Showing 216001 words to 219000 words out of 512766 words

Chapter 73 - Asanadin Makwabtaka Book 3 Hausa Novel Complete

Unknown   

27 Dec 2024

1581

ki zama likita da kike buri" yar dariya Fatun tayi kawai, suna haka aka turo kopar d'akin duk suka kai idanunsa wurin, Haisam ne ya shigo hannun shi ruk'e da tea cup asaman saucer, har saida gaban Fatuu ya d'an fad'i ganin shi, ciki ya shigo ya nufo wurin su,a gaban Fanan ya tsaya idonta akan shi da d'an murmushi ya mik'a mata cup d'in tea d'in ta amsa a hankali ta furta mashi thanks Fuskar shi a sake ya jinjina mata kai, d'agowa yay idon shi akan Fatuu da ke kallon k'asa sai taji duk ta takura, mik'ewa tay ta kalli Fanan tace mata saida safe tace ta tsaya su sha tea d'in mana da d'an murmushi ta girgiza mata kai tace taci Abinci sosae dama saida safen ta shigo yi mata, godiya tayi mata tace sai sun had'u da safe daga haka Fatun ta juya ba tare data kalli inda yake ba ta nufi k'opa ta fuce. Tana tafiya tana ta zancen zuci har ta k'araso part d'in su, tun a parlor ta gasgata Haisam ya shigo jin k'amshin turaren shi,

Bedroom ta wuce tana shiga ta nufi bakin gado ta zauna tay zuru tana cigaba da zancen zucinta, sosae Fanan take bata tausayi tasan itama ba K'aramin so take ma Ya Haisam d'in ba yanzu kuma ace ya auri wata tasan dole ta shiga matsananciyar damuwa, mamakin ta yadda akai tay saurin amincewa ba kamar data ce mata saida aka tura sak'on nan ta sani duka kuma ba'a fi kwana shidda ba, wata zuciyar ce ta raya mata wato da ya kasa fad'a mata saida asiri ya tonu ta amince shine suka taho da hakan bata faru ba tasan baida niyyar zuwa, wani abu taji mai kaman 6acin rai ta raya yanzu dai ta tabbatar ba son ta yake ba tunda saida Matar shi ta amince zai waiwaye ta dama kuma tasan Saboda Hajiya yake zaune da ita, rayawa tayi to miye amfanin zaman ta dashi wai tunda bai son ta kawai ya saketa ya huta Aunty Fanan ma ta huta da damuwa, tunanin ta nemi ya saketa ta shiga yi, wata zuciyar ta raya mata tana tunanin a yanzu zai saketa bacin yasan sirrin zuciyarta ita kanta Fanan ai don ta nuna tana son shi ya aure ta, sosae taji bata ji dad'in sak'on da ya gani ba amman duk da haka ta sama ranta zata ce ya sake ta kawai, ta d'auki lokaci a zaunen kafin ta mik'e don taje tayi wanka, bayan ta aje gyalen ta gaban mirror ta tsaya tana kallon kanta ta kai hannu tana cire yan kunnan ta fashion bayan ta cire su ta cire agogon hannunta ta d'aura su akan dressing mirror, daidai ta juyo aka turo kopar Bedroom d'in har saida gaban ta ya fad'i, shi ne ya shigo idon shi akanta yasa hannu d'aya ya tura kopar, a wurin ya tsaya suka kafe juna da ido fuskar shi a sake kaman zai yi murmushi ita kuwa yanayin tata kaman a d'aure, kauda idon ta tayi gefe zuciyarta ta raya mata tsayuwar mi take ta tafi tay wankan ta, nufar hanyar Laundry room tay idon ta a k'asa har tazo daidai inda yake a tsayen, tana niyyar wuce shi kawai taji ya kamo hannun ta na gefen da yake, yamutsa fuska tay fuskarta na kallon gefe wurin gado kirjinta ya hau bugu da sauri da sauri, wani irin haushin shi taji ya kamata wato sai yanzu da aka amince mashi ne zai yi lokacinta ta raya hakan, kaman daga sama taji ya furta "Zaraah" wani kalan murmushin takaici ta yi nan take ta fara k'ok'arin k'wace hannunta, k'ara kiran sunanta yay aikuwa a fusace ta juya idanunta har sun ciko da k'walla tace "ba suna na haka ba sunana Fatuu ka kira ni da hakan" cikin yanayin muryar kuka tayi Maganar tana rufe baki k'walla suka zubo mata sharr da sauri ta juyar da fuskar inda take kallo da, still yay yan kallonta don ya gane dalilin daya sa ta fad'i hakan, k'ok'arin matso da ita ya fara nan take ta fahimci rungume ta zaiyi aikuwa ta tirje ta fara jan hannunta sai ga abu ya zama kaman kokowa, da dai taga ta kasa kwace hannun sai ta fashe mashi da kuka ta fara fad'in ita ya sakar mata hannu, janyota yay ya had'a jikinsu ta kafe tak'i yarda ya mannata da k'irjin shi ta hau girgiza kan ta cikin k'araji take fad'in ita ya k'yaleta, sosae take kuka tana girgiza kai idonta a rufe gaba d'aya ta fara rud'a shi fuska a yamutse yake kallon tata fuskar, da k'yar ya manna ta da k'irjin nashi ya rungumeta gam sai faman kuka take, d'aura ha6ar shi yay a saman sumar ta mai santsi da tuni kallabin dake sama ya fad'i, lumshe idanunshi yay underneath his breath yake furta "am sorry for hurting u Zaraah, it was never my intention" shiru tay tana cigaba da kukan saidae sautin kukan ya d'an ragu sai sheshsheka take ga fitinannan k'amshin jikin shi duk ya cika mata hanci hakan ne yasa natsuwarta ta d'an daidaita, Moving yay da ita zuwa bakin gado ya zauna da ita ta kasance a saman cinyoyin shi har lokacin kuma yana rungume da ita gam, maida ha6ar shi yay saman kan nata breathing d'in shi na fita slowly idanun shi a d'an lumshe shi kad'ai yasan abunda yake ji a cikin ran shi ganin ta cikin halin nan, ganin kaman ta d'an natsu yasa shi janye beard d'in shi ya maida fuskar shi saitin kunnanta whispering in to her ear ya furta "I came all because of you" da sauri ta girgiza mashi kai ta d'ago idanunta sharkaf da hawaye ta juyar da fuskar ta gefe cikin fushi tace "ni ban son Auren ka sake ni!" jimm yay yana kallon ta can yay sigh calmly ya furta "Zarah kina fad'a man haka a matsayi na na mijin ki ba kyau fa" sheshshekar kukan ta ce ta k'aru, ji tay yace "Kin daina sona ne??" Kaman tana jira da sauri ta d'aga mashi kai alamar eh har saida ya d'an runtse idon shi kafin slowly ya bud'e sai kuma ya d'an cize le6en shi na k'asa, nisawa yay yace "are u serious Zarah?"da sauri ta k'ara d'aga mashi kai alamar eh wannan karon har saida yaji gaban shi ya d'an fad'i, shiru yay idon shi a kan gefen fuskar ta, mutsu mutsu ta fara yi tana son ta k'wace daga jikin shi saidae ta kasa a hasale tace ita ya k'yaleta, still shiru yay bai kuma sake tankawa ba sai dae zuciyar shi ta fara gasgata mashi abun da take fad'an, muryarta ce ta k'ara ziyartar kunnan shi tace ya saketa, sigh yay Slowly ya furta "Ok, I want you to look into my eyes and tell that u don't love me sai in maki abunda kike so in hakan zai saki farinciki" yana rufe baki ta juyo ta kalle shi cikin idon da k'arfi gaban shi ya fad'i don yana ganin fad'in zata yi, bin juna sukai da ido tana d'an huci wani irin kallo yake bin ta da shi sai motsa baki take ta kasa furta mashi Maganar gaba d'ayan su gaban su fad'uwa yake bai ta6a jin zullumin magana ba sosae irin haka, da k'yar ta fara bud'e baki tace "ba.......n......." Zuciyarta ce ta fara tariyo mata Alkhairan shi a gareta ta shiga raya mata yanzu duk son da take mashi da wahalar da tasha Saboda shi ta za6i ta rabu dashi, kawai sai gani yay ta fashe da matsanancin kuka ta fad'a mashi, wani irin lumshe ido Haisam yay sosae yaji sanyi a ran shi, Kuka take sosae ta had'e fuskar ta da k'irjin shi, daga jin yadda sautin kukan ke fita yasan ba K'aramin K'ona ranta ke mata ba zuciyar shi ce ta shiga tunano sak'on data tura mashi irin wahalar data bayyana mashi ta sha Saboda son shi, wani irin tausayin ta ne ke ratsa shi sam bai jin dad'in yadda take kukan har Fuskar shi ta nuna fararen idanuwan shi sun d'an yi ja, hannun shi d'aya ya d'ago ya d'aura a saman kan ta ya fara shafa gashin ta alamar lallashi cikin breaking voice ya fara magana "am very sorry Wife, am not happy I caused u pain, kiyi hak'uri don Allah, bansan komai ba game da haka" cigaba da shafa kan yayi a hankali sautin kukan nata ya fara raguwa, sun d'an d'auki lokaci a haka saida yaji tayi shiru sai ajiyar zuciya da take ta faman yi ya d'ago da kanta suka fara kallon juna idanunta sun yi luhu luhu sunyi ja har lokacin ajiyar zuciyar take ta saki,

"Forgive your Husband pls, bana jin dad'in ganin ki haka Wife, ba kamar in na tuna duk Saboda ni ne, ki manta komai ya wuce pls" yana Maganar d'umin numfashin shi na sauka akan Fuskar ta, shiru kawae tay tana kallon shi ba alamun zata tanka, fuskar shi a sake kaman zai murmushi yace mata tayi mashi magana pls sai lokacin ta d'an juyar da fuskar ta, hannu ya kai ya juyo da Fuskar ta sake kallonshi ya lumshe mata ido nan take ta gane Magana yake nufin tayi, da k'yar ta bud'e baki cikin muryar kuka da yar in ina tace "t...to ai kai baka sona ko shiyasa gara a bar Auren" d'an murmushi yayi yace mata in sun rabu to ya zatayi da son nashi,

"A...ai dama baka sani ba ko na 6oye sai in yi hak'uri kuma nasan zan daina daga baya, d...dama ai har na hak'ura za'a min Aure ko" tana Maganar ya zuba ma bakinta ido Fuskar shi kaman zai murmushi har ta gama ta d'an tura baki, murmushi yay ya d'an d'age gira yace "in kuma ni ban son rabuwa dake fa Saboda nima ina son ki" ba shiri ta waro ido bakinta ya d'an bud'e, sosae taji Al'ajabin Maganar don ta gama yanke bai sonta, hannu ya kai ya rufe mata bakinta da ta bud'e ta tura mashi bakin had'i da d'an juyar da fuskar ta, ji tayi yace bata bashi amsa ba sannan ta maido idon ta kanshi a sanyaye tace ai tasan da wasa yake tunda da yana son ta ai da ya nuna mata, murmushi yay kawae suka zuba ma juna ido Fatuu sai d'an kikkafta ido take idan tace bata jin sabon son shi na ratsa zuciyar ta to ta shirga babbar k'arya, ganin bai da niyyar cewa komai gashi ta k'osa taji da gaske yana son ta yasa ta d'an yamutsa mashi Fuska, d'age mata gira yay yace "What?" a d'an shagwabe tace he should tell her da gaske abunda ya fad'a, Sigh yay kafin a nutse ya fara Magana,

"Lokacin da Hajiya ta kira ni tay informing nawa game da Auren da za'ai maki na shiga damuwa because nasan miye burin ki kina son kiyi karatu, hakan yasa naji ba dad'i sosae har nayi mata magana kan bai kamata ayi maki Aure ba kuma ma wannan Auren dole ne I asked her to do something tunda hakan ya shafi aikinta na NGO but sai ta nuna man haka al'adan ku yake in ta shiga Maganar har ta hana ayi maki auren zai zama wani seriou issue Dad d'in ki zai shiga matsala sosae a lokacin ta fad'a man a halin da yake ciki kuma kema kin amince, karshe I have no option dole na bari suyi maki yadda suke so din, abun ya dame ni sosae bayan na kira ki kin sanar man kema baki so Saboda Dad d'inki kika amince haka nayi ta tuna Maganar ki da kukan da kike yi a lokacin, I thought damuwan nawa zai ragu tunda kin nuna man kin amince da Auren but sai abun yay ta gaba thinking of u all the time, nayi tunanin don na damu da halin da kike ciki ne a Lokacin amman abun sai yay ta k'aruwa damuwan yayi man yawa ko yaushe Zarah ce a raina abun har ya fara affecting bacci na bana samun enough ko ya d'auke ni it's Zarah gaba d'aya cikin shi, while eating, while driving ko mi nike Zarah ce abun har ya kaini ga hullicinations da naga yar baturiya daidai girman ki sai inta ganin ke ce inna zauna shiru sai inta jin muryar ki kina magana ko kuma in wata tayi magana naji kaman voice d'inki....." Dakatawa yay dama Maganar yana yi yana d'an tsayawa yake yin ta, idon su cikin na juna Fatuu tayi k'uri tana saurarar shi cike da Al'ajabi, d'an yamutsa mata fuska yay yace "kin man nauyi" wani kallo tay mashi ta d'an tura baki, K'ok'arin sauka daga saman jikin nashi ta fara ya maidota yay wrapping nata sosae, kai Fuskar shi yay gefen kunnanta whispering into her ear ya furta "just kidding wife, bana jin nauyin ki in ma kina da shi" yadda Maganar ke sauka acikin kunnanta har saida ta runtse ido fuskar ta d'auke da murmushi, shiru suka d'anyi can ta d'ago da fuskarta taga ita yake kallo, ganin baida niyyar cigaba yasa ta d'an yamutsa mashi Fuska tare da d'an motsa kai, murmushi yay don ya fahimci mi hakan ke nufi slowly ya kai bakin sa saman goshinta yay pecking wurin har saida ta d'an lumshe ido tana bud'ewa suka shiga cikin nashi kunya ce ta kamata da sauri ta kife fuskarta a broad chest d'in shi, hannu ya kai ya cigaba da shafa sumar ta mai santsi da laushi,

"I don't know what's happening to me a lokacin,but I know am not alright don ban ta6a fuskantar irin hakan ga wani ba besides ni ban sa damuwa a raina, in dai abu naga zai zaman man damuwa da wuri nike maganin shi, a lokacin Fanan ta gane abu na damuna ta fara tambayana farko na nuna mata kawai banjin dad'i ne amman daga baya ta fara nuna man damuwarta kan sai na fad'i mata abunda ke damuna don ta ganni abnormal, na rasa mi zance mata yana damuna na barshi a banjin dad'i ne tace to muje Asibiti na nuna mata ba wani ciwo nike ba itace take ganin kaman ban lafiya, nasan kawai ta k'yale ni ne ba don ta yarda ba daga lokacin na fara k'ok'arin 6oye abunda ke damuna Saboda ita sai kuma na fara samun sleepless nights don sai damuwan ya dame ni in dare yayi hakan ke sa in kasa bacci, daga k'arshe na yanke zuwa inga Doctor, banje Asibitin su Fanan ba sai na je wani daban naga likita, bayan nayi mashi duk bayanin abunda ke damuna ban 6oye mashi komai ba shine yay assuring nawa cewa.....Na fad'a Son ki ne....." dakatawa ya k'ara yi suka k'ura ma juna ido cike da k'auna yayin da numfashin su ke had'uwa dana juna, kasa jurewa Fatuu tay ta sauke idanunta don wani irin kallo mai saukar da kasala yake mata,

"Nayi mamakin jin hakan sosae Saboda tunda nike dake ban ta6a ji ko yi maki kallon hakan ba, ina d'aukar ki a matsayin blood sis tawa, kallon da nike maki kenan Zarah, saidae ban k'aryata Maganar shi ba na yarda da hakan, nan ya bani shawarwari saidae wadda yafi bani itace in mallake ki shine solution kawai a lokacin, jin hakan har saida na d'an yi murmushi sanin it's impossible, daga lokacin na dage kan sai na cire son naki a raina na dage da rok'on Allah akan hakan sosae nike yak'i da zuciyana, ban gane son ki yamun mugun kamu ba sai bayan na tafi wani Seminar da Company d'in mu suka tura ni, ina cikin yin bayani na rink'a ambaton sunan ki saida aka man magana sannan na gane shirmen da nike tafkawa, k'arshe dai ranar a gadon Asibiti na kwana don wani duhu na fara gani har ya kai na fad'i......",

dakatawa ya k'ara yi ya d'age mata gira yace "tunda kike ciwon sona kin ta6a koda shan drug ne Saboda hakan?" d'an jimm tay alamar tunani kafin a sanyaye tace mashi a'a saidae maganin bacci da Kawu Amadu ya ta6a amso mata data kasa yin bacci, d'an murmushi yay yace "kin ga ni nasha drugs, na kar6i injections k'arshe harda drip all because u" wani irin tausayin shi ne ya mamaye mata zuciya nan da nan idanuwanta suka ciko da k'walla yana ganin haka ya girgiza mata kai da sauri alamar kar tayi kukan ta hau kikkafta idanu, cikin karyayyar murya tace mashi yaci gaba, d'an tura mata baki yay irin yadda take yi slowly yace mata ya gaji da Magana har saida yasa ta d'an yi yar dariya dama don ta washe kada tayi kukan yayi Mata hakan,

"Kwana na d'aya a asibitin na nuna gida zan koma aka matsa man kan in bari in k'ara samun sauk'i, bayan nayi kwana biyu lokacin na warware sosai na dawo gida ba tare dana k'arasa abunda naje yi ba...., wani iko na ubangiji ranar Abbas ya kirani yake sanar dani ai gaki kin gudo wai baki son Auren da za'a maki na tambaye shi dalili nan ya sanar dani irin mijin da ake son Aura maki, lokacin na tambaye shi to miye mafita sai yace man ai ya yanke zuwa garin shida Grandma d'inki nace mashi Shikenan duk abunda ake ciki sai ya sanar man, a next wayan da mukai da Abbas lokacin yay man Maganar Auren ki, bazan 6oye maki ba lokacin duk da halin da nike ciki ban ji zan amince ba don ina ganin ba abu bane mai yuwuwa, ban dad'e da nayi Aure ba so nasan Matana da iyaye na bazasu amince ba, k'arshe da yake Allah ya k'addaro Aure tsakanin mu Abbas yay convincing ena ya tsara yadda za'ai, I guess you know everything about dat" kai ta jinjina mashi wani irin kallon tausayi mai had'e da tsantsar kauna take mashi, shima fuskar shi da d'an murmushi idanun shi a d'an lumshe yake kallonta shi kad'ai yasan irin nishad'in da yake ji a cikin zuciyar shi jin

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login