Showing 207001 words to 210000 words out of 512766 words

Chapter 70 - Asanadin Makwabtaka Book 3 Hausa Novel Complete

Unknown   

27 Dec 2024

1664

man ba face Ya Haisam, duk abunda ake man Saboda shi ne kuma shi bai damu dani ba ya tafi ya barni Saboda bai sona, na tabbatar da yana sona ba yadda za'ai ya tafi tsawon wata guda da rabi ba tare da ya waiwaye ni ba tunda yana da halin ko duk sati yaso zuwa nan hakan ba wani abu bane a wurin shi, ni na rasa gane kan wannan Auren namu da yasan haka zai man da tun farko bai amince yaci gaba da zama dani ba, in don abunda ya faru ne naje na bashi hakuri kuma yace ya hak'ura to miyasa ya canza man, miyasa bai damu dani ba...., miyasa son shi yak'i barina kwata kwata, miyasa nike tunanin shi tunda shi bai damu dani ba....miyasa ba zai sake ni ba kawai in San ban tare dashi ko na cire shi daga cikin zuciya ta....." tana Maganar k'walla na zubo mata har tazo ga6ar da ta saki kukan mai cin rai ta fad'a jikin Fauzy da itama kwallan ne suka fara zubo mata, wani irin tausayin ta da bata ta6a ji ba ya kamata ta shiga d'an bubbuga bayanta tana rarrashin ta, ita kanta ta fara kokonton anya Ya Haisam na son Zarah kaman yadda suke hasashe kuwa, zuciyar ta ce ta fara raya mata aikata wani abu......

Kafin a tashi tace ma Fauzy zata rink'a bin ta Hostel sai yamma ta koma gidan don gaba d'aya bata jin dad'in gidan tace to Hajiya fa ba matsala taga bata komawa da wuri tace zata fad'i mata suna tsayawa karatun jarabawa ne tasan zata fahimta tace to, kiran Tk tayi ta sanar dashi kada yazo d'aukar ta ya d'aukko Mino kawai ita sai yamma zata dawo kuma ba sai yayi wahalar zuwa d'aukarta ba zata hau Keke Napep, bayan an tashi suka nufi Hostel, suna zuwa salla suka fara yi bayan sun gama Fauzy ta had'a mata Madara da biscuit tace ta fara sha bari ta dafa masu Abinci, tana gama sha lokacin Fauzy na cikin dafa masu Abincin ta mik'e tace bari taje ta watso ruwa har Fauzy nace mata zata iya shiga toilet d'in su kuwa tana yar dariya tace mi zai hana, cire kayanta tayi ta d'aura towel Fauzy ta kalleta tace mata wllh duk tayi d'an wuya tay murmushi kawai, bayan fitar ta Fauzy ta mik'e ta nufi inda ta tashi ta zauna ta kai hannu ta d'auki wayarta, zurfin tunanin anya Ya kamata tayi abunda take tunanin yi kuwa ta shiga, fargaba ce tay mata yawa ta maida wayar ta aje ta bar wurin, bayan Fatun ta fito tace ma Fauzy ta bata yar riga mara nauyi tasha iska kafin ta tashi tafiya ta d'aukko mata, bayan ta gama saka rigar hayewa tay saman gado ta kwanta suna d'an yin hira da Fauzy, a hankali ta fara lumshe ido Fauzy na fad'in kada tayi bacci bata ci Abincin ba tace ai ba yunwa take ji ba in ma tayi sai ta ci in ta tashi, baccin ne ya dauketa Fauzy ta zuba mata ido tana ta wasi wasin abunda take son yi acikin zuciyar ta can ta mik'e ta nufi gadon da take ta kai hannu ta d'aukko wayarta ta dawo ta haye saman gadon zuciyarta nata harbawa hannuwanta har d'an kerma suke ta shiga daddana ta......."

____________________

Fanan zaune asaman doguwar kujerar dake a cikin parlon su ta haye saman ta gaba d'aya tana sanye da yar fingilar riga da iyakarta tsakiyar cinyoyinta hannun ta kuma irin na vest kaman dai rigar bacci ce ta d'an rankwafa tana lallatsa computer d'in dake gabanta hakan yaba brown gashin ta damar zubowa ta gefe da gefen fuskar ta, daga gefen ta kuma takardu ne lokacin su can dare ne don har anyi sallar isha, tun bayan da Haisam ya aje wayar shi ya tafi had'o masu Coffee take ta damun ta da k'arar notifications, dakatawa tay ta kai hannu ta d'aukko wayar don ta kashe Wi-fi d'in wayar ko sakonnin sun daina shigowa, tana latsa power haske ya kawo jikin Screen d'in idon ta ya sauka akan sunan da tasan ya saka ma Fatuu alamar ta turo mashi sako, d'an murmushi Fanan d'in tayi a ranta ta raya wato da ita ne ta daina zumunci kenan, bayan ta kashe ta maida wayar ta aje, har taci gaba da abunda take kawai taji tana son ganin sak'on miye Zarah ta turo mashi, hannu ta kai ta d'aukko wayar ta sake kunna hasken ta bud'e, kan sakonnin WhatsApp ta danna ta shiga ciki, sak'on Fatuu ne last da aka turo hakan yasa ya kasance a sama ta kai hannu ta ta6a ya bud'e, gyara zama tayi ta fara Karantawa...................




_Littafin A Sanadin Makwabtaka part 2 Naira 300 ne za'a tura ma Mutum har part 1 ga mai so zai turo kudin ta wannan Account din, 1509618776, Zainab Bature Access Bank, za'a turo shedar biya ta wad'annan nos din 09013804524 ko 08169856268
[5/8, 19:29] +234 901 700 4868: *ASM 072*


~_*✊💋BOSS LADIES WRITERS💋✊*_~



*DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI*



.......Ranar Laraba bayan su Fatuu sun tashi Mino ta tafi ta kwashe kayan shimfid'ar da tayi masu don yanzu da tsiya sun koma kwanan Falo don duk dare nan Farha ke zuwa ta kwana kuma duk abun nan Hajiya bata sani ba don ita a tunanin ta a d'akin da ta sauka take kwana dama bari take sai ta tabbatar Hajiya tayi bacci sannan ta taho, haka take ta faman yi masu cin kashi iri iri Harda ce ma Fatuu mayya ta lik'e tak'i tafiya gidan su, ita dae duk abunda zata mata bata biye ta, bayan ta maida kayan Farhar na kwance kan gado tana bacci, toilet ta wuce don tayi wanka, lokacin data fito cikin sauri ta fara shiryawa don yau test biyu gare su d'aya da safen nan za'ai masu d'ayar kuma sai After break so take taje da wuri don su k'ara yin karatu, bayan ta gama shiryawa ko tunanin tsayawa yin breakfast bata yi ba ta d'auki jakarta ta nufi k'opa zata fita, tana kama handle taji Muryar Farha tana mata magana hakan yasa ta dakata ta juya, tana kwance saman gadon ta d'an d'ago da kai tace mata wai taje tayi mata Breakfast, wani kallo Fatuu ta bita dashi kafin tace mata ai a part d'in Hajiya ake yi don haka taje can taci, yar tsawa ta kwatsa mata tace ita zata bata Umarni ta k'i yi mata to miye amfaninta dama in ba hakan ba miji bai son ta ya tafi ya barta yana can wurin wadda yake so suna shan soyayya amman ita da yake mayya ce ta lik'e to yau anan take son yin breakfast d'in, sosae Maganar ta daki zuciyar Fatuu har idanun ta sun fara tara k'walla amman sai tayi saurin maida su tace mata Aunty Saude zata kawo nata sai taci a fusace tace bazata ci shi ba ita take so ta dafa mata, d'an jimm Fatuu tayi sai kuma ta d'ago hannu ta duba agogon hannunta ganin da d'an sauran lokaci yasa ta juyo ta aje jakarta ta fita, bada jimawa ba ta dafo mata indomie ta kawo mata har lokacin tana a kwance, a saman bedside drawer ta aje mata tace gashi nan, tasowa Farhar tayi har Fatuu zata juya ta tsaidata ta juya tana yatsina tace mata ba ita take so ba Chips zata had'o mata, wani kallo Fatuu ta bita da shi kafin tace mata gaskiya bata da lokacin yi mata wannan School zata tafi tana da test kuma lokaci ya k'ure, tana gama fad'in hakan ta juya Farhar na mata magana cikin tsawa tay banza da ita ta tafi,

Saida suka hau hanya bayan sun d'auki Mino ta kira Aunty Saude tace mata ta wuce ba sai ta kawo mata breakfast ba, tace da wuri haka ta sanar mata test gareta ne, har suka isa Makarantar tana ta tunanin irin wulakancin da Farha ke mata. Ana gab da tashi ta kira Tk tace mashi yau ya zo ya d'auketa lokacin tashi Fauzy tace mata yau bazata tsaya ba kenan tace mata eh akwae abunda zatayi sai dae gobe. Bayan ta koma gida tana shiga cikin parlon wani irin k'amshi ya bugi hancin ta, da mamaki ta shiga bin parlon da kallo tana son gane k'amshin na minene don yayi yawa kuma tasan ba haka ta bar parlon ba, hanyar corridor ta nufa tana zuwa saitin inda su Tv suke kaman ance ta waiga taga kwalaben turaren wutar ta dake jere a wurin gaba d'aya zube a k'asa sun yi kwatsa kwatsa turaren barbaje a koina, da Al'ajabi take bin su da kallo aranta ta shiga mamakin yadda akai sukai haka, ranta ne ya bata ko Farha ce tayi masu haka, da sauri ta juya ta nufi Bedroom tana tura kopar nan ma k'amshin ne ya dakar mata hanci tay tsaye tana bin kwalaben humra d'inta dake watse a k'asa da kallo gaba d'aya an fasa su harda su turaren fesawarta ga kayanta na cikin Wardrobe duk an watso su wardrobe d'in a bud'e, kai idonta tayi akan gado nan ma indomie d'in data dafo mata ce a warwatse ko ina, tsaye Fatuu tay ta kasa yin wani kwakkwaran motsi idanunta cike da k'walla take bin bedroom d'in da kallo, da k'yar taja k'afa ta idasa shiga ciki ta nufi bakin gado ta zauna a inda ba indomie d'in, kifa Fuskarta tayi cikin tafin hannunta ta fashe da kuka, tana cikin kukan ta tuno da Kitchen ta mik'e da sauri ta nufi k'opa ta bud'e, tana tura kopar kitchen d'in taja ta tsaya idanu waje take kallon cikin shi gaba d'aya duk wani abun fashewa ta fasa shi kayan Abinci ma bata k'yale su ba duka ta barbaza su harda mai duk ta zuzzubar dashi a k'asa wasu daga cikin Warmers d'in ta ma bata k'yale su ba saida tasa ta6arya ta faffasa su sosae tayi mata Asara abun ba kyan gani, wani irin 6aci ran Fatuu Yay tama kasa cigaba da yin kukan sai huci take, tana tsaye a wurin Aunty Saude ta shigo kawo mata Abinci, a kan c-table ta d'aura kayan Abincin ta nufi Bedroom a ranta tana Maganar k'amshin da take ji tayi tunanin ko turare ne ya 6are, tana shiga corridor d'in taga Fatun tsaye ta bata baya ta isa wurinta tana fad'in "Fateema an dawo yau da wuri kenan, Tk ne ya shiga d'aukar Abinci yake fad'a man kin dawo ai" jin shiru bata ce komai ba kuma bata juyo ba yasa Sauden kai hannu ta ta6o ta still bata juyo ba, matsawa tay tana fad'in Fateema lafiya mi kike kallo haka itama ta kallo cikin Kitchen d'in ba arziki ta bud'a baki tace garin Yaya haka ta faru ya akai kayan sukai haka, sai lokacin Fatuu ta juyo ta fad'a jikinta ta fashe da kuka, tambayar abunda ya Faru Sauden tay ta d'ago cikin kuka ta fara bata labari, Bedroom d'in Saude ta nufa ta shiga taga yadda shima tay mashi ta kai hannu ta ruk'e ha6a ta shiga jinjina kai, fitowa tay tazo taga na parlon ma sosae itama ranta ya 6aci don ba k'aramar asara tayi ma Fatun ba, juyowa Saude tay ta koma cikin Corridor inda Fatuu ke tsaye bakin Kitchen rai 6ace tace "Yanzu ke Fateema kin za6i ki zuba mata ido tay ta maki wannan cin kashin, nace in sanar ma Hajiya kin hana gaskiya to yanzu an zo ga6ar da dole ma in sanar mata" girgiza kai Fatuu tayi cikin kuka tace "Don Allah Aunty Saude kar ki sanar mata hakan ba k'aramar matsala zai Haifar ba...."Katseta Saude tay tace "to wai ita Mahaifiyar tasu ta isa tayi maki abunda Allah bai nufa akan ki bane" girgiza kai Fatuu ta k'ara yi "a'a Aunty Saude, nidai ki kyaleta kawai banso in shiga tsakanin su tayi ta gama ta tafi",

Shiru Saude tayi tana kallon ta can tace "Shikenan indai kina son kada na fad'i mata sai kinyi abu guda in ba haka ba gaskiya bazan zuba ido ina ganin tana maki wannan iskancin ba" ce mata tay to mi zata yin,

"so nike kiyi maganinta ta daina maki wannan wulakancin, kinsan irin haka saika had'a jiki da mutum yaji a jikin shi sannan yake kiyayar ka, nasan ba fin k'arfin ki tay ba wllh kawae jikin ne ba abunda zata iya maki don haka ki dawo Fateemar ki ta da ki sameta ki lakad'a mata dukan tsiya wllh zaki ga ta shafa maki lafiya" baki adan bud'e Fatun ke kallon ta jin kalaman sak irin na Fauzy, bayan ta gama tace mata tana ganin ba matsala ita bata son Hajiya ta sani,

"Ba wata matsala, ai anan part d'in in tazo zaki mata hakan kuma tunda tasan ita ke bata da gaskiya bazata bari a ji ba tunda dama duk abunda take maki a 6oye take yi bata son Hajiya ta sani, shiru Fatuu tay tana nazarin Maganar, Sauden tace zata yi ko kuwa taje ta fad'i ma Hajiyar, kallonta tayi ta jinjina mata kai alamar zata yi tace to tazo taci Abincin ta k'ara samun k'arfin yin maganin mara mutunci ta kamo hannunta suka nufo cikin parlon duk fargaba ta cika Fatun don rabon data yi fad'a da wani har ta manta, da kanta ta zuba mata Abincin bayan ta cire Hijab d'inta ta aje a gefe ta fara ci, har saida taga taci ta k'oshi sannan ta bar part d'in bayan ta jaddada mata abunda take son tayi ma Farhar,

Saude na fitowa cikin harabar ta hango Farhar ta fito ta baya ta nufo part d'in suna had'a ido ta wurga mata uwar harara ta kauda idon ta, Sauden tay d'an murmushin yau zaki gane kuran ki, bayan Fatun ta gama toilet ta je tayo Alwala ta dawo parlon don tayi sallar anan da niyyar inta gama sai ta fara gyara inda ya 6aci, tana kokarin sanya hijab taji an turo kopar ta kai idon ta da sauri, cikin isa kaman yadda ta saba ta nufo cikin parlon tana yatsina, a gaban Fatun ta tsaya hakan yasa Fatuu dakatawa da saka hijab d'in ta bita da ido gabanta nata fad'uwa kan abunda aka ce tayi matan, ce mata tayi tana fatan taga sakamakon k'in yi mata abunda ta sakata don haka gobe ma in ta k'ara sata abu tak'i yi zata ga abunda yafi wannan kuma tunda dai ita mayyace ta lik'e bada jimawa ba zatayi maganin ta gaba d'aya, tana rufe baki ta tsitta ma Fatun miyau a fuska aikuwa hakan ba K'aramin fusatar da ita yay ba duk da fargabar da take ciki a fusace ta kai hannu ta wanka mata mari ji kake Tasss! a gigice Farha ta kai hannu ta dafe kuncinta ido waje take kallon Fatuu data d'aure Fuska tana huci, nuna kanta tayi da yatsa tace ita ta mara a fusace Fatun tace eh taje ta mara aikuwa itama ta d'aga hannu zata sharara mata Mari da sauri Fatuu ta goce kafin Farha tay wani yunkurin ta shammaceta ta turata sai gata ta fad'a saman kujera tumm da alama k'ibar biredi ce dama, kan ta yunk'ura ta taso Fatuu ta haye samanta ta fara dukanta ba ji ba gani ta shiga sauke fushin duk wani bakin ciki data cusa mata dama kuma ita a yadda ta taso bata iya fad'an cacar baki ba tafi gane ta kai bugu kawai...........

Saude na shiga parlor ta nufi Hajiya dake Zaune akan Kujera tana kallo, tana zuwa da alamun rud'ewa tace mata ga Farha can a part d'in Fateema suna fad'a tayi tayi ta raba su sun k'i rabuwa, ba shiri Hajiya ta mik'e ta d'auki sandar ta tace suje, suna kan hanya Hajiya nata faman dogara sandar tana yin sauri da alamun mamaki take tambayar abunda ya had'a su Sauden ta shiga fad'i mata asarar da tayi ma Fatun wani irin bacin rai ne ya bayyana akan fuskar ta, Har lokacin su Fatun fad'a suke sai tumurmusa suke a k'asa har ta fitar ma Farhar da jini, lokacin data ga ta fasa mata hanci da baki tsoro ya kamata ta fara k'ok'arin k'yaleta saidae ita Farhar tak'i sai k'ok'arin ganin itama ta cutar da Fatun take hakan yasa Fatun cigaba da kare kanta har jikin c-table taso bugata k'arshe ita Fatun ta buga, Saude ce ta fara shigowa sai Hajiya tana shigowa ta rafka uban salati tare da sakin sandarta ta fad'i k'asa tay k'ara aikuwa a firgice Fatuu ta k'wace ta mik'e tana ta huci, itama Farhar kokarin mikewa tay da k'yar tana ma Fatun wani kallo a fusace sai nishin wahala take tun daga k'asan hancin ta har zuwa k'asan bakin ta duk jini ne haka goshinta ma yayi jawur ita kuma ta kakkarce Fatun a wuyanta da kuma gefe gefen Fuskarta da yake k'umbuna gareta zak'o zak'o, cikin Fushi Hajiya ta kira sunan Farhar tace Saboda bata da mutunci da Matar Yayanta take fad'a haka, shiru tay sai nishi take ta kumburo baki da gani kiris take jira ta saki kuka don idanunta a cike suke taf da k'walla, kallon Fatuu data sunkuyar da kai Hajiya tayi ta tambayi miya had'a su ta d'ago cikin rawar murya ta fara fad'i mata daga breakfast da ta ce tayo mata zuwa dawowar da tayi ta iske abunda tayi mata Saude ce ta k'ara yi ma Hajiya bayani tun daga farko, sosae ran ta ya 6aci tay ma Saude nuni da ta d'ago mata sandarta, hanyar Bedroom ta nufa saida ta tsaya taga 6arnar da tayi mata a parlon sannan ta wuce ta gano sauran, bayan duk ta gani cikin parlon ta dawo Fuskarta a tamke ta tsaya daga gaban Farha rai 6ace tace "dama tunda na gan ki kinzo nayi zargin ba abun Alheri ya kawo ki ba kawae don anaso arinka kyautata zato yasa na kauda zargin hakan da tunanin mutum na canzawa, wato ke ta turo kizo kiyi mata abunda na hanata Saboda ta raina ni son d'iya yasa ta daina jin

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login