Showing 210001 words to 213000 words out of 512766 words
Chapter 71 - Asanadin Makwabtaka Book 3 Hausa Novel Complete
Unknown
27 Dec 2024
1539
maganata, yayi kyau ai ga sakamakon ki nan kin zata don kina mata cin kashi tana k'yale ki tsoron ki take ji, uhmm baki san wacece Fateema kuwa, kin ci sa'a tayi sanyi ne da sai tayi maki fiye da hakan don har hak'oran gaban ki sai ta cire maki su, yanzu sai ki wuce muje ki tattara kayan ki kibar man gida ni ban sauke wanda ba abun Arziki ya kawo shi ba a gidana, don ma yamma tayi da wllh bazaki kwana ba amman Allah ya kaimu gobe ko ba Jirgin Lagos Kya hau na Kano daga can ki wuce, muje!" Ta daka mata tsawa ta juya tu6i tu6i ta nufi k'opa dama skin tight ne a jikinta, kallon Fatuu Hajiya tay ta bata hak'uri tace duk abunda tayi mata asarar shi za'a maida mata tace ma Saude ta taimaka mata su gyaggyra wuraren tace to daga haka ta juya itama ta nufi k'opa, bayan fitar ta hannun Fatuu dake d'an gunji da gani kukan zuci take ta kama ta zaunar da ita kan kujera, itama zama tayi ta fara lallashin ta aikuwa kaman tana jira ta saka mata kuka a cikin kukan take fad'in miyasa ta fad'o ma Hajiya ba sunyi da ita bazata fad'i mata ba Sauden tace to ba gashi ta kawo k'arshen komai ba, lallashinta ta shiga yi tana kwantar mata da hankali kan ba wani abunda zai faru in sha Allah, saida taga ta saukko tayi shiru sannan tace taje ta cire uniform sai su gyara wuraren tace to ta mik'e.
Suna shiga cikin parlor Hajiya ta nuna mata hanyar Bedroom tace taje ta shirya kayanta, juyawa tay ta nufi hanyar ba tare da tace komai ba don ba alamun wasa a Fuskar Hajiyar, cikin parlon Hajiya ta wuce ta zaune inda take da kafin Saude tazo, Wayarta takai hannu ta d'auka ta shiga kiran Hajiya Maryam, bayan ta d'aga ta gaishe da ita Hajiyar tay banza bata amsa ba a kausashe tace "Ga yar Aiken ki nan zata dawo gobe in Allah ya kaimu, sannan a matsayina na Mahaifiyar ki in kika k'ara yin wani yunkuri don ki raba auren Fateema ko kuma ki cutar da ita BAN YAFE MAKI BA!!!" tana gama fad'in hakan ta katse Wayar.
Da daddare lokacin tuni su Fatuu sun gyara ko ina bayan tayo wanka ta shirya cikin kayan bacci tana niyyar fita parlor don taci Abinci har ta kai k'opa taji wayarta na ringing ta juyo ta nufo bakin gado inda take ajiye, zama tayi ta kai hannu ta dauka tay Jim tana kallon sunan Haisam dake kan screen d'in alamar shi ke kira, Kaman bazata d'aga ba saida ta kusa yankewa sannan ta d'aga ta kaita kunne, shiru tay ko sallama bata yi mashi ba shima kuma bai ce komai ba, sai d'an bayan wani lokaci taji ya tambayi tana lafiya, sai data amsa mashi sannan ta gaida shi shima bai amsa ba ta d'an ta6e baki, tambayar ta karatun ta yay tace mashi Alhamdulillah suka d'an yi shiru taji yace sun kusa fara Exams ne a tak'aice tace mashi eh, tambayar ta yay tana karatu har saida ta curo wayar ta kalli screen d'in da alama so take ta tabbatar shi d'in ne ya kira ta, bayan ta ce mashi eh tana yi shuru suka k'ara yi daga baya yay mata saida safe ya kashe, bin wayar tay da kallo a cikin ranta ta fara kokonton kodai yaga sak'on ne wata zuciyar ta bata inda ya gani ba iya haka zai mata ba tunda dama ai duk in ya kirata yana tambayar karatun ta, tana cikin cin Abincin a parlor Mino ta shigo tana sanye da doguwar rigar material ta yafo gyale saman kanta daga baya yayi tudun kitson shukun da akai mata ta nad'e da k'aton ribbom, tun bayan zuwan Farha zuwa gidan bai mata dad'i sai jefi jefi zaka ga tazo da rana dama kuma ta fara zuwa islamiyya da daddare ne kullum sai tazo, cikin parlon ta shiga Fatuu dake kallon ta da murmushi ta nuna mata gefen ta alamar tazo ta zauna, bayan ta zauna ta gaishe da ita ta amsa tace mata suci suka cigaba da ci tare, bayan sun gama Minon ta kwashe kayan ta kai Kitchen ta dawo Fatuu tasa ta d'aukko masu ruwa da lemu cikin freezer d'in dining, kallo suka d'an yi daga baya Fatuu ta kalli Minon tace mata in tana jin bacci taje Bedroom ta kwanta, har saida fuskarta ta kasa 6oye mamakin Maganar data ji tace mata ba anan suke kwana ba, yar dariya Fatun tay tace yau suna da yanci a gado zasu kwana da tsananin mamaki tace mata ina ita mai idanun magen yau bazata kwana ba, dariya taba Fatuu jin sunan data kira Farha dashi dukda da gaske idanun nata kaman na magen suke, nan Fatuu ta bata labarin abunda ya faru tace mata gobe ma zata tafi, zo kaga murna a wurin Mino harda mik'ewa da yin tsalle daga baya suka je suka kwanta.
Washe gari cikin nishad'i Fatuu ta tashi duk da tana d'an jin yar fargabar abun da zai iya zuwa ya dawo in Hajiya Maryam taji abunda ya faru, Bayan taje Makaranta Fauzy ta lura da yanayin ta ba kamar yadda ta saba ganinta ba da damuwa ta tambaye ta ko Ya Haisam d'in yaga sak'on sunyi Magana ne tace mata a'a itafa bata tunanin ya gani don ko jiya sunyi waya bata ga alama ba, nan ta kwashe abunda ya faru tsakaninta da Farha ta fad'i mata, cike da jin dad'i Fauzy tace amman ta burgeta wllh tuntuni abunda yakamata tayi kenan ai da duk ba'a zo nan bama. Lokacin da Fatuu ta dawo tuni Hajiya ta iza k'eyar Farha ta tafi.
_______________________
Ranar Asabar da wuri Mino ta tashi ta had'a Breakfast bayan ta gama ci ta tafi gida don zuwa islamiyya lokacin Fatuu nata shan bacci, sai wuraren k'arfe 10 ta tashi ba dan ta gaji da baccin ba sai don yunwa data isheta, bayan ta gama yin breakfast d'in toilet ta wuce tayo wanka tazo ta fara shiryawa, doguwar rigar material tasa ta yafa d'an gyalenta bayan ta d'auki wayarta ta nufi part d'in Hajiya, tare da ita sukai Abincin rana da Saude bayan an taso su Mino ta isketa nan, anan suka ci Abincin rana bayan sun gama suka zauna parlor harda Hajiya da Saude suna yin kallo, wuraren k'arfe ukku da rabi Mino tayi masu sallama zata je tay shirin islamiyya Fatuu ma ta mik'e tay masu sallama suka fito tare, part d'in su ta koma ta wuce toilet tayo wankan rana dama kusan kullum wanka ukku take yi k'aranci tayi biyu, bayan ta fito gaban mirror ta tsaya tana yin shafa ta k'ura ma kanta ido ita kanta tausayin kanta take game da irin rayuwar auren da take yi, bayan ta gama shafe shafen bata yi wata kwalliya ba iya powder sai lip glow ta shafa, wata fitted gown ta Atamfa ta fiddo ta saka, bayan ta gama shiryawa ta shimfid'a qq abun salla ta d'aukko Hijab ta kabbara sallar la'asar, lokacin da ta gama zaune tay a wurin ta jingina da gado tay shiru hakanan take jin ta wani iri, ta d'an d'auki lokaci a haka daga baya ta mik'e ta d'auke abun sallar ta mayar inda yake ta cire Hijab d'in itama ta linke, saman gado ta haye ta zauna ta fara latsa wayarta can ta aje wayar ta mik'e ta d'aukko jakarta ta fiddo littafi don tayi karatu, shima karatun ji tay duk bata jin dad'in shi ta maida littafin cikin jakar ta zame ta kwanta ta runtse ido tamkar mai yin bacci saidae tunane tunane kawai take, bata dad'e da kwanciya ba sosae lokacin wurin karfe biyar da rabi wayarta ta fara yin ringing, bud'e ido tay kafin ta juyo ta kai hannu gefenta ta d'auka, ganin Hajiya ce mai kiran nata yasa tay saurin tashi zaune ta jingina da headboard,picking tay tare da yin sallama on the other hand Hajiyar ta amsa ta tambayi tana gida ne da sauri ta amsa mata da eh tana nan, ce mata tayi tazo part d'in ta to yanzu tace to, saukkowa tayi daga saman gadon ta nufi wardrobe ta fiddo d'an madaidaicin gyale da ba zai rufe bayanta ba gaba d'aya ta yafa, a cikin Corridor ta d'aukko takalma Flat shoe da suka hau da kayan jikinta ta wuce, Wata irin Fargaba take ji tun bayan data fito, ba yau Hajiya ta fara kiran ta ba amman wannan kiran duk sai take jin gabanta nata d'an fad'uwa, tana sanya kanta cikin parlon gabanta yay wani irin bugu mai k'arfi ba shiri taja ta tsaya, Zuba ma Mutumin da idanunta ke ganin mata ido tay wanda ko a nisan da ya ninninka wannan ta hango shi kallo d'aya zata gane shi, sosae tay Al'ajabin ganin su don bata ta6a zaton zata gan su ba, Haisam ne zaune akan 3 seater jikinshi sanye da Suit bak'ak'e saidai ya cire ta saman sai farar ciki mai santsi da dogon hannu sai bak'in wandon, daga gefen shi Fanan ce itama tana sanye da bakar doguwar riga jallabiya mai kayataccen adon stones gyalen rigar bai a saman kanta hakan ya bayyanar da brown sumar ta dake fake a tsakiya, gaba d'ayan su akan kujera d'aya suke zaune Haisam ya d'an zamo ta yadda ya jingina sosae da kujerar idon shi akan Tv ita kuma Fanan tana daga gefen shi itama ta jingina bayanta da jikin kujerar hannun ta d'aya dafe da forehead d'inta Hajiya har magana tay mata kan taje ta kwanta amman tace a'a sai an kirawo Zarah, sun d'an jima da zuwa don Fatuu bata dad'e da barin part d'in ba lokacin data koma tana toilet tana yin wanka suka iso, wani irin bugu da k'arfi da k'arfi zuciyar Fatuu ta hau yi ba kamar data ga Fanan ji tay kaman ta juya tunda ba wanda ya ganta ta koma, har zata juyan zuciyarta ta raya mata kenan k'in amsa kiran Hajiya zata yi hakan yasa ta dakata, Kamar Haisam yaji ajikin shi ana kallon shi a wani irin slow ya juyo da Fuskar shi ya kalli direction d'in da Fatun take nan take idanunsu suka shiga cikin na juna, zuba mata ido yay yana bin ta da kallo tun daga samanta har k'asa kafin ya tsaida su cikin nata, Hajiya ce ta kalle shi da niyyar yi mashi magana da yake Facing d'in su take a zaune ganin inda ya zuba ma ido yasa ta waiga ta kalli wurin, ganin Fatuu tsaye a wurin yasa ta d'an d'aga murya tace "Fateema ki shigo mana" har saida Fatun ta d'an firgita don bata san ta ganta ba, Fanan na jin Hajiya ta furta haka da wani irin sauri ta janye hannunta daga kan goshinta ta juya ta kalli inda Fatun take, gaba d'aya dabarbarcewa Fatun tay Hajiya ce ta k'ara mata magana kan ta shigo ta nufo cikin parlon idon ta a zare tana tafiya a d'arare, a bakin kujerun ta k'ara ja ta tsaya aikuwa kamar Fanan na jiran ta k'araso ta mik'e ta nufeta fuskar nan ba d'igon annuri, mik'ewar da tayi ta bayyana irin rigar jikinta mai bin shape d'in jikin mutum ce tayi kyau over, wani irin harbawa zuciyar Fatuu ke yi numfashinta ta fara kokowar fitar dashi, da za'a auna bp d'in ta a lokacin to kuwa daba makawa za'a ga ya hau, a gabanta ta tsaya daddad'an k'amshin jikin ta ya baza wurin, kyakkyawar Fuskarta a tamke take kallon fuskar Fatuun nan da nan jikinta ya hau 6ari ta hau kikkafta idanu, jin sun fara tara k'walla suna niyyar zubo mata da sauri ta sunkuyar da kanta k'asa, A kausashe Fanan ta kira Sunanta "ZARAHHH!!!" murya na rawa ta amsa mata, ce mata tayi ta d'ago ta kalle ta, da k'yar ta d'ago ruwan hawaye sun lullu6e k'wayar idon ta,
"Zaraah u married my Husband!" Fanan ta fad'a muryarta har wani vibration take, shiru Fatuu tayi tana gunji kiris ya rage ta saki kukan, cigaba Fanan tay "na d'auke ki matsayin my own Sister Zaraah, amman shine kikai man haka, kin san yadda nike son ki na damu dake amman duk da haka kika iya auran man Miji?" Yanayin muryar ta tamkar itama zata saka kukan idanunta har sun canza, girgiza kai Fatuu ta fara yi fuska a yamutse da k'yar ta bud'e baki cikin trembling voice tace "D...on Allah Aunty Fanan kiyi hakuri wllh nima ban san ya Aure ni ba....kin ji na rantse maki..." Kuka ne yaci k'arfinta ta sadda kanta k'asa tana cigaba da yi, d'an ta6e baki Fanan tayi tace "But u loved him Zarah, Ur Message said it all!" d'agowa Fatun tay ta kalleta ta kasa cewa komai don ta gane sun ga sak'on da Fauzy ta tura,
"Kinsan abunda ke tsakani na dashi tun farko amman kika fara son shi kuma kinsan ya Aure ni amman baki daina son na shi ba Saboda cin Amana!" Sautin kukan Fatun ne ya k'aru tace "Don Allah ki yi hak'uri Aunty Fanan wllh kinji na rantse maki ni bansan abunda ke tsakanin ku ba saida kika zo, bai ta6a fad'i man ke zai Aura ba kuma gashi can ki tambaye shi" yamutsa fuska tay "daga baya da kika sanin miyasa kika cigaba da son shi!" A fad'ace take Maganar, shiru tay ta maida idonta k'asa tana gunji, da d'an tsawa tace ta bata amsa miyasa ta ci gaba da son shi,
"Kiyi hakuri nasan nayi maki ba daidai ba amman na daina son shi" d'age gira tay tace shine kuma ta turo mashi sak'o tana bayyana mashi son da take mashi, girgiza kai Fatun tay tace "Yanzu na daina son shi wllh kin ji na rantse maki" sai lokacin Fanan d'in ta d'an saki fuska tace "Good! haka yakamata" tana furta hakan ta juya tana tafiya cike da isa ta nufi wurin Haisam da har lokacin yana zaune a yadda yake, a gaban shi ta tsaya ta mik'a mashi hannunta dake sanye da zoben diamond, still yay yana kallonta ta wani yamutsa mashi Fuska, hannu ya kai gefen shi ya d'aukko wata takarda plain sheet dake nannad'e ya mik'a mata, juyawa tay ta koma wurin Fatun, a gabanta ta tsaya yanayin Fuskarta kamar zata yi murmushi tace "am sorry Zaraah we do not welcome u in our Fam, bazan iya yin kishi dake ba, not only u da Kowacce mace ma because yayi man Alk'awarin zamu rayu tare mu biyu until Death do us part" tunda ta fara Maganar Fatuu ke jinjina mata kai har ta gama ta mik'o mata takardar hannunta, tana amsa ta juya har cikin ranta taji dad'in hakan tana fara tafiya taji Muryar Hajiya ta kira Sunanta, juyawa tay ta kalleta da kai tay mata alamar tazo, daga gefenta ta tsaya da alamun damuwa akan Fuskarta ta fara Magana "Kiyi Hak'uri Fateema ban so hakan ta faru ba saidae gaba d'aya sun nuna basu son Auren ban so ki cutu ne shiyasa na goyi bayan ya sallame ki kawai, yanzu kije ki kai ma Dije ina nan zuwa" kai Fatun ta d'aga mata idanunta sharkaf da k'walla, har zata juya Hajiya tace mata ta bud'e ta fad'i mata saki nawa yayi mata Saboda sheda, hannunta sai kakkarwa yake ta fara warware takardar.............. ALHAMDULILLAH, Ba don na gama ba sai don nazo inda nike son in tsaya😀
_Littafin A Sanadin Makwabtaka part 2 Naira 300 ne za'a tura ma Mutum har part 1 ga mai so zai turo kudin ta wannan Account din, 1509618776, Zainab Bature Access Bank, za'a turo shedar biya ta wad'annan nos din 09013804524 ko 0816985626
*ASM 073*
~_*✊💋BOSS LADIES WRITERS💋✊*_~
*DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI*
.......bayan ta gama warware takardar, zuba ma content d'in ciki ido tay tana Karantawa, lokacin data gama a matuk'ar razane ta d'ago idanunta a waje ta kalli Hajiyar kawae sai taga tana mata dariya, kai idon ta tay kan Haisam shima taga yayi mata d'an guntun murmushi tare da lumshe ido, rud'ewa tay ta kasa Fahimtar komai hakan yasa ta k'ara maida idon ta kan takardar ta k'ara karanta abunda aka rubuta a ciki kamar haka,
_WE ARE SO HAPPY TO WELCOME YOU INTO OUR FAMILY ZARAH_
_It's such a joy to be with u, We hope your presence will brightens up our days. You're a Wonderful person Zarah, we are so lucky to know u._
*We look forward to all the Wonderful things you'll bring to our lives. We love u so much Zaraah.*
Lokacin data gama d'agowa
tay ta waro idanu ta kalli Fanan dake tsaye a gabanta har lokacin kawai sai gani tay itama tay mata d'an murmushi, gaba d'aya sun rud'ata har Fuskarta ta bayyanar da hakan, d'age mata gira Fanan tayi Calmly ta furta "Nima na rama halin da Message d'in ki ya sani Zaraah" ta6e baki ta fara kawae sai ta fashe da Kuka Fanan ta kai hannu ta rungumo ta a jikinta a hankali take furta mata is okey, d'agota tayi bayan wani lokaci ta kama hannunta suka nufi ciki har lokacin Fatuu kuka take tasa gefen gyalenta tana ta goge k'wallan dake zubo mata, Kujerar data taso ta nufa da ita ta Zaunar da ita itama ta zauna a gefenta ta yadda suka saka Fatun a tsakiya har lokacin tanata sharar k'walla da gyalenta, Hannu Fanan ta kai ta dafa Shoulder d'inta tana ce mata ya isa haka kada tayi ciwon kai tayi mata wasa ne, Hajiya itama ta fara bata hak'uri tace mata sune suka shirya mata haka ita ba ruwan ta, daina yin kukan tayi ta sadda kanta k'asa har lokacin gabanta na d'an fad'uwa ganin komai take kamar a Mafarki don bata ta6a zaton haka daga Fanan d'in ba, a hankali ta d'an juyar da kanta ta saci kallon Haisam dake gefenta karaf suka had'a ido dashi ya kafeta da idanun shi dake a d'an lumshe da sauri ta maida kanta k'asa, Hajiya ce tayi d'an gyaran murya tace masu suyi ma