Showing 168001 words to 171000 words out of 512766 words

Chapter 57 - Asanadin Makwabtaka Book 3 Hausa Novel Complete

Unknown   

27 Dec 2024

1639

yay ba wani da ake irin shi, ta gane wakokin yake nufi tace mashi ko an canza ba lalle ana yi ba dama nan an fi sa su, shiru yay can ya kai hannu ya d'auki remote d'in ya canza channel d'in da yake kallo farko suka cigaba da kallon American film d'in tare, gaba d'aya Fatuu ta takura don sai yin abubuwan sa kunya suke, suna cikin kallon aka nuno jarumin Film d'in da budurwar shi suna romancing juna ji Fatuu tay kaman ta nutse a wurin don abun bana Arziki bane, can abun ya kai ga an sa6ule rigar budurwar har boobs d'inta sun bayyana Fatuu na ganin hakan ta mik'e zumbur ta nufi hanyar corridor without even looking at him ya bi bayanta da kallo shi sai ma ta so bashi dariya yadda tayi, tana shiga Bedroom d'in ta nufi gado ta zauna a baki ta d'an waro ido tay shiru kaman mai tunanin wani abu, a hankali ta kwanta ta takure a guri guda tana cigaba da tunanin da take yi, bata dad'e da kwanciyar ba aka kira sallar la'asar, har tayo Alwala ta zo ta kabbara sallar bai shigo ba, bayan ta gama zaune tay kan abun sallar ta jingina da gado tana haka taji wayar ta na ringing ta mik'e ta nufi bedside drawer inda wayar take ajiye, d'an jimm tay ganin shine ke kiran kafin ta d'auka a hankali tayi sallama amsa mata yay yace mata ya je ya dawo ta yi mashi adawo lpy, tambayar ta yay akwae abunda take so tace mashi a'a daga haka yay cutting kiran, bin wayar tay da kallo bayan ta cire ta daga kunnan ta a ranta ta shiga raya shi d'in ba dai kula ba duk zai fita sai ya tambayi ko tana son wani abu, d'an murmushi tay tana jin k'aunar shi na k'ara ninkuwa a cikin ranta, tunanin tafiya part d'in Hajiya tay ta taya Saude girkin dare tunda ko ta zauna ba abunda zata yi ta mik'e, bayan ta d'aukko gyale da takalma ta k'ara gyara fuskar ta a gaban mirror sannan ta tafi, saida ta tsaya Kitchen ta d'aukko wasu daga cikin kayan da aka kawo masu Abinci don ta maida sannan ta tafi, tare sukai aikin Abincin daren kaman da rana a nan tayi sallar Magrib da isha'i sannan ta baro part d'in tare da Abincin su ta dawo part d'in su har lokacin Haisam d'in bai dawo ba, bayan ta aje kayan Abincin kan table ta wuce Bedroom, har ta zauna bakin gado zata fara latsa wayar ta Zuciyar ta ta ayyana mata yakamata tayi wanka ta mik'e bayan ta aje wayar ta nufi gaban dressing mirror ta cire jewellery d'in jikinta ta maida komai ma'ajiyar shi sannan ta wuce laundry room, after some minutes ta fito sanye da bathrobe kanta ba kallabi sai short towel tana goge fuskar ta da gefen gashin ta, gaban dressing mirror ta tsaya ta shafa mai da su humra bayan ta gama ta wuce wurin kayanta a ranta ta ayyana yakamata ta jera kayan a cikin closet ta yanke gobe tunda ba Makaranta zata je ba tayi hakan, ruwan idon kayan da zata sa ta shiga yi daga k'arshe ta yanke ta saka sleeping dress kawai tunda dare ne kwanciya zatayi ta bud'e jakar da suke ta fiddo wasu riga da wando silk cikin wanda aka kai mata rigar gajeran hannu gare ta ta d'an saukko zata kai cinyoyin ta, gefen gado ta koma ta fara saka su ba tare da ta d'aukko undies ba tunda dare ne, gaban mirror ta koma ta k'ara gyara parking d'in gashinta, bayan ta gama ta maida su bathrobe d'in ta d'aukko phone d'inta ta haye gado ta fara latsa ta, bata dad'e da hawa ba taji an turo kopar da sauri ta kai idonta suka had'a ido dashi ya shigo da yar sallama tana d'an murmushi ta amsa mashi, a gaban gadon ya tsaya tayi mashi sannu da zuwa ya d'aga mata kai, mik'a mata ledar daya shigo da ita yay ta matso ta amsa tana kallon shi kafin ta maida kallon kan ledar shi kuma ya nufi gaban mirror ya fara cire Wrist watch d'in shi, bud'e ledar tay ta lek'a sai kuma ta kai hannu ta fara fiddo abubuwan dake ciki nan taga Pop corn ne da tuwan Madara harda gullisuwa sai Chocolates manya manya with surprise written on her face ta d'ago tana kallon shi don bata tsammaci ganin su ba tunda bata ce mashi tana so ba, hanyar laudary room ya nufa ba tare da ya kalle ta ba da d'an d'aga murya tace "Thank u so much, Allah ya k'ara bud'i na Alkhairi" d'an juyowa yay ya kalleta fuskar shi a sake ba tare da ya ce komae ba ya juya yaci gaba da tafiya har ya shige, tana ta sakin murmushi da alama taji dad'in kawo mata su da yay ta bud'e ledar tuwon madara ta fara sha nan take wani dad'i ya ratsa ta harda lumshe ido lokaci guda zuciyar ta ta tariyo mata can baya irin su ne kyauta ta farko da ya fara mata da hannun shi ta dingi zuba mashi santi harda bashi labarin irin Pop corn d'in da ake kawo masu a Makaranta duk tsakuwowi da gishiri don an raina masu wayau, tunowa da lokacin yasa tay ta dariya can tay tunanin yakamata ta bashi wuri tasan wanka yake in ya fito ya shirya ta saukko daga kan gadon ruk'e da ledar ta nufi hanyar fita, tana zaune a parlor tana cigaba da cin abubuwan ta tana yi tana kallon sabon shirin dad'in kowa ya fito shima ya shirya cikin sleeping dress riga da wando tun kafin ya k'arasa shigowa k'amshin shi ya karad'e parlon, tana ganin shi ta mik'e da hannu tay mashi alama da Dining area ya nufi can ta bi bayan shi, ba wani Abinci sosae yaci ba ya dawo cikin parlon, bayan ta gama ta gyare wurin ta had'o mashi Fruit salad, a kan c-table ta d'aura mashi tace gashi nan ya sha ya furta mata thanks tay d'an murmushi ta koma inda ta taso ta zauna taci gaba da kallon ta, bayan an gama ta juyo suka had'a ido lokacin har ya gama sha tay mashi d'an murmushi taji yace zasu iya yin Assignment d'in yanzu tace eh, bud'e Computer d'in yay dama tana nan ba'a d'auke ba ya fara operating nata tana ta kallon shi can taga yay mata alamar tazo da hannun shi ba tare daya d'ago ba ta mik'e ta nufe shi, a gefen shi ta ja ta tsaya ya k'ara mata alamar ta zauna a kusa da shi still bai kalleta ba, a d'arare kaman mai jin tsoro ta raku6a gefen nashi ta zauna ya shiga nuna mata yadda zatai, tun dai bata saki jiki ba har ta washe suka cigaba da yi har ta kai ya kama hannunta yana koya mata yadda zata d'aukko zanen, tuni jikin su ya had'e da na juna gaba d'aya sun cika juna da fitinannan k'amshi, ba'a d'au wani dogon lokaci ba suka gama har an tura ma malamin tana ta murmushin jin dad'i ta hau yi mashi godiya, d'an murmushi kawae yake ba tare daya ce komai ba ta mik'e ta kai hannu ta d'auki book d'in tana shirin juyawa ta tafi kwatsam tay tuntu6e da kafar shi ta tafi gaba d'aya zata kifa aikuwa cikin zafin nama ya jawo ta tayo baya ta fad'o jikin shi gaba d'aya, tsit kake ji Wutar Fatuu ta d'auke don ba k'aramar razana tayi ba gaba d'aya ta runtse idanunta gam jikinta sai d'an rawa yake tana fitar da numfashi da sauri da sauri, still yay yana bin fuskar ta da kallo ya kasa cewa wani abu idanunta sai rawa suke, bayan wani lokaci natsuwar ta ta daidai ta a hankali ta fara bud'e idanun ta, bayan ta ware su gaba d'aya suka sauka akan face d'in shi dake gab da ta ta, sam kowa ya kasa yin kwakkwaran motsi sunyi tsit gazing in to each other's eye and inhaling each other's sweet scent, Fatuu ce tay k'arfin halin ce mashi ta gode da taimaka da yay ta fara k'ok'arin d'agowa sai dae ta kasa don ya ruk'e ta tightly, slowly ya d'ago da fuskar ta ta yadda saura kad'an su had'e Fatuu na ganin haka da sauri ta runtse idonta breathing d'in su ya fara had'uwa zuciyarta ta fara beating da sauri da sauri, numfashin ta ne ya nemi tsayawa jin ya had'e bakunan su.........



_Littafin A Sanadin Makwabtaka part 2 Naira 300 ne za'a tura ma Mutum har part 1 ga mai so zai turo kudin ta wannan Account din, 1509618776, Zainab Bature Access Bank, za'a turo shedar biya ta wad'annan nos din 09013804524 ko 08169856268
[5/8, 19:28] +234 901 700 4868: *ASM Bk2066*

_Destiny may be delayed but cannot be changed...._


*DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI*


.........Tun bayan data shiga ta gaishe da shi ya amsa bata k'ara ce mashi komai ba ta juyar da kanta tana kallon gefen hanya, lokacin da suka iso Unguwar suna zuwa gab da gidan su ta juya ta kalle shi yana kallonta ta mirror ta d'an cije baki had'i da d'an yamutsa fuska, dage mata gira yay ba tare da ya kalleta ba yace "What?" A marairaice tace mashi don Allah ya bari ta shiga gida ta gaida gwaggo idon ta akan shi taga ya d'an girgiza kai alamar a'a, 6ata rai tayi idanunta sukai rau rau tana ta d'an kikkafta su bata yi tunanin zai k'i barin ta ta shiga ba, suna shiga kwanar gate tace mashi ya aje ta anan ta shiga ta k'aramar kopa ya parker ba tare da ya ce komai ba, saida ta juya zata bud'e kopar taji voice d'in shi yace ta bari wani time zata je yanzu in taje za'ai mata fad'a ne, juyowa tay ta kalle shi fuskarta a d'an kwa6e ya bud'a mata ido alamar taji ta jinjina mashi kai sannan ta juya ta bud'e, bayan ta fita yaja Motar ya tunkari gate ita kuma ta shige, tana isa part d'in a bakin kopar parlor ta cire takalmanta kafin ta wuce ciki, tana shiga Bedroom tay sensing k'amshin Haisam a ranta ta raya ko ya shigo d'akin ne, wata zuciyar ta ce k'ilan wanka yazo yayi, wucewa tayi ciki ta aje jakar ta ta cire Hijab sannan ta dawo wurin gado ta fad'a alamar ta kwaso gajiya, tana kwanciya taji k'amshin ya cika mata hanci fiye da yadda taji shi da ta shigo, hancinta ta kai jikin zanen gadon ta shinshina nan ta tabbatar da k'amshin shi ne ke tashi a jikin zanen sosae, cigaba da bin jikin zanen tai tana sunsunawa kafin ta d'ago mamaki shimfid'e akan fuskar ta, tambayar kanta ta shiga yi mi zai kawo k'amshin shi haka a wurin in dae ba kwanciya yay ba wata zuciyar ta bata kwanciyar yayi kenan, jikinta ne yay sanyi tay shiru a ranta tana raya kenan had'a gado da ita ne bai son yi, sosae abun ya dame ta don har Fuskar ta ta bayyana, ta d'an d'auki lokaci haka can ta tuna da bata yi salla ba ta saukko jiki sa6ule ta wuce laundry room, Alwala tayo tazo ta kabbara salla har ta gama bai shigo ba ta wuce Toilet don tayi wanka, bayan ta fito shiryawa tay cikin sabuwar doguwar rigar Atamfa tana tsaye a gaban mirror tana d'an yin light make up yayin da a ranta take ta juya kwanciyar da yayi akan gadon tana haka ya turo k'opar ya shigo suka had'a ido ta cikin mirror d'in, ganin yayi tsaye yana ta kallon ta ba tare daya ce komai ba yasa ta juyo ta kalle shi lokacin yace mata ga Abinci can an kawo ta fito ta ci ta d'aga mashi kai daga haka ya juya ya fita ta bi shi da ido, Bayan sun gama cin Abincin ta gyara wurin ta wanke komai a ranta ta yanke tafiya part d'in Hajiya don ta bashi wuri k'ilan ya k'ara kwanciya kan gadon in zai yi bacci, tana can har yamma suka fara aikin girkin dare da Saude, suna cikin yin girkin ne ta tambayi Sauden akan yau da safe ita ta dafa mata indomie, yar dariya tayi don ta d'ago dalilin yin tambayar tata tace mata ba ita ta dafa ba wanda ya kai mata shi ya dafa, ganin Fatun tayi d'an jimm yasa tace mata tayi mamaki ko ta d'aga mata kai tace "nima sosae nai mamaki lokacin dana fito na gan shi a cikin Kitchen yana dahuwar, na kuma rud'e don abu ne da ban ta6a gani ba, ni tunda nike da shi ban ta6a ganin yazo ko bakin Kitchen d'in nan ba balle ta kai shi da yin girki, bamma yi tunanin ko ruwan zafi ya iya dafawa ba sai gashi da yin girki kuma da ga ji Abincin yayi dadi don baki ji yadda k'amshi ya cika wurin Kitchen d'in ba" Murmushi kawae Fatuu ke yi a cikin ranta tana raya a haka kai kace Saboda yana son ta ne yayi amman kawai kulawa ce, ji tay Sauden ta k'ara cewa "ni bansan zaki Makarantar bane ai da nayi maki Breakfast din da wuri, saida ma nace ya bari in yi amma yace in bar shi kawae dai in rink'a tashi da wuri ina maki" shiru Fatuu tay still da murmushi akan fuskar ta Saude ta shiga tsokanar ta tana fad'in ai daga yau da tayi sallar Asuba bazata koma ba kar tayi ma Ango laifi kan Amaryar shi, sai bayan da tayi sallar isha'i ta koma part d'in su tare da Abincin nasu, lokacin da suka yi shirin kwanciya tana zaune akan gado tana yin rubutu ya shigo tana ganin shi ta san mi ya shigo yi da kanta ta d'auki pillow d'in ta mik'a mashi ya amsa Fuskar shi a sake ya furta mata thanks da kuma Gud night ya juya tabi shi da kallo ta d'an kwa6e fuska.

Ranar Laraba bayan ya d'aukko ta daga Makaranta sun gama cin Abinci ta gyara wurin, tana cikin Bedroom ya turo kopa ya shigo tana zaune a bakin gado ta juya ta kalle shi, daga bakin gadon ya tsaya Fuskar shi a sake itama da murmushi take kallon shi ya d'an d'auki lokaci ta fahimci kaman wani abu yake son cewa amman kuma yayi shiru, tambayar shi tay ko akwai abunda zata yi ya girgiza mata kai slowly taji yace in tana so taje gida yanzu da daddare zai zo ya d'aukko ta, waro ido tay baki bud'e take kallon shi ta kasa ce mashi komai don Maganar tazo mata a bazata, ganin yadda tayi yasa shi d'an d'age mata gira yace ko bata son zuwa ne aikuwa da sauri ta mik'e tana girgiza mashi kai had'i da yin murmushi ta hau yi mashi godiya farinciki bayyane akan fuskar ta ta nufi wurin wardrobe don ta shirya ya bita da ido, ba 6ata lokaci ta gama shiryawa da wata rantsattsar sabuwar shadda a cikin kayan da aka kawo mata ta ca6a ado ta fito a Amaryar ta sak sai k'amshi take bazawa, lokacin da ta fito yana zaune akan kujera yana lallatsa Computer ya d'ago ido yana kallon ta har ta k'araso ta tsaya daga gefen shi tana ta murmushi shima murmushin ya mayar mata tace mashi ta tafi ya d'aga mata kai ta juya, har ta fice idon shi na akan kopar sai bayan wani lokaci ya janye idon ya maido shi kan abunda yake, tana tafiya tana faman sakin murmushi sai kace wadda ta shekara bata je gidan ba, lokacin da ta iso kopar gidan shagon Kawu Amadu a kulle yake dama tunda suka wuce da aka d'aukko ta daga Makaranta taga shagon a kulle, a ranta ta raya k'ilan yana Makaranta daga haka ta shige cikin gidan, daga bakin k'opa ta tsaya tsakar gidan wayam ba kowa tana murmushi ta kwad'a sallama ba'a amsa ba saida ta k'ara d'aga murya tayi wata sallamar sannan ta jiyo Muryar gwaggo ta amsa, d'an lek'o da kanta tayi don taga waye nan tay arba da Fatuu dake tsaye tana mata murmushi, hannu gwaggo ta kai ta rufe baki sai kuma ta janye kan ta koma ciki bada jimawa ba sai gata ta fito hannun ta ruk'e da tsintsiya ta d'agata alamar bugun Fatun zatayi ita kuwa mi zatay in ba dariya ba ta nufe ta da gudu suna had'e wa ta k'ank'ame ta gaba d'aya harda tsintsiyar, dariya itama gwaggon tasa tana fad'in waya fito da ita Fatun tace Ya Haisam din ne ai yace tazo ko, d'aki suka nufa Fatun tay ma gwaggon side hug, bayan sun shiga a bakin gado suka zauna idon su a cikin na juna sai faman dariya suke ma juna, sosae gwaggo taji dad'in yadda ta ganta duk da Fuskar ta ta d'an fad'a amman wannan dama tun kafin ta tare ne Saboda ciwon laulayin da tayi amman ta k'ara haske fuskar ta sai sheki take fatar nan tayi lukui ko d'igon k'urji babu, Fatuu ce ta katse shirun ta gaishe da ita bayan ta amsa ta tambayi suna lafiya tace mata eh,

"Amman ya akai kika fito haka da wuri, bana ce banson ki rink'a zaryar zuwa ba miyasa wani lokacin baki jin magana" tay Maganar ta d'an d'aure fuska, a shagwa6e tace "Wllh shine fa yace in zo..." tunkan ta rufe baki ta katseta "to tunda kin matsa ba dole yace ki zo ba" da sauri ta ce mata wllh bata matsa mashi ba nan ta kwashe yadda akai ta fadi mata gwaggon ta gyad'a kai alamar ta yarda, tambayar ta tayi Kawu Amadu tace bai dawo ba yana Makaranta tace dama saida tayi tunanin haka, hira suka shiga yi kai kace sun dad'e da rabuwa, suna cikin yin Hiran Fatuu ke mata Maganar kud'in da suke a cikin Account d'in ta tace ana ta ajiyar su zata turo mata tayi wani abun dasu, gwaggon na yar dariya

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login