Showing 177001 words to 180000 words out of 512766 words
Chapter 60 - Asanadin Makwabtaka Book 3 Hausa Novel Complete
Unknown
27 Dec 2024
1648
ya k'ara tanka wa balle ya motsa still idon ta na k'asa shi kuma ya kafeta da nashi idon wata irin kunyar shi taji ta rufe ta, jin bai k'ara cewa komae ba kuma yayi tsaye yasa ta d'an d'ago ta kalle shi suka k'ara had'a ido da sauri ta juyar da face d'in ta gefe ta fara motsa baki murya na d'an rawa ta fad'i mashi zata part d'in Hajiya ne, shiru bai ce komae ba hakan yasa ta d'an juyo still kallon ta yake sai kace mai nazarin wani abu, tambayar ta yay bata lafiya ne ta d'aga ido ta kalle shi sai kuma ta girgiza mashi kai had'i da maida idon k'asa, ji tay ya k'ara cewa in bata lafiya ne su je Hospital ba tare da ta kalle shi ba a sanyaye tace mashi lafiyar ta lau k'asa k'asa ya furta Ok ya fara k'ok'arin wucewa ciki, har zata fita sai kuma ta tuna da breakfast d'in da aka kawo ta juya ta koma ciki daga gefe ta tsaya ta d'an kalle shi yana zaune kan kujera tace mashi ga breakfast can an kawo ya jinjina kai yana kallonta, ganin tayi tsaye yace taje in da zata tace zatay serving nashi ne yace no problem zai yi da kan shi ta je, kallon shi ta sake yi idon su ya k'ara had'uwa da sauri ta juya ta nufi kopa ta fita, Tana tafe tana zancen zuci gaba d'aya ta kasa gane ma wannan auren nasu, tasan ana aure ne in ana son juna to su ita ce ke sonshi shi ba son ta yake ba kawae ya aure ta ne don ya taimaka mata ba don suyi rayuwar Aure ba abun kuma turns out this way, yanzu haka zasu cigaba da yin tasu rayuwar auren? Ta jefa ma kan ta tambaya, ta so ace shima yana jin son ta ya kuma nuna mata tasan da ba k'aramar rayuwar Aure mai dad'i zasu yi ba, idanun ta ne suka ciko da k'walla daga baya suka fara zubowa, saida ta iso bakin part d'in sannan tasa gefen gyalenta ta goge Fuskar sosae sannan ta shiga, ganin ba kowa a parlon yasa ta wuce Bedroom d'in Hajiya nan ta iske ta tana bacci ta fito ta nufi Kitchen ba kowa a ciki ta juyo ta nufi d'akin Saude, ciki ta isketa tana ganinta ta washe mata baki tana fad'in har ta samu sauk'i da ta fito, a gefen Katifarta ta zauna tana murmushi tace mata ai fa dama ba sosae yake mata ciwon ba yanzu ma ta samu sauk'i ta zo ta taya ta aikin Abinci Sauden tace a'a yau dae ta huta ko ta k'ara samun sauk'i Sosae tay murmushi kawae, kwanciya tay akan Katifar Sauden don tak'i yarda ta taya ta aikin bada jimawa ba kuma bacci yay awon gaba da ita, saida akai sallar Azahar Saude tazo ta tashe ta don tayi salla, bayan ta gama sallar ta nufi Bedroom d'in Hajiya ta isketa zaune akan prayer mat tun bayan da ta gama salla bata tashi ba ta nufi gefen ta ta zauna tana gaishe da ita da murmushi ta amsa tana tambayar ina Angonta ta sanar da ita ai tun d'azun tazo ta iske tana bacci shine ta wuce d'akin Aunty Saude nan bacci ya kwashe ta, tana zaune a d'akin Hajiyar sai ga Haisam ya shigo tunda suka had'a ido ta maida kanta k'asa ya zauna a bakin gado bayan ya gaida Hajiyar suka shiga d'an yin fira jefi jefi daga baya Saude ta shigo ta sanar da ita an shirya table tace ai sai su tashi suje suci gaba d'aya tunda suna nan, Fatuu ce tay Serving d'in su bayan itama ta zuba nata ta zauna saidai kasa sakin jiki tay taci sosae sai faman Jujjuya cokali take har Hajiya ta gane ta tambaye ta ko bata son Abincin ne da sauri tace mata a'a tace to taga tak'i sakin jiki taci sosae in bata son shi tayi Magana sai a samar mata wani abun tace a'a tana so dole ta daure ta rink'a turawa, bayan sun gama Haisam ya tafi dama shi ya fara tashi su kuma suka koma Parlor suna kallo, sai bayan la'asar sannan Fatuu ta koma part d'in su tana zuwa ta wuce toilet don tayi wanka, bayan ta fito ta shirya cikin doguwar rigar Atamfa A shape ta d'an shafa powder da lip glow ta fesa turarurruka, wayarta ta d'auka ta haye gado ta fara yin Azkar bayan ta gama tay tunanin kiran Haulat don tun ranar tarewar ta rabon ta da ita, ta dai san da ita aka kawo ta amman bata san lokacin data tafi ba, sai bayan isha Haisam ya dawo yau ma harda ledar su ice cream ya kawo mata tayi mashi godiya daga baya suka wuce dining area don cin Abinci, bayan Fatuu ta gama duk abunda zata yi na shirin kwanciya ta d'aukko Al'qur'ani ta zauna a saman gado tana karantawa lokacin Haisam ya shigo shima tuni yayi shirin kwanciya, dakatawa tay da karatun ta kalle shi ba laifi ta rage jin kunyar tashi Fuskar shi a sake ya nufo gadon ya d'auki pillow yace mata "Gud night" kai ta d'aga mashi ya juya ta bishi da ido har ya fita sannan taci gaba da karatun, Washe gari ana kiran sallar Asuba ta farka, tana gama yin sallar ta wuce toilet tayo wanka, bayan ta fito ta fara shirin zuwa Makaranta, Yana kwance kan kujera idanun shi a rufe ta fito sanye da Uniform ta nufo cikin parlon, daga gefen shi ta tsaya tana kallon fuskar shi ta fara tunanin ko bacci yake yi, slowly taga ya fara bud'e idon suka sauka a kanta, gaishe da shi tayi ya jinjina mata kai cikin yar inda inda tace mashi dama Makaranta take son zuwa, kafeta yay da ido ba tare da yace komai ba hakan yasa ta maida nata k'asa, tana haka taji yace tayi breakfast ne ta girgiza mashi kai alamar a'a, shiru yay ta d'ago ta kalle shi yace to zata tafi School d'in ne ba tare da tayi breakfast d'in ba tace mashi eh,
"Dama kina yin haka?" taji ya tambaya, ta gane yana nufin dama tana zuwa Makarantar ba tare da tayi breakfast d'in ba, a hankali tace "a'a, amman in na tsaya jira zan iya makara, nasan bata san da zanje Makarantar bane yasa bata yi da wuri ba" tana Maganar ya kafeta da ido, sigh yay taji yace sai tayi breakfast zata je ta kalle shi yanayin fuskar ta ya sauya, tunawa tay da ice cream d'in daya kawo mata ko roba d'aya bata sha ba tace mashi bari tasha ice cream da cin cin to, wani kallo yay mata ya d'an yamutsa fuska yace ya zata sha abu mai sanyi da safe ta yamutsa fuska a shagwa6e tace to ai lafiya lau in ta tsaya jira sai an kawo zata makara ne fa, shiru yay kaman bazai ce komai ba can yay mata alamar ta zauna da hannu, bayan ta zauna ya yunk'ura ya mik'e tana ta kallon shi ya nufi kopa ya fita, bayan fitar shi tana zaunen idanunta suka sauka akan pillow tay tunanin ta d'auke tunda tasan shi zai kai ta School d'in kuma daga can ba lalle ya dawo nan ba, mik'ewa tay ta nufi kujerar ta kai hannu ta d'aukko filon, wani abu ta ji ya fad'o akan k'afarta ta kai idanunta k'asa don taga minene, duk'awa tay ta kai hannu ta d'aukko abun, k'aramin kwali ne wanda ya d'aukko jiya ta bishi da kallo, daga yanayin sunan dake jiki da hotunan jiki ya nuna magani ne saidae ta kasa gane maganin ko na miye daga sunan shi amman daga yanayin hoton jiki ya nuna kaman na ciwon ciki ne don wani mutum ne a jiki ya daddafe cikin shi ya d'an duk'e sai kuma daga gaba gashi nan bayan yasha maganin a kwance yanata bacci harda d'an murmushi akan fuskar shi, jujjuya kwalin ta shiga yi a ranta tana raya Ya Haisam bai lafiya ne amman bata ga alama ba wane irin ciwon ciki yake yi, ranta ne ya bata ta bud'e k'ilan akwae leaflet a ciki sai ta duba k'ilan ta gane na ko wane irin ciwon ciki ne, har zata bud'en sai kuma wata zuciyar tace mata bafa kyau yin bincike hakan yasa ta fasa sai ma ta maida pillow d'in kawae ta tura maganin a karkashi don tana tunanin anan yake ya fad'o, bata dad'e sosae ba da komawa ta zauna sai gashi ya shigo hannun shi ruk'e da d'an babban tray ta bi shi da ido har yazo ya aje akan c-table, matsar mata yay da table d'in yace gashi nan ta kalli tray d'in sai kuma ta kalle shi ya koma ya zauna, hannu ta kai ta bud'e plate d'in da aka rufe wani plate nan take k'amshi ya bugi hancin ta taga indomie ce tasha vegetables harda soyayyun cinyoyin kaza guda biyu tayi gwanin kyau a ido daga gefe kuma Cup d'in tea ne an had'a shima an rufo shi, da alamun mamaki ta d'aga ido ta kalle shi ya jingina bayan shi yana kallon ta mamaki ta shiga yi a cikin ranta na badai shi ya dafa ta ba, hannu ta kai ta d'auki fork ta fara ci sosae tay mata dad'i, kasa jurewa tay tana cikin ci ta dakata ta kalle shi yana ta latsa wayar shi,
"Amman kai ka dafa ta ne?" da k'yar ta tattaro kalmomin ta tambaye shi, shiru kaman bai ji tambayar da tayi ba har ta fidda ran zai amsa taga ya d'ago ido ya kalle ta taji yace ta tambayi Abincin mana, d'an tura mashi baki tay ta maida idon ta kan Abincin, tana cikin ci taji yace shi ya dafa akwai matsala ne, har saida ta maimaita Maganar tsabar mamaki ba wai don ya dafa matan ba sai don bata ta6a tunanin ya iya girki ba koda dafa tea ne, saida ta cinye ta duka farko ta rage yace mata wa zata bar mawa tana d'an murmushi tace shi d'an murmushi yay kawai ya gane wasa take mashi tunowa da can baya, naman ne ta rage ta kwashe kayan ta kai Kitchen, saida ta wanke komae ta d'ebi su dublan don ta kai ma su Fauzy harda ice cream ta d'aukar mata sannan ta koma Bedroom ta d'aukko jakar ta da takalma dama ta saka safa tun da tasa uniform.
Bayan sun isa ya fiddo kud'i ya bata ba tay mashi musu ba don tasan ba maidawa zai ba tayi mashi godiya ta bud'e Motar ta fita, tun kan ta shiga aji wasu da suka ganta sukai shelar zuwanta, tana zuwa bakin Class d'in su Zainab suka fito da gudu suna mata oyoyo Amaryar su suka rungume ta tana ta masu dariya, bayan sun saketa ta tambaye su Fauzy suka ce bata kai ga zuwa ba suka nufi cikin ajin suna ta tsokanar ta wai k'amshin Amarci take gashi tayi Fresh ita dai sai murmushi take kawai, bata dad'e da zuwa ba Fauzy tazo tun daga bakin Class ta hango ta ta shigo da gudu tana fad'in k'awarta Amarya tana zuwa seat d'in ta rungume ta Fatun nata dariya, zama tay sai kallon Fatun take tana sakin murmushi tace "ai banyi tunanin zaki zo yau d'in ba, nayi zaton zaki k'ara kwana biyu kaman yadda na baki shawara" d'an girgiza mata kai tay alamar a'a, "wai badai duk Amarcin bane yasa baki magana" Fauzy ta fad'a baki bud'e Fatun ta sa dariya tace mata a'a,
"Amarci dad'i, Wai kinga yadda kikai Fresh duka kwana ukku, gaskiya nima na fara jin son aure wllh" ta k'arasa tana dariya itama Fatuu dariyar take suna haka malamin su ya shigo, bayan anyi break sun fito ne Fauzy ke tambayar Fatuu wai ko wani abun na damunta ta lura da suna class kaman tana yawan yin tunani a sanyaye tace mata ba komai saidae Fauzyn bata yarda ba tace in wani abu ke damunta ta fad'i mata in na shawara ne sai ta bata barin damuwa ba zai mata magani ba har da ce mata ko bata yarda da ita bane tace mata a'a, ganin yadda duk ta damu da son jin ko wani abu na damunta yasa a sanyaye tace "ba wani abu ke damuna ba Allah Fauzy, kawai dai....na rasa gane kan Ya Haisam, gani nike bai so na kaman yadda ake hasashe kawai ya yarda yaci gaba da zama dani ne ba wai don yana sona ba" idanun ta ne suka ciko da k'walla da sauri ta fara k'ok'arin maida su, ajiyar zuciya Fauzy ta sauke duk da bata san dalilin da ya sa tace haka ba ranta ya bata wani abu, tambayar ta tay dalilin daya sa tace haka tay d'an murmushi tace mata ba komai kawae dai yak'i sake mata ne, hak'uri Fauzyn ta bata tace ita tana ganin a k'ara bashi lokaci k'ilan da dalilin hakan amman tana kokonton ace bai sonta kuma ya za6i cigaba da zama da ita to miye ribar hakan, ai indae dama ya aure ta tun farko don ya taimaka mata ne to ba dalilin da zai cigaba da zama da ita Fatun tace bata ganin ko don abunda ya faru yaga bai kyauta mata ba in ya rabu da ita yasa, Fauzy ta girgiza kai tace gaskiya bata tunanin hakan koda da hakan to akwae wani dalilin wanda kuma tana ganin so ne Fatun tay shiru kawai, Fauzy na son ta yi mata Maganar magunguna amman dalilin wannan Maganar yasa ta fasa, ana tashi Haisam yazo d'aukar ta saida Fauzy ta rakata har bakin Mota ta gaisa da shi sannan ta wuce Hostel su kuma suka tafi........
_Littafin A Sanadin Makwabtaka part 2 Naira 300 ne za'a tura ma Mutum har part 1 ga mai so zai turo kudin ta wannan Account din, 1509618776, Zainab Bature Access Bank, za'a turo shedar biya ta wad'annan nos din 09013804524 ko 08169856268
[5/8, 19:28] +234 901 700 4868: *ASM Bk2068*
~_*✊💋BOSS LADIES WRITERS💋✊*_~
*DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI*
.........Har tuntu6e take yi tsabar sauri, tana zuwa part d'in su ta shiga parlor ta wuce Bedroom, tana shiga ta maida kopa ta k'ulle harda saka Key ta juya da gudu ta nufi gado ta Fad'a sai faman numfarfashi take ta zaro ido hannuwan ta har d'an kerma suke sai tuno abunda ya faru take Fuskar Hajiya Maryam na mata gizo, tafin hannunta ta kai ta rufe baki tasa Kuka, Sosae Senator yaji Fatuu ta burge shi da Hajiya na bashi Labarin ta da Haisam Fuskar shi d'auke da Murmushi, suna nan har aka yi La'asar ya tashi don yaje Masallaci yace mata daga can zai wuce G.r.a ya d'an huta, fuskar ta da murmushi tace to ba ga d'akinta ba in ya dawo ya kwanta ya huta yana dariya yace mata to ta bari zai zo ya kwana akan gadon nata itama dariyar take ta mik'e don taje tayi sallar itama, Lokacin da ta shiga cikin d'akin nata anan ta iske Hajiya Maryam aciki pacing up and down sam ta kasa zama tun d'azu abunda take kenan, sai ta zauna sai ta mik'e ranta a tsananin 6ace, Hajiya na shigowa suka had'a ido da ita ba tare data ce mata komai ba ta nufi hanyar toilet, Alwala tayo ta fito ta nufi cikin d'akin, saida ta shimfid'a abun salla sannan ta kai idonta kan Hajiya Maryam da ta zauna a bakin gado k'afar ta d'aya akan d'aya idon ta na kallon wuri guda ta cije le6en ta na k'asa tana d'an jinjina kai, ce mata tay bata ji an kira salla bane ba tare data kalle ta ba tace taji zatayi, saida Hajiya ta fara yin Salla sannan ta mik'e ta nufi Toilet, ita ta fara tashi bayan sun gama ta cire Hijab d'in jikinta ta aje a gefen gado ta koma ta zauna kaman yadda take d'azun sai faman d'an jijjiga jiki take tsananin bacin rai kwance akan fuskar ta, bayan Hajiya ta shafa Addu'a ta juyo ta kalleta na d'an wani lokaci ta d'an girgiza kai, tasan halin ta tana da d'aukar zafi sosae sam bata 6oye fushi,
a nutse ta fara mata magana "Yanzu Maryam abunda kika aikata ma Yarinyar nan daidai ne, ita miye laifin ta a ciki ne, kusan fa ita akai ma ba daidai ba ma, an aureta bada sanin ta ba kuma sannan yazo ya hakke mata tunda ita bata san da ya aureta ba abu ya kai ga har da samun ciki yazo kuma ya 6are wanda hakan yasa ta a mawuyacin hali, in rai ya 6aci ai bai kamata hankali ya gushe ba sai a bi komai a sannu asa tunani, komai ki ka ga ya faru to dama can haka Allah ya k'addara, don haka sai mu d'auka dama Allah ya k'addaro Aure tsakanin su" Tunda Hajiyar ta fara Magana bata juyo ta kalleta ba sai da tay Maganar k'arshe sannan ta juya a zafafe tace "Pls Hajjaju stop saying that, komai sai ace kaddara, Yes an san komae sai Allah ya amince yake Faruwa amman harda sa kai, don uban shi in son taimaka mata yake ai akwae hanyoyi da yawa da zai yi hakan, Why not yayi amfani da kud'i akwai abunda basu yi bane balle kuma su da suke yan k'auye ma tuni zai sa a fasa yi mata auren in yay amfani dasu, kuma ma wai miye nashi na damuwa da wanda zata auran kowa ai da kalar k'addarar sa, watak'il in ta aure shi ya canza amman Saboda ya isa da kan shi shine yay gaban kan shi shiga isasshe ko, to zamu nuna mashi haihuwar shi akai ba a komae yake da iko da kan shi ba" tana huci ta k'arasa Maganar, d'an guntun murmushi Hajiya tay "kinga dae kenan Magana ta na kan hanya, kince kowa da kaddarar sa to suma hakan kaddarar su ce kenan shiyasa komai ya