Showing 396001 words to 399000 words out of 512766 words
Chapter 133 - Asanadin Makwabtaka Book 3 Hausa Novel Complete
Unknown
27 Dec 2024
1600
sallar isha suka fito zasu tafi harda Jidderh tana jaye da wani madaidaicin trolley bayan sunyi sallama dasu Mom suka fito, a parking space suka had'e da Sameer yayi wanka ya canza kaya suka hau wata dankareriyar Jeep Sameer d'in ne ya shiga driver seat Fauzy na niyyar shiga baya Aunty Laila tace ta hau gaba su kuma suka shiga bayan yaja suka tafi. Wani sananne kuma tsadadden wurin hoto suka je wurin mai girman gaske ne gashi ya matuk'ar Had'uwa don iya ginin wurin abun kallo ne fitilu masu k'ayatarwa ne ta ko ina kai kace da rana ne, akwai manyan Studios d'in d'aukar hoto sai kuma na kwalliya haka akwae restaurant a wurin sannan akwai had'addan parlon hutawa ko jira, suna zuwa ba 6ata lokaci don ansan da zuwan su sunyi booking aka fara yi ma Fauzy Makeup abunka da kwararru ba'a d'au lokaci ba aka gama sosae Fauzy tayi kyau abun ba'a magana harda gashinta aka gyara, shima Sameer d'in saida aka gyara mashi fuska ya k'ara fitowa sosae, bayan sun gama ne suka nufi wurin canza kaya aka bud'e trolley d'in da suka zo da su wanda gaba d'aya sababbin kaya ne aciki wanda aka d'inka ma Fauzy tsadaddu kuma had'add'un gaske kala daban daban, hotuna daban daban aka shiga yi masu saida sukai kala goma kuma kowanne da kaya kala daban kama daga atamfa, lace, shadda, material, Abaya, English wears harda wanda aka yi masu da kayan aikin Sameer d'in irin kayan da injiniyoyi suke sakawa itama Fauzyn ta saka na mata ta saka irin hular da suke sakawa daga baya wurin wuyanta gashinta ya fito sosae tayi kyau kai kace ba bahaushiya ba, bayan sun gama ne aka yi masu wasu tare da su Aunty Laila. Aunty Mareeya bata yi niyyar fad'i ma iyayensu game da tafiyar Fauzyn Abuja tare dashi ba don tasan baban su bazai so hakan ba dole ya kalubalanci hakan saidai kuma tasan in aka yi hotunan dole suyi trending a social media kuma tabbas sai yan gidansu sun gani k'arshe Baban nasu zai iya gani shima, tunanin mafita ta shiga yi k'arshe ta yanke zata ce mashi kawai Katsina yazo akai masu. Washe gari ya sako Fauzyn jirgi ta dawo, a ranar da daddare saiga hotunan ya turo mata lokacin da ta gansu har saida tayi d'an ihun farinciki don sosae suka d'akku sunyi kyau har sun gaji gashi sun saka sutturu masu tsada haka d'inkunan da akai ma Fauzyn sun hau da jikinta sosae abundai saidai ace ma sha Allah, lokacin da Aunty ta gansu kasa rufe baki tayi tana ta faman yabawa tana fad'in Fauzyn kamar ba ita ba ta wanku iya wankuwa, kan kace mi hotunan har sun baza social media a daren Fatuu ma tun kafin Fauzy ta tura mata sai gashi ta kirata tana fad'in yayi kyau matar injiniya wannan zafafan hotuna haka, tambayar ta tayi a ina ta gansu tace gasu nan Aunty Laila ta d'aura a status harda su Jidderh har su Mom ma duk sun d'aura, sosae Fauzy tay mamakin yadda ake ta kiranta ana yaba hotunan tare da fatan Alkhairi abun har ta kasa rufe bakinta ma, gaba d'aya yan'matan Sameer sai yanzu suka san da zai yi aure ganin hotunan sosae mutane da dama sukai mamakin wadda zai aura sakamakon Comments d'in da aketa yi ana fad'in yar talakawa ce a Funtua local Government d'in Katsina take, haka aketa faman yin Comments mafi yawanci yabo ne ake tayi ana jinjina yadda d'an Governor ya auri d'iyar talakawa wasu na fad'in da ana yin haka a K'asar nan da an rage talauci sosae, wad'anda suka san Sameer d'in nata jinjina Al'amarin suna basu ta6a tunanin zai auri yarinya k'arama kuma yar talakawa ba, haka dai aketa maganganu gaba d'aya hotunansu sai trending suke ko ina ka shiga Maganar ake, ta 6angaren Sameer d'in yan matan shi sai kiran shi suke suna fad'in ya zai masu haka tare da jaddada mashi irin son da suke mashi wanda ya sani amman zai auri k'aramar yarinya kuma yar talakawa, to gaba d'aya dai amsa d'aya yake basu itace ita Allah ya k'addara mashi zata zama Matar shi kuma yana sonta, abokanan shi ma suna ta kira suna mashi Allah ya sanya Alkhairi.
MUJAHEED
Zaune yake a cikin parlon part d'in shi dake a cikin gidan su, dama gidan nasu Family House ne gaba d'aya shi da matar shi Rukky iyayen su anan suke dama Cousin ne shi da ita, gaba d'aya ya canza kamar ba Mujaheed d'an gayu ba yanzu sam ba wannan gayun don tun bayan daya yi aure kwanciyar hankali tayi mashi k'aranci, tashin farko matsalar daya fara fuskanta da Rukky itace bai sameta a budurwa ba bayan da suka yi auren haka dai aka yi Amarcin aka gama ba tare daya nuna mata komai ba don ita a zaton ta bai gane ba Saboda gyaran da ta sha, matsala ta biyu daya k'ara fuskanta itace k'azama ce sam bata san ta gyara muhallin da suke ciki ba ta dai iya tayi wanka tayi kwalliya amman kullum gida kaca kaca gashi sam bata iya wani girki ba, matsala ta ukku daya fuskanta a tare da ita itace sam bata bashi lokaci yadda yakamata Saboda aikin Asibiti da take dama da suka yi karatu a Malaysia ita medicine ta karanta shi kuma Business admin, a daddafe auren su yayi shekara guda don matsalolin daya ke fuskanta a tattare da ita sunyi yawa gashi har lokacin ko 6atan wata bata ta6a yi ba, Babbar Matsalar daya fuskanta a tare da ita wadda ta kusa zauta shi itace kamata da yayi red-handed tana aikata lesbian a cikin gidan shi, a lokacin yayi kuka kamar kamar me ita kanta hankalinta ya tashi sosae ta dingi bashi hak'uri tana ta tuba bazata k'ara ba amman ina dama ya gaji da auren ta hakan yasa ya tunkari iyayen su ya zayyana masu irin matsalolin da yake fuskanta a tare da ita k'arshe har lesbian daya kamata tana yi bai 6oye masu ba, suma hankalin su ya mugun tashi bama kamar Mahaifiyar shi anan tace ma Daddyn shi gaskiya a raba su amman ga mamakin su sai cewa yayi baza ayi hakan ba tunda dai abun duk na gida ne in abun ya bud'u to suma zai shafe su k'imar gidan ce zata ta6u a bari su kirata sai suyi mata fad'a insha Allahu zata bari, wani k'ululun bakin ciki ne ya tokare Mujaheed yana kuka ya shiga rok'on mahaifin nashi kan shidai a raba su kawai ya shiga girgiza mashi kai yana fad'in baza'ayi haka ba ai ba had'a su akai ba su suka fara son juna har sukai aure don haka kawai yayi hak'uri ayi mata fad'an, a lokacin Mujaheed ji yayi kamar ya mutu, bayan an kirawo ta sosae mahaifin nasu yayi mata fad'a ya nuna ta bashi mamaki yana ganinta mai hankali mai ilimi wanda a addinance da kuma a aikinta na likitanci duk tasan illolin hakan taya zata 6ata wayonta haka, sosae take kuka tana fad'in ayi hak'uri sharrin shaid'an ne amman ta bari in sha Allah zata gyara duk wasu matsalolinta da Mujaheed ya fad'a, sam Mahaifiyar shi bata so hakan ba amman ba yadda zata yi tunda Mahaifin nasu ya kafe, a haka suka ci gaba da rayuwa ba laifi a lokacin ta d'an gyara saidai sam shi hakan bai burge shi ba don ta riga ta fitar mashi a rai gaba d'aya sai lokacin ne ya gane dalilin da yasa ya sameta a ba budurwa ba ya shiga tunanin Allah kad'ai yasan tsawon lokacin da ta d'auka tana aikata hakan ashe shiyasa sam bata damu da ta bashi hakkin shi ba saboda tana bin mata yan'uwanta, yasan Rukkyn ta waye sosae amman bai ta6a tunanin zata aikata haka ba, a lokacin ne son Fauzy ya taso shi a gaba kullum cikin aikin tunanin ta yake haka cikin baccin shi yayi ta mafarkin ta saidai shi kan shi yasan samunta a lokacin abu ne mai matuk'ar wahalar gaske don yasan mahaifinta ba laifi yana da zafi hakan yasa bai ma yi tunanin zuwa gidan su ba, da yaga abun yayi mashi yawa ne ya yanke ya fara tuntu6arta in ta saurare shi sai yayi duk yadda zai yi yaga ya shawo kanta watak'il a bashi ita, Da wani yammaci ne ya shirya cikin Motar shi ya nufi gidan su Fauzy lokacin daya je a d'an nesa da gidan ya parker yana ta kallon kopar gidan yana dakon fitowar wani saida aka d'auki lokaci sannan yaga wani k'aninta da suke ce ma Abba ya dawo daga islamiyya a saman Keke yana ginin shi ya fito da sauri ya fara kiran sunan shi hakan yasa Abban tsayawa ya juyo Mujaheed d'in ya nufe shi ai koda yay arba da fuskar shi kawai sai gani yay ya tamke mashi fuska hakan yasa Mujaheed shan jinin jikin shi amman duk da hakan ya dake yana d'an murmushi yayi mashi sallama tare da ce mashi an dawo daga islamiyya ne kaman bazai amsa ba can dai cikin d'aure fuska yace mashi eh, jinjina mashi kai yayi yace yayi kyau Allah ya bada sa'a anan Abban bai amsa mashi ba sai ma ce mashi yay zai shiga gida da sauri Mujaheed ya dakatar da shi cikin yar in ina yace "a...m Fauziyya na nan?" Wani kallo mai kamar harara yayi mashi kafin yace bata nan, tambayar shi yay tana ina cikin kumbura baki yace "Oho ban sani ba nima" yana fad'in hakan ya ja keken shi ya shige, tsaye Mujaheed Yay sototo hakan da yayi mashi ba K'aramin k'aryar mashi da zuciya yay ba don bai zata yaron zai mashi hakan ba Saboda lokacin da yana tare da Fauzy suna shiri sosae da yaron don mutumina ma Mujaheed d'in ke ce mashi, da k'yar yaja k'afafun shi ya koma cikin Mota a ranshi ya shiga tunanin yaro ma yayi mashi hakan to ina ga Mahaifin kuma Fauzyn, jiki a mace ya ja Mota ya fara kokarin barin layin, yana driving yana tuna rayuwar shi da Fauzy a ranshi yana raya yasan da ita ya aura da ba K'aramin more mata zai yi ba don yarinyar na bala'en son shi kuma duk yadda yake so haka zai tafiyar da ita, haka ya dingi tuna abubuwa har ta kai yana kai ma steering Motar d'an bugu alamun takaici, tunanin yadda zai ga Fauzy ya shiga yi don tun kafin ya taho saida yayi trying layinta bai shiga, yana haka abokin shi Usman ya fad'o mashi a rai yay tunanin watak'il shi zai san inda take da sauri ya d'auki wayar shi ya kira shi bayan ya d'aga sun gaisa ne ya tambayi yana ina yace mashi gashi nan gidan shi yana shirin zuwa Masallaci yace Ok bari yazo, a tare suka tafi Masallacin bayan an gama sallar suka dawo ganin ya tsaya a bakin Motar shi Usman d'in yace mashi su shiga mana ya girgiza mashi kai, shiru yay yana kallon Mujaheed d'in don duk matsalolin da yake ciki ya sani,
"Kayi hakuri ka daina saka damuwa haka sosae a ranka Mujaheed kada ka ja ma kan ka wata matsalar kuma, ka dage da Addu'a Allah kad'ai ne zai maka maganin matsalar da kake ciki" shiru yay kafin ya jinjina mashi kai tare da kai hannu ya shafi gaban kan shi can yace "Usman bazaka gane ba amman ina cikin matsala wllh" ya k'arasa tare da cize lip d'in shi na k'asa,
"na sani abokina ai rashin dacen mata babbar matsala ce baka ji wak'ar nan da ake ta mace ta gari ba wllh duk abunda aka fad'a a cikinta hakanne da kaga mutum ba natsuwa duk ya firgice to da ka bincika zaka samu bai yi dacen mata bane, yanzu dai look at you kaman ba Mujaheed d'in dana sani ba duk ka fara fita hayyacin ka ko rannan saida nayi maka magana kan ka rage wannan k'asumbar taka wanda a da yaushe ma har wani zai maka magana kan haka" d'an murmushin takaici Mujaheed d'in yayi ba tare daya ce mashi komai ba, shiru suka d'an yi can Mujaheed d'in yace mashi don Allah suna magana da Fauzy har saida Usman ya d'an waro ido jin sunan wadda ya ambata tare da maimaita sunan Fauzy Mujaheed ya jinjina mashi kai, tambayar shi Usman d'in yayi mi zai da lambar tata yace mashi hakanan yana son suyi magana da ita ne zai bata hak'uri don yana tunanin duk abun nan dake faruwa dashi harda hakkinta, d'an murmushi Usaman yayi yasan ba iya dalilin daya sa yake son lambar ta ba kenan, k'ara tambayar shi Mujaheed yay in yana da lambar ta pls ya bashi Usman d'in yace gaskiya baida ita yana tunanin ta canza layi ne don ada suna gaisawa amman yanzu sun dad'e ma basu yi magana ba, tambayar shi yayi to yana ganinta cikin gari haka yace mashi a'a ai bata cika zama a nan ba yanzu Saboda ta koma Katsina wurin Yayarta acan take karatu, shiru Mujaheed yay yasan Yayar tata wato Aunty Mareeya amman bai san a ina take ba a Katsina, daga baya dai sukai sallama ya tafi Usman nata d'an girgiza kai ba yadda bai nuna mashi ba kar ya bar Fauzy don in yayi mata hakan bai kyauta ba amman ya k'i ji k'arshe ma abun ya zamar masu kamar fad'a gashi nan yanzu tun ba'a d'auki lokaci ba sosae ya fara nadama mara amfani. Tun daga wannan lokacin son Fauzy ke ta d'awainiya dashi gashi yayi duk yadda zai yi don ya had'u da ita ko kuma ya samu lambarta abun yaci tura, Wata rana ne kwatsam ya ganta a bakin titi duk yadda yaso ta tsaya ta saurare shi ta k'iya hakan yasa Ranar ya bi bayanta gida da daddare aikuwa yana zuwa suka had'e da Mahaifinta ya same shi yay mashi tatas yace Idan ya k'ara ganin shi a k'opar gidan shi to hukuma ce zata raba su nan Mujaheed d'in yayi ta bashi hak'uri yana fad'in yasan yayi kuskure bai kyauta ba amman don girman Allah ya bashi dama a yanzu zai gyara kuskuren shi ne, a lokacin wani murmushin yaro yaro ne mahaifin nasu yay kafin ya d'aga yatsa sama yace mashi "Na rantse da Allah daya hallicce ne ko bayan ba raina bazaka auri Fauziyya ba, yarinyar da kaso kashe man ita kawai don Allah yasa da sauran numfashinta a gaba shine yanzu don baka da kunya ka iya tako k'afafun ka kazo man gida, to bari kaji, ka bar kopar gidan nan tunda arzuki in ba haka ba....ka jira in shiga in fito zaka ga abun da zan sa ayi maka" cike da 6acin rai ya k'arasa maganar tare da juyawa ya shige cikin gidan, jiki a sa6ule Mujaheed ya juya ya nufi Motarshi yana k'walla ya bud'e ya tafi, duk wannan abun Fauzy bata san da an yi ba, tun daga ranar Mujaheed ya hak'ura da neman Fauzy amman fa kullum son ta da nadamar abunda yayi mata k'aruwa yake a cikin ran shi, (Allah ka kiyashe mu aikin dana sani mara amfani Amin).
Yana zaunen idon shi akan Tv wayar shi dake a gefen shi ta shiga yin ruri, kai idon shi yay kanta yaga Usman ne mai kiran nashi ya kai hannu ya d'aukko ta tare da yin picking, bayan sun gaisa ne yace mashi yaga hotunan dake ta trending a social media Mujaheed d'in yace mashi a'a tun d'azun rabon shi da online Usman yace mashi Ok ya hau Facebook yanzu tambayar shi yay lafiya yace ya dai hau zai gani yace Ok, bayan ya katse Wayar kunna Data d'in shi yayi a ranshi yana ta raya to miye zai gani, yana hawa hotunan su Fauzy ya ci karo dasu farko bai ganeta ba koda ya karanta rubutun dake sama wanda aka sa d'an Governor d'in Nasarawa Sameer Bello Abdullahi zai yi Wuff da yar talakawa daga jahar Katsina a garin Funtua mai suna Fauziyya Ahmad Rufa'i, shiga yay cikin uban comments d'in mutane ya fara bi yana karantawa duk da hakan bai gane ita bace yana cikin karantawar Usman ya sake kiran shi bayan ya d'aga yace mashi yaga wadda zata auri d'an Governor d'in yace mashi eh ya gani ance yar nan Funtua ce wannan maganar yasa Usman ya gane bai ganeta ba yace "wai baka gane Amaryar bane?" Amsa ya bashi da eh da alamun mamaki Usman yace "lallai Mujaheed baka a cikin hayyacin ka wllh, yanzu Fauziyya d'in ce baka gane ba?" jin sunan Fauziyya yasa shi maimaita sunan sai lokacin hankalin shi ya koma kan sunan Amaryar da ya gani an rubuta nan take ya gane Fauzy ce, wani irin bugu gaban shi yayi da sauri ya mik'e tsaye.........
96
_ASM BY ZAINAB BATURE_
~_*✊💋BOSS LADIES WRITERS💋✊*_~
............Da tsananin Al'ajabi Mujaheed yace "U.....sman wai kana nufin Fauziyyata ce wannan Amaryar?" Amsa ya bashi da eh mana bai duba hoton bane sosae, kan Mujaheed ne ya d'aure fuska a hautsine ya shiga fad'in amman taya hakan zata faru taya za'a ce zata auri d'an Governor, Usman na murmushi yace abun Allah ai ba abun mamaki bane don wannan kad'an daga cikin ikon sane,
"ka gane Usman abunda nike nufi irin wannan Mutanen had'uwa da su ba abu ne mai sauk'i ba balle kuma har ta kaiga ace zasu yi aure kuma nasan labarin mahaifin yaron ba K'aramin mai kud'i bane yana daga cikin Governors masu kud'in gaske fa taya za'a ce hakan zai faru kodai ba ita bace suna ne yazo d'aya!" hankali tashe yake Maganar,
"Wannan duk ba wani abu bane Mujaheed da Allah ya so Shikenan zaka ga ya kasance cikin sauki tunda gaba d'ayan mu duk bayin sane shi yake iko da mu" yarfa hannu Mujaheed yay kaman zai saka kuka yace amman wai taya suka had'u ma, Usman yay yar dariya yace "ta yadda Allah ya had'a ku haka shima ya had'a su, ance ta dalilin karatun da take a Katsina suka had'u ni kaina nayi