Showing 468001 words to 471000 words out of 512766 words

Chapter 157 - Asanadin Makwabtaka Book 3 Hausa Novel Complete

Unknown   

27 Dec 2024

1627

yanzu ba yadda za'ai in yi aure saboda ban daɗe da fara yin karatu ba kinga ba aiki nike ba da zan iya auren ki" da yanayin damuwa yayi Maganar itama fuskarta a yamutse tace mashi ba wani bambancin dake tsakanin su tunda ai duk ɗaya suke a wurin Allah kuma ai ba dole sai ana aiki za'ayi aure ba tunda yana yin business lafiya lou zasu iya yin aure sai a faɗaɗa business ɗin, ganin dai da gaske take yasa shi bata haƙuri yace gara su ci gaba da ƙawancensu su bar Maganar soyayya da aure don abu ne da shi yasan ba mai yuwuwa bane a tsakanin su ba lalle gaba ɗaya a amince masu ba ba kamar shi za'a ga yayi ƙarami da yin aure, idanunta ne suka ciko da ƙwalla cikin karyayyar murya tace yanzu duk da yana da ikon cire mata damuwa shine zai watsa mata ƙasa a ido tunda take dashi tana jin wannan ce buƙata ta farko data zo mashi da ita amman shine bazai taimaketa ba ya amince mata kuma da yake cewa baza'a amince masu ba sai dai in basu nuna suna son junansu ba sannan Maganar yayi ƙarami ai tasan shekarunshi yana da shekaru 26 ɗin ne zai ce bai isa aure ba wasu ma basu kai shekarun shi ba suke yin aure wani ma Matar ta girme shi suke yin auren balle su da ya girmeta, duk tabi ta ruɗa shi ganin yadda take magana tana yin ƙwalla sai bata haƙuri yake tace ita ba wannan take so ba kawae ya amince mata don in yaƙi za'a mata auren dole ne kuma ita shi take so in bai aureta ba to zata mutu kowa ya huta, zo kaga ido a wurin ɗan fillo yaji zancen za'a mutu saboda shi a razane ya shiga roƙonta kan ta daina cewa haka yanzu ta ɗan bashi lokaci zai yi shawara tunda yanzu tazo mashi da Maganar yana buƙatar yayi shawara idanunta sharkaf da ƙwalla tace har tsawon wane lokaci zai yi shawarar yace bada daɗewa ba zai kirata tace shikenan tana jiran shi, tana yanke kiran hannun shi har rawa yake wurin kiran Fatuu saida ta yanke sai gashi ta kira suka gaisa ta tambayi mutanen gidan da karatun shi ya amsa mata tana jin yanayin muryarshi ta tambayeshi ya akai ne da damuwa yace mata akwae matsala ne da sauri ta tambayi miya faru nan ya shiga faɗi mata yadda sukai da Farha ita kanta ta jinjina abun tace mashi to ita dae a shawarce ya rabu da ita don ta tabbatar ba abu bane mai yuwuwa ƙarshenta rayuka ne zasu 6aci ba kamar yanzu da Mamanta take babba a da ma ba son talaka suke ba balle yanzu ita kanta Farhar don ta nuna ta canza ne amman ba ƙaunar talaka take ba, nan ta kwashe komai daya ta6a shiga tsakanin su ta faɗi mashi tace koda ace auren ya yuwu a tsakaninsu to bata tunanin zata mutunta yan'uwansu don ance mai hali baya barin halin shi don haka ya bata haƙuri kawae kada wani tsara kalamenta su ruɗe shi gara taga bai mata daidai ba akan abunda zai je ya dawo ya amsa mata da to sukai sallama, zaune yay jugum bayan sun gama yin wayar gaba ɗaya ya rasa mike mashi daɗi Maganar Fatuu ta kashe mashi jiki sosae, suna gama yin wayar Gwaggo Fatuu ta kira bayan sun gaisa ta kwashe komai ta faɗi mata itama sosae ta jinjina abun ta kuma goyi bayan abunda Fatun tace mashi tace gara haka zama lafiya yafi zama ɗan sarki, Kamalu na zaunen har aka kira Magrib ya tashi don yaje masallaci jikinshi duk yayi sanyi lakwas, tun akan hanyarsu ta zuwa Kawu Amadu ya lura da kamar akwae abunda ke damunshi ya tambayeshi amman sai yace mashi ba komai ya gaji ne Amadun yace mashi halan kuma yayi baccin yamma ya bashi amsa da eh yace shi yasa, bayan an gama sallar sun dawo suna niyyar tsayawa shago Gwaggo ta kira Amadu ta tambayi sun dawo daga salla ne yace mata eh gasu nan sun tsaya shago tace to su shigo shida Kamalun tana son ganin su yace to, a falonta suka isketa zaune suma duk suka nemi wuri suka zauna cikin kwantar da murya ta fara magana idonta akan Kamalu tace taji yadda sukai da Farha a wurin Fatuu tana son ya sani ba wai ana ƙoƙarin hana shi yin soyayya da ita bane kawae ana gudun matsala ne don duk abunda Fatun ta faɗa mashi gaskiya ne ya faru don haka kamar yadda sukai da ita ya bata haƙuri shi ya fi don ko ya amince mata mawuyacin abu ne a barta ta aure shi, kai Kamalun ya jinjina a sanyaye yace to zai yi yadda suka ce da alamun rashin fahimta kawu Amadu ya tambayi mike faruwa ne tsakaninshi da Farhar Gwaggo ta kwashe komai ta faɗi mashi, shima jinjina abun yay yace ina ai ba abu bane mai yuwuwa ma shi dama tunda yaga take takenta yasan da wuya bata ce tana son shi ba to gara ya bata haƙuri kawae don ko kowa ya amince mamarta yasan bazata ta6a yarda wai ta aure shi ba an auri mijin ɗiyarta tayi ma mutane tijara ina ga kuma yanzu ace ɗiyar tata za'a aura ai sai yaƙi tsakaninsu balle yanzu da ta zama wata a ƙasa ita kanta Farhar ai ba kanwar lasa bace kawai dai don suna shiri ne yasa yake ganin kamar bata da matsala, ɗan murmushi Gwaggo tayi tace ƙilan da gaske ta canza tunda tun kafin tasan Kamalun ta canza sai ai mata kyakkyawan zato Amadun yace to ko dai ita lafiya lou wannan Maman tata ba lafiya lou ba, haka suka dingi tattaunawa daga baya suka fito suka koma shago, bayan sallar isha yana shago sai ga kiran Farha saida ya fito daga shagon ya nufi gate ɗin shiga gida sannan yay picking, bayan ya ɗauka tace yay keeping nata tana ta jira kuma yace bada daɗewa ba zai kirata, haƙuri ya bata yace dama yana niyyar kiran nata bai gidane amman gashi nan zai je ɗaki sai suyi magana tace Ok, bayan ya shiga cikin ɗakin da yake zaune ya nufi katifa ya zauna saida yay ƙoƙarin daidaita natsuwarshi sannan ya fara mata magana ya nuna mata yayi magana da yan'uwan shi kanta gaskiya duk sun nuna ba abu bane da zai yuwu don haka yana bata haƙuri ba wai don bai sonta ba sai don ba'a goyi baya ba,

"Nasan saboda abubuwan da suka ta6a faruwa tsakani na da Sister ɗinka ne yasa zasu ƙi goyon bayan ka aure ne amman ai i'm a changed person now, na canza tun ba yanzu ba kuma nayi dana sanin komai bazan sake ba, yanzu nasan da mai kuɗi da wanda baya dashi duk ɗaya ne at least they should give us chance zan tabbatar masu da na canza gaba ɗaya bazan basu matsala ba" cikin breaking voice take Maganar gaba ɗaya tausayinta ya kama shi don daga yadda take yin Maganar ya tabbatar da gaske tana son shi kuma yaji ya amince da cewa ta canza ɗin, jin yayi shiru tace mashi in shi bai son tane to zata haƙura amman ya sani tana ƙaunarshi kuma ta fara son shi ne tunda ta fara ganinshi wannan dalilin ne yasa suka shaƙu bata gane hakan bane sai yanzu da sauri yace mata a'a wllh shima yanzu yaji yana son ta to amman kowa gani yake hakan ba mai yuwuwa bane za'a iya samun matsala don ba lalle iyayenta su Amince ba, katse shi tayi tace ita buƙatarta itace shima ya sota ya kuma amince zai aureta Maganar iyayenta zata yi duk yadda zata yi in ma basu amince ba tasa su amince yace mata shikenan shima yana sonta kuma zai je yanzu suyi magana da gwaggon shi zai nuna mata ta canza yasan zata amince tunda tana da sauƙin kai tace Ok tare da yi mashi godiya yana murmushi yace to ta daina yin kuka bai jin daɗin hakan ace tana kuka saboda shi, a hankali tace ai ba kuka take ba yace shida ya santa sosae ai daya ji muryarta zai gane tace to ta bari sai kuma ta ƙara cewa ai duk laifin shi ne da son shi yay mata babban kamu yay yar dariya yace to ai shidai yasan abota suke bai san ya akai abun ya koma haka ba nan ta shiga bashi labarin bayan ta dawo gida gaba ɗaya ta shiga damuwar rashin shi a kusa da ita kullum cikin tunaninshi take nan ta gane son shi take yace to ai shima duk hakan ya faru dashi bayan tafiyarta ko abinci bai mashi daɗi duk sai ya rinƙa jin shi kamar mara lafiya har Uncle ɗin shi saida ya gane saboda tafiyarta ne ya shiga damuwa haka a School ma Friends ɗinshi suna ta tambayarshi mike damunshi koda ya faɗi masu saboda tafiyarta ne sai suka ce sonta yake shi kuma ya ƙaryata su yace kawai abota suke, tana murmushi tace duk sun faɗa son juna ba tare da sun sani ba yace hakane, daga haka suka shiga shan soyayya Farha ba wasa dama gata ruwa biyu ta wani bangaren a wurinta ba abun kunya bane don ta riga cewa tana son shi nan fa ta shiga yi mashi kalamai harda faɗi mashi irin soyayyar da zasu sha in suka zama married couple, shima Kamalun ba laifi ya shigo birni ya iya kalaman soyayya masu daɗi, sun ɗan ɗauki lokaci suna wayar kafin Farhar tace mashi ga Brother ɗinta yazo zata taimaka mashi yayi wani Assignment Kamalun yace Ok sukai sallama cike da nuna ƙaunar juna, bayan gama wayar zaune Kamal yay yanata sakin murmushi wani irin nashaɗi yake ji sai yanzu yake jin son Farhar sosae na shigarshi amman ada bai ta6a tunanin jin yana sonta ba don gani yake tafi ƙarfin shi ta ko ina, yana haka ya tuna da kalaman su Gwaggo zuciyar shi ta bashi yaje ya faɗi ma Gwaggon yadda sukai da ita da sauri ya miƙe ya nufi hanyar fita, bayan ya fito part ɗin Gwaggon ya nufa lokacin daya shiga a parlor ya isketa zaune tana kallo ruƙe da Abdallah yaron Amadu yana bacci, ciki ya shiga gabanshi na ɗan faɗuwa saboda fargabar kada ta ƙi amincewa da zancen Farhar, bayan ya zauna yay mata sannu da fulatanci idonta akan shi ta amsa mashi daga haka ya sunkuyar da kai ya rasa ta yadda zai sanar mata, tana ɗan murmushi da fullanci tace mashi ya akai ne ya ɗago cikin kama kai yace dama sunyi magana da Farhar ne Gwaggon tace to ya sukai da ita nan ya faɗi mata abunda tace na ta canza yanzu tasan mai kuɗi da talaka duk ɗaya ne bazata bada matsala ba in aka bata dama za'a tabbatar da haka, yar dariya Gwaggo tay tana kallon shi tace to ai su dama ba matsalarta suke hange ba ta iyayenta da za'a iya samu ba kamar Mahaifiyarta, da sauri ya tari numfashin Gwaggon yace suma tace ita tasan yadda zata sa su amince Gwaggon tay shiru kamar mai nazarin wani abu can ta tambayeshi yana Son Farhar ne da sauri ya sunkuyar da kai alamar kunya tace ita ya bata amsa ba wani sunkuyar da kai ba a yadda yake ya ɗaga mata kai alamar eh yana sonta tay ɗan jimm tanata kallon shi bayan ɗan wani lokaci tace ya tashi yaje zuwa da safe zata neme shi yace to tare da miƙewa yay mata saida safe ta amsa da Allah ya basu Alkhairi, bayan tafiyar shi tunani ta shiga yi a cikin ranta ita dai sam bata son Al'amarin ya haifar da fitina ƙarshe ta yanke zuwa ta sanar ma Hajiya kawai.

Washe gari ya kama Juma'a da safe wurin ƙarfe sha ɗaya da rabi Gwaggo ta nufi gidan Hajiya sai da ta tsaya a bakin gate suka gaisa da Securities wanda yanzu sun kai su Biyar don bayan Senator ya zama shugaban ƙasa an ƙaro wasu, bayan ta shiga a parlor bangaren Hajiyar ta isketa zaune tana ruƙe da ɗiyar Tk tana mata wasa da abubuwan wasa, da murmushi Gwaggo ta ƙarasa cikin parlon Hajiya ta ɗago tana mata maraba bayan ta zauna kan kujera suka gaisa,

"Ana wasa da ƙawa ne"

Gwaggo ta faɗa tana yar dariya Hajiyar tace wai ta hana uwar yin aiki ne shine ta riƙe mata ita take mata wayo duk su kai yar dariya, shiru Gwaggo tayi ta rasa ta ina zata fara yi mata Maganar data kawo ta don sai kuma taji tana jin nauyi,

"Ya akai Amaryar Mani kinyi shiru koda wani abune?" Hajiya ta faɗa idonta akan Gwaggon tana murmushi itama murmushin take mata tace eh,

"sai kuma ki kama kiyi shiru koda yake mufa yanzu surukai ne ko, to ina jin ki ya akai ne Allah yasa in ji Alkhairi" yar dariya Gwaggo tayi jin abunda Hajiyar tace na su surukai ne, a nutse ta fara faɗi mata tiryan tiryan yadda Kamal yay da Farha Hajiya ta ɗan ta6e baki tana murmushi take sauraronta har ta gama,

"To Ke Dije Matar Mani ina ruwan ki da shiga harkar yara irin haka, ta bayyana mashi tana son shi in shima yana sonta sai kiyi masu fatan alkhairi ba shikenan ba" shiru Gwaggo ta ɗanyi kafin tace "Dama ni kawai ina gudun abunda zaije ya dawo ne shiyasa",

"Mi zai je ya dawon?" ta tambaya ta kafeta da ido da ƙyar Gwaggon tace mata can bangaren iyayen Farhar kar azo hakan bai masu daɗi ba ƙarshe abun yazo ya haifar da bacin rai,

"Uhm, to ke kin isa ki hana faruwar wani abun ne, yaran yanzu ana hanasu abunda suke so ne, kina iya kiga ai kin hanashi yin tarayya da ita su zagaye can suna soyayyarsu ƙarshe kuma abunda kike gudun yazo ya faru don haka ki rabu dasu ayi masu fatan alkhairi ba abunda zai faru face abunda Ubangiji ya ƙaddaro zai faru", kai Gwaggo ta jinjina tace hakane Allah ya tabbatar da alkhairi Hajiyar ta amsa da Amin tace shikenan, Gwaggo har taji ta ɗan samu natsuwa bayan wani lokaci tayi mata sallama ta tafi. A ranar Minister Hajiya Maryam ta sauka Lagos dama duk Friday take dawowa sai ranar Lahadi da yamma ta koma a yadda suka tsara da maigidan nata wani lokacin shi zaije can Abujar tare da yara, sosae sukai murnar zuwan Momyn nasu tayi shiga ta alfarma ada ma tayi ado balle yanzu da suke da ƙasa, bayan an gama murnar zuwan nata Bedroom ɗin Daddyn su ta wuce dama shiya ɗaukkota daga Airport, da daddare tare suka ci abinci cikin nishaɗi bayan sun gama suka koma falo nan ta shiga tambayar yaran nata buƙatunsu kowa na faɗi da aka zo kan Farha yamutsa fuska tay tace ita bata da wata buƙata kawai so take su kasance tare koda yaushe don kula da yaran nan na bata wahala Hajiya Maryam ɗin na dariya tace to wace wahala take sha abunda akwae masu aiki ba girki take masu ba ba wanki da guga take masu ba haka ba shara take ba Farhar tace duk da haka basu barin kunnuwanta su huta Hajiya Maryam ɗin tace to ta ɗan ƙara haƙuri bada jimawa ba zasu koma Abuja baki ɗaya sai suci gaba da yin School acan nan kuma da Weekend ko lokacin hutu sai su rinƙa zuwa nan fa su Abraham suka shiga yin murna, sun ɗan dauki lokaci a falon kafin sukai ma juna saida safe kowa ya wuce part ɗin shi itama suka wuce tare da Dr Mohammad part ɗin shi suna saƙale da hannun juna, Washe gari Asabar tun da wuri aka kai yaran gidan islamiyya ya rage sai Farha don ita tunda tayi sauka ta daina zuwa, wuraren ƙarfe goma suka zauna yin breakfast duk sunyi wanka sai ƙamshi suke, Farha ce ta fara tashi daga kujerarta alamar ta ƙoshi Dad ɗinta yace ta jira shi a parlor zasu yi magana tace Ok, a tare suka gama da Hajiya Maryam ɗin suka nufi parlon duk suka zazzauna tun ma kafin Dad ɗin yayi magana ta yanke a ranta Maganar Emran zai mata, bayan sun zauna a nutse da turanci Dad ɗin nata ya fara mata magana yace mike faruwa ne tsakaninsu da Emran ya kirashi cikin tashin hankali yace tace bazata aure shi ba gaba ɗaya ya tada ma iyayen shi hankali suma sun kira shi kan Maganar, da alamun mamaki Hajiya Maryam ta maimaita bazata aure shi ba Dad ɗin yace haka Emran ɗin yace mashi tace, kallon Farha tayi tace miya faru tsakanin su ne da zata ce haka ta fara yamutsa fuska ta kasa yin magana Dad ɗinta yace kar taji komai ta faɗi masu in wani ƙwaƙƙwaran dalili ne zasu goya mata baya, muryarta kaman zata yi kuka tace ita ta daina son shi gaskiya ta samu wani wanda take so shi zata aura, a tare iyayen nata suka kalli juna alamar mamaki,

"Yaushe kika samu wanin da mu bamu sani ba?" Hajiya Maryam ta tambaya Farhar ta shiga motsa baki kafin tace sun ɗan daɗe tare sun fi shekara, tambayarta Dad ɗinsu yay waye shi kuma a ina yake saida cikinta ya ɗan kaɗa fargabar faɗin ko waye ta kamata ba kowa take tsoron yaji ko waye ba face Hajiya Maryam don inda Dad ɗinta ne kaɗai bazata ji komai ba zata faɗi mashi, Mom ɗin su ce ta ɗan ɗaga murya tace ita suke saurare suna da abun yi, da ƙyar ta tattaro ƙwarin gwuiwa idonta akan Dad ɗinsu tace a Katsina y
ake Yayan abokiyar zaman Sis Fanan ne, ɗan waro ido Hajiya Maryam tay tace wace abokiyar zaman Fanan ɗin badai wannan dangin shanun take nufi ba cikin tura baki Farhar tace ita, wata gigitacciyar tsawa data daka mata sai da suka tsorata su duka hada

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login