Showing 399001 words to 402000 words out of 512766 words

Chapter 134 - Asanadin Makwabtaka Book 3 Hausa Novel Complete

Unknown   

27 Dec 2024

1625

mamaki sosae lokacin da naga hotunan don ina gani na gane itace amman don in tabbatar sai na kira wani abokina d'an layin su shine ya tabbatar man yace suma duk basu san da abun ba kawai dai suna ganin ana yin manyan bak'i a gidan sannan kuma yanzu haka ma an canza ma gidan nasu suffa ya zama had'addan ginin benen gaske gaba d'aya dai komai cikin k'ank'anin lokaci ya faru har ma hoton gidan nasu ya turo man bari ka gan shi" yana fad'in hakan ya katse kiran don ya tura mashi hoton, komawa Mujaheed d'in yay cikin Facebook ya shiga sake kallon hotunan gaban shi na mashi wani irin bugu, sai yanzu ya tabbatar da ita d'in ce yana haka Usman ya turo mashi hoton gidan su Fauzy, Safa da Marwa ya shiga yi wayar shi ruk'e a hannunshi da k'yar yake fitar da numfashin shi da yaji yana neman k'wace mashi k'arshe ma sai yay wurgi da wayar tashi ya durk'ushe k'asa saman gwiwowin shi wasu irin k'walla masu zafi suka shiga zubo mashi..........


Washe gari Friday ya kama saura sati biyu cuf d'aurin auren Fauzy da Sameer, a ranar ne aka tura wasu daga cikin akwatunan lefen Fauzy set biyu guda goma cuf wai nan kayan da zata ci biki ne sauran sai an kaita kamar dai yadda Hajiya Zainab ta fad'a ma Aunty Mareeya harda invitation cards masu kyaun gaske aka had'o, akwatuna ne ubansu su kan su abun kallo ne kai da gani ba sai an fad'a maka ba kasan zasu yi kud'i saima da aka bud'e kayan ciki Naira ta sha kashin gaske don kaya ne na gani na fad'a kuma duk a d'inke suke a ciki harda wanda Fauzy ta saka suka yi hotuna, kowa ya gani cikin yan uwansu cewa yake yo iya wannan ma ai lefe ne na gaske, lokacin da aka tura ma su Aunty Mareeya kayan zo kaga murna ita kanta fad'i take yanzun duk wannan uban kayan har sai an k'ara wasu, itama Fauzy har ta kasa rufe bakinta don farinciki koda ta tura ma Fatuu ita kanta ta yaba sosae anan take tambayarta sai yaushe zata tafi Funtua d'in ne tace mata sai zuwa jibi Lahadi akwae shirye shiryen da Aunty take son k'arasawa, itama Fauzy ta tambayi Fatun sai yaushe zata je can tace mata sai satin bikin ana saura kwana biyu aikuwa Fauzy tace ita dai bata yarda ba gaskiya inama laifin ana saura sati d'aya ta taho, dariya Fatuu ta saka tace wannan sai kace ita ce dai Amaryar inama laifin ana saura kwana biyun Fauzy ta kafe kan ita dai yayi kad'an Fatun tace mata gaskiya daga haka bazata k'ara ba don Lokacin Hubby dinta ya dawo taya zata taho ta barshi, dariya Fauzy ta saka tace ai sai ta fito tayi mata bayani ba taita yan kame kame ba duk suka yi Dariya. Ranar Lahadi tunda safe su Aunty suka d'auki hanyar Funtua a cikin Motar Fauzy driver d'in da ya koya mata Motar ne zai kai su. Alhamdulillah sun isa lafiya anata murnar ganin su ba kamar Fauzy Amarya sai faman nan nan da ita ake, sosae sukai mamakin yadda aka canza ma gidansu fasali duk da sun gani a waya amman yanzu da suka ganshi a zahiri sai suka fi ganin kyaun shi ya zama gidan yan gayu sosae wanda kaf layin su da duk ma rukunin su ba gida tamkar shi kai a yanzu ma yana d'aya daga cikin jerin gidaje masu kyau in za'a lissafa a garin, shirye shiryen hidima sun kan kama sosae bayan zuwan nasu duk da ba wani abu da Fauzyn zata yi anan Funtua Sameer har magana yayi mata kan ko zasu yi wani event tace mashi a'a abar wanda su zasu yi kawai wato Dinner bayan an kaita sai kuma Walima wadda za'a yi matsayin bud'ar kai. Ranar Laraba Haisam ya iso yana dawowa washe gari suka tafi Abuja da Fatuu harda Hajiya acan ma dai duk shirye shiryen bikin aketa yi, Ana saura kwana biyu bikin ya kama ranar laraba kamar yadda Fatuu tace Haisam yasa driver ya tafi da ita harda Jidderh, Bayan sun isa Fauzy tayi murna da ganin su sosae haka Aunty Mareeya da sauran yan gidan sai faman nan nan ake da su anata nuna Fatuu ana cewa itace k'awar Fauzy wadda zata auri d'an uwan mijinta nan fa akai ta yi ma Fatuu godiya hatta Mahaifinsu da kanshi yazo inda suke yay masu sannu da zuwa shima saida yayi mata godiya da Addu'ar Allah ya bar zumunci haka yayye da k'annen Fauzy duk saida suka zo suka gaishe da ita hadda Yaya Mubarak ma fuska a sake Fatuu ke amsa masu ana ta son a d'auki twins amman sun ki yarda sai faman fad'in Tubarkallah ake dama lokacin sun k'ara girma sosae, Yaya Fareeda harda cewa Allah yasa Fauzy itama ta haifi irin su anata dariya aka amsa da Amin. Hidima ta kan kama tun a ranar Jami'an tsaro keta faman sunturi a cikin garin ana ankarar da mutane hatta gidan su Fauzy an zuba security, Washe gari Alhamis su gwaggo suka iso tare da Kawu Amadu da Mino harda Haulat da Saude bayan zuwan su kuma su Zainab Muhammadu da wasu daga cikin k'awayen su ma suka zo haka makwabtan Aunty Mareeya ma su Maman taufiq suma sunzo gida dai ya cika sai zuwa ake.

FRIDAY....

Alhamdulillah Allah ya kawo mu ranar d'aurin aure, a ranar tunda farar safiya jiniya ta fara tashi ta ko ina wurin k'arfe sha d'aya na safe Abbas ya iso tare da Feenah, tuni Amarya Fauzy tasha had'addan k'unshi an kuma gyara mata kai haka jikinta ma yasha gyara don tun a Katsina ake ta mata gyaran jiki skin d'inta tayi wani irin sumul sai shek'i take, zuwa k'arfe sha biyu da rabi na rana garin Funtua ya cika makil da jama'a ba abunda kake ji sai jiniya ga kuma jibga jibgan motoci masu numfashi dake ta kai kawo a saman tituna da tuni an rufe su an hana mutanen garin bin su saidai suyi zagaye, kamar yadda Ango Sameer yaci alwashin bazai k'ara zuwa a Mota ba hakan ce ta faru don kuwa a helicopter suka zo harda Haisam bama su kad'ai ba wasu daga cikin manyan mutane ma a helicopter d'in suka zo daga filin da suka sauka ne Motoci na Alfarma suka daukko su, Jama'a kuzo kuga ango Sameer yasha kyau har ya gaji yana sanye da rantsattsiyar shadda light ash d'inkin yar ciki da babbar riga ba K'aramin kyau ya k'ara ba a cikin kayan ko don bai saba sakawa ba ne, su Haisam angwaye suma babbar rigar shadda duk suka saka gaba d'ayansu Abokan ango iri daya sukai suma tasu ash ce amman tafi ta Angon cizawa ba K'aramin tsaruwa sukai ba dama duk gasu yan Madara harda Abokan shi turawa da suka zo suma duk shigar suka yi abun dai sai wanda ya gani, shima Mahaifin Sameer d'in His Excellency da muk'arraban shi duk sun iso gaba d'aya jiniya ta karad'e ko ina a lokacin harabar Masallacin Juma'an da za'a d'aura auren ta cika makil da Jama'a kama daga manyan yan siyasa masu Mulki da masu Sarauta, manyan yan kasuwa da sanannun masu kudi, Manyan Mutane wanda sune Nigeria aka had'a a wurin wasu sun zo da kan su wasu sun turo wakilci taro dai yay taro malam Yan Jarida ko ta ina suna d'aukar rahoto nima dai ina daga cikin su inata rubuto maku rahoton cike da taka tsantsan gudun kada in sha na jaki a wurin jami'ai dake ta kai kawo a wurin don na lura a fusace suke duk suna ruk'e da manyan makamai gaba d'aya sun yi shirin ko ta kwana. Daga cikin wad'anda suka zo bikon Amarya harda su Mom da Aunty Laila Aunty Mareeya ta shiga gabatar dasu wurin yan uwansu tana ce masu yadda suka ga Mom haka Mahaifiyar Angon take don yan biyu ne, sosae Mom ta sakar masu fuska anata faman kawo mata gaisuwa tare da yi mata godiya da murmushi take fad'in ba komai duk an zama daya. Ana gama sallar Juma'a dubban mutane suka shaida d'aurin auren Sameer da Fauzy wanda Aminin Governor wato Senator Ali Adamu Zakee ne ya kar6a mashi akan sadaki Naira dubu d'ari biyar kamar yadda iyayen Fauzy suka buk'ata Jama'a sai fatan Alkhairi suke ma Governor mahaifin Sameer da Mahaifin Fauzy da kuma shi kanshi Angon da ba laifi ya saki fuska yana d'an murmushi haka Haisam ma sai murmushi yake shima ana mashi Allah ya sanya Alkhairi, ana gama d'aurin auren aka nufi inda aka tanada don yin reception wasu dai da yawa tafiya sukai, manyan motoci ne masu d'auke da Abinci iri iri aka bud'e a bakin Masallacin nan aka shiga rabama mutane a nutse don da mutum yay wasa yaji saukar dorina a gadon bayan shi, har gidan su Fauzyn ma Motar Abinci taje an sauke masu abun dai sai godiyar Allah, cikin wanda suka halarci sallar Juma'a aka kuma d'aura aure dasu bayan an tantance su Saboda tsaro harda Mujaheed da tun bayan daya san da Maganar auren baida cikakkar lafiya, daga nesa ya tsaya shida Usman suna hango Sameer lokacin da ake d'aura auren bayan an gama Usman yace mashi su tafi fuska kamar zai yi kuka yace mashi don Allah ya za'ai ya ga Fauziyya, waro ido Usman yay ya maimaita abunda yace Mujaheed din yace eh yana son ganinta kafin ta bar garin, ce mashi Usman yay gaskiya ganinta a yanzu abu ne mai wahala gara kawai su tafi amman ya kafe kan ya taimaka mashi yana son ya ganta ido da ido ko ya nemi yafiyar ta watak'il ya samu sauk'in abunda yake ji, nuna mashi yay Fauzy bata da matsala yasan tuni ma ta yafe mashi don haka ya hak'ura da ganinta karma suje suja ma kan su matsala, kafewa Mujaheed yay harda k'wallar shi ba yadda Usman ya iya gashi ya bashi tausayi sosae hakan yasa yace mashi suje gidan nasu amman shi yasan ganin Fauziyya a yanzu ba abu bane mai sauk'i suka nufi Motar Mujaheed bayan sun shiga yaja suka nufi gidan su Fauzy.

Ana gama d'aura Aure ba 6ata lokaci aka shiga shirin tafiya da Amarya don tafiyar Mota za'ai zuwa Abuja anan za'ai Dinner in an je daga baya sai a wuce da ita Nasarawa amman an sanar ma Aunty Mareeya cewa ba mutane da yawa za'a dasu Nasarawa ba iya mutum goma suke buk'ata zuwa dai Abuja wannan ko mutum nawa suka bada lafiya lou, tun bayan da su Mujaheed suka iso kopar gidan wuri suka samu daga can gefe don kopar gidan dank'am yake da mutane ga marok'a dake ta aikin kirari da masu kad'e kad'e, rasa ta yadda zasu ga Fauzyn sukai Usman yace mashi dama saida ya fad'i mashi bafa zai iya samun ganinta ba gara su tafi daga baya shi zai mashi k'ok'arin samun lambarta sai ya kirata ya rok'eta yafiyar, Shiru Mujaheed yayi shi kad'ai yasan abunda yake ji a cikin ranshi ga tsananin mamaki da yake ganin wai duk wannan taron Fauzy akai ma shi a ranshi ya shiga raya Allah kenan sosae nadama ke dawainiya dashi. Dank'ara Dank'aran Motoci ne suka shararo cikin layin zasu kai goma sai kuma motocin Security dake a gaba da baya tare da ta yan jarida abun burgewa gaba d'aya motocin bak'ak'e ne sai k'yalli suke, cirko cirko mutane sukai suna kallon yadda ake shirya motocin, bayan an gama ne aka sanar cikin gidan cewa a fito da Amarya, rantsattsan leshi Fauzy ta saka wuyanta da hannunta na sanye da gold an d'aura mata alkyabba sai walwali take, su Aunty Mareeya iyayen hidima itama kaya ta canza daga ankon atamfar da suka yi zuwa had'add'an kuma tsadaddan lace da aka mata half gown ta coge d'aurin kallabi ya kalli gabas maso kudu harda uban glass ta k'wama, haka sauran yan gidan su ma duk sun canza shiga zuwa lace su Fatuu ma duk lace d'in ne a jikin su, ba tare da 6ata lokaci ba yan kai Amaryar suka fara fita, Akan idon Mujaheed Aunty Mareeya ta fito da ita ta rungumo kafad'arta yana ganinta ya zabura zai nufeta aikuwa da sauri Usman ya maido shi yana ce mashi bai ga Jami'ai bane a wurin, wata jibgegiyar bak'ar Jeep dake ta salk'i aka bud'e ma Aunty anan za'a saka amaryar ta kalli Fatuu dake biye da ita tace mata itama ta shigo ta zagaya ta d'aya 6angaren aka bud'e mata ta shiga itama Fauzyn aka shigar da ita tana ta yar sheshsheka da tun bayan da akayi mata fad'a take kukan, Bayan Aunty ta saka Fauzyn fitowa tayi ta rufe k'opar ta shiga nuna wanda za'ai tafiyar dasu ana bud'e masu motocin suna shiga, su gwaggo dai Motar Abbas suka shiga ita da Feenah da Saude sai Kawu Amadu Haulat kuma da Mino Mota d'aya suka shiga da Jidderh haka su Zainab k'awayen Fauzy suma Mota guda akai masu su Mom dai dama da Jeep d'insu suka zo ita suka shiga su Twins d'in Fatuu na hannunta ita da Aunty laila, saida Aunty Mareeya ta tabbatar da an shigar da kowa Mota cikin masu tafiya sannan ta dawo tasu ta bud'e ta shige ba wanda ya shiga gaban tasu don bayan driver da zai ja Motar akwae Security zaune a seat d'in gefe, wai akace ga k'oshi ga kwanan yunwa tun bayan da aka shigar da Fauzy Mota Mujaheed keta kallon Motar gaba d'aya takaici ya cika shi ji yake tamkar ya fasa ihu, da shi a haukanshi da Usman bai hana shi ba zuwa zai yi wurinta yanzu kuwa saidai sukai tsaye suka bi sahun yan kallo, sai bayan da Aunty ta koma cikin Motar ne ta natsu tana k'are mata kallo tana yi tana jinjina kai a ranta tana raya ta dai had'u ba k'arya kuma da gani sabuwa ce don seats d'in harda ledar sabuntar su ga kujerun lumtsuma lumtsuma gwanin taushi a gaban seat d'in da suke akwae screen manne da kowacce kujera da mutum zai iya yin kallo ko yayi game har internet ma zaka iya shiga ko kai connecting Bluetooth da wayar ka da dai sauran su, tsakanin su da Mutanen dake zaune a gaba akwae d'an labule na leather kalar seat d'in Motar hakan yasa basu ganin su sannan gaba d'aya glass d'in Motar tinted ne ta yadda ba'a iya hango wanda ke ciki sai dai kai kaga na waje, sosae Motar dai ta jugunu sanyin Ac nata ratsa sassan jikin su, Bayan kowa ya shiga Umarnin tafiya ake jira daga wurin Jami'an dake clearing Main titi da zasu hau su tafi, hannu Aunty Mareeya ta d'aura jikin Fauzy tace "Amarsu har yanzu kukan ake" shiru Fauzyn bata ce komai ba kuma bata d'ago ba daga sadda kan da tayi hular Alkyabbarta ta rufe mata fuska Fatuu dake latsa wayarta ta d'ago ta d'aura idonta akanta tana d'an murmushi can ta kira Sunanta k'asa k'asa ta amsa tace mata tayi hak'uri ta daina kuka don Allah,

"Uhm kukan gulma ne ba wani abu ba, nan data shige daga ciki sai munci sa'a zata tuna damu" yar dariya Fatuu tay Aunty Mareeyar tace Allah kuwa Zarah, hannu Fatuu takai ta janye hular Alkyabbar ta d'an d'ago da Fuskar Fauzyn suka had'a ido idanunta sunyi jajur ta kai hannu tana goge mata k'wallan tana fad'in ya isa hakanan kada tayi ciwon kai tana Amarya Aunty tace ta fad'i mata dai, saida tasata ta daina yin Kuka ta d'ago Fuskarta sosae, a hankali ta fara bin Mutanen dake tsaye cirko cirko suna kallon Motocin nasu da kallo, tana haka idanunta suka sauka akan Mujaheed daya tsura ma saitin inda suke ido, har zata janye idanun nata sai kuma ta tsaya kamar an dakatar da ita ta k'ura mashi ido farko bata gane shi ba kawai dai sai take jin kamar tasan mutumin dake a tsaye saida ta d'an d'auki lokaci tana kallon shi ne ta fara ganin kamar shi, a ranta ta raya anya kuwa shine taya zai zo nan k'arshe ta yanke bashi bane k'ilan dai mai kama dashi ne tana janye idanunta ta d'aura su akan Usman dake gefen shi, tana ganin shi ta ganeshi a ranta ta raya Usman tana fad'in hakan da sauri ta maido idonta kan Mujaheed lokaci guda ta shaida shine da tsananin mamaki ta furta "M...UJAHEED!" har Kusan rigen kallonta su Aunty sukai da sauri tace "ina Mujaheed d'in" hannu Fauzy ta d'aga tana nuna saitinshi ta cikin glass gaba d'ayansu harda Fatuu suka zuba mashi ido shima kuma har lokacin saitin su yake kallo saidai baisan suma kallon nashi suke ba,

"To uban me ya kawo shi nan kuma, koda yake nama ji dad'i daya zo ya gane ma idon shi komai" Aunty ta fad'a ta d'aure fuska tare da yamutsa baki can kuma sai cewa tayi bari ma a bud'e glass d'in don ya shaida da kyau itace Amaryar, duk yadda taso ta sauke glass d'in ta kasa har ta kai tace ma Fatuu wai ta bud'e tunda dai ita tafi ta sanin takan kayan masu arzuki Maganar har saida taba Fatuu yar dariya itama ta fara k'ok'arin sauke glass d'in amman ta kasa can Aunty tace bari ta tambaya tunda ai dai sun san Amaryar yar talakawa ce bazai zama sun yi k'auyanci ba, dariya Fatuu tasaka Aunty Mareeyar ta kai hannu ta d'an janye labulan dake tsakanin su da Driver ta d'an lek'a a Kusan tare su duka na gaban suka juyo suka kalleta yadda ta sak'a kan kamar mage, da d'an murmushi tace masu sannun su suka amsa kafin tace don Allah glass d'in baya za'a sauke masu su dai sun duba basu ga inda ake saukewa ba, suma murmushin ne akan fuskar su Security d'in dake gefen driver duk da shima driver d'in kamar security d'in ne daga yanayin shigar shi yace mata kodai basu iya bud'e glass d'in bane,

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login