Showing 354001 words to 357000 words out of 512766 words

Chapter 119 - Asanadin Makwabtaka Book 3 Hausa Novel Complete

Unknown   

27 Dec 2024

1572

tana son yi mata magana amman ba dama sai faman kallon ta take da alamun Al'ajabi, sallama ta k'ara yi masu ta shiga ciki har ta rufe k'opar sai kuma suka ga ta bude, kud'i ta mik'a ma Zainab rafar yan dubu dubu sabbi dal ta dubu d'ari tace gashi ance su raba saidai Sa'adatu ce ta amsa don gaba d'aya Zainab tayi Mutuwar tsaye, har Motar ta bar harabar Makarantar suna tsaye cirko cirko saida ta 6ace ma ganin su sannan suka juya kan Zainab nan fa suka shiga yaba irin kyaun shi har Sa'adatu na fad'in ko ina ta samo shi sai kuma tace ta tuna lokacin da aka raba kayan saka ranarta ance d'an uwan mijin Fateema Ard'o ne ba mamaki don an gan shi haka, Safiya ce tace amman dai da gani ya jik'u da Naira wllh ga mugun aji ji yadda yay masu magana ma, sai lokacin Zainab da still tsananin mamaki ke a kwance akan fuskar ta tace "to ku duk baku ma san wani abu ba, wllh wanccan mutumin da kuke ganin shi d'an Governor ne" zaro ido sukai tare da bud'e baki a tare suka furta "d'an Governor!!!" Kai ta d'aga masu cike da tabbaci tace masu da suka je bikin Fateema Ard'o Abuja a kan idonta suka zo shida Mahaifiyar shi da yan uwan shi a cikin jiniya d'an Governor d'in Nasarawa ne... Nan ta kwashe komai har yadda Sameer d'in ya fito daga cikin Mota ya shiga cikin gidan da dangantakar shi da Mijin Fatuu ta fad'i masu, nan fa duk suka shiga tsananin mamaki ba dai kamar Zainab da kanta ya gama daurewa ta yadda akai har suka san juna shida Fauzy har abun ya kai ga za'ai aure, a fili ta furta ashe shiyasa suna dawowa ta canza waya zuwa latest iPhone, gaba d'aya al'ajabi ma ya hana su yin murnar kud'in da aka basu da alama kuma gobe dole Fauzy tasha tambayoyi a wurin Zainab.

Suna fitowa daga cikin Makarantar cikin girmamawa driver d'in ya d'an juyo ba tare daya kalli Sameer d'in ba ya tambayi ina zasu, kallon Fauzy yayi da tayi zuru yace ta bashi address d'in gidan Sister d'in ta tace to, basu wani d'auki lokaci ba suka karaso Unguwar don kusa take da Makarantar tasu, kallon shi tay bayan sun tsaya ya d'an d'age kanshi jikin seat idanunshi a lumshe, ce mashi tay sun iso ya d'an d'aga mata kai ta k'ara cewa suje, shiru kaman bazai tanka ba can ya juyo suka had'a ido yace taje ta sanar ta d'aga mashi kai, lokacin data fito Driver d'in na tsaye yana ganinta cikin girmamawa ya tambayi kayan boot fito da su za'ai tace mashi eh, yana k'ok'arin d'aukar mata bayan ya fito dasu tace mashi ya bashshi zata d'auka yace to bari ya kai mata ko bakin gate tayi gaba yana biye da ita a baya, lokacin data shiga cikin parlon tsaye tay tana bin shi da kallo yasha uban gyara sai uban k'amshi ke tashi har labulaye an canza haka kujerun ma da gani har goge su akai don sunyi haske a ranta ta raya lalle Aunty tayi kokari, d'akin Aunty ta nufa lokacin data shiga a zaune ta isketa gaban mirror tana yin shafa, jin sallamar Fauzyn yasa ta juyo suka had'a ido, d'an waro ido tay tace to lafiya ta ganta da kaya nik'i nik'i tana murmushi tace sabon mai iko da ita ne yace ta dawo ta gama yin boarding, k'ara waro ido Aunty tay sai kuma tayi dariya, tambayar ina yake ta yi ta bata amsa da yana waje,

"Amman dai Fauziyya wani lokacin kaman d'an kai gare ki wllh ya zaki bar shi a waje maimakon ki shigo da shi" a d'an harzuk'e tayi maganar Fauzy ta bata amsa da ai shine yace ta shigo ta fad'i, da sauri Aunty ta mik'e tana fad'in don Allah taje ta shigo da shi ta nufi gaban wardrobe don ta saka kaya, a tare da shi suka shigo cikin parlon yana biye da ita, nuna mashi kujera tayi tana murmushi tace "have a sit" saida ya kalleta cikin ido sannan ya nufi kujera 2 seater ya zauna, tsaye tay ta had'e hannuwanta tana kallon shi da murmushi shi ma idon shi na kanta yana bin ta da wani kallo da sai kace yar harararta yake amman ta fahimci wani lokacin haka yake kallon shi, ganin tayi mashi kerere yasa ya furta mata bata iya neman wuri ta zauna, kujerar dake gefen tashi ta nufa ta zauna,

"Aunty tana zuwa yanzu" bayan d'an wani lokaci ta fad'a ya jinjina mata kai,

"Ka zo lafiya" ta tambaya still Murmushi take yay shiru sai kuma ya amsa mata da lafiya, janye idon shi yay daga kan ta ya jinginar da shi ajikin kujerar tare da lumshe ido, tana ta kallon shi can ta furta ya gaji ne yana a yadda yake ya d'an girgiza mata kai, juyar da kai tayi daga barin kallon shi a ranta tana raya magana dashi aiki ce babba, lokacin Aunty ta fito ta nufo cikin parlon tana sanye da doguwar rigar had'addan lace ta sa d'an kunnan zinari hannunta sanye da Agogo haka kanta tayi d'aurin kallabi mai kyau, tun kafin ta k'araso ta shiga washe baki idon ta akan Sameer da ya lumshe ido, saida tayi sallama sannan slowly ya bud'e idon nashi, a kujerar gefen wadda Fauzy take ta zauna tana faffad'an murmushi tace "Barka da zuwa, fatan an zo lafiya" amsa mata yay da lafiya lou ya janye idon shi daga kanta, k'ara tambayar ya ya baro Mutanen gida tayi ya amsa da lafiya ba tare daya k'ara kallon ta ba, shiru duk sukai tana murmushi idon ta akan shi can ta k'ara cewa "an gode da abubuwan Alkhairi Allah ubangiji ya k'ara girma da daukaka" slowly ya furta "Ameen" ta d'an kalli Fauzy dake d'an murmushi itama shine akan fuskar tata, shiru duk sukai parlon sai kace ba mutane Aunty Mareeya sai d'an kai idon ta take tana kallon shi acikin ranta ta shiga tuno da ranar data fara ganin shi da suka zo Abuja bata ta6a zaton akwai ranar da zasu zauna haka da shi bama balle ta kai ga zancen Auren k'anwarta, mik'ewa tay tayi ma Fauzy alamar ta biyo ta da hannu ta mik'e saida ta kalleshi tace mashi tana zuwa ya d'aga mata kai, wurin dining suka nufa Aunty ta nuna mata kayan abinci dake sama k'asa k'asa da murya tace "gashi nan sai ki mashi magana yazo ki serving nashi" kai Fauzy ta d'aga idon ta akan jigunannun Warmers d'in da aka jera a saman table d'in set biyu babba da k'arama set d'aya na Aunty ne ta san su d'ayan kuma sam bata san Aunty dasu ba a ranta ta raya k'ilan duk na chef d'inne amman sun had'u ba k'arya, bubbud'e mata su ta shiga yi babba d'aya farar shinkafa ce washarr washar gata zak'o zak'o sai k'aramar warmer d'inta tana bud'e ta wani irin kamshi mai dadi ne ya karad'e wurin vegetable soup ce gwanin kyau a ido ingredients d'inta an yanka su manya manya taji hanta, d'ayar babbar Warmer d'in kuma fried spaghetti ce tayi brown gwanin burgewa itama sai faman zuba k'amshin spices take gashi tasha vegetables su tsanwan tattasai Karas koran wake da dai sauran su gashi tasha nama ca6a ca6a, d'ayar warmer d'in ta k'arshe kuma pepper chicken ne ciki, bayan ta gama bubbud'a mata tace mata akwae coleslaw a cikin Fridge,

"Amman Aunty duka order d'in nasu kikai?" Fauzy ta tambaya k'asa k'asa,

"eh mana daga lokacin da kika fad'i man zai zo zuwa yanzu ina zan iya yin wani lafiyayyen Abinci har gara ma spaghetti za'a iya yi amman kuma ba komai nike da shi ba na kayan had'ata tayi kyau haka, kai Fauzy ta jinjina tace hakane, "amman ai sun yi haka ko?" da sauri Fauzy tace "ah sosae ma kin yi mana dubara naji dad'i wllh" yar dariya Aunty tay tace "jin dad'in ki your excellency shine nawa" hannu Fauzy ta kai ta gumtse dariya,

"Yanzu kije ki mashi magana yazo ya ci" kai Fauzy ta d'aga sai kuma tace "Allah ma yasa ba wahalar banza akai ba ta tanadar su don yana iya k'in ci wllh" da sauri Aunty Mareeya tace "in ya ki ci ai ke zaki sashi dole yaci ko, taya zai tako yazo kuma yace bazai ci komai ba ke kuma ki bishi da ido, anya Fauziyya, gaba d'aya wani lokacin sai ki kaman ba wayyaya ba wllh na lura kaman baki iya soyayya ba ko dai kin k'arar da ita a wurin shashasha d'in can, kije ki mashi magana in ya nuna bazai ci ba kice baki yarda ba sai ya ci a cikin sigar yar shagwaba shagwaba zaki mashi magana dole fa sai kin zage damtse wllh ke ce zaki koya mashi sakin jiki da mutane bama kamar ke in ba haka ba yana a haka d'in can wllh kece Masha wuya ki ga fa yadda magana ke mashi mugun wahala ga ba sakin fuska don ma dai d'aurewar na mashi kyau tunda kyakkyawan ne....kinga an bar shi shi kad'ai jeki ki mashi magana bari in d'aukko coleslaw d'in akwai ma lemuna a cikin Fridge d'in sai ki tambayi wanda yake so in kuma sai giyar da kika ce yana sha sai kije ki nemo mashi" gwalo ido Fauzy tay jin Maganar tata ta k'arshe Auntyn ta sa dariya ta juya tana fad'in taje, komawa tayi cikin parlon Sameer d'in nata latsa waya har zata zauna a inda ta tashi sai kuma ta tuna da hud'ubar Aunty a d'arare ta nufi inda yake a hankali ta zauna daga gefen shi, idonta akan shi tace "am sorry an bar ka kai kadai naje yin abu ne" kai ya jinjina mata ba tare daya kalleta ba,

"Muje ka ci Abinci" d'an jimm yay kafin ya juyo suka had'a ido tana mashi murmushi, kokarin mik'ewa ta fara taji yace mata ya k'oshi hakan yasa ta koma ta zauna,

"Amman ya zaka ce ka k'oshi bayan nan kazo dole ai kaji yunwa" d'an girgiza mata kai yay yace ba nan ya fara zuwa ba so ya ci Abinci a inda ya sauka, tambayar shi tay a ina ya sauka ya bata amsa da Government House, marairaice mashi fuska tay tace "to amman dai ai nan ma yakamata kaci Abinci tunda nasan Saboda n...." Kasa k'arasa Maganar tay idon shi a kanta slowly yace yana jin ta alamar taci gaba, kikkafta idanu ta shiga yi tana motsa baki ganin irin kallon da yake mata ne yasa da k'yar ta furta "Saboda ni ka zo" kawai sai gani tay yay d'an murmushin gefe wanda tunda yazo bai yi kamar shi ba don har gefen fuskar tashi ya d'an lotsa, d'age mata gira yay yace "Who told you dat?" shiru tay tana cigaba da kikkafta ido taji ya sake cewa ba tambayar ta yayi ba,

"Ba kowa, ni nayi tunanin hakan" shiru yay yana kallon ta cikin k'arfin hali ta furta "hakane?" wani kalan motsa baki yay tare da yi mata wani kallo yace in ta cancanci hakan to hakane, faffad'an murmushi tayi tace "eh nayi deserving hakan" d'an ta6e baki yay da alamun murmushi yace a matsayinta na wa ba tare da jin wani d'ar ba ta furta "Your wife to be in sha Allah" bin ta yay kawai da ido sai murmushi take tana niyyar k'ara yin magana Mijin Aunty Mareeya ya sawo kai cikin parlon da sallama su Hanif na biye da shi gaba d'aya suka kai idon su akan shi ganin shine yasa Fauzy saurin sauke kanta don sai taji kunyar zamanta a kujera d'aya da Sameer ta kamata, inda suke ya nufo yana zuwa gaban Sameer cikin sakin fuska ya bashi hannu suka gaisa yayi mashi an zo lafiya nan ma ya amsa mashi, d'an rankwafawa Hanif yayi yace mashi ina wuni ganin haka yasa su sultan ma suka yi duk ya amsa masu fuskar shi a d'an sake, juyawa Abban Hanif yay bayan sun gama gaisawar ya nufi hanyar Bedroom su Hanif na biye dashi gaba d'ayan su Uniform ne ajikinsu sun goya School bag da gani daga Makaranta ya d'aukko su ,

"Pls muje kaci Abincin" Fauzy ta fad'a da yar sigar shagwaba idon shi akanta yay shiru, mikewa tayi tana mashi wani kallo a kokarin ta na tayi abunda Aunty tace, shiru ya d'an yi kafin yace shi bai cin Abinci in ya riga ya koshi ya fad'a mata ya riga ya ci so ba sai yaci wannan ba, tsaye tayi tana kallon shi bayan ya gama yin Maganar shima kallon nata yake can ta nufi kujerar gefen shi ta zauna ta maida fuskarta tana kallon gefe,

"Are u angry?" tana haka taji ya jefo mata tambayar, juyowa tayi suka had'a ido tay shiru bata bashi amsa ba, "I'm asking you!" Ya sake fad'a, saida ta d'an had'iya miyau kafin a sanyaye tace "a'a kawai dai naji ba dad'i ne, saboda ni kazo kuma gashi kace bazaka ci Abinci bana at least ko d'an Yaya ne sai ka ci pls" d'an murmushi yay bai ce komai ba tana ta kallon shi can taji yace Ok zai ci sai taji dad'i, washe baki tay tana yar dariya sosae taji dad'in cewa da yayi zai ci don ko ba komai hakan ya nuna zata iya sashi abu, mik'ewa tayi tace suje ya taso shima ya mik'e, bayan sunje dining area d'in da kanta taja mashi kujera ya zauna, fara serving nashi tay ta zuba mashi farar shinkafar da veg soup d'in bata sa da yawa ba don tana son sauran ma yaci, a nutse ya fara ci tana zaune daga gefen shi can ya kalleta yace ita bazata ci ba tace sai ta gama Serving nashi, da kai yay mata alamar ta zauna ta ci murmushi tayi ta mik'e don ta zuba, yana kusa gama cinye shinkafar ya aje spoon d'in tana ganin haka tay saurin mikewa ta fara zuba mashi taliyar itama yar kad'an tasa ta janye plate d'in gaban shi ta tura mashi na taliyar ganin haka yasa shi d'agowa yana mata wani kallo cikin marairaicewa ta d'an langa6ar da kai tace "pls shima bai da yawa ai" cigaba da kallon ta yay yana d'an motsa baki kokarin mikewa ya fara yana fad'in bai san a ina take son ya zuba shi ba wannan ma ya gaya mata ai a k'oshe yake kawai sai ji yay ta kawo hannu ta ruk'e nashi alamar kar ya tashi ita kanta bata san ya akai ta aikata hakan ba, dakatawa yay ya kai idon shi akan farin hannunta dake a ruk'e da nashi kafin ya d'ago ya kalleta sai d'an zare ido take gabanta na faduwa, a hankali ta saki hannun nashi tare da sadda kanta k'asa bayan d'an lokaci jin shiru yasa ta d'an d'ago idanunta ta kalle shi karaf suka had'a ido yana ta kallon ta yan kame kame ta shiga yi ta kasa tsaida idon ta cikin nashi don idanun shi nada kaifi bazata juri irin kallon ba,

"Ka yi hak'uri, dama don Saboda kai ne akayi shiyasa" tana d'an kikkafta idanu ta fad'i hakan, bai ce komai ba sai gani tay ya kai hannu ya d'auki fork d'in ciki ya fara ci a nutse har bata san lokacin data saki murmushi ba ta koma ta zauna, kaman rabin wanda ta zuba mashi yaci tana ganin ya aje fork ta d'ago ya d'age mata gira yace Shikenan hakan yayi mata ya ci kai ta d'aga mashi still da d'an murmushi sai kuma tace amman da sauran wanda bai ci ba wani kallo mai kaman harara ya wurga mata tayi dariya tare da mik'ewa, pepper chicken d'in ta bud'e tasa mashi k'atuwar cinya hada tambayar shi ta k'ara yay mata shiru yana dai ta kallon ikon Allah don hakan bak'on abu ne a wurin shi yace bazai yi abu ba a matsa mashi zai iya cewa ba wanda ya ta6a mashi haka, turo plate d'in tayi gaban shi bayan ta janye na taliyar tace gashi itama ya ci don Allah ba yawa abu d'aya ne kawai, maida bayan shi yay jikin kujerar da yake zaune ba alamar zai ci sosae ta marairaice fuska tana mashi yar shagwabar ya ci daga shi shikenan, k'arshe dai saida tayi nasarar saka shi yaci cinyar rabi da kan shi ya tsiyaya ruwa a cup yasha kad'an yana k'ok'arin mik'ewa tace lemu fa ya d'an d'aga mata hannu, ganin ya tashi yasa itama ta rufe sauran abinciccikan ta biyo bayan shi, kujerar daya tashi ya koma ya zauna itama ta sake zama a gefen shi, bata dad'e da zama ba taji yace ita bata wanka ne har saida taji yar kunya tana d'an murmushi tace tana yin wanka sosae don kada ta barshi shi kad'ai ne yasa bata je ta yi ba, shiru ya d'an yi sai kuma taji yace taje tayi zasu je government House tare, har saida gaban Fauzy ya d'an fadi jin inda yace zasu je amman bata nuna komai ba tace mashi to,

"Amman lafiya lou a barka kai kad'ai ko in ma Auntynah magana?" ta fad'a bayan ta mik'e da bud'ar bakin shi sai cewa yay tayi mashi mi tace wai ko ta taya shi hira, d'an yamutsa fuska yay ya fara k'ok'arin mik'ewa bayan ya tashi tsaye yace zai jira ta a Mota amman kar tay keeping nashi bai hakurin haka ta d'aga mashi kai ya nufi hanyar fita daga parlon tabi bayan shi da ido har ya fuce, wani k'ayataccen murmushi ta saki tana jin son shi na ratsa mata zuciya tabbas tasan indai ta aure shi ba k'aramar mai sa'a bace ita, da sauri ta nufi hanyar Bedroom d'inta tana zuwa direct toilet ta nufa a can ta cire Uniform d'in jikinta, after some few minutes ta fito d'aure da towel a

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login