Showing 21001 words to 24000 words out of 512766 words

Chapter 8 - Asanadin Makwabtaka Book 3 Hausa Novel Complete

Unknown   

27 Dec 2024

1535

ta amsa kwanan shi biyu ran Friday ya tafi, Bayan sati guda suka shirya zuwa Niamey K'asar Nijar bikin Haulat harda Kawu Amadu gwaggo tayi masu hidima sosae don kayan kitchen d'in Fatuu ta d'ibar mata masu yawa harda zannuwan gado da labulaye innarsu haulat d'in kafin su tafi lokacin tay tsananin farinciki da yake su da wuri suka tafi su kuma su Fatuu saida bikin ya zo, Tafiya yankin Azaba Fatuu an ji jiki sai lokacin ta gane daga Katsina zuwa Adamawa ba komae bane akan wannan tafiyar da sukae don farko Marad'i suka fara zuwa daga can suka hau luxurious bus suka kwana suna tafiya don ma Motar nada dad'in hawa akwae su Ac harda Tv, lokacin da suka isa da k'yar take iya taka k'afafunta don tafiyar tayi daga Katsina zuwa Lagos in ma bata fi ba, Haulat tay tsananin farinciki da zuwan nasu haka danginsu sun tarbe su hannu bibbiyu an sha shagali an ci an sha anyi wadaqa da nama don mutan Nijar badai cin nama ba bakamar in suna hidima gashi ba Laifi dangin mijin nada d'an hali saidae wani Abincin fa su Fatuu kasa ci sukae sai wanda yay irin namu na nan, Alhamdulillah ranar Asabar aka d'aura auren Haulat da Angonta wanda yake d'an uwanta ne wato Nuraddeen suna zaune Fatuu na dariya tace mata da rabon dae sai ta rigata yin aure duk sukae dariya, Sosae Fatuu akai kasuwa don wanka na Mutunci ta rink'a d'auka da bikin don ma gwaggo na taka mata burki har samari ta hanata saurara tace ba wannan ne a gabanta ba to itama dai dama ba mai kula samarin bace, bayan biki da kwana biyu suka sake d'aukko hanya aka taita yi har Allah ya maido su Lafiya Fatuu cike da kewar Aminiyarta, tun suna can aka saki result d'in Waec suna dawowa Abbas yazo ya dauketa suka je dubawa gaba d'aya ta samu credit saidae chemistry ne ta samu pass tun can ta fara k'walla don bata tsammaci hakan ba sakamakon tasan ta maida hankali lokacin da sukae exams d'in gashi dole saida shi zata iya yin School of nursing din Abbas ne ya shiga kwantar mata da hankali yace a jira Neco ta fito in sha Allahu yasan zata samu, koda ta dawo gida ma gwaggo duk da bata ji dad'i ba amman bata nuna mata damuwa ba sosae itama tace a jira d'ayar daga baya ma sai ga Haisam ya kirata don Abbas ya fad'i mashi komae harda yarda ta tashi hankalinta sosae ya kwantar mata da hankali yace ai akwae alternative so a jira Neco fuska jage jage tace mashi to anan ma saida ya k'ara ce mata lazy ta tura mashi baki daga baya sai gashi har saida yasata dariya, bayan sati biyu Neco ta fito wannan karon k'in zuwa tay dubowar saidae Abbas ne yaje, a k'opar gida ya tsaya bayan ya dawo ya kirata ta fito tunda ya tafi dubowar dama gabanta keta fad'uwa duk ta sha jinin jikinta ba kamar da taga fuskar Abbas d'in bai dariya a gefe ta tsaya ta gaida shi a sanyaye ya amsa duk ya d'an damu kaman zatai kuka tace mashi itama akwae matsala ko ya d'aga mata kai alamar eh nan da nan tasa hannu zata fara matsar kwalla ya fiddo result d'in daga gefen shi ya mik'a mata, k'in amsa tay tace ita mizatai dashi tunda bata ci abunda ake so ba saida ya d'an matsa mata sannan ta amsa ta amman ta k'i dubawar yace ta duba mana, hannunta har rawa yake ta d'aga da ido d'aya ta d'an kalli paper d'in da sauri kuma ta ware idanun a tunaninta ko abunda take gani gizau ne ba gaske ba, tabbatar ma da kanta tay da sauri ta kalli Abbas taga yana murmushi a rud'e tasa hannu ta rufe bakinta ganin ta cinye duka harda su A (distinctions) nan da nan ta fara murna tana yarfa hannu sai faman fad'in Alhamdulillah take Abbas na mata dariya, koda ta shiga gida gwaggo ta gani tay matuk'ar murna harda duk'awa wai Fatun ta hau ta goyata ta kuwa haye aikuwa da k'yar ta mik'e don ma gwaggon k'akk'arfa ce dik'ir take, ganin tana ta nishi yasa Fatun saukkowa tana ta kyalkyatar dariya,

Lokacin da aka fara saida Form na Makarantar Abbas ne yaje Bank ya siyo mata ya kawo mata suka cike tare suka maida can School d'in bayan wani lokaci suka je don yin jarabawar shiga wato Entrance exam a lokacin ne ta had'u da wata da suka zauna tare har ta fad'a mata sunanta Fauziyya Ahmad ta tambayi Fatun itama ta fad'i mata nata Fauziyyar tay masu Fatan Nasara Fatuu ta amsa da Amin, bayan sun gama ne tace ma Fatuu ta bata phone no d'inta ta bata don ta lura tana da kirki ga fara'a bunu bunu tayi murmushi, bayan kaman sati biyu da yin jarabawar aka kafe lists d'in wanda suka ci Fauziyya ce ta kira Fatun ta sanar mata ta samu itama haka don taga sunanta cikin yan Katsina local Government itace ma ta biyu sosae Fatuun tay murna duk da da sauran rina a kaba don dama farko sai su d'auki Mutane fin d'ari cikin mutane wurin 500 koma fi da sukai applying sai a hankali za'ai ta zubar da su don bai wuce Mutum 130 ko 150 bane zasu ci entrance exam d'in suma kuma wurin interview za'a k'ara zubar da wasu haka Bayan an fara karatunma, cikin Nasara Fatuu taci interview da sukae ta samu Admission d'in Kasimu Kopar Bae School Of Nursing Katsina dake acikin General Hospital, kowa yay farin ciki karma dae gwaggo taji haka Abbas ma har Haisam saida ya kira ya tayata murna daga baya suka fara Class ranar farko har Video call sukai da Haisam tana cikin fararen Uniform d'inta da takalma sai faman zabga dariyar dad'i take ya k'ara tayata murna ya kuma ce sai ta d'age don still bata zama cikakkar daliba ba har sai tayi passing Intro Exam tace in sha Allahu, tun ranar da suka je interview Fauzy kamar yadda Fatun ta fara kiranta dama kuma tace haka ake ce mata ta tambayi Fatuu Day zatai ko Boarding tace mata Day Fauzyn tace mi zai hana tayi Boarding don itama ita zatai Fatuu ta tambayeta ba'a nan garin take bane tace eh ita yar Funtua ce amman akwae Yayarta dake Aure nan Katsina a Goruba Road, Fatuu tace to ba sai ta zauna a wurinta ba Fauzyn tace ita tafi son zama a school don mutum yafi samun time na karatu balle wannan Makarantar da ba'a wasa da karatu dole sai Mutum ya dage zadai ta rink'a zuwa wurinta weekend, to bayan sun fara shiga Class ma saida ta k'ara yi ma Fatuu Maganar tace an bata d'aki dama akwae wata yar garinsu da suka gama a d'akinsu zata zauna Don Allah ta dawo boarding sai su zauna tare ganin yadda ta dage tana ta nuna mata Muhimmancin zama a cikin Makaranta ne yasa Fatuu tace to in ta koma gida zata tambaya in an barta sai ta dawo Fauzy harda yi mata Addu'ar Allah yasa a barta ita dae Fatuu yar dariya kawae tay, A ranar da daddare bayan sallar Magrib ta iske gwaggo a d'aki ta gama salla ta zauna gefenta bayan tay mata sannu ne tayi mata Maganar komawarta boarding, shiru gwaggo tay tana kallonta can ta nisa ta tambaye ta miyasa take son zama a Makarantar Fatun tace an fi samun lokaci kuma ko Assignment aka bada mai wuya za'a taru ayi tare sannan ana tattaunawa game da abunda aka koya, d'an jimm gwaggo tay kafin tace "Gaskiya ni banson zaman Makarantar nan don yana da illoli ba kuma wai don ban yarda dake bane amman nafi son ki rink'a zuwa kina dawowa" gyad'a kai Fatuu tay tace Shikenan Gwaggo ta fahimci yanzu duk inta nuna ga yadda take son abu bata gardama mata hakan yasa tace mata in kamar an basu aikin ko zasu tattauna kan karatun zata iya tsayawa can amman ba wai ta koma gaba d'aya ba Fatun tace to ta tashi ta koma d'akinta............





_Littafin A Sanadin Makwabtaka part 2 Naira 300 ne za'a tura ma Mutum har part 1 ga mai so zai turo kudin ta wannan Account din, 1509618776, Zainab Bature Access Bank, za'a turo shedar biya ta wad'annan nos din 09013804524 ko 08169856268._
[5/8, 19:28] +234 901 700 4868: *ASM Bk2037*

_Destiny may be delayed but cannot be changed...._


*DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI*





.........A bakin gate ta tsaya suka gaisa da Officer har yana ce mata yaushe za'ai mashi allura tana dariya tace sai ya shirya daga haka ta shige, lokacin data shiga Parlon ba kowa saidae a gyare yake tsab sai daddadan k'amshi ne ke tashi, Bedroom d'in Hajiya ta wuce ta tura ta shiga a hankali da yar sallama idonta suka sauka akan Hajiyar dake kwance saman gado ta d'ago kai don ganin mai shigowa suna had'a ido Fatuu ta sakar mata murmushi Hajiya ta yunk'ura tana kokarin tashi zaune itama da murmushin akan fuskarta, daga gaban gadon ta tsaya tace "Hajiyar Sanata ina wuni an dawo lafiya" da hannu ta nuna mata gefen ta alamar ta zauna tana amsa gaisuwar tata, dafa Shoulder d'inta tay da murmushi tace "Ma sha Allahu Fateema yar Makaranta naji dad'in ganin ki haka sosae, ashe abu haka ya kasance da bani nan?" Kai Fatuu ta d'aga a hankali tace mata eh, tace "An gode ma Allah daya kawo k'arshen Al'amarin cikin sauk'i duk aikin Addu'a ne da kuma biyayya da kika ma mahaifin ki shiyasa ya za6a maki abunda yafi zama Alkhairi" ita dae Fatuu murmushi kawae take can tace mata ya jiki still da fara'a ta amsa "Ah k'afa Alhamdulillah na samu sauk'i tuni fa sune suka hana ni dawowa wai sai in zauna can" yar dariya Fatuu tay tace "suna son su rink'a ganinki a kusa dasu ne Hajiya" ta6e baki tay "suda suke tafiyar su aiki su barni yini zungur daga ni sai mai aiki to ba gwara a k'yale ni in dawo ba, shiyasa ina ganin Azumi ya taho nace to wllh gida zan dawo in yi shi cikin yan'uwana ba Arziki da suka ga ina niyyar hana masu sukuni aka barni na dawo" ta k'arasa tana yar dariya itama Fatun dariyar take Hajiyar tace "To ya Karatun Fateema ana maida hankali ko" kai ta d'aga tace mata eh sosae, tace "Kin iya allura?" Fatuu na dariya tace "na iya ta tuni bama ita kadae ba na iya abubuwan duk da aka nuna mana sosae don yanzu muna cikin Asibiti ne" jinjina kai Hajiya tay tace "Ma sha Allahu kice ni yanzu ina da mai duba ni a gida, Allah Ubangiji yasa ma karatun Albarka ya bada sa'a Amin" itama Fatuu ta amsa da Amin, shiru suka d'an yi can Hajiyar tace "Fateema kije ki ci Abinci naga kaman yanzu Kika dawo daga Makarantar dama Akwae na Yayan ki da bai ci ba akan table d'in" da sauri Fatuu ta d'aga ido ta kalli Hajiya jin abunda tace kafin da mamaki akan fuskarta tace "Ya Haisam yazo ne?" Hajiya tace "Eh tare muka zo shi ya maido ni saida nace ma ya tsaya Saboda aikin shi zan iya dawowa amman ya k'iya sai kace zan 6ace, tunda muka dawo ma ya fita kinga har yanzu bai dawo ba k'ilan ko wurin Abbas yaje" shiru Fatuu tay fuskarta da d'an murmushi sai kuma ta sunkuyar da kanta ta rasa gane farinciki take da jin yazo ko kuwa can ta d'ago tace ma Hajiya bari ta barta ta huta anjima ta dawo hajiyar tace bazata ci Abincin ba tace a k'oshe take daga haka ta mik'e tay mata sai anjima Hajiyar nata mata Murmushi sosae take jin dad'in ganin Fatuu haka da ka kalleta yanzu kasan bata da damuwa ta dawo kamar da koma ta fi don har kumatu ta k'ara sai kace ba Student ba ga Fuskarta ta k'ara yin Smooth hakan yasa Farinta ya fito sosae, Fatuu na fitowa ta maida glasses d'inta a fuska dama da zata shiga d'akin Hajiyar ne ta cire, kamar taje d'akin Saude sai tay tunanin k'ilan ma bacci take hakan yasa ta nufi hanyar fita daga parlon, tana zuwa kopar Fita Haisam na shigowa har saura kad'an su bangaje juna da sauri Fatuu ta dawo baya ta tsaya ta kai idonta kan shi shima kallon nata yake yana sanye da farar shadda k'al anyi mata Fav d'inkin shi wato sen style ta amshe shi Sosae d'inkin ya bayyanar da kirar shi ta k'akkarfa kan shi ba hula sai sumar shi dake faman salk'i, wani fitinannan k'amshi ke tashi daga jikin shi, bin juna sukae da ido Fatuu ta kasa tanka mashi sai faman had'iyar abu take a yadda taga Fuskar shi ta dawo daidai ba kamar can baya ba da ta fad'a Saboda ciwon da yace mata yayi gashi yay wani irin fresh Fatar nan ta k'ara mulkewa to weather ba d'aya ba ga sajen da ya fara bari sumar ta d'an k'ara yawa a kwance lub amman bai barta ta taru sosae ba, wani kalan kallon k'urulla yake mata tun daga sama har k'asa ganin haka yasa ta kai hannu a hankali ta cire glass d'in fuskarta ta ruk'e a hannu kafin da k'yar Saboda tunda ta gan shi k'irjinta ke wani irin bugu ga wani abu da ya tsarga mata tun daga kanta har zuwa babban yatsan ta tace "Sannu da zuwa, anzo lafiya" bai bata amsa ba sai yay mata alamar su shiga da hannu ta ja gefe ya fara wucewa kafin ta bi bayanshi tana kallon yadda yake tafiyar shi mai cike da isa duk da ba don nuna isar yake yin ta ba haka yake tafiya dama, saman sofa 3 seater ya zauna Fatuu na kokarin zama kan 1 seater dake can gefe yay mata nuni da d'an can gefen shi alamar ta zo ta zauna, bayan ta zaunan shiru tay tana d'an kallon shi sai kuma ta kauda kai shima still idanun shi na akanta sai duk ta tsargu da kallon nata da yake tayi sanin shi ba mai kafe mutum da ido bane kamar yadda shima bai son a kafe shi da idanun,

"Ya School?" taji saukar cool voice d'in shi lokacin ta d'an duk'ar da kanta tana wasa da glass d'in hannunta, d'agowa tay suka had'a ido a hankali tace mashi Alhamdulillah ya jinjina kai sai kuma ya k'ara cewa "hope u'r concentrating?" Da sauri ta d'aga mashi kai alamar eh bai ce mata komae ba sai ita tace mashi ya Aunty Fanan ya amsa da tana lafiya tana gaisheta tace tana amsawa suka d'an k'ara yin shiru ta maida kanta k'asa kaman daga sama taji yace "baki tambayi ko ta haihu ba" da sauri ta kalleshi sai taga yay d'an murmushi d'an kwa6e fuska tay tace "ai in ta haihu zan ji ko" ta6e baki yay kawae wata shirun ta biyo baya sai take ganin kaman ya canza mata don a waya sosae yake sakar mata baki suyi Magana duk da a nan ma d'in wata Maganar sai ya d'an ja lokaci kafin yayi ta tunawa tayi da koda can ai baya Maganar sosae itace ke ja har yayi yasa bata kawo komae a ranta ba, wayarta ce da ke acikin Aljihun rigar uniform d'inta ta fara ringing ta kai hannu ta ciro sunan Fauzy ne ya bayyana akan Screen d'in tay picking bayan ta kara a kunne suka fara magana tambayarta tay ya taje gida ya su gwaggo ta amsa mata da lafiya lou suke itama ta tambayeta Aunty Mareeya daga baya suka yi sallama Fatun na jin da ita kad'ai ce da ta fad'i mata Ya Haisam yazo, bayan ta cire wayar ruk'eta tay a hannu tana d'an tatta6a ta jin shirun Haisam d'in yay yawa yasa ta juya ta kalleshi sai taga shima ya d'ago ya kalleta ranta ne ya bata wayar hannunta yake kallo hakan yasa lokaci guda ta kama kanta cikin d'an rawar murya tace "D....dama ba waccan wayar bace daka siya man, ita lokacin da zan tafi Yola ne sai mukai musanya na amshi ta Kawu Amadu Saboda naga shi zata fi mashi amfani a nan tunda mu bamu da network mai kyau to dana dawo aka fasa auren shine ya maido man sai nace ya barta nak'i amsa da ya matsa man, to da Baffana yazo maido kaya ne ya bani dubu d'ari duba hamsin Ya Abbas ne ya bani sai dubu hamsin shi ya bani yace in yi amfanin Makaranta to shi ya Abbas dama Saboda Auren ne ya bani su da nayi mashi maganar su daga baya sai yace ai ya riga ya bani ne kyauta shine na had'a da wayar Kawu Amadun da kud'in na bashi ya canza man wannan" ta k'arasa tana nuna mashi wayar shi kam tunda ta fara mashi Maganar bakinta kawae yake kallo har ta gama ganin tana mik'o mashi wayar ya d'an ta6e baki kawae had'i da d'an murmushin gefe don ya fahimci tayi tunanin wayar yake kallo yasa tay mashi dogon bayanin abunda bata sani ba shi yanzu yama manta wace irin wayace ya siya mata, ganin ya k'i amsa ya bita da ido kawae yasa ta d'an tura mashi baki ta janye wayar shi kuma gyara zama yay ya d'an kwantar da kan shi yana facing sama ganin haka yasa tace "Bazaka ci Abinci ba?" d'an jimm yay sai kuma ya jiyo da fuskar shi ya kalleta ta sake cewa "Hajiya tace baka ci Abincin ba ka fita" fuskar shi a sake ya d'age mata gira yace "Tambayarta kikae ne?" Da sauri ta girgiza mashi kai ta fad'i mashi yadda akai ta sani yay shiru kawae, ba wata yunwa yake ji ba amman jin ita bata ci ba yasa ya yunk'ura ya fara kokarin mik'ewa bayan ya tashi yace mata zaije Masallaci in ya dawo sai su ci daga haka ya nufi hanyar fita don da

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login