Showing 381001 words to 384000 words out of 512766 words

Chapter 128 - Asanadin Makwabtaka Book 3 Hausa Novel Complete

Unknown   

27 Dec 2024

1667

itama haka, cikin d'akin ya nufo ya tsaya d'an nesa da ita yace bazatai welcoming nashi ba tunda shi bak'o ne yanzu, yar dariya tayi ta mik'e ta nufe shi tana zuwa gabanshi ta fad'a jikin shi ya rungumeta suna ta sakin murmushi ga k'amshin jikinsu ya cika ma kowa hanci, d'agowa tay tace mashi ya zauna atare suka zauna idon shi akan yaran ya tambayi ya suke itama kallon su take tace mashi lafiya lou, juyowa tay suka had'a ido ta d'an langa6ar da kai cikin lumshe ido Slowly ya furta mata "I'm missing you" dan buda ido tayi still da murmushi akan Fuskar ta k'asa k'asa tace "ba gani a kusa da kai ba" d'age gira yay yace ba shi ba itama ta d'age mashi tace wanne, wani irin kashe mata ido yay ta saki dariya shima yar dariyar yay ya jawota jikin shi, kai hannu tayi
tana shafa beard cikin salo tace "na gode ma Allah dayasa na haihu lafiya naci gaba da yin rayuwa da kai" lumshe mata ido yay a hankali yace shima haka tana niyyar k'ara yin magana suka ji an shigo a tare suka kai idon su kan kopar Jidderh ce tayi shirin bacci tana ganin su ta dan waro ido tana murmushi kunya ce ta kama Fatuu ta fara k'ok'arin raba jikinta da nashi saidai yak'i bata dama ganin haka yasa Jidderh cewa ta bashi 10 minutes zata je ta dawo harda jaddada mashi da hannu duk sukai yar dariya, bayan ta fita Fatuu ta maida idonta kan shi tace tana son yi mashi wata Magana ya d'aga kai kafin yace yana ji,

"Dama so nike in ce kaman yakamata Ya Sameer yaje Funtua su gaisa da iyayen Fauzy Saboda ba wanda yasan shi fa" shiru yay idon shi akanta can yace mata sun yi magana kan hakan ne da sauri tace a'a kawai itace tayi tunanin hakan, Wani kallo yay mata yace "Kai yar fillona yaushe kika iya yin wannan tunanin" dariya ta saka tace mashi tunda tay hankali ya d'age gira yace to shi miyasa bata ta6a ce mashi yakamata yaje garin su ba da sauri tace "to ai kai kaga Baffana ya sanka tun ma kafin muyi aure kuma gwaggota ma ta san ka amman shi fa ba wanda ya san shi gashi yanzu bai fi saura wata ukku ba bikin" shiru yay da alama nazarin Maganar yake can yay sigh yace mata yanzu dai bai K'asar amman yace zai zo bada dad'ewa ba in yazo zai ga abun da za'ai ta d'aga kai sai kuma tace "amman in kaga fa kaman da takura ko kawai ka bar Maganar in yaje bikin sun ganshi, kai ya girgiza mata yace ai yakamatan yaje saidai yazo,

"To ni yaushe zaka je garin mu?" yana murmushi yace biyanta zai yi kenan tace eh, yace Ok zasu je sai Babies sun k'ara girma harda tambayarta hakan yayi mata tace mashi eh, dawowar Jidderh tasa yayi mata sallama ya tafi. Washe gari Misalin k'arfe ukku na rana su Gwaggo suka iso yanzu ma kamar da biki Mota biyu suka yo da Tk da Saude da Aunty Mareeya, Feenah, Kawu Amadu, Abbas, Fauzy, Mino harda Nana wannan karon ba'a zo da Zainab ba, zo kaga murna wurin Fatuu suma sai murnar ganinta suke ba kamar da suka ga yaran Mino har ta kasa rufe bakinta don dad'i gwaggo ma sai faman murmushi take haka su Aunty Mareeya da Feenah Abdul ma sam ya kasa matsawa daga kusa da yaran sai d'auka d'auka ake d'akin ya cika anata farinciki, harda uban yajin jego gwaggo ta kawo, a Ranar bayan la'asar yan Adamawa suka iso su Yadikko da Kamalu Yaya sai wata k'anwar Baban su Fatuu da d'ayar Matar Ardo wadda ba'a zo da ita biki ba wannan karon ba'a zo da innar su Altine ba duk da taso tazo kamar kamar me amman ba'a zo da itan ba don gwaggo ta fad'i ma Baffan su Fatuu kada azo da yawa tunda ba'a dad'e da aka zo biki ba, wannan karon ma harda shanu suka kawo saidai ba daga Baffan Fatuu ba daga mai girma Ard'o ya ba yan tatta6a kunnan shi saida kowa yayi mamakin yadda suka ciri tuta har ya d'au shanu sukutum ya basu don abu ne da bai ta6a yi ma wani a yaran dangin su ba, basu dad'e da zuwa ba gab da Magrib wasu yan'uwan su Haisam yan d'aura suma suka iso nan fa gida ya dauki haramar suna, wannan karon ma a part d'in baya duk aka sauke su amman su Mino da Fauzy duk a part d'in Fatuu suka ce zasu kwana, Kusan raba dare sukai suna hira gwanin nishad'i. Washe gari Lahadi suna tun bayan da akai sallar Asuba ba'a koma ba aka fara hidiman suna wannan karon ma masu aikin Abinci aka d'aukko tunda safe aka fara yanka raguna harda shanun da Ard'o ya aiko aka yanka aka kuma k'ara da kaji nan fa aka shiga soyen hanji, Misalin k'arfe goma na safe lokacin Fatuu tayi wanka tayi shigar suna ta farko da babbar atamfa da akai mata half gown da straight skirt wuyanta da hannunta tasha gold Aunty Laila tayi mata makeup da daurin kallabi mai kyau sosae tayi kyau abun sai wanda gani, lokacin yan uwansu Mom daga Ethiopia suka iso Haisam da Nameer ne da Jidderh suka je d'aukko su, mutum biyar ne suka zo da Kakarsu sai k'annen Mom guda biyu sai kuma cousin dinta da kuma d'iyar yayan su wato Jahad da Mom taso Nameer ya aura, musamman Saboda sunan Kakarsu ta baro Qatar tazo Ethiopia shine suka taho, sosae akai farinciki da zuwansu su Aunty Mareeya sai yaba kyaun k'annen su Mom suke gaba dayansu suna yanayi da Haisam haka Jahad d'in ma kyakkyawace saidai bata da tsawo sosae kuma ba ramamma bace don zata fi Mino jiki amman Mino zata fita tsawo dukda da gani ta girmi Minon ma, nan fa hidiman suna ta kankama, zuwa sallar Azahar har an gama Abincin suna Kusan kala takwas anan gidan akai wasu wasu kuma k'awar Mom aka ba kwangilar yi haka Drink ma kala hud'u akai banda uban lemuna jibgi guda sai abunda mutum ke so zai ci ya kuma sha nama kuwa gashi nan cikin abinciccikan baje baje, ana yin salla Mai jego ta canza shiga zuwa rantsattsan leshi d'an dubu d'aruruwa anyi mata riga da skirt da suka hau jikinta sosae lokacin su Mom gaba dayansu su kuma ankon tsadaddiyar atamfa sukai ita da Aunty da Laila gaba d'aya dai yan gidan kaya iri d'aya suka saka harda Hajiya da Fanan haka Dad ma dasu Haisam suma ankon shadda sukai da sauran yara mazan gidan, kowa dai yaci gayun suna Gwaggo tasha leshi haka Mino ma lace tasa Fauzy kuma fitted gown d'in atamfa ta saka iri d'aya sukai da Aunty Mareeya, kai kowa dai yasha gayu don in natsaya bayyana kayan da kowa ya saka zamu 6ata lokaci, bayan an gama cin gayun an ci Abinci photographer da aka d'aukko ya shiga aikin d'aukar hutuna, ana cikin yin hotunan jiniya ta karad'e cikin gidan su Jidderh suka nufi kopar fita daga cikin parlon gidan da gudu suna fad'in ga Momyn Nasarawa nan ta iso jin hakan har saida gaban Fauzy yay wani irin bugu Aunty Mareeya ta kalleta tana yar dariya Fauzyn ta waro mata ido, matsawa Aunty tay wurinta tace mata tazo suje su tarbo surukarta da sauri ta girgiza mata kai Aunty ta juya tana fad'in ita bari taje, hakanan Fauzy taji gabanta na wani irin fad'uwa da sauri ta juya ta nufi baya inda suka sauka, cikin Fara'a her Excellency ke amsa barka da zuwan da ake mata tasha adon dangwatsetsen leshi da gold haka yaranta ma duk sunyi shigar alfarma Aunty Mareeya na kallon fuskar Ashraf dake a d'aure a ranta ta raya wannan da gani irin Sameer ne, bayan an gama yi mata barka da zuwa aka d'unguma ciki, suna shiga cikin parlon Aunty Mareeya ta wurga ido tana kokarin hango Fauzy saidai bata ganta ba, saida suka rakata har d'akin Mom sannan suka fito tana ta godiya, part d'in su Fatuu ta nufa don ta duba Fauzyn amman bata a ciki hakan yasa ta fito ta nufi baya, d'akin da suka sauka ta nufa tana tura kopar ta hangota zaune a bakin gado tayi zuru, k'arasa shigowa Aunty Mareeya tayi ta nufeta tana fad'in "lafiya kika zo kika k'umshe anan" d'an ta6e baki Fauzyn tayi ba tare da tace komai ba, a gefenta Aunty ta zauna ta dafa Shoulder d'inta tace mata wai lafiya, a sanyaye tace mata hakanan take jin ta wani iri zuwan Mom d'in su Sameer din gani take kaman bata yi na'am da ita ba Aunty tace "to in bata yi na'am dake ba kuma ta amince mashi ya aure ki, kar ki wani damu ni ina ganin ba wani abu don da alamun bata da wata matsala" da yanayin damuwa Fauzy tace "amman Aunty tunda aka saka Ranar mu fa bamu ta6a ko magana ta waya da ita ba yanzu har wata hud'u shiyasa dama can nike tunanin kaman bata son Auren namu kawai dai k'ilan don ya nuna yana so ta amince" d'an jimm Aunty tay don tasan da zancen basu ta6a magana da ita ba ita da kanta tana tambayar ta game da hakan, yar ajiyar zuciya ta sauke "kada ki damu Fauziyya in sha Allahu ba haka bane k'ilan dai abubuwa ne sukai mata yawa shiyasa bata nemi kuyi wayar ba kinsan Manyan Mutane yadda suke uzururruka yawa suke masu balle ita kuma da take First Lady, yanzu ki tashi muje sai kiyi mata sannu da zuwa" waro ido Fauzy tayi tace taje kuma ta d'aga mata kai tace haka yakamata, sakata tayi ta canza kaya zuwa lace mai kyau riga da skirt Aunty harda yi mata yar kwalliya ta kuma yi mata d'aurin kallabi mai kyau ta feshe ta da turare, komai dai Aunty tayi mata sai gata ta fito tayi kyau sosae dama kanta a kwance yake ta faka gashinta ya fito ta k'asan d'aurin da aka yi mata bayan ta gama shirya ta tasata ta d'aukko gyale mahad'in kayan da takalma masu d'an tsini suma sun hau da kayan ta kama mata hannu suka fito, sosae gaban Fauzy keta bugawa wata irin fargaba ce ta cikata har suka iso bakin part d'in Mom nan taja ta toge Aunty tace suje mana ba gata ba tare da ita, parlon Mom d'in cike yake da Mutane yan suna suka nufi hanyar Bedroom da anan Hajiya Zainab d'in take lokacin da suka shiga cikin d'akin nan ma dai cike yake da mutane k'awayen su Mom wasu a saman gado wasu asaman doguwar kujerar dake cikin d'akin wasu kuma zaune suke a saman Carpet sun jingina da tuma tuman tuntun d'in dake ajiye saman lallausan carpet d'in, Jidderh na zaune gefen Her Excellency tana zuba mata shagwaba da yake yar gidanta ce haka ma K'annansu da suka zo daga Ethiopia suma duk suna zagaye da ita a saman gadon su Aunty Mareeya na shigowa akan idon Jidderh cikin d'aga murya tace "Ga Bride d'in Ya Sameer nan" gaba d'aya yan d'akin suka maido idonsu kan su Fauzy yadda taji tamkar ta nutse a wurin ta kasa cigaba da tafiyar tay tsaye cak a wurin idonta a k'asa jikinta har d'an rawa yake, Jidderh ce ta taso da sauri ta nufo su tana zuwa ta kamo hannun Fauzyn ta jata ciki, kusa da Hajiya Zainab ta kai ta tace "Momy ga Daughter in-law d'in ki" Fuskarta da d'an murmushi ta kalli Fauzy data sunkuyar da kai cikin muryar ta mai dad'i ta furta "She's My Daughter not inlaw" jin haka yasa Aunty Mareeya dake a tsaye gefen Fauzyn sakin murmushin dadi ita kanta Fauzyn ta d'an ji wani sanyi a ranta da k'yar ta d'ago suka had'a ido cikin d'an rawar murya ta gaishe da ita tare da yi mata an zo lafiya tana ta murmushi ta amsa mata kafin tace ma Jidderh ta bata wuri ta zauna tace to tare da mik'ewa ta kalli Fauzyn tay mata nuni da hannu tace ta zauna, d'an can gefe da ita ta zauna har lokacin idonta na a k'asa taji tace mata ya School sai lokacin ta d'ago ta k'ara kallonta da d'an murmushi tace mata Alhamdulillah ta jinjina mata kai, kallon Aunty dake tsaye Hajiya Zainab d'in tayi tace mata ko itace Sister d'inta da take wurinta da sauri Aunty tace mata eh tana murmushi ta jinjina mata kai, Kallon k'annansu yan Ethiopia tayi da yaren su tace masu ga Wadda Sameer zai Aura su gaisa duk suka d'an d'aga ma Fauzyn hannu suka ce sunyi farincikin ganinta da turanci itama tace masu haka tay masu godiya, kallon Amal k'anwar Sameer tayi tace mata ita baza su gaisa ba tayi d'an murmushi tace ma Fauzyn ina wuni itama tana murmushin ta amsa mata daga haka suka yi shiru can kuma Her Excellency ta kalli Aunty tace mata ta zauna mana tayi tsaye ko ba wuri Aunty ta fara k'ok'arin zama akan Carpet Hajiya Zainab d'in tace ya zata zauna a k'asa ta kalli Amal tace ta bata wuri da sauri Aunty tace a'a don Allah ta k'yaleta ai ba k'asa bane tunda carpet ne tayi Maganar tare da zaunawa, ko ba komai sosae taji dad'in yadda ta mutunta su a cikin ranta, Mom ce ta shigo ta nufo gaban Hajiya Zainab tana murmushi ta kalli Fauzy tace mata suna gaisawa da Daughter ne ta d'aga mata kai sai kuma tace ita wadda Nameer zai aura bata zo bane da sauri Jidderh tace tazo bari ta kirawota ta mik'e ta nufi hanyar fita, gaba d'aya Fauzy ta takura da kallon da ake bin ta dashi ba kamar Yar'uwar su Sameer wato Jahad wani irin kallon k'urulla take bin ta dashi da alama tana tantance waya fi kyau tsakanin su don tana son Sameer sosae, ba'a dad'e ba sai gasu sun dawo tare gaba d'aya Minon rud'ewa tayi bayan sun shigo ganin yadda aka bita da kallo a harhard'e ta rink'a tafiya, gaban su Mom ta kaita sam ta kasa d'agowa ta kalli kowa kanta a k'asa ta gaishe da su, Hajiya Zainab na murmushi jin yanayin voice d'inta data gaishe su tace "to Daughter yar fillo in baki d'ago ba taya zamu san juna" duk akai murmushi da k'yar Minon ta d'ago suka had'a ido da ita a d'an dabarbarce ta k'ara gaishe da ita ta amsa, kallon yan Ethiopia ta k'ara yi tace masu ga Wadda Nameer zai aura kuma duk suka d'aga mata hannu tare da ce mata itama sunyi farincikin ganinta ta amsa masu Hajiya Zainab ta kalli Mom tace mata sunyi kama sosae da matar Son Mom d'in tace mata eh daka kalle su zaka gane yan'uwa ne, bayan sun gama gaisawar Mom tace masu su zo su gaisa da mutane gaba d'aya ji sukai kamar su nutse ba yadda zasu yi Fauzy ta mik'e suka bita ta shiga cikin d'akin dasu tana nuna ma mutane su, to duk dai yabon su suke suna fad'in suna da kyau wasu su ce gasu yara dasu, bayan sun gama gaggaisawar tace masu suje su gaisa da Ummin su wato Kakar Haisam sukai hanyar fita, mik'ewa Aunty tayi tay ma Hajiya Zainab sallama har zata juya ta tafi ta dakatar da ita tace mata anjima da daddare in an gama taro tana son zasu yi magana in ba damuwa da sauri Aunty tace to Allah ya kaimu ta k'ara yi mata sallama sannan ta tafi.

Taro ya kankama Mutane sai zuwa suke suna kuma kawo abun arziki, tun Fatuu na gane yawan kayan da ake kawo mata har ta kai bata ganewa, wasu kayan daga part d'in Mom ake aikowa dasu wasu daga wurin Aunty wasu daga wurin Hajiya har daga wurin Laila wanda k'awayenta suka kawo, wasu ma yan'uwan wanda Laila zata aura sun zo suma sun kawo abun Arzik'in haka ta 6angaren Jidderh ma wasu k'awayenta da suka zo sun kawo kaya harda surukarta Maman wanda zata aura wato Matar Minister tare da k'anwar shi da kuma Yayar shi sun zo suma duk sun kawo kayan suna, haka wasu daga cikin Matan Abokan Haisam ma duk sun zo harda Saleema matar Saleem itama ya kawota da yake dama a Abujar suke zaune Sa'adiya ma k'anwar Khalid tazo tare da Mahaifiyarsu wato Hajiya Rabi'atu sosae Fatuu tayi farincikin ganinta harda sak'o khalid ya bada a kawo mata, abun Arziki dai ta ko ina Aunty Laila da Fanan suna ta kai da kawon ganin an tarbi kowa yadda yakamata sai sannu ake masu. Ana yin sallar la'asar duk suka canza shiga Fatuu ta saka shadda da tasha ubansun aiki su Mom dasu Laila gaba d'aya yan gidan suka saka lace su Fauzy ma duk suka canza shiga nan aka shiga sake yin hotuna yanzu harda su Hajiya Zainab akai, Haisam na fitowa daga Masallaci shi dasu Abbas Fanan ta kira shi ta sanar dashi Mom d'inta sun iso suna Airport yace Ok bari suje su d'aukko su, Mota biyu suka tafi da ita shida Abbas da kuma Saleem, lokacin da suka iso gidan gaba d'ayan su sunyi shiga ta Alfarma abun gwanin sha'awa ita da Farha duk tsadaddun lace ne a jikin su kowannen su na sanye da zinari sai sauran yaran ma duk suna sanye da tsadaddun kaya Fanan na ganinsu ta nufo su da gudu cike da Farinciki ta tarbe su haka ma su Mom duk sun nuna farinciki da zuwan su, tunda suka shigo falon Mino da Fauzy suka bi Farha da kallo haka ma Fatuu komai ya shiga dawo mata daya faru tsakaninsu, amsar kayan su Fanan da Laila sukai suka nufi part d'in Hajiya dasu Aunty Mareeya da bata santa ba ta tambayi Feenah wacece ta sanar mata da d'iyar Hajiya ce Mom d'in Fanan tace Ok suje su gaisa da ita, duk an gaggaisa da ita an mata sannu

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login