d'in abokin shi to da muka je bamu dad'e ba muka bar wurin...to da muka taho shine nay fushi Saboda bai bari mun dad'e ba shine ya wuce dani G.r.a bayan ya siya abubuwan ci, koda muka je ni ban so shiga cikin gidan ba hakanan na bi shi.....da muka je wani d'aki nan ma saida na tambaye shi abunda muka zo yi shine yace wai zan k'arasa abunda bai bar ni nayi ba a wurin dinner d'in har nike fushi......to bayan mun ci Abinci tare da shi sai aka kira shi a waya shine ya d'aukko laptop ya fara latsawa da na ga dare yayi sosae nayi mashi magana akan yakamata mu tafi shi...shine yace in bari zai d'an ida wani aiki ne to nan har nace bari in yi salla bayan na gama na koma kan kujera ina kallo sai bacci ya fara d'aukata ina haka na farka nace mashi mu tafi dare yayi sosae yace to ya mik'e nima na mik'e bayan na fita wurin kujeru shima ya tafi ya d'aukko makullin Mota kawae sai aka d'auke da wuta shi......." Kafin ta k'arasa gwaggo ta daka mata wata irin tsawa tace "DUM HETSI FATUU!!!" a razane Fatuu ta kalli gwaggon haka ma Hajiya da mamaki take kallon gwaggon jin yadda ta daka mata tsawa bayan ita aka cutar idanun gwaggon ne suka ciko da kwalla gani take sam ba'a kyauta ma Haisam ba wannan tonon sililin har ina ya muzanta, cikin harshen fulatanci murya na rawa ta hau yi ma Fatuu Magana tana rufe baki a wani irin zabure Fatuu ta mik'e tana zare ido baki bud'e idonta akan Haisam da still kan shi na k'asa, cikin d'aurewar kai Hajiya tace "a'a Dije, a'a, kada muyi haka dake ya za'a cuci yarinya har haka sannan ki hau daka mata tsawa tamkar itace mai laifi bugunta za'ai kuma a hanata kuka? to mi Haisam d'in yayi maki da har ya shanye ki haka??" rai 6ace take Maganar ita kuwa gwaggon maida kan ta tay k'asa ba alamar zata yi magana Hajiya ta maida idonta kan Fatuu da ke tsaye cike da tashin hankali jikinta sai 6ari yake tace "fad'a man mi tace maki ne Fateema? ba don ma na watsar ba ai nima ina d'an jin fullancin za'a canza harshe a cuci yarinya" sake tambayar Fatuu tay kan ta fad'a mata abunda tace mata a d'imauce Fatun tace "C...cewa cewa tay w...wai shi MIJINA NE!" sakin baki Hajiya tay jin wata magana kamar ta wanda ya sha giya Haisam mijin Fateema ta ina!!! wani kallo Hajiya ke bin gwaggo dashi cikin d'aurewar kai tace "Dije ko dae kema chemicals d'in da Kike amfani dasu a wurin aiki suna bugar da ke ne da har yasa kike magana mara kan gado haka?" d'agowa gwaggo tay fuskarta share share da hawaye ta girgiza kai tace "Hajiya da suna bugar da ni zuwa yanzu ai da ban tunanin za'a same ni da cikakken hankali....." Da sauri Hajiya ta katse ta tace "ai Maganar da ki kai Dije ta nuna babu cikakken hankali a tare dake kwata kwata Haisam fa kika ce wai mijin Fateema ne Saboda Allah har ki tunanin kina da Hankali? A yaushe aka d'aura masu auren da har mu bamu sani ba???" Shiru gwaggo tay ita kuwa Hajiyar ta kafeta da ido can ta juya ta kalli Haisam da still kan shi na k'asa ganin yadda bai ce komae bane yasa jikin Hajiyar idasa mutuwa don da alamu da gaske ne kenan tunda gashi bai ce komae ba cikin daka tsawa tace masu bazasu yi mata bayani ba ta ya akai Haisam ya auri Fateema?? Had'iye abu gwaggo tay cikin rawar murya tace "tabbas akwae igiyar auren shi ukku akanta hakan ne ma yasa aka fasa auren ta da wanda aka so aura mata bayan munje can ni da Abbas lokacin da ta gudo, saidae ita Kanta bata san da hakan ba Saboda wani dalili Abbas ne zai yi maki bayanin komae" da alama Hajiya mutuwar zaune tay don kuwa idanunta ko kyaftawa basa yi ita kuwa Fatuu jin wannan bayanin na gwaggo ya k'ara jefa ta cikin matsanancin tashin hankali nan take taji mararta ta fara murd'a mata ta kai hannu ta dafeta tana nishi da k'arfi, wani abu mai d'umi taji ya fara zubo mata ta k'afafun ta hannu na rawa ta d'an d'aga jallabiyar nan take idanunta su kai tozali da jinin dake ta zubowa tamkar ana koro shi a razane ta d'ago ta kai idon ta kan Haisam da shima idon shi ke akan jinin dake zubowar shi kadae ya lura da abunda ke faruwa wani irin jiri ne ya kwasheta ta kai hannu ta dafe goshi kafin ta tafi gaba d'aya zata kifa cikin zafin nama ya yunk'ura ya isa gareta ya tarbeta ta fad'a jikin shi..........


Yau akwae yak'i tsakanin team Fatuu da team Haisam🤣 Wllh yan team Haisam kada ku yarda ku bi mashi hakkin shi gurin duk wanda ya zage shi ko ya muzan tashi da munanan kalamai☹️



_Littafin A Sanadin Makwabtaka part 2 Naira 300 ne za'a tura ma Mutum har part 1 ga mai so zai turo kudin ta wannan Account din, 1509618776, Zainab Bature Access Bank, za'a turo shedar biya ta wad'annan nos din 09013804524 ko 08169856268
[5/8, 19:28] +234 901 700 4868: *ASM Bk2051*

_Destiny may be delayed but cannot be changed...._


*DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI*



.............A razane duk suka mik'e ganin abunda ke faruwa Hajiya ta fara fad'in" gashi nan ai zaku kashe masu D'iya..." Gwaggo duk ta rud'e hannunta sai rawa yake daukarta Haisam d'in yayi yay hanyar fita parlon da ita duk suka rufa mashi baya, yana fita ya kira Amadu da k'arfi ya fito daga cikin shagon da sauri koda yaga abunda ke faruwa da gudu ya nufi Motar ya bud'e mashi baya ya sakata lokacin Hajiya ta fito ta nufi Motar itama ta shige bayan ta d'aura kan Fatuu akan cinyoyinta sai ga gwaggo itama ta fito tana kokarin sanya hijab hannunta ruk'e da wata hijabin da sauri Amadu ya tunkare ta cikin tashin hankali ya fara tambayarta abunda ke faruwa idanu cike da k'walla tace "Maganar da tsawo ka kula da gidan" daga haka ta nufi Motar Haisam yay mata nuni data shiga gaba tace to ta bud'e kopar ta shiga shima ya shiga driver seat ya tashi Motar bayan ya juyata suka tafi Amadu na tsaye jikin shi gaba d'aya ya mutu yabi Motar da kallo har ta 6ace ma ganin shi sannan jiki a mace ya koma shago, tunda suka hau hanya Hajiya ke sababi tana Fad'in "Wllh idan wani abu ya samu yarinyar nan duk sai nayi k'arar ku tunda kun d'auki aure abun wasa abu kamar a shirin film ko littafi ace wai Haisam ya auri Fateema ba tare da sanin mu ba Saboda bamu da amfani ke Dije da nike gani mai hankali amman kika goyi baya...." Dakatawa tay tayi k'wafa kafin ta maida idonta kan Haisam dake driving tace "ko ba abunda ya faru da ita sai na bi mata hakkinta hakanan kusa yarinya tay ta yawo da aure a saman kanta ba tare da ta sani ba kaman baku san darajar shi ba, sannan wllh kukan daka sani shima sai na bi hakki na hakanan kasa ni kuka share share ko mahaifin ka daya kwanta ciwo bamma shi kuka haka ba don iskan ci kasan yarinyar matar ka ce shine bazaka sanar dani ba da kazo sanar man da aika aikar da kayi mata ka nuna man raping d'inta kai kana ganin kuma yadda hankali na ya tashi na d'imauce amman ko a jikin ka Saboda shegen miskilanci wato in mutu ma kai ko a jikin ka ko bari dae Allah ya tashi Fateema dani kake zancen" tsit kowa yay gwaggo kanta na k'asa shi kuma idon shi na akan hanya yanata driving bai ko kalleta ba ta cikin mirror can ya kai hannu cikin aljihun jeans d'in shi ya fiddo wayar shi kokarin kiran Dr Habeeb wanda ya ta6a duba Fatuu da ya kaita har yasan ta fara period ya shiga yi saidae layin nashi baya shiga kusan 3 times yana jarabawa but isn't available Abbas ya koma kira ringing biyu ya d'aga tun kafin yace wani abu Haisam d'in ya riga shi ta hanyar kiran sunan shi Abbas d'in ya amsa yace mashi Don Allah idan yana da wani phone no d'in Dr Habeeb ya kira shi yaji in yana Hospital gasu nan kan hanya zasu kai Zarah and is Emergency, hankalin Abbas d'in ne ya tashi ya hau tambayar shi abunda ya faru da ita yace mashi yana driving ne zasu yi Magana pls ya kira Dr d'in yanzu daga haka ya katse Hajiya ta kya6e baki tace "ai da sai kayi mashi bayani yarinyar mutane zaku kashe tunda shima da sa hannun shi" still bai tanka ta ba sai dae ya d'an kalleta ta cikin mirror suka had'a ido ta wurga mashi uwar harara ya maida idon kan hanya yana cigaba da driving.

YADDA HAISAM YA AURI FATUU,

A Lokacin da Alhaji Lawal yazo wurin Ard'o ya sanar da batun janye Maganar auran Khalid da Fatuu Saboda yarinyar bata

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login