Showing 54001 words to 57000 words out of 512766 words

Chapter 19 - Asanadin Makwabtaka Book 3 Hausa Novel Complete

Unknown   

27 Dec 2024

1584

bata nan tana wurin aiki, gado ta nufa ta aje bag d'inta ta fara cire uniform d'in hannuwan ta har kerma suke ta k'agara taga yadda Rigar zata mata, bayan ta cire kayan ta fara kokarin saka rigar sai dae da k'yar ta shigeta don ta kamata sosae don ma roba ce yasa ta shiga, tsaye tay a gaban mirror tana kallon kanta hannunta rufe da baki ganin yadda shape d'inta yay bala'en fitowa tana jin tunda take bata ta6a saka kayan da suka fiddo mata da dirinta haka ba har jujjuyawa take tana k'are ma kanta kallo tunanin anya yakamata ta je da ita wurin ta fara yi kodae ta kira shi tace a canzo d'in haka taci gaba da yin wasi wasi saidae ita kanta yadda Rigar tay mata ya burgeta can ta yanke kawae ta tafi da ita komawa tay gefen gado ta d'auki wayarta ta kira gwaggo ta sanar mata zancen zuwa dinner d'in tace to Allah ya kaimu. Da daddare tana cikin yin shirin tafiya don ya sanar mata sai k'arfe 10 za'a fara gwaggo ta dawo makeup tay sosae ta saka rigar tunanin wane kalar takalma zata saka ta fara can wata zuciyar ta raya mata ta kira shi taji su wane kalar kaya zasu saka sai tasa irin takalmin da sauri ta juya ta d'auki wayarta tay sending mashi kira bayan ya d'aga ta gaishe dashi ya tambayi ta shirya ne cikin yar in ina tace eh tana son taji shi wane kalar kaya zai saka yace mata Ash suit ne da red tie tace to ta katse kiran ash d'in takalma masu tsini ta d'aukko da hadaddar purse d'in su tasa d'an kunne mai yar ziririyar sarka silver da agogon su ta jiguno dai ba k'arya, bayan ta gama ta fara tunanin gyalen da zata saka sai kuma tay tunanin tabbas ta fita da gyale gwaggo bazata barta ta fita da rigar ba haka ma Ya Haisam d'in tasan in ya gani ba lalle ya bari ba dubara ce ta fad'o mata ta yanke sa ash d'in jallabiyarta in suka je sai ta ajeta a Mota sosae hakan yay mata ta d'aukko rigar dama a goge take ta saka ta zuge zip d'in gaban yadda ta cikin zata fito tay rolling veil d'in rigar ko a hakan ma ba k'aramin had'uwa tay ba sai faman sakin murmushi take tana haka goma saura yan mintuna ya kira yace in ta gama yana waje tace to, bayan ta fito ta nufi d'akin gwaggo tayi mata sallama lokacin har ta kwanta amman idonta biyu ta tashi zaune tana kallon Fatun da murmushi ta hau yaba Kwalliyar tana fad'in had'in yayi kyau Fatun ta sanar mata shi ya kawo mata rigar ita za'a saka ta d'aga mata kai tace taje kar yay ta jira ta ce to ta juya tana fad'in sai sun dawo, a Ash d'in Mota zasu tafi tana zuwa ta bud'e front seat ta shiga bayan ta rufe kopar ta juya ta k'ara gaida shi a hankali ya amsa dama Motar a kunne take ya ja suka nufi Paramount Event Center inda za'ai dinner d'in.........


_Littafin A Sanadin Makwabtaka part 2 Naira 300 ne za'a tura ma Mutum har part 1 ga mai so zai turo kudin ta wannan Account din, 1509618776, Zainab Bature Access Bank, za'a turo shedar biya ta wad'annan nos din 09013804524 ko 08169856268
[5/8, 19:28] +234 901 700 4868: *ASM Bk2043*

_Destiny may be delayed but cannot be changed...._


*DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI*





........ Lokacin da suka iso harabar Event Center d'in shak'e take da jigunannun motoci masu numfashi kai ko ba'a fad'a ba kasan wani wanda ya kai ne zai yi aure, bayan ya parker Motar ya kai hannu ya d'auki phone d'in shi dake ajiye gefe bayan ya bud'e ya shiga call log ya fara kokarin kiran Abbas ringing biyu ya d'aga kafin yace wani abu Abbas ya riga shi tambayar sun isa wurin ne yace mashi eh yace Ok shima gashi nan ya kusa shigowa jin haka yasa yay cutting kiran ya maida wayar inda ya d'auke ta ya d'ago ya kalli Fatuu suka had'a ido da yake wurin fayau yake kai kace da rana ne don ba abunda ba'a gani hakan yasa har cikin Motar akwae d'an haske da za'a iya ganin mutum duk da glass d'in blacktinted ne amman widescreen d'in gaban bai da duhu sosae kamar na k'opopin, maida kan shi yay jikin headrest itama ta juya tana kallon abubuwan dake faruwa a wajen cikin ranta tana jinjina irin Motocin Alfarmar da aka tara ga Mutane ne sai kai da kawowa suke, bada jimawa ba Abbas ya shigo akan idon Haisam bayan ya parker Motar ya bud'e ya fito yana lallatsa wayar shi ganin hakan yasa Haisam ce ma Fatuu yana zuwa ta d'aga mashi kai ya d'auki wayar shi ya bud'e ya fita, tunkarar Abbas dake k'ok'arin kiran wayarshi yay yana ganinshi yay dariya suka ba juna hannu ya d'an kalli gefen shi ganin bai ga Fatuu ba yace "ina Zarah badai kai kad'ai d'in ka taho ba?" Fuskar shi a sake yai mashi nuni da tana cikin Mota ya jinjina kai shima ya tambaye shi ina Feenah bai bashi amsa ba sai dariya kawae yake can ya juya ya bud'e Motar ya d'an duk'ar da kan shi da alama Magana yay ya fiddo ya rufe aka bud'e front door d'in d'ayan side d'in ta fito tana sanye da irin rigar Fatuu tunda ta fito Haisam ya tsuke fuska yana mata wani kallo ganin ba Feenah bace wata ce daban yar doguwa ce don zata fi Fatuu tsawo saidae bata da jiki amman ba za'a kirata siririya ba kuma fara ce duk da da gani an k'ara dana kanti ko daga yanayin hasken fuskarta zaka gane, rigar ta amshe ta da yake roba ce amman fa da gani wurin hips d'in anyi ciko don bai tafi sosae ba kamar na gaske, tana k'arasowa Haisam ya kauda idon shi ba kamar ganin yadda ta kafe shi da ido Abbas ne yace mata ga Aminin shi Haisam su gaisa cike da kwanare da kisisina cikin mak'e murya ta gaishe dashi k'asa k'asa ya amsa ba tare da ya sake kallonta ba suna haka Motar ango ta iso wata rantsattsar jeep mai bugun zuciya tasha adon su balloons ga security gefe da gefe Motocin suka ja layi suka tsaya ba tare da wani ya fito ba Abbas ne yace ma Haisam ya kamata Zarah ta fito tunda sun iso yanzu za'a shiga ya d'aga mashi kai kawae dama wayar shi na ruk'e a hannun shi ya kira ta bayan tayi picking yace ta fito da yake yasan tana ganin su tunda Motar a saitin su take, saida ta cire jallabiyar ta aje anan cikin Motar ta gyara rolling d'in gyalen ta yadda daga bayan kan ta ya d'aga sosae Saboda gashin ta dake a fake ta kai hannu ta bud'e Motar ta fito bayan ta rufe ta tunkare su tana tafiya slowly hips d'inta na wani sama da kasa sakamakon takalmanta dake da tsini sosae kai kace da gayya take yin tafiyar saidae ita tsakaninta da Allah lafiya lou take yin tafiyarta tunda ta fito Abbas ya kafeta da ido bako k'yaftawa haka budurwar tashi, kallon Abbas Haisam yay da niyyar yi mashi magana ganin gaba d'aya attention d'in shi ya tafi kan wani abu yasa shi d'an juyawa ya kalli direction d'in da idanun Abbas d'in suke idanun shi suka sauka akan Fatuu da take nufo su har bai san ya hadiyi abu ba lips d'in shi suka d'an motsa kad'an wani iri yaji ganinta haka sam bai yi tunanin zata cire jallabiyar bane ganin ta hau da dressing d'in sosae yama kasa gane dad'in ganinta haka yaji ko kuwa akasin hakan kawai dae abunda ya sani shine sam bai dace a ganta a haka ba, tana murmushi ta k'araso ta tsaya gefen Haisam tana kallon Abbas da shima yake d'an murmushi shi kan shi bai so ganin ta haka ba har saida yay mamakin yadda akai Haisam ya fito da ita a haka, rigar ta kamata sosae shape d'inta ya fita over ita kanta budurwar Abbas d'in duk sai ta raina kanta sai faman kikkafta ido take tana had'iyar abu bakinta na d'an motsawa ta kafe Fatuu da ido tana mata kallon k'urulla Abbas ne ya katse shirun da fad'in "Mom Zarah an yo rakiya kenan" tana murmushi ta d'aga mashi kai kafin ta gaishe dashi ya amsa ta kalli budurwar Abbas d'in suka had'a ido ganinta da irin kayan jikinta yasa tay tunanin tare take da Abbas tana murmushi tace mata sannu ta d'an yi murmushin itama amman na yak'e tace yauwa had'i da d'an juyar da kai, d'aga kai Fatuu tayi ta kalli Haisam da shima kallonta kawai yake bazaka gane yanayin fuskar shi ba d'an murmushi tay mashi bai ce komai ba kuma bai maida mata martanin murmushin ba suna haka aka sanar amarya da ango zasu fito a shirya entrance Abbas yace su je kaman Haisam d'in bazai je ba saida Abbas ya k'ara cewa su tafi sannan slowly ya kalli Fatuu yay mata alamar suje tana a gefen shi suka tunkari wurin, cikin shiga ta Alfarma da ni kaina bazan iya k'iyasta adadin dukiyar dake a jikinsu ba Bride and Groom suka fito suna ruk'e da hannun juna Amaryar na sanye da rantsattsiyar farar wedding gown da ke sakin wani irin k'yalli mai d'aukar ido da alama dai stones d'in da akai adon rigar kilan diamond ne dama tun daga kunnanta wuyanta har hannunta duk diamond ne sannan aka bi da kuma irin sark'ar su da suke sawa ta duwatsu mai kaman murjani har a saman kanta tayi kyau ba k'arya dama gasu jajur da su shima Ango Prince Obinna fararen suit ne a jikinshi sai bak'in tie da bak'ak'en takalma shima kunnuwan shi na manne da barimar diamond haka agogon hannunshi ma, bayan duk an fito an jera layi abun gwanin burgewa ashe ba iya shigar su Fatuu bace wasu bak'ak'e suka sa Matan na sanye da fararen gown wasu marron suit Matan na sanye da gown golden brown da sauran shiga kala kala sosae suka tsaru duk masu shiga iri d'aya sun jera wuri guda ga makad'an su na gargajiya sunyi shigar su suna irin kid'an su suna ma ango da Amaryar shi kirari bayan komae ya tsaru yadda ake so aka nufi cikin Hall d'in, Wow wow just wow don bansan ma ta ya zan fara bayyana tsaruwar wurin ba don duk iya hasashen mai hasashe ba zai iya k'iyasta ainihin nawa aka kashe ba wurin tsara wurin don wurin ya fitinu abun ba'a Magana suna shiga duk na ciki aka mik'e tsaye police bands suka d'auka busar sarewa kake ji ta ko ina ga kid'an su da ke sa mutum ya tausaya ba tare da yama sani ba wuri fa ya kacame da kid'e kid'e ga yan rawar gargajiya ma na nasu jikin Fatuu har tsuma yake sai faman sakin murmushi take ji take ina ma anzo da Fauzy tazo taga sha'ani da ya amsa sunan sha'ani, saida suka je suka zauna a high table sannan sauran Mutane duk aka zazzauna aka dakatar da kide kiden don fara gabatar da abunda aka zo yi, bayan MC yay welcoming kowa wani abokin ango ma yazo tare da budurwar shi ce ko matar shi oho yay ma kowa sannu da zuwa da gabatar da abunda aka taru yi bayan ya gama babban Abokin Ango da Amarya inyamurai suka fito suka bada tarihin Ango da Amarya bayan suma sun gama aka buk'aci Bride and Groom suka fito don taka rawa zo kaga yadda suke cashewa abunsu cike da nuna ma juna kauna abun sai yama ba Fatuu kunya sai faman sunnar da kai take yayin da ake ta masu ruwan lik'i masu lik'a dollars nayi masu lik'a Naira nayi manyan mutane masu sanye da shigar su ta gargajiya ta ko ina sai tasowa suke suna lik'i daga baya aka bukaci kowa ya koma Abokan Ango da Amarya inyamurai suka fito aka fara casu mai sunan casu Fatuu sai dariya take haka ma su Abbas ji take kaman tay tsuntsuwa ta ganta a cikin filin itama tayi rawar saidae ba dama, bayan duk an gama abubuwan da ya dangance su aka dawo kan hausawa shi Angon da kanshi ya fara bayanin irin alak'ar shi da mutanen Katsina da irin karar da suka yi masu tun bayan da suka tsinci kan su a cikin garin ba tare da nuna k'yama ko tsangwama ba Saboda bambancin Addini ya tabbatar ma Mutane da musulunci addinin zaman lafiya ne sa6anin wasun su da suke masu kallon yan ta'adda yace shi shaida ne game da Mutuncin hausawa don sun nuna masu k'auna ta yadda har sun zama daga cikin Family d'in shi a k'arshe yay godiya ga musulman da suka zo wurin ya nuna hakan ba k'aramin abu ne a wurin shi ba yay fatan Allah ya k'ara had'a kan su suci gaba da zama da juna da Amana yay Addu'ar samun zaman lafiya da kwanciyar hankali da wadata ga K'asar mu Nigeria sannan yay godiya ga Governor d'in Katsina da Sarakunan D'aura da Katsina da sauran manyan mutane Mutane nata amsawa da Ameen bayan ya gama itama Amaryar aka bata tayi godiyar bayan duk sun gama aka buk'aci babban Abokin Ango bahaushe da ya fito ya bada tarihin Ango na nan garin irin alak'ar shi da mutane da sauran su MC ya tambayi angon waye zai fito ya nuna mashi Haisam duk ido ya dawo kan shi a nutse ya mik'e ganin zai fito shi kadae MC yace the equation isn't balanced nan take duk aka gane abunda yake nufi da yake d'an barkwanci ne duk aka sa dariya dakatawa Haisam yay ba wai fita da Fatun ne bazai yi ba sam shigar ta bata dace da wurin ba a matsayinta na Musulma Abbas ne ya kalli Fatuu yace ta tashi suje ganin Haisam d'in bai ce komae ba yasa ta mik'e ta fito suka jera wohoho all eyes on them ita kanta Fatuu duk sai ta ji ta takura, tunda suka fara saukkowa daga kan steps d'in MC ya saki baki galala kamar rainon sakarai yana bin su da kallo tun daga sama har k'asa, lokacin da suka k'araso gaban shi suka tsaya fuskar Haisam dai ba wata walwala don duk ji yake wurin ya fice mashi a rai maimakon MC d'in ya bashi loudspeaker d'in sai yace mashi wait ya juya kan Mutanen wurin yace "People are u seeing what am seeing???" gaba d'aya aka sa dariya ya sake juyawa kan angon harda d'an rankwafawa alamar girmamawa cikin harshen turanci da yake dashi ake Magana a wurin yace ya gafarce shi amman abokin shi bahaushe ya tambaya ba Arab ba ko Indian gaba d'aya wurin aka kwashe da wata irin dariya har dai shi Haisam d'in saida ya d'an dara Fatuu ma haka daga inda Angon yake zaune yace ma MC ya ba Haisam d'in speaker ya tambaye shi tarihin shi da Hausa anan zai gane wanene shi ya juyo kan Haisam yace suna rok'on Alfarmar jin tarihinshi da hausa farko kafin ya fad'i abunda aka bukace shi ya fito yi, shiru ya d'anyi MC d'in nata fad'in please can ya kai hannu ya amshi speaker d'in cikin cool voice d'in shi ya fara bada tarihinshi a tak'aice cikin harshen hausa aikuwa masu jin hausa a wurin aka hau tafi da sowa Haisam d'in na d'an murmushi MC sai faman jinjina kai yake baki bud'e alamar mamaki bayan ya gama ya canza harshe zuwa turanci ya fara bada tarihin Ango da mu'amalar shi da mutane anan sai ka rantse ba shine ya gama Magana da Hausa ba gaba d'aya ya gama tafiya da mutane sai faman sakin murmushi ake bayan ya gama ya mik'a ma MC d'in speaker d'in amman sai yak'i amsa yace yana son yay mashi few questions ba yadda Haisam d'in ya iya dole yace mashi yana jin shi farko tambayar shi yay miye alak'ar shi da Fatuu har saida gabanta ya fad'i Haisam d'in yay d'an shiru kamar mai nazari Abbas kuwa mi zaiyi in ba Dariyar mugunta ba can ya nisa yace mashi girlfriend d'in ce da sauri Fatuu ta kalle shi sai kuma ta kauda kanta gudun kada a gane ba gaskiya ya fad'a ba saidae bata yin zaton zai boye gaskiya ba, tambayar shi yadda akai suka had'u ya k'ara yi anan bai 6oye ba yace mashi Neighbor d'in shi ce daga baya ya koma kan Fatuu itama ya tambayeta tsakanin su waya fara cewa yana son wani shiru tay ta rasa amsar da zata bashi kawae sai ji tay Haisam d'in yace mashi shi ya fara MC d'in ya k'ara tambayarta ya taji da ya furta yana sonta tace taji dad'i sosae har bata san yadda zata bayyana ba tana fad'in hakan ta sunnar da kai, haka dae yaci gaba da yi mata tambayoyi daga baya Haisam yace ya d'an yi excusing nasu yay ma Fatuu alamar su je suka juya MC nata kod'a su yana fad'in "What a match, What a perfect Match......." Maimakon su koma high table d'in sai gani tay ya nufi hanyar fita daga hall d'in hakan yasa ta bi bayan shi suka fice, inda Motar su take ya nufa tay tsaye tana kallon shi ya bud'e ya kalleta yace ta shiga cikin rashin fahimtar dalilin fitowar su ta kai hannu ta bud'e ta shiga tana ta kallon shi har yay ma Motar Key ya fara yin reverse tana dae ta kallon shi da alamun mamaki har ya juya Motar suka tunkari gate d'in fita, suna hawa hanya sai ga kiran Abbas yana yin picking tun kafin Abbas yace wani abu yace mashi yaba Prince hak'uri he has an urgent call ya tafi daga haka yay cutting call d'in yaci gaba da driving baki bud'e Fatuu ke kallon shi sam bata yarda da Maganar

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login