Showing 447001 words to 450000 words out of 512766 words
Chapter 150 - Asanadin Makwabtaka Book 3 Hausa Novel Complete
Unknown
27 Dec 2024
2324
sun dawo sai su wuce Yolar tunda shima komawa zaiyi Alhaji yace yauwa to hakan yayi, Part ɗin da aka sauke su Haisam ya wuce don ya shirya lokacin daya je Fatuu har ta gama shiryawa cikin doguwar rigar shadda ta saka sarƙa da yankunnan Diamond su twins ma ta saka masu ƙananun kaya iri ɗaya, yana shigowa ta nufeshi tana murmushi ya buɗe mata hannu yay hugging nata can ƙasan maƙoshi ya furta mata "I luv you with every single beat of My Heart Baby" lumshe ido tayi jin yadda hucin Maganar ya bugi kunnanta, shiru yay yana breathing a hankali can ta ɗago da fuskarta ta kalle shi sai taga kaman wani yanayi da bata sani ba akan fuskar shi, tambayar shi tayi ko da wani abu a hankali ya lumshe ido tare da ɗan girgiza mata kai daga haka yay pecking goshinta ya saketa yace bari yay wanka, juyawa yay ya nufi hanyar toilet tabi bayan shi da kallo can ta ɗan ɗaga murya tace "....Know dat am breathing because of you Hubby" dakatawa yay ya juyo yay mata murmushi itama shi tayi mashi kafin ya juya, zama tayi a bakin gado tay shiru kamar mai nazarin wani abu, bai daɗe ba ya fito sanin tafiya zasu yi ita ta taimaka mashi ya shirya yasa brown shaddar cikin wanda Alhaji ya kawo mashi sosae ta hau jikinshi ita ta ɗaura mashi agogo ta saka mashi links ta feshe shi da turare yanata mata murmushi, bayan sun gama shiryawa sun tattara komai suka fito kowa na ɗauke da yaro guda abun gwanin sha'awa, koda su Alhaji da Hajiya suka gansu saida suka yi santin kyaun da sukai Khalid dai murmushin karfin hali kawai yake shi kaɗai yasan mike faruwa a cikin zuciyarshi, har bakin Mota su Alhaji suka rako su sukai masu sai sun dawo, tunda suka hawo hanya Fatuu bata bari ta kalli saitin Khalid ba shi ke driving ɗin Haisam na a kujerar gefe ita kuma tana baya saitin kujerar Haisam, bai wuce sau ɗaya zuwa biyu ba sukai magana shida Haisam har suka iso, a tare gaba ɗaya suka je ɗakin Arɗon bayan sun gaishe shi Khalid ɗin ya shiga dadduba shi tare da yi mashi tambayoyi da fulatanci yana bashi amsa bayan ya gama ya faɗi ma su Baffan su Fatuu ranar da zasu kai shi asibitin suka ce to nan Haisam yayi mashi sallama da fatan Allah ya bashi lafiya ya amsa yana ta mashi godiya da saka mashi Albarka, wani ƙumshin leda yasa Baffa ya ɗaukko mashi yaba Fatuu yace ga magungunan nan ya faɗi mata yadda zata masu da yadda zata rinƙa ba su twins har itama yace tasha da Haisam sukai mashi godiya, bayan sun fito ƙopar gida Khalid ya koma su kuma suka nufi bangaren su Yadikko sai faman leƙowa ake ana kallon su, a parlor aka zazzauna suka shiga gaisawa bayan ɗan lokaci Haisam yayi ma Yadikko sallama tanata mashi godiya da saka albarka ya kai hannu aljihun rigarshi ya fiddo kuɗi masu yawa ya miƙa ma Baffa yace gashi a raba ma mutanen gidan sannan ya tambayi Account ɗin shi yace zai tura kuɗin da za'ai ma Arɗo amfani a Asibitin Baffan nata roƙonshi kan ya barshi za'a kai shi yana murmushi yace ba wani abu yayi niyya ne, kuɗi masu yawan gaske ya tura har saida Baffa ya jinjina kuɗin yace hidiman tayi yawa shidai ba komai kawae yake cewa, Godiya sosae sukai mashi ya miƙe yace ma Fatuu in ta gama yana waje Baffan ma ya miƙe suka fita tare, bayan fitar shi ne Yadikko ke mata tsegumin Khalid don taji dashi suka zo Fatuu ta faɗi mata yadda akai suka taho tare tace kuma Haisam bai nuna komai ba tace mata a'a, itama Fatun saida taba Yadikko kuɗi harda Baffanta ta bada ta bashi dasu Aysha sukaita Godiya ta ɗaukko mata wasu magunguna da zasu inganta lafiyar ta data cikin jikinta da kuma wanda zata samu sauƙin haihuwa ta faɗi mata yadda zatayi amfani dasu, tare da Yadikko suka zazzagaya yi ma sauran mutane sallama nan fa aka shiga ba su twins kyautar abubuwa su kaji, zabbi harda akuyoyi cikin wanda suka basu akoyoyi harda Yaya, duk Yadikko ta amsa tace zata kiwata masu kafin daga baya a aika masu tunda ba'a Mota zasu koma ba, bangaren su Yadikkon ƙwai masu yawa suka basu da uban dawon fura da Nono harda zuma mai yawa da man shanu duk akai masu dubara yadda ƙwan bazasu fashe ba haka Nonon ma harda ƙanƙara aka saka mashi yadda zai tsaya da sanyin shi gaba ɗaya cikin wata jaka aka saka su a haka ma kayan sunyi ma Yadikko kaɗan tace inda da Mota suka zo sai an cika boot ɗinta da fura da Nono saboda su twins Fatuu nata dariya tace a haka ma ai da yawa, kusan gaba ɗaya gidan aka fito rakiyar su waje anata masu Allah ya tsare hanya, bayan sun baro rugar gidan su Khalid suka koma anan suka ci abincin rana kafin sukai masu sallama Hajiya Rabi'atu taba Fatuu kyautar atampopi masu kyau guda biyu da lace harda humra masu ƙamshi da turarurrukan wuta su twins ma ta basu kaya sosae tayi mata godiya harda Haisam, har bakin Mota suka rako su lokacin da suka baro gidan ƙarfe ukku na rana zuwa karfe huɗu da wasu mintuna suka iso Yola, har gidan Senator Buba Khalid ya kai su da har yace bari ya jira su sai ya kai su Airport Haisam yace mashi ya bashshi kawai kar su 6ata mashi lokaci akwae Driver da zai kai su yayi mashi godiya kafin ya amshi lambar shi yace zai kira yaji yadda ake ciki dangane da jikin Arɗo Khalid ɗin yace Ok, harda kuɗi yaba su twins Fatuu tace ya barshi yana murmushi yace ai ba ita yaba ba yaranshi yaba ta amsa tayi mashi godiya tare da cewa ya gaishe da iyali yace zasu ji daga haka ya tafi, da suka shiga cikin gidan basu daɗe ba salla kawai sukai koda aka basu abinci cewa sukai a ƙoshe suke sukai masu sallama nan ma saida aka ba Fatuu da twins kaya Senator Buba ma ya basu kyautar kuɗi masu yawa zumunci mai daɗi, a wata jibgegiyar Jeep aka tafi kai su Airport harda Senator Buba yay masu rakiya, suna akan hanyar ne Fatuu taji ƙarar shigowar saƙo a wayarta, lokacin data duba saƙon har saida gabanta yay bugu da ƙarfi don ta gane Khalid ne ya turo duk da bata da lambarshi amman daga yanayin saƙon ta gane nashi ne, da turanci ya rubuto mata yana mai bata haƙuri da kuma neman yafiyarta akan abunda ya faru a tsakaninsu a baya yayi nadama da kuma danasanin da yasan har ya mutu bazai daina yi ba sai dai ta wani bangaren yayi farincikin shigowarta rayuwarshi don ta dalilinta Allah yasa ya daina duk wani abu mara kyau a ƙarshe yana son ta sani ta zamo wani bangare na rayuwarshi wanda hakan ne ma yasa shi saka ma ɗiyarshi sunanta, tana gama karantawa ta ɗan saci kallon Haisam dake gefenta taga idon shi na a gaba suna yar hira da Senator Buba dake a seat ɗin gaba, kamar ta share Khalid ɗin ba sai ta mayar mashi da amsa ba sai kuma wata zuciyar ta raya mata yana iya cewa zai ƙara turo mata wani saƙon saboda rashin jin amsarta hakan yasa ta maida mashi da amsa, itama da turanci tace komai ya rigada ya wuce don har tama manta kuma tun bayan da aka fasa aurensu ta yafe mashi don haka tana fatan shima ya manta sannan ta gode da karar da yayi mata ya gaida mata da Zarah da Mamanta, tana tura saƙon ta goge duka nashi daya turo mata da nata data tura mashi sannan tayi blocking ɗin lambar tashi yadda bazai iya sake turo mata saƙo ba ko ya kirata tay shiru zuciyarta ta shiga tariyo mata da abubuwan da suka faru tsakaninsu yadda ya rinƙa yi mata a cikin Mota da gidan gonarsu da ya kaita, idanunta ne suka fara tara ƙwalla da sauri ta fara ƙoƙarin mayar dasu tare da kawar da tunanin daga ranta.
Bayan sun dawo Abuja Washe gari Fatuu taje gidan Mino kai mata tsaraba Haisam ne ya kawota su twins a gida ta barsu, taji daɗin ganin yadda Mino ta saki jiki suna ta shan amarci da Nameer ta sha kananun kaya riga da wando, bayan data je ne Nameer ɗin ya fita, sosae Mino taji daɗin tsarabar data kai mata tace itama bada daɗewa ba zata je Yola Fatuu ta ɗan harareta tace ba yanzu ba sai ta shekara Minon ta noƙe kai tace "kai Adda Fatuu shekara yayi yawa ni dai gaskiya nan bada daɗewa ba zanje nasan dana nuna ma My Love ina son zuwa zai bar ni ƙilan ma tare zamu je" ɗan buɗa ido Fatuu tay ta ruƙe haba ta maimaita My Love ɗin da ta faɗa Mino ta saka dariya tare da rufe fuska alamar kunya, hira suka cigaba da yi anan Fatuu ke mata zancen Karatunta tace kar ta bari soyayya tasa ta shashantar dashi koda SSCE ne tayi ta samu result ɗin gama Secondary Minon tace eh rannan sunyi magana yace zata zana jarabawar sannan in zai tafi yin Master's Degree ɗin shi US zasu tafi tare sai taci gaba da Karatu a can, sosae Fatuu taji dadin jin hakan anan take sanar mata zancen komawarsu Us Mino ta marairaice fuska kamar zatayi kuka tace yanzu shikenan tafiya zatayi ta zama bata da kowa a nan Fatun tace mata kada ta damu tasan bazata yi maraicin rashinta ba tunda ga yan gidan su Nameer nan tasan zasu zame mata tamkar yan'uwa, tare suka shiga Kitchen yin abinci suna cikin yin aikin ne Mino ke faɗi mata wai Nameer yace in tana so a samo mata mai aiki da sauri Fatuu tace to ya tace mashi Minon tace cewa tayi ba sai an samo ba tunda ba wani aiki sosae sai yace wai ko gyaran gida ne a rinƙa yi mata, girgiza kai Fatuu tay tace kada a samo mata wata mai aiki ai gyaran gidan ma zata iya tunda ba wani datti yake yi ba inda take amfani dashi kullum kamar Bedroom, toilet da Kitchen su ta rinƙa gyara su kullum shi kuma falon tunda yana da girma in kamar taga bai 6aci ba tana iya bari sai bayan kwana biyu ta rinƙa sharewa amman zata iya kullum tasa towel ta goge kayan kallo da kujeru sai ta rinƙa saka turaren wuta akai akai koda zata yi mai aiki a bari ba yanzu ba sai kamar in ta samu ciki tayi nauyi kuma mai aikin ma kada ta bari a samo mata yarinya ko budurwa in ba haka ba a kwace mata My Love tana gani, dariya Mino tayi tace ita so take ma Aysha ta dawo wurinta shikenan ma ba sai tayi wata mai aiki ba Fatun tayi ɗan jimm alamar nazari kafin tace mata hakan ma yayi amman ta bari ba yanzu zata ɗaukkota ba tace to, bayan sun gama girkin saida suka gyara ko ina sannan suka zauna suka ci tare, Sai bayan Magrib Haisam yazo ɗaukarta lokacin Nameer ya dawo ya shigo cikin parlon suka gaisa Mino ta kawo mashi abun ta6awa da lemu daga baya sukai sallama. A ranar da daddare Haisam ke faɗi mata nan da sati guda zasu tafi Us, ana saura kwana ukku su tafi taje Katsina yin bankwana, har gidan Aunty mareeya da Feenah taje sannan taje gidansu Aminiyarta Haulat harda abun arziƙin data saba tayi mata taba Kawu Amadu makullin Motarta tace yaci gaba da yin amfani da ita, kwananta biyu ta dawo Abuja Washe gari wurin ƙarfe sha ɗaya suka tafi harda Mino amarya akai masu rakiya Airport daga nan Lagos zasu je wurin Fanan sai da daddare zasu tashi zuwa Us.
Fauzy taso zuwa Funtua bayan zuwan su amman Sameer yace tayi haƙuri ba yanzu ba don tana iya samun matsala in tayi wannan tafiyar a mota dole ta haƙura anan Nasarawa suka tsaya don zasu ɗan kwana biyu kafin su koma London, Bayan bikin Mino da kamar wata ɗaya lokacin satin su Fatuu biyu da komawa da daddare bayan sallar isha Gwaggo na zaune kan abun salla tun bayan data gama sallar take zaune a wurin kamar mai tunanin wani abu can ta kai hannu ta ɗaukko wayarta dake ajiye gefen abun salla ta shiga kiran Amadu, bayan ya ɗaga ta tambayi sun dawo daga masallaci ne yace mata eh ta ƙara tambayar ina Kamalu yace gasu nan tare a shago tace to shi ya shigo tana son ganin shi yace to, bada daɗewa ba ya shigo ɗakin da sallama ta ɗaga kai ta kalleshi tana amsawa ya nufi kan kujera ya zauna, gaishe da ita yayi ta amsa yace gashi ta ɗaga kai, shiru ta ɗan yi yanata kallonta can tace "Dama so nike in tambayeka wai kai baka son yin Aure ne?" ɗan waro ido yay sai kuma yayi yar dariya yace yana so mana amman miyasa tace haka ta ɗan ta6e baki tace taga baida niyya ne gashi yanata girma yanzu har ya fita daga shekara talatin amman bata ta6a jin yayi zancen yana da budurwa ba, yana dariya yace kawai shi soyayyarce ya ɗauketa 6ata lokaci don da yawa sai yaga an daɗe ana soyayya amman sai kaga anzo ba'a yi aure ba shiyasa Amman daya samu wadda suka fahimci juna zai yi auren, kai Gwaggo ta jinjina ta ɗan yi shiru tana kallon ƙasa ya fahimci kamar akwae wani abu a ranta hakan yasa shi tambayarta koda wani abu ta ɗago tana murmushi tace "Dama wata shawara ce nike son baka nace mi zai hana ka auri Haulatu duk da ba budurwa bace amman bata da wani aibu ina son yarinyar don tanada halin kirki kuma abunda aka fi buƙata kenan a wurin macen aure na tabbatar duk wanda ya aureta sai yaji daɗin zama da ita saboda tana da haƙuri sosae, ka duba yadda aka kasa yin ƙawance da Fatuu saboda halinta lokacin kuruciyarta amman haka Haulat ta jure duk da halinta na cika mutum haka taita haƙuri sa ita sukayi ƙawance har suka zama tamkar yan'uwa",
Shiru Kawu Amadu yay idonshi a ƙasa ganin haka yasa Gwaggon tace ita shawara ce ta bashi ba dole take mashi ba in bata yi mashi ba shikenan tana mashi Addu'ar Allah ya bashi wadda zasu daidaita mai halin kirki, ɗagowa yay yana murmushi yace a'a bawai bata yi mashi bane kawai yana mamakin yadda tunaninsu yazo daya ne don tun bayan dawowarta yaji yana son aurenta saida ya bari ta gama takaba sannan kwanaki yaje mata da Maganar amman sai bata yi na'am ba tace wai tursasa mashi akai kan ya aureta kuma tasan bai wuce Fatuu ce tasa saboda tausayinta da take amman in akace ya aureta ai an ƙware shi tunda ita yanzu ba budurwa bace, lokacin ya nuna mata shi ba wanda yasa shi shiya kawo kanshi to sai tace wai ya bata lokaci zata yi shawara to har yanzu zaman jiran amsarta yake ko bayan bikin su Mino saida yayi mata maganar amman sai ta ƙara cewa ya dai ƙara mata lokaci, Murmushi Gwaggo tayi tace ina ruwan Haulatu, duba agogon wayarta tayi taga lokaci kafin ta fara ƙoƙarin miƙewa tana faɗin bari taje gidan su, miƙewa yay shima yace suje ya rakata, bayan sun fito Amadu ya kwala ma Kamalu kira ya leƙo yace mashi zasu je su dawo yace to ya gaishe da gwaggo ta amsa tana murmushi, suna tafe suna hira gwanin sha'awa har kama Gwaggon yake lokacin da suka iso gidan a waje ya tsaya ita ta shiga, lokacin da tayi sallama innarsu Haulatun na a tsakar gida ta tarbeta da fara'a tana mata sannu da zuwa suka nufi ɗaki, bakin gado ta nuna mata Gwaggon tace bari ta zauna a kan tabarma dake shimfiɗe innar tace ya zata zauna a ƙasa don Allah, Gwaggo tana murmushi tace to ai ita ba baƙuwa bace ko kuma ai ba'a ƙasa bane tunda kan tabarma ne, itama innar zama tayi gefen gwaggon suka shiga gaisawa ta tambayi wurin su Fatuu da Amarya Mino duk tace mata suna nan lafiya, bayan sun gama gaisawa Gwaggo tace mata ina Haulat ne ta bata amsa da tana ɗakin ta ko ta kirata Gwaggon tace a'a tukunna, tambayar innar tayi ko sunyi magana data danganci Amadu da itane da alamun rashin fahimta ta bata amsa da a'a gaskiya, Gwaggo na murmushi a nutse ta shiga yi ma innar bayanin abunda ke faruwa tsakaninsu da Amadu sosae tayi mamaki har fuskarta ta bayyana tana murmushi tace wllh sam bata san da Maganar ba,
"To ko dai tana da wanda take so ta aura ne?" Gwaggo ta tambaya innar ta ɗan yi jimm kafin tace gaskiya bata tunani don har yanzu bata ga ta tsaya ma da wani ba tun bayan data gama takaba amman dai bari a kirata sai aji, Haulat na kwance a saman gado tun bayan data gama yin salla ta kwanta don tasa ummasalma bacci, tuni ma yarinyar tayi baccin ita kuma ta faɗa duniyar tunani wanda a yanzu ya zamar mata jiki ciki harda na Kawu Amadu don idan tace bata son auren shi to tayi ƙarya saidai gani take shi ba don yana sonta bane zai aure ta, innarsu ce ta shigo da sallama ta ɗago kai ta kalleta tare da amsa mata, tambayarta tay ko har ta fara bacci ne tace mata a'a ta kwantar da salma ne tace mata to tazo ɗakinta yanzu da sauri ta tambayeta lafiya innar tay ɗan murmushi tace in tazo taga ko menene ta juya, innar na shiga ɗakin itama ta shigo tana sanye da doguwar rigar bacci ta yafo gyale a kanta, koda taga Gwaggo bata kawo komai ba a ranta ta ɗauka an kirata ne su gaisa ta duƙa a gabanta tana ɗan murmushi ta