Showing 249001 words to 252000 words out of 512766 words
Chapter 84 - Asanadin Makwabtaka Book 3 Hausa Novel Complete
Unknown
27 Dec 2024
1666
ya jinjina mata kai had'i da d'an lumshe ido a hankali yace ta cire, ba'a dad'e ba aka sanar ai fastening seat belt ba 6ata lokaci Fatuu tasa har saida ta kalli Haisam yay mata murmushi, lokacin da jirgin ya fara tafiya wani irin bugu k'irjinta ya fara yi da zai d'aga sama ba shiri ta sauke kanta ta runtse idanunta da k'arfi Haisam ya kai hannu ya ruk'e nata da k'arfi, bayan ya kai kololuwa ya mik'i hanya ta bud'e idon ta juya ta kalle shi slowly ya furta "Are u okey?" Kai ta d'aga mashi ta d'an tsuke baki da d'an waro ido hakan har saida yasa shi yin yar dariya, daga baya sai gashi ta saki jiki taci gaba da yin kallo ma ita kuwa Hajiya ma d'an kishingid'awa tay idanunta a rufe da alama bacci take, Lokacin da suka iso bayan an sanar sun maida seat belt tun kan su k'araso yadda tayi da zai tashi haka ta k'ara yi da zasu sauka saidae na yanzu ma yafi don kamar zata sa kuka jikinta har rawa yake Haisam d'in ya k'ara ruk'e hannunta gam har jirgin ya tsaya sannan yace ta Kantar da hankalinta sun iso ta bud'e idanun tana numfarfashi, shi ya cire mata seat belt d'in tana mik'ewa tace mashi juwa take gani ya maida ta kan seat ya zaunar da ita Hajiya ta matso tana tambayar Yaya ko amai take ji yace mata a'a she feels dizzy, sannu Hajiyar tayi mata tace ai tama yi kokari tunda boarding d'in ta na farko ne wasu da zasu yi ta amai wasu harda bayan gida, bayan d'an lokaci ta mik'e cike da kulawa Haisam d'in yace mata zata iya tafiya tana murmushi ta d'aga mashi kai Hajiya sai sannu take mata,
Haisam na janye da trolley d'inta dana Hajiya ita kuma tana ruk'e da K'aramin nashi sai Hajiya na ruk'e da yar madaidaiciyar jaka a hannunta d'aya d'ayan kuma tana dogara sandar ta ba yadda Fatuu bata yi da ita ba ta bata jakar ta ruk'e tace mata ta barshi zata iya, suna isowa Arrival Jidderh da Nameer da suka zo tarbar su suka hango su, da gudu Jidderh ta nufe su tana sanye da Turkish dress riga da wando pink colour ta yafa gyalen a saman kanta gaban bak'ar sumar ta ya d'an fito Nameer kuma na sanye da k'ananun kaya jeans da t-shirt duka Navy blue ba K'aramin kyau yayi a cikin kayan ba sun k'ara fito mashi da hasken shi gashi ya k'ara girma ya zama cikakken saurayi sumar shi shima dake a nad'e sai salk'i take duk da bata kai yawan ta Haisam ba, tana zuwa ta rungume Fatuu tana fad'in "Oyoyo sis Fatuu our bride" dariya kawae Fatuu ke yi, Nameer na k'arasowa ya nufi Hajiya ya rungumeta yana sakin k'ayataccen murmushi, bayan ya saketa tana yar dariya tace mashi yaushe ya dawo K'asar yace mata ranar laraba shima yazo biki ne tambayar shi Laila tayi yace mata itama tazo, sakin Fatuu Jidderh tay suna ma juna dariya tayi mata sannu da zuwa bayan ta amsa ta juya kan Hajiya tace "Welcome granny" yar harara Hajiya ta wurga mata tace sai yanzu zata yi lokacin ta da sauri ta nufeta ta rungumeta tana fad'in tayi hak'uri, kallon Haisam Nameer yayi yana murmushi yace "Welcome Big Bro" yana murmushi shima ya jinjina mashi kai kafin yace mashi yazo lafiya ya karatu ya amsa mashi, kallon Fatuu yay suka had'a ido tana mashi murmushi kawae sai gani tay ya d'an harareta sanin halin shi yasa bata ji komai ba taci gaba da yin Murmushin,
Jidderh ce ta amshi trolley d'in hannun Fatuu shi kuma Nameer ya amshi jakar hannun Hajiya da trolley d'aya na hannun Haisam suka nufi hanyar barin wurin, ganin Nameer abu biyu ne hannun shi yasa Fatuu komawa kusa dashi tace "ka kawo jakar in ruk'e" hararar tata ya k'ara yi tana murmushi tace "laifin mi na maka ne kake ta hararata?" k'asa k'asa da murya yace "ai kin fi kowa sani, don wulakanci kin san ina son ki shine zaki auri big bro d'in mu" ba shiri Fatuu tay yar dariya sai kuma ta girgiza kai tace "wllh Nameer baka Ji Allah ya shirye ka" wani kallo yay mata yace "dole kice haka ai tunda kin yaudare ni" ya k'arasa Maganar tare da d'an murgud'a mata baki ita dai murmushi kawae take, wata dank'areriyar Jeep ce suka zo d'aukar su da ita, Hajiya da Fatuu da Jidderh suka shiga baya Jidderh ce a tsakiya sai Haisam a seat d'in gaba Nameer ya zauna driver seat bayan duk sun rufe kopopin yaja suka tafi, suna a kan hanya Hajiya ke tambayar Dad d'in su yace tunda yaje Masallaci bai dawo ba amman k'ilan da suka taho ya dawo, Jidderh sai jan Fatuu da hira take da sun had'a ido da Nameer ta mirror sai ya fakaici idon mutane ya harareta ita dai murmushi kawae take,
Lokacin da suka iso gidan tun a babban gate Fatuu ta sha jinin jikinta ganin had'uwar gidan ga Jami'an yan sanda da civil defence dake tsaron gate d'in, ko tsaida su basu yi ba ganin Motar gidan ce suka shige, yar tafiya sukai suka k'araso wani gate d'in na k'arafa wanda ana hango cikin gidan ta cikin shi kuma a bud'e yake masu gadi biyu ne ke tsaron shi suka shiga d'aga ma Motar hannu da zata shiga, suna shiga suka nufi roundabout suka sha shi bai nufi parking space da su ba sai ya tunkari dank'areren ginin gidan, a gaban Entry Hall ya parker Hajiya ta furta Alhamdulillah ta bud'e k'opar, jiki a mace Fatuu ta bud'e ta side d'inta ta fito, wasu daga cikin ma'aikatan gidan ne jikinsu sanye da brown uniform suka nufo su don d'aukar kaya suka shiga yi masu sannu da zuwa suna d'an rankwafawa Fatuu dai sai wurga ido take, Haisam ne ya zo wurinta ta kalle shi yana murmushi yace mata su shiga kai kawai ta d'aga mashi suka nufi shiga cikin gidan, suna shiga hall d'in sai ga Senator ya fito dasu Momyn Haisam harda Aunty da Laila da sauran yaran gidan duk sun sha gayun Juma'a manyan na sanye da had'addan lace, iyayen dogayen riguna ne Laila kuma riga da skirt haka Yasmeen ma, a gaban su duk suka tsaya kowa fuskar shi da fara'a Senator dake sanye da riga da wando na farar shadda da gani yan cikin babbar riga ne ya cire babbar rigar yana faffad'an murmushi ya Mik'o hannu yana fad'in "You are Welcome My Daughter" ganin hannun da ya Mik'o yasa a sanyaye Fatuu ta k'ara matsawa kusa dashi ya dafa Shoulder d'inta kanta a k'asa ta gaishe dashi ya amsa yay mata ya hanya tace Alhamdulillah, nuna mata su Aunty yay yace taje su gaisa ta nufe su ta tsaya a gaban su, d'an rankwafar da kai tayi tace ma Mom d'in ina wuni tana murmushi ta amsa ta kawo hannu ta rungumo ta jikinta tace "Marhaban bik ya aibnati" d'agota tay ta nuna mata Aunty ta nufeta itama ta kai hannu ta dafa Shoulder d'inta tana murmushi tace "Sannu da zuwa Daughter munyi farin cikin ganin ki" a hankali ta furta mata ta gode, Laila ce ta Mik'o mata hannu ta nufeta itama rungume ta tayi tana Fad'in "We're Welcome our bride" bayan ta d'ago ta suna ma juna murmushi ta furta mata Thank you,
Hajiya ce dake tsaye tace "to in kun gama tarbar sabon jini sai ku ba tsohon jini hanya ta wuce kafin ta fad'i" Senator na dariya ya matso kusa da ita ya rungumota jikin shi tana fad'in sai da tayi magana sannan ya ganta, sosae ya rungumeta gaba d'aya ta shige cikin jikinshi kanta ko kafad'ar shi bai kai ba gaba d'aya sai dariya ake masu, bayan ya saketa ne su Mom da Aunty suka shiga gaishe da ita suma duk saida tay masu mitar sai yanzu zasu yi lokacinta wato don sun samu sabon jini shine suka shareta, suna dariya duk suka bata hak'uri, Jidderh ce tace ma su Yasmeen bazasu yi ma sabuwar Yayar su sannu da zuwa ba duk suka yi murmushi suna kallon Fatun suka hau yi mata Welcome tana murmushi take amsa masu kafin ta tsaida kallon ta akan su twins dake ta faman kallon ta sun girma sosae don yanzu zasu yi shekara tara, ganin suna ta kallon kallo yasa Jidderh cewa "ko baku gane sis Fatuu bane genie d'in ku" ta k'arasa tana dariya suma yar dariya suke sun san ta amman sun manta da lokacin da suka ce mata genie d'in, ganin ana ta tsayuwa yasa Hajiya cewa to a shiga ciki mana sai a gaisa sosae duk suka nufi ciki, ganin yadda su Mubeen da Mubeena keta kallon ta yasa ta kama hannuwan su suka shiga,
bayan sun shiga mai parlor d'in sosae Fatuu ta raina kanta Saboda had'uwar parlon da irin dukiyar data ga an narka a cikin shi, bayan sun zazzauna aka shiga k'ara gaisawa Senator ya kalli Fatuu da murmushi yace "muna matuk'ar farincikin kasancewar ki cikin wannan family d'in muna fatan ki zamo Alkhairi a cikin shi" tana ta murmushi tayi mashi godiya duk idon kowa na a kanta da murmushi suke kallonta, kallon Hajiya yay yace "Hajiyata table ashirye yake muje sai ku ci Abinci ko" ce mashi tay ba wata yunwa suke ji ba sun ci snacks da lemu a jirgi a bari su d'an kara hutawa ya ce to, mik'ewa Laila tayi tana kallon Fatuu da murmushi tace suje ciki ta huta zumbur Jidderh ta mik'e a shagwabe tace d'akinta zata ta huta gaskiya, d'an bud'a ido Laila tayi Senator na dariya yace "Jidderh fa ba K'aramin ji take da Yayar nan tata ba indai tana kusa ban tunanin zata bari wani yayi mata wani abu" juyawa Laila tayi ta kalle shi tace "I see Dad" komawa tay ta zauna Jidderh ta na murmushin jin dad'i ta kama hannun Fatuu data Mik'e tace suje, ganin su twins ma sun mike yasa Fatun mik'a masu hannu tace su taho suka nufeta suna murmushi, bayan sun fito daga wurin kujerun Jidderh ta nuna kayan su tace wanne ne nata a ciki ta nuna mata, sakin hannunta tayi taje ta d'aukko trolley d'in da jakar Fatun ita kuma ta kama hannun su twins dawowa tayi tace ma Fatun suje, bayan tafiyar su Mom d'in su ta mik'e tace ma Hajiya suje ta huta ta mik'e Aunty ma da Laila suka mik'e suka tafi, kallon Haisam Senator yay yana murmushi yace "Ango kasha k'amshi" murmushi kawae yay haka ma Nameer, cigaba yay "dama inata son in yi maka magana amm....akwae wanda akace ya tsaya maka wurin d'aurin Auren ka ina tunanin yakamata yazo Walima da za'ayi" shiru haisam ya d'an yi kafin yace suna communicating da Abbas dama yana niyyar ya samu time yaje yayi ma shi godiya Senator yace to sai a tuntu6e shi aji in zai iya samun zuwa daga baya sai yaje har gida yayi mashi godiyar yace to,
k'ara cewa yay "sai relatives d'in ita matar taka suma yakamata su zo, kayi mata magana kaji in sun yi zasu zo sai a tura masu Mota ta d'aukko su kawae" kai Haisam d'in ya jinjina suka cigaba da yin fira yana tambayar Nameer karatun shi na Software Engineering wanda Haisam d'inne yasa ya karance shi Saboda Company d'in da yake so ya bud'e.
Wani corridor suka shiga sukai yar tafiya nan suka k'araso bakin wasu kopopi dake opposite da juna Jidderh ta tura ta 6angaren hagu ta juyo tace ma Fatuu ta shigo, d'aki ne mai d'an girma akwae madaidaicin gado daya sha bedsheet da side drawers d'in shi da dressing mirror sai wall cabinet sosae d'akin ya tsaru yasha decorations su frames da artworks da flowers harda wall stickers ga labulayen ciki ma masu kyau fentin d'akin ma kusan kala ukku ne amman yadda akai masu wani design sun k'ara k'awata dakin , suna shiga Jidderh ta juyo tace "Welcome to Jidderh's palace" jinjina kai Fatuu tay tana murmushi Jidderh tace "ya kika ga d'akin nawa" Fatuu tace "it's a beautiful palace gaskiya ya tsaru" dariya Jidderh tay tace ta gode, bayan ta aje trolley d'in a gefe ta nuna ma Fatuu gado tace ta zauna itama a gefe ta zauna su twins suka saka Fatun tsakiya,
"Kinsan abunda nike karanta kenan interior design yanzu haka na kusa gamawa kuma ina gamawa zan tafi Dubai in k'ara yin wasu courses d'in kan hakan, so nike in bud'e babban company in nagama da zai rink'a supplying kayan decorations irin su furniture, labulaye, carpets, flowers harda fitilu da dai sauran su sannan kuma ba iya saidawar ba harda tsara wuri kamar gidaje, Offices, Hotel rooms da dai sauran su" Fatuu nata jinjina mata kai har ta gama sannan tace gaskiya tayi tunani mai kyau don irin aikin na kar6uwa yanzu Jidderh d'in tace sosae ma, kallon su twins tay ta d'an d'aure Fuska tace "wai ku bazaku k'yaleta ta huta ba ku tashi ku tafi tunda kun gaisa" mak'e mata kafad'a sukai suka tura mata baki sai kace ana latsa masu remote komai a tare suke Fatuu ta kai hannu ta rungumo su jikinta tace ta k'yale su ai an dad'e ba'a had'u ba, Jidderh na murmushi tace "koda yake suma zauna kita kallon su pls ki haifo mana irin su amman ba masu irin halin su ba don sai su haukata ki kullum cikin ba mutane ciwon kai suke" tana rufe baki suka murgud'a mata baki ta yunk'uro zata make su suka k'ank'ame Fatuu suna dariya itama dariyar take tace ma Jidderh tayi hak'uri don Allah, mik'ewa tayi ta nufi wardrobe, bud'eta tayi ta kai hannu ta fiddo wasu kaya dake a goge bayan ta rufe ta nufo gadon, a kan cinyar Fatuu ta d'aura su tace "kinga anko d'in da akayi na Walima da Dinner" sakin jikin su twins tay ta kai hannu ta fara d'aga kayan Jidderh tace ta warware mana ta gan su sosae, atamfar ta fara warwarewa sosae ta burgeta saidai da gani bata rasa kud'i, kallon Jidderh tayi tace "amman dae tayi kyau wllh" tace "sosae ma Chiganvy gold mix and match embroidery ne" jinjina kai Fatuu tay sai kuma ta tambayeta nawa take tace "kinga atamfan kaman kashi ukku ne, mutum zai iya yin Chiganvy gold d'in kawae ko yay mix and match da embroidery d'in ko kuma yayi embroidery d'in kawae gaba d'aya dai duka Atamfa kala d'aya ce ai kin gani kawae ita wannan normal atamfa ce mai gold ita kuma d'ayar sai akai mata aiki gaba d'aya jikinta, so mutum in yayi mai mix d'in zai iya ai mashi style mai kyau da mai aikin da mara aikin kaman yadda akai man, in Normal Chiganvy gold d'in mutum zai yi just 18k ne in kuma mix and match d'inne 37k sai kuma mai gaba d'aya embroidery 50k, su Aunty Laila mai gaba d'aya sukai nima naso ayi man ita amman aka k'i saida aka d'inka man mix and match d'in kuma sukai ta cewa dama ita sukai" ta k'arasa tana murmushi itama Fatuu murmushin take kafin ta tambayi lace d'in tace shi 35k yake, shiru Fatuu tay tana tunanin kawae dae in mutum zai yi ankon sai wurin 100k ya tashi harda kud'in d'inki saidai in ko mutum yayi normal Chiganvy d'in, tambayar ta tayi ina ake saida su Jidderh d'in tace Zee Collections ce ta kawo masu tace Ok zata mata magana tana son siya ma su gwaggon ta da k'anwarta da sauri Jidderh tace "ai fa Big Bro ya siya masu dama cewa yayi a bari kizo sai a tambaye ki wand'anda za'a d'inka mawa atamfa biyar da lace biyar yasa aka amsar maki yace in kinzo basu isa ba sai ayi mashi magana" d'an murmushi Fatuu tay yana daga abunda ke sawa tana k'ara son shi kenan akwae shi da sanin yakamata, tunanin wanda zata sa a d'inka ma su ta shiga yi nan ta yanke gwaggo da Mino sai Fauzy da Yadikko sai Aunty Mareeya, tunanin Haulat ko zata zo tayi don sunyi waya tace mata zata zo in sha Allahu k'arshe ta yanke tunda tana da number d'in Zee Collections d'in zata mata magana kawae ba sai Haisam din ya k'ara siya ba tunda tana da kud'i da yawa a account d'inta sai ta siya ma Haulat da k'annanta su Aysha tasan inta rok'i Kb mai d'inki zai d'inka masu, daga baya Jidderh tayi mata Maganar zuwa taci Abinci tace tunda Magrib ta kusa ta bari in tayi salla sai ta ci.
Bayan sunyi sallar Laila ta shigo tana murmushi ta k'ara yi ma Fatuu ya gajiyan hanya tace mata ai ba wata gajiya, kallon Jidderh tay tace "ke haka ake kula da bak'o kin ruk'eta ashe har yanzu bata ci Abinci ba yanzu Mom ke man magana akan haka, so kika Big Bro yace mun bar mashi mata da yunwa ne" ta k'arasa tana d'an harararta tura mata baki tay tace ai saida tayi mata magana ita tace a bari sai tayi salla, ce mata Laila tayi ta taso suje taci Abinci tana murmushi tace to ta mik'e, ganin zata fita da Hijab Laila d'in tace ya zata je cin Abinci da Hijab, cire Hijab d'in tay Laila tabi jikinta da kallo ganin tana niyyar d'aukar gyalenta dake akan gado yasa Jidderh yin saurin d'auke shi tana dariya tace wai miye zatai ta wani lullube lullube nan fa gida ne Laila tace ato ta fad'a mata dai, ba yadda Fatuu ta iya haka ta bita duk ta takura suka fita.
Da daddare sun gama shirin kwanciya cikin kayan bacci Jidderh ma tasaka nata Fatuu na kwance saman gado ita kuma tana zaune a gefen ta suna hira aka turo kopar d'akin duk suka kai idanuwan su wurin, Mom d'in su ce ta shigo da yar sallama itama tana sanye da kayan bacci riga da wando brown kanta ta yafa bak'in gyale, Fatuu na