Showing 261001 words to 264000 words out of 512766 words

Chapter 88 - Asanadin Makwabtaka Book 3 Hausa Novel Complete

Unknown   

27 Dec 2024

1620

ta yafa mayafinta kawai tace Ok, nufar k'opa tay tana ce mata sai ta dawo Fatun tace a gaida mata shi. Bayan fitar Jidderh bada dad'ewa ba wayar Fatun ta fara ringing, ganin mai kiran nata yasa ta saki murmushi kafin tay picking, gaishe da shi tay bayan ya amsa ya tambayi sun dawo ne tace mashi eh tun d'an d'azu ma,

"Shine ko ki kira ni kina mantawa da ni ko" murmushi tay a shagwa6e tace "zan iya mantawa da kai na kenan, ai kai ne ni so ban iya mantawa da kai Hubby u'r always in my heart, kai ne ma zuciyan nawa ai" tana jiyo sautin murmushin shi can yace "ya akai kika iya wannan d'in?"

Dariya ta saki tace "ai da mutum ya samu abunda ran shi ke matuk'ar so yake iyawa" murmushin ya k'ara yi kafin ya tambayi mi take yi ne tace mashi Abinci take ci tama gama, ce mata yay in ba abunda zata yi tazo part d'in shi yana son su gaisa da Cousin brother d'in shi da suka zo tace to, bayan sun gama wayar mik'ewa tay ta nufi toilet don ta wanko hannuwanta, bata dad'e ba ta fito ta nufi gaban mirror ta fara gyara fuskarta ganin bata dad'e da saka rigar ba yasa ta yanke ta barta kawae ta gyara gyalen kanta daga gaban kanta ya kwanta sosae don harda salon aka mata, d'aukar kayan Abincin tayi ta nufi hanyar fita saida ta saka takalmanta dake a bakin k'opa sannan ta tafi, bayan ta aje kayan Abincin a Kitchen d'in nan parlon ta k'opar baya ta yanke ta bi sai tabi ta k'opar dake kai mutum sama don kunya take ji ta bi ta parlor wani ya ganta, tana fitowa bayan suka had'e da Fauzy itama tayi wanka tana sanye da k'ananun kaya riga da skirt ta yafo gyale, tsayawa Fatuu tay ta k'araso wurin ta tace dama wurin ta zata je ashe itama nan zata zo tace mata suje d'akin su to, Fatun tace mata ba nan zata ba Ya Haisam ne ke neman ta zata gaisa da wani d'an uwan su,

"Ok bari in koma to, in kin dawo zaki shigo ne muyi fira?" Fatun tace "to ki zo mana ki rakani in muka dawo ba sai mu wuce nan d'in ba" kallon kanta Fauzy tay tace to bari taje ta sako Hijab ko babban gyale wannan kaman yayi k'arami Fatun tace tayi lafiya lau ai dare ne kuma zuwa kawae zasu yi su gaisa su juyo, tare suka tafi ta k'opar bayan suka bi, Haisam na Zaune a parlor jikin shi sanye da jallabiya mai gajeran hannu ya d'an kishingid'a yana kallo daga gefen shi Sameer ne a saman 2 seater daga shi sai farar vest Kal da short basu dad'e da suka dawo daga Masallaci ba yayi wanka Haisam yasa aka kawo mashi Abinci, a saman center table Abincin yake saida wadda ta kawo tayi serving nashi sannan ta tafi, knocking d'in kopar Fatuu tay k'asa k'asa ta jiyo Muryar Haisam d'in yana bada izinin a shigo, a hankali ta tura k'opar tana sa kai suka had'a ido ya sakar mata murmushi itama murmushin ta maida mashi ta idasa shigowa Fauzy ma ta shigo da sallama suka nufi cikin parlon, a kujerar dake Opposite da su Haisam d'in 3 seater suka zauna, Fauzy sai yaba had'uwar parlon take a ranta sosae ya burgeta don baida hayaniya, gaida Haisam d'in Fatuu tay tana murmushi ya amsa Fauzy ma ta gaishe dashi, kallon Sameer Fatuu tay ta gaishe da shi idon shi akan Abincin da yake ci ya jinjina mata kai ita Fauzy sai lokacin hankalinta ya kai kan shi itama ta gaishe shi yadda yayi ma Fatuun haka yayi mata, Haisam ne yace mashi ga wife en tashi, nan ma kai ya d'aga, gaba d'aya su Fatuu mamaki ne ya kama su suka bi shi da ido ganin ko kallon su ya k'i yayi,

"If you Don't look at her ta ya zaka san ta?" Haisam yay Maganar yana kallon shi, shiru kaman bai ji abunda yace ba sai da aka d'an d'auki lokaci sannan slowly ya d'ago da fuskar, gaba d'aya saida gaban su ya fad'i ba don komai ba sai ganin kamar shi da Haisam d'in, nuna mashi Fatuu Haisam yay ya jinjina kai daga haka ya maida shi kan Abincin shi, gaba d'aya Al'ajabin shi ne ya kama Fauzy har ta kasa janye idonta daga kan shi ita kuwa Fatuu maida kan ta tay kan tv tana kallon Film d'in da Haisam ke kallo suna yi suna kallon juna suna sakar ma juna murmushi, Fauzy ta saki baki tana ta kallon Sameer dake cin Abinci a gayance ba zato kawai sai gani tay yayi mata kallon k'asan ido ba arziki ta sunnar da kanta ta koma kallon Carpet don da ganin kallon hararar ta yayi, can bayan wani lokaci ta k'ara d'agowa tana kallon shi kawai sai gani tay ya d'ago gaba d'aya Fuskar nan a tamke da sauri ta sauke idon ta k'asa gaban ta na wani irin bugu tsoron ta kar yace mata wani abu game da kallon shi da take, janye idon shi yay daga kanta ya yago tissue ya fara goge bakin shi, mik'ewa yay bayan ya gama ya nufi hanyar Bedroom Fatuu ta d'an kalle shi da sauri ta kauda idon ta ganin yanayin shigar jikin shi ita kuwa Fauzyn bin shi tayi da kallo har ya shige cikin d'akin sannan ta maida idonta kan tv, bayan wani d'an lokaci Fatuu ta mik'e tace mashi bari su tafi Fauzy ma ta mik'e, ganin shima ya mik'e yasa Fauzy yin gaba, tare suka fito har bayan gidan ya tsaya daga bakin k'opar wurin Fatun ma ta tsaya lokacin ita Fauzy ta yi gaba, tana murmushi tace mashi saida safe yay shiru yana kallon ta fuskar shi a sake, ganin ya k'i cewa komai yasa ta d'age mashi gira tace koda wani abu, slowly ya furta "ba zaki taya ni kwana ba" waro ido tay ta d'an bud'e baki sai kuma tay yar dariya tace "to taya zan taya ka kwana bacin ba kai kadae bane" shiru ya d'an yi idanun shi a d'an lumshe kafin yace "in zaki taya ni ai akwae wani d'akin" da d'an alamun mamaki tace "anan gidan?" Kai ya girgiza mata yace a wani wuri, d'an bud'a ido tay tace "Hotel?" d'an murmushi yay ganin yadda tayi Maganar yace mata ba dole sai hotel ba ai akwae wani gidan, shiru ta d'an yi tana kallon shi yace ko bazata je ba tay d'an murmushi tace in yana so sai taje, hannu ya kai ya shafi forehead d'in shi bayan ya cire ya ci gaba da kallon ta, gaba d'aya ta gama fahimtar shi hakan yasa tace mashi suje d'in, shiru yay lokacin ya tuno sun yi da Fanan zasu fita, sigh yay yace ba wani abu taje ta kwanta ta huta, yamutsa mashi fuska tay a shagwabe tace to ba tace suje ba yana murmushi yace ta bari to sai gobe, ce mashi tay ya tabbatar ba fushi yay ba yana murmushi yace Saboda bai da wuya, itama murmushin tayi yace taje Friend d'inta na jiran ta tace "Good night and dream of me" yana murmushi yace mata wannan ko yaushe ne in dai zai yi bacci, wani irin lumshe mashi ido tay tana dariya dimples d'inta suka lotsa sosae yadda tay ta tafi dashi ji yake kaman ya jawota jikin shi sai dai ba dama don Fauzy ta tsaya daga can gaba tana jiranta, yanata sakin k'ayataccen murmushi yace mata taje ta fara tafiya da baya baya tana murmushi tay blowing mashi kiss, lumshe ido yay ya furta "I love you so much Zaraah" washe baki tay da d'an d'aga murya ta furta "I love too Ya Handsome d'ina" dariya suka saki a tare yace ta tafi lafiya lau kar ta fad'i ta d'aga mashi kai, juyawa tay tana tafiya tana waiwayen shi tana mashi bye bye, sai da ta kusa isa wurin Fauzy sannan ya juya ya koma, tana zuwa wurin Fauzy ta dafa Shoulder d'inta tana dariya tace sorry ta barta tana ta jira tana sallama da Hubby d'inta ne, d'an ta6e baki Fauzyn tay tace "I see, luv birds" k'ara sautin dariyar Fatuu tay, har zasu tafi sai kuma Fauzy ta tsaya tana Kallonta tace "Wai wanccan mutumin da muka je ku gaisa ya suke da Ya Haisam ne?" fad'i mata tay cousin brother d'in shi ne d'an Governor d'in Nasarawa kuma maman shi twins ne da Mom d'in su Haisam nan ta shiga fad'i mata irin yadda suke kama sosae ita bata ta6a ganin yan biyu ba haka,

jinjina kai Fauzy tay tace "amman dai ba K'aramin miskili bane, ke ni tunda uwar data haife ni ban ta6a ganin miskilanci irin nashi ba, kiga fa, wai ya iya ya d'ago ya kalle mu ma abun duniya ya gagara kuma yasan shi aka je gaidawa, ko ba haka bama matar d'an uwan shi ce fa tazo wurin ai ko ba shi aka je gaidawa ba ya dai d'ago a gaisa amman wai har saida aka mashi magana sannan yayi mana wani kallon rashin Arzik'i" dariya Fatuu ke ta yi ganin yadda take Maganar a d'an harzuk'e, cigaba Fauzy tay "nifa Al'ajabi ma ya sa na kasa daina kallon shi wllh, har ko ya kama ni ina kallon nashi akai man wani d'an iskan kallo da saida yan cikina suka juya dama gashi da suffar ban tsoro kinga uban Power d'in daya tara a damtsen shi ni ban ta6a ganin Namiji bama a yadda na ganshi sai ko dai yan gidan mu wannan kuma su ai kaman muciya damatsen su suke in aka had'a da nashi" dariya sosae Fatuu ke yi,

cigaba da tafiya sukai Fauzyn ta k'ara cewa "amman dai suna bala'en kama da Ya Haisam wllh har k'irar jikin kawae bambancin kala ne, amman kin san mi, ni ina son Namiji haka banson wanda ya cika fari" harara Fatuu ta wurga mata tace da bata samu ba ko amman k'arya ne tace wai bata son Namiji fari, dariya Fauzy tay tace "Allah ya baki hak'uri matar fari maida wukar nima na fad'i ne kawai dana samu wanda nike so ni ina ruwana da wani fari ai ko Yellow ne in dai ina son shi auran shi zanyi"

"Yanzu ace yace yana son ki zaki so shi?" tambayarta Fauzyn tay wa, Fatun tace "shi wanccan d'an uwan Ya Haisam d'in" zaro ido Fauzy tay ta kai hannu ta ruk'e ha6a tace "tabbb kema dai da wani bahagon tunani kike wllh, ke yanzu ko wani yace maki wanccan zai so ni zaki yarda mutumin da daga gani zai yi izza ba kad'an ba, ai irin wanccan mutumin wllh matar shi ta bani don kuwa ba k'aramar wahalar shi zata sha ba don daga gani baza'a iya mashi cikin sauki ba, irin su komai akai masu ba'ai masu gwaninta" Fatuu dake dariya tace kawae ta bata amsa in ya ce yana son ta misali da aure zata iya auren shi, shiru Fauzy tay kaman mai nazari can tace "kinga don Allah mu bar Maganar nan abunda baka samu aka ce had'a shi da baka so don haka bai man ba" dariya sosae Fatuu ke yi tana fad'in Allah don bai ce yana son ta bane amman tasan tabbas zata so shi don ta fahimci ya yi mata, murmushi kawae Fauzyn tay zuciyarta na suffanto mata shi a ranta ta raya wannan ta ina ma zai iya wani son ta mima zai yi da ita, daidai lokacin suka iso part d'in da suke suka shiga.

Bayan sun shiga d'akin Toilet Fatuu ta wuce tayo Alwalar sallar isha, bayan ta gama hira suka dasa wadda yawanci duk akan Walimar gobe ce saida suka kai tsakar dare sannan Fatuu ta tashi don tafiya Fauzy tace ta kwana anan kawae mana tace ai gadon bazai ishe su ba tunda akwae wuri can bari taje kawae suka yi sallama dasu Haulat Fauzy ta rakota har waje kafin suka yi sallama ta koma. Washe gari Juma'a ana tashi aka fara shirye shiryen Walima ba kama hannun yaro masu aikin girki tuni sun fara dama tun jiya aka fara aikin nama banda shanun da Baffan Fatuu ya bada harda raguna da kaji aka yayyanka, Misalin k'arfe sha d'aya lokacin duk an gama breakfast Laila tasa Fatuu taje tayi wanka, da kanta taje d'akin Hajiya da yake nan aka kai akwatunan lefenta ta d'aukko mata kayan da zata saka wanda babbar Super ce ta had'u ba k'arya anyi mata straight skirt da riga half gown tare da sark'a da yankunan gold harda yan hannu da su jaka da takalmi da mayafi mahad'in kayan, bayan ta saka kayan Laila ta yi mata yar light make up kafin anjima wadda zata yi mata Bridal makeup d'in ta zo, da kanta ta d'aura mata kallabi abun sai dae ace Tubarkallah, nan fa aka hau yi mata hotuna bayan sun gama Laila ta kamata ta nufi d'akin Mom d'in su da ita, a parlor suka isketa da wasu mutane cikin yan uwan su da suka zo bikin Mom d'in na ganinta ta hau yi mata murmushi tace a kawota gefenta, bayan ta zauna ta gaishe da ita da sauran mutanen ana ta fad'in Ma sha Allah Amarya, mik'ewa Mom tayi ta kamo hannun Fatuu itama ta mik'e suka shiga cikin Bedroom harda Laila, wurin Hajiya Zainab ta kai ta, itama da murmushi ta tarbeta Mom ta sata ta zauna a bakin gado itama ta zauna a d'ayan gefen, gaida Hajiya Zainab d'in tayi da fara'a ta amsa ta yaba gayun nata tare da Addu'ar fatan Alkhairi Laila na amsawa daga baya ta kama hannun Fatun tace suje wurin Hajiya ta mik'e suka nufi hanyar fita idanun su Mom akan su, bayan sun fita Hajiya Zainab tace yarinyar nada kyau Mom dake murmushi tace sosae, part d'in Hajiya suka wuce bayan sun fito, duk suna zaune a parlor suna ta hira harda gwaggo suka shigo Laila tayi sallama duk suka maido idon su kan su suna amsa sallamar, gaishe da Mutanen parlon tay duk suka amsa, gefen Hajiya ta kai Fatun ta zaunar da ita tana murmushi tace "ga kishiyar ki na kawo kiga adon ta" d'an murmushi Hajiya tay ta ta6e baki tana kallon Fatuu da itama kallon ta take tana murmushi sai cewa tay ina ta wani yi kyau haka kamar an bad'a mata k'asa a fuskar, gaba d'aya yan d'akin sukai dariya suna fad'in duk kyaun nan da tayi wannan dai kishi ne ba wani abu ba Gwaggo dae sai murmushi take farinciki fal ranta ganin yadda Autarta ta fito sai kace d'iyar manyan mutane, gaishe da Hajiyar tayi bayan ta amsa ta juya kan sauran mutane ta gaishe da su da fara'a duk suka amsa suka hau yin Addu'oi Laila dasu Hajiya na amsawa daga baya suka bar part d'in, baya suka wuce inda su Haulat suke, lokacin da suka shiga cikin parlon su Yadikko dasu Yaya duk suna zaune suna yin kallo, wurin su Laila ta nufa duk suka maido idon su kanta suna washe baki, zama tayi akan kujera Fatuu ma ta zauna a gefen ta suka hau gaishe da ita, da fara'a ta amsa Yadikko ce tace "wannan kaman Amarya" sai lokacin Laila ta gane ashe basu gane Fatun ba tana yar dariya tace itace ta kawo masu suga gayun ta gaba d'aya suka k'ara washe baki suna fad'in ai su basu ganeta ba Fatuu dai sai murmushi take ta gaida su,Yadikko ce ta daddage ta rangad'a gwad'a sai ga su Mino sun fito da gudu ta nufo ta ai koda taga Fatuu da gudu ta koma cikin d'akin tana fad'in azo aga Adda Fatuu Amarya tayi kaman sarauniya, nan duk suka firfito harda su Aunty Mareeya Fanan ma na a d'akin su tafi zama a wurin su duk da a d'akin Laila ta sauka, nan fa aka shiga yabon gayun aka hau yin hotuna da ita Fanan tace ai yakamata a kawo photographer Saboda ayi hard copy na tarihi Laila tace zai zo sai anjima sunyi Magana yace na iPhone d'in ma lafiya lou zai wanke su tace Ok, bayan sun gama hotunan Laila ta k'ara kamo hannunta ta fito da ita, part d'in Haisam ta wuce da ita suka shiga ta baya, knocking k'opar tayi aka bata izinin shigowa ta tura, su biyar ne a zaune, Haisam, Sameer, Salim, Abbas sai wani abokin su d'an nan Abujar Na'eem, da murmushi Laila ta nufi cikin parlon idanun su gaba d'aya akanta banda Sameer da yake sanye da headphones da alama ma bai san ta shigo ba, tunda suka shigo idon Haisam na akan Fatuu suna ta sakar ma juna murmushi, gaishe su Laila tayi tace ga Amaryar su nan ta kawo masu su ga gayunta na farko duk suka maido idon su akan Fatuu, kunya ce ta kamata da sauri ta sunnar da kanta k'asa ta gaishe dasu Abbas ya shiga tsokanar ta, mik'ewa Haisam yay jikin shi sanye da k'ananun kaya basu dad'e da gama yin Breakfast ba, inda suke tsaye ya nufo yana zuwa ya kai hannu ya kamo Fatun kawai sai ya rungumeta gaba d'aya Abbas da Na'eem suka sa sowa shi dai Saleem murmushi yake, abunda su Abbas ke yi ne ya jawo hankalin Sameer ya d'ago ya kalle su Abbas ya fara masu Video, gaba d'aya wata irin kunya ce ta kama Fatuu ji take kaman ta nutse k'asa, kokarin d'ago da kanta ya fara yi ta kafe kan tak'i yarda ya d'ago ta, d'ukar da kan shi yay can k'asan mak'oshi ya furta tayi kyau sosae murya can k'asa tace don Allah kunya take ji ya fita da ita ya furta Ok, d'agota yay tak'i yarda ta kalli side d'in da su Abbas suke yace ma Laila suje yana ruk'e da Fatun yayi mata side hug suka nufi hanyar fita ta cikin parlon

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login