Showing 300001 words to 303000 words out of 512766 words
Chapter 101 - Asanadin Makwabtaka Book 3 Hausa Novel Complete
Unknown
27 Dec 2024
1647
Mino ta shigo da yar sallama jikinta sanye da Hijab duk suka kai idon su kan ta suna amsawa, kan ta a k'asa ta k'araso cikin parlon, a d'ayan bangaren ta zauna ya zamana suna facing juna da Nameer, gaishe dasu tay ba tare da ta d'ago kanta ba duk suka amsa, shiru suka d'an yi kafin Dad yay d'an gyaran murya idon shi akan Nameer yace mashi Hajiya ta fad'i mashi sak'on shi shine suke son ji daga gare shi da gaske yana son ta, shiru Nameer yay kan shi a k'asa gaba d'aya idanun su na akan shi, ganin yak'i magana yasa cikin d'an d'aga murya Dad yace,
"C'mon Ka bud'e baki kai mana magana my friend! baka ji nauyin wadda ka ba sak'on ba sai mu" duk murmushi akai k'asa k'asa Nameer yace Eh,
"Eh what?" da k'yar ya furta eh yana sonta ba tare da ya d'ago ba, "kuma zaka Aure ta?" kai ya d'aga kafin yace eh,
"Ka sani in muka riga muka gama magana ba zancen ka dawo ka ce ka canza ra'ayi" da sauri ya jinjina mashi kai, maida idon shi yay kan Mino itama ya tambayeta tay shiru bata ce komai ba, k'ara tambayar ta yay nan ma tak'i tace komai baffan Altine ne cikin d'aga murya da fulatanci yace mata bata ji ana magana bane still bata ce komai ba idon Baffan ta na a k'asa, Ardo ne yay yar tsawa Dad yace su rabu da ita hakan data yi ta nuna masu ita cikakkiyar bafullatana ce, Albarka ya saka masu duk aka amsa da Amin yace su tashi su je,
A tare suka mik'e dukkan su kan su na k'asa suka nufi hanyar fita daga part d'in su Dad suka cigaba da tattaunawa, suna fitowa bakin k'opar part d'in Nameer ya kai hannu ya kamo hannunta ta waro ido ya jata tana ta waige waigen kada wani ya gan su, bayan part d'in ya nufa da ita sannan ya sake ta suka bi juna da kallo fuskokin su d'auke da murmushi,
"Yanzu hankalin ki sai ya kwanta sosae kin zama tawa na zama naki" Nameer ya fad'a yana dariyar farinciki, itama dariyar take sosae take ganin abun kamar a mafarki daga fara soyayyar su har an yi Maganar aure ta wani bangaren dad'i ne cike da ranta,
"Yanzu ya za'ai Maganar karatun ki don ni gaskiya dana gama nan da one year in sha Allah za'a d'aura mana Aure tare da Yaya Laila" cikin tabbatar mata da hakan yay Maganar, shiru ta d'an yi sai kuma tace mashi to yayi duk yadda yake so, yana murmushi ya d'age mata gira "kenan k'in amince muyi aure ko baki gama Secondary d'in ba?" Kai ta jinjina mashi tace in dae zai barta taci gaba,
"in kuma ban son kici gaba da karatun fa?" Still da murmushi akan fuskarta ta d'an yarfa hannu tace mashi Shikenan zata hak'uri, wani k'ayataccen murmushi ya saki yace ashe haka take son shi ita dai murmushi kawae take,
"Ki sha kurumin ki zaki karatu har sai kin ce ya ishe ki, saidae gaskiya bana son a rink'a kalle man ke ya za'ai kenan?" Yar dariya tayi tace sai ta rink'a rufe Fuskar ta to, lumshe mata ido yay ya furta "that's what makes me love u more babe, duk abunda nike so kina so in sha Allahu zan yi bakin kokarina wurin saka ki farinciki bazaki ta6a yin dana sanin amince mani ba" jinjina mashi kai tay tana ta murmushi,
"Kema zaki man haka?" Da sauri ta d'aga mashi kai kafin ta furta "in sha Allah" yace Allah ubangiji ya basu iko ta amsa da Amin,
"Gaba d'aya ji nike inama ba sai nan da one year zamu zama ma'aurata ba don gaba d'aya kin mamaye heart ena" yar dariya tay sai kuma tace "ni kai ne heart d'in nawa" tana furta hakan tasa tafukan hannuwanta ta rufe fuska, sosae yaji dad'in Maganar sai zabga uban murmushin jin dad'i yake, hannu ya kai ya cire hannuwan nata suka zuba ma juna ido wani sabon son junan su ke ratsa zuciyoyin su, kasa jurewa Mino tay ta sadda idanun ta k'asa,
"I'm going to miss you" d'ago ido tay a hankali tace itama haka, yar Ajiyar zuciya yayi yace yaso ya canza mata waya amman bai samu yin hakan ba, tambayar ta yay tana da bank account ta girgiza mashi kai alamar a'a, d'an jimm yay kafin yace Shikenan zai tura ma Uncle d'inta sai ya canza mata wayar don su rink'a yin Vedio call lafiya lou suna rage kewar juna, ce mata yay itama yakamata ace tana da account d'in zai sa a bud'e mata don ya rink'a tura mata kud'in da zata rink'a yin hidindimun ta, tana ta kallon shi har ya gama sannan tace mashi ya bar shi ba sai ya rink'a tura mata ba tunda ana mata komai, tun kafin ta rufe baki ya d'an yi mata hararar love yace tun yanzu ta sani hakkin ta ya hau kan shi tana dariya tace ai ba'a d'aura auren ba shima dariyar yake yace eh ai an bashi ita ko.
Bayan su Nameer sun tafi Senator yay ma Alhaji Ibrahim Maganar bada kud'in neman Aure, daga cikin Aljihun jallabiyar shi ya ciro kud'in bandir d'in yan dubu guda biyu wato 200k ya ba Alhaji Ibrahim d'in, mik'ewa yay ya nufi su Ard'o da sauri Baban Altine ya mik'e shima ya tare shi ya bashi kud'in, bayan duk sun koma sun zauna aka yi Addu'oi aka shafa. Bayan tafiyar su Senator Baffan Altine ya bud'e ledar daya basu nan suka ga shaddoji ne guda shidda wato kowa kala biyu, sam bakunan su sun kasa rufuwa tsabar farinciki sai yabon kirkin su Senator suke, mik'ewa sukai don suje su k'arasa shiryawa kowanne su bakin shi a washe, tsayawa Baffan Fatuu yay bayan sun tafi ya fara k'ok'arin kiran Yadikko, lokacin da kiran ya shiga tana cikin d'aki suna shiryawa Kusan ma sun gama kimtsawa, bayan ta d'auka cikin ladabi ta gaishe dashi ya amsa, tambayarta yay sun gama shiryawa tace mashi eh, d'an shiru yay kafin kuma yace Albishirinta tana Jin hakan da sauri ta bashi amsa da goro fari Kal, yadda tay Maganar har saida ta d'an bashi dariya yace mata wani abun Alkhairin ne ya same su yanzun nan, cike da k'aguwa ta tambayi miye, fad'i mata zancen neman Auren Mino dasu Senator suka zo yanzu yay harda shaddoji daya basu da kuma kud'in neman Auren, tun kafin ya gama fad'i mata ta mik'e tsaye don da a zaune take a bakin gado, gaba d'aya mamaki ne ya kamata ta kai hannu ta rufe baki shi kuma sai murmushi yake don ya fahimci taji Al'ajabin Maganar, muryarta na rawa tace "Yanzun Mino itama yaron gidan nan zata aura, to yaushe suka san juna haka mu bamu da Labari" fad'i mata yay a wurin bikin nan kuma an kira shi a gaban su ya tabbatar yana son ta zai aureta, wani irin farinciki ne ya lullube yadikko wanda tunda take bata ta6a jin irin shi ba a rayuwar ta gaba d'aya ta kasa rufe baki su Aysha da suka zuba mata ido ganin yadda take farinciki yasa suma suka shiga washe bakin haka innar su Altine ma dake zaune a cikin d'akin idon ta na akan ta, bayan sun gama wayar da sauri ta tambayeta ya akai taga tana ta farinciki ne nan take sanar mata, itama tsananin mamaki ne ya kamata ta waro ido can kuma sai ta mik'e zumbur ta nufa hanyar fita, d'akin su Yaya ta nufa duk sun shirya suma suna zaune a bakin gado suna had'a jakunkunan kayan su ta fad'o kamar an jefo ta duk suka d'ago kai suka kallo ta, Yaya ce ta d'an 6ata fuska tace lafiya zata fad'o masu haka ba sallama, hak'uri ta basu tay tsaye tanata zare ido ta ma rasa ta ina zata fara, ganin yanayin ta yasa Yaya tambayar ta lafiya, ai kaman tana jira ta hau fad'i masu zancen an nemi auran Mino itama zata auri yaron gidan nan, wani kallon mamaki gaba d'ayan su suka bita dashi Yaya ta maimaita Maganar cikin d'aurewar kai Babar su Altine tace wllh yanzun nan mahaifin su ya kira innar su yana fad'i mata, hannu Yaya ta kai ta ruk'e ha6a tana jinjina kai ita kuwa kishiyar tata murmushi ta shiga yi tana fad'in "kaga ikon Allah, ashe da rabon zamu k'ara zuwa gidan nan shan wani bikin, lallai iyalin Muhammadu masu jinin sa'a ne....." A dak'ile Yaya ta katseta da fad'in "Uhmm wai jinin sa'a, ai ni gaba d'aya sai yanzun ma na fahimci komai, wannan sa'ar ba ta Allah da Annabi bace, wato da suka ga ita ta farkon ta samu mai Arziki shine itama wannan sukai kulle kullen su suka tura ta binni, kai da ganin wannan kasan aikin asiri ne ace yana ganin ta ya fara sonta har an tsaida magana, ita kadae ce yarinya a wurin bikin ba ga yan mata nan yan binni ba, ke ita kanta babbar ma ni yanzu ban yadda hakanan mijin nata ya aure ta ba tun farko k'ulla soyayyar ta su akai shiyasa ta tashi hankalin ta da taji Ard'o ya bayar da ita, gaba d'aya sai yanzu na gano komai, ita ce ta kitsa ma Yarinyar ta gudu ta koma bayan tayi shiri sosae kan shi mai kud'in da shi Alhaji Lawan d'in shine ta zo har tayi nasarar sa shi janye Maganar aka kawo ta wanccan" Fuska a hautsine take Maganar cikin harshen fulatanci duk sun zuba mata ido, mik'ewa tay ta cize baki idon ta a kan su rai 6ace tace "gaba d'aya sai yanzu na gane komai daya faru mak'ark'ashiya akai, shima Ard'o harda shi aka ma Asiri shiyasa ya yarda aka fasa da wanccan ya kafe kan sai anyi da wanda ta Auran" jinjina kai innar su Altine ta hau yi fuskarta a yamutse gaba d'aya wata irin hassada ce ta mamaye mata zuciya, kai da kawowa Yaya ta shiga yi ta k'ank'ance idanunta ta shiga zurfin tunani,
"in dai ina raye to bazan bari Yaron ya auri Mino ba, tunda abun hakane nima zan yi abunda suka yin in sa a maida Auran kan d'aya daga cikin jikokina tunda ai ba fina iyawa su kai ba, ba abunda nike bari ya sha man kai, itama uwar Muhammadun da ta nemi zame man matsala ai ba k'aramar uk'ubata tasha ba kafin Allah ya d'auke abun sa, suma jikokin nata ban ta6a zaton haka abun zai kasance ba da tun wuri na d'auki mataki a kan su amman duk da haka lokaci ai bai k'ure man ba ko ya k'ure ba abunda zai gagara, har ita ta farkon sun ja bazan k'yaleta ba sai na raba Auran nata nasa ta dawo ruga anan zatai Aure......
86
...........bata samu k'arasa Maganar tata ba sakamakon buga katifa da d'ayar Matar Ardon mai suna Mero dake a zaune tayi fuska a matuk'ar d'aure ta fara magana "Sam bazan bari ki aikata hakan a gare su ba matuk'ar ina numfashi, duk abubuwan da kike yi mana k'yale ki kawae nike ba wai don ina tsoron ki bane, to yanzu an zo ga6ar da bazan zuba maki ido ba wllh sai in da k'arfi na ya k'are" gaba d'aya Al'ajabi ne ya kama su ganin yadda take maida mata martani ba tare da nuna shakkar ta ba kamar yadda suke yi tana juya su, hannu Yaya ta kai ta nuna kanta tace ita take gaya ma magana haka ta manta wacece ita,
"Ban manta ba, ke Mutum ce kamar ni saidai muna da bambanci sosae, ke mushirika ce wadda bata yarda da Allah ba ni kuma na Yarda da Allah ban yarda da shirka ba, don haka a wannan karon na d'aura d'amarar yin yak'i da shirka za kuma muga wanda zai yi nasara tsakanin k'arya da gaskiya, hakanan Saboda tsabar mugunta da rashin tsoron Mahallici mi Mutanen nan sukai maki da kika d'au karan tsana kika d'aura masu, in don mahaifiyar shi da take kishiyar ki ai ta bar maki duniyar ko, in kuma don kina ganin Ardo yafi ji dashi ne ai don yafi sauran yaran nashi gaskiya ne da ruk'on Amana, wato don kina aikata shirka shine kike ganin ita kowa ma ke yi, to tsaya kiji sirrin, matuk'ar mutum zai tawakalli ya dogara ga Allah ya mik'a mashi dukkan lamuransa to zai ta samun cigaba a rayuwar shi wannan dalilin ne yasa kika ga a komai Muhammadu da iyalan sa suke nasara koda kuwa kin aikata masu wani abu ina mai tabbatar maki bazaki yi nasara ba da iznin ubangiji, Idan kuwa ya baki sa'a don wani lokacin yana tara bawa ne kafin ya d'au mataki akan shi in har kika aikata wani abu da yay sanadiyyar fasa yin auren nan to sai na tona maki Asiri kowa yasan ke kika aikata masu wani abu kuma kinsan Mutanan binni bazasu ta6a kyale ki ba kotu za'a kai ki daga can sai gidan yari kuma na tabbatar d'aurin rai za'a maki don sai na fad'a cewa kina da sa hannu wurin mutuwar Innar Muhammadun k'ilan ma harda matar shi innar su inna wuro, a yanzu zan zuba maki ido ne amman zan sanar da Muhammadu da matarsa harda su yaran da Kakar su akan su dage da Addu'a dama dai kinsan ai su ba daga baya ba wurin ruk'o da Addini to har nima zan taya su zamu ga tsakanin mu da ke wanda zai yi nasara" rai a tsananin 6ace tana huci ta k'arasa Maganar dama can tara Yayar take, sototo sukai suna bin ta da ido,
mik'ewa tay tana d'an murmushi tace "ni zanje in taya murna don basu kad'ai abun Arzik'in ya shafa ba harda mu don haka ina mai baku shawara da ku kauda komai a ran ku kuyi farinciki hankali kwance ku dangwali Arziki, ke Yaya in kika kwantar da hankalin ki ma k'ilan Makka da kike ta mafarkin zuwa Masoyin ki Ardo da Ya'yan ki suka kasa kai ki duk da suna da halin hakan sai kiga ta sanadiyyar su kinje har ki k'ara ma sau ba adadi tunda kinfi kowa sanin halin iyalan Muhammadu basu da ruk'o in ba don haka ba da ko kallo a yanzu bazaki ishe su ba amman duk da tsangwama da tsanar da kike nuna masu hakan bai hana su jan ki a jiki ba wanda na tabbatar su wad'anda kike k'ok'arin ganin kin aikata shirka don ki jawo su a cikin Arzik'in ba lalle ko Habujar su bari ki rink'a zuwa wurin su ba balle har ta kai ga su biya maki Makka in ma ace burin naki ya cika kenan, in baki sani ba ki sani duk na kusa dake da kike ganin suna goya maki baya munafukan ki ne da sun samu dama zasu kaskantar da rayuwar ki kamar yadda kike masu" tana gama Maganar ta juya ta nufi k'opar fita, a razane Yaya ta bita da ido har ta fice haka Babar Altine ma, kallon juna sukai sun kasa cewa komai don abu ne da basu ta6a zato ba, sun d'an d'auki lokaci haka da k'yar innar Altine ta ja kafa ta matsa kusa da Yaya dake tsaye kamar an dasa ta, k'ok'arin k'arfafa mata gwuiwa ta shiga yi tana ce mata kada Maganganunta su dame ta ita tana tare da ita abunda za'ai kawae itama ai maganinta ta yadda bazata iya aikata abunda ta fad'an ba sai ayi yadda za'ai Auren ya koma kan d'aya daga cikin yaranta ita kuma ta mata alk'awarin duk abunda take so shi za'a rink'a yi in aka shigo cikin Arzik'in, bin ta da ido kawae Yayar tay daga yanayin fuskarta zaka fahimci ba k'aramar razana tay ba, ci gaba da k'arfafa mata gwuiwa tay can Yayar ta fara girgiza mata kai har saida gaban innar su Altinen ya fad'i,
matsawa Yaya tay ta zauna a bakin gado cikin mutuwar jiki tace mata akwae babbar matsala, dama bokan ta ya ta6a fad'a mata sai ta bi a hankali don a cikin gidan su akwae wadda zata kawo k'arshenta lokacin ta buk'aci sanin ko wacece yace bai samu gano kowacece ba amman tabbas sai tayi taka tsantsan don ba K'aramin tagayyara rayuwarta zata yi ba, a lokacin ta rok'e shi ya bata abunda zatai amfani dashi wurin yin maganin ta amman sai ya nuna bazai iya ba don a yadda ya gani ita bada asiri zata yak'e ta ba da ayar Allah ne, baki bud'e innar su Altine data durk'ushe a k'asa take sauraren ta, nannauyar ajiyar zuciya Yaya ta sauke ta hau jinjina kai tace "yanzu na gano k'arshe na da yace zata kawo wato shine in ta tona man Asiri aka kai ni gidan yari" sosae Yaya ta tsorata abun ka da mutumin kauye, nazarin Maganganun kishiyar tata ta shiga yi a cikin ranta tabbas tasan abunda ta fad'a kan iyalan Muhammadu gaskiya ne duk abubuwan da take masu basu nuna rashin d'a'a a gareta in akwae wadda zata ce tana mata rashin kunya to Fatuu ce ita kuma wannan ba ita kad'ai take mawa ba halinta ne haka kuma bayan ta girma yanzu duk ta bari, zuciyarta ce ta raya mata in tayi wasa to fa zata tashi a tutar babu ne, da sauri ta kalli innar su Altine tace mata su hak'ura kawai in ba haka ba zasu shiga matsala in dai suka aikata wani abu gara su goyi baya suma su ci Arzik'in ala bashshi in bikin yazo sai su tattaro sauran yaran da basu da Aure suzo dasu watak'il suma su dace, cike da amincewa innar su Altine ta jinjina mata kai don itama ta tsorata da Maganar da tace bokanta yayi don tasan muddin asirin Yaya ya tonu to itama kuwa bazata sha ba, da sauri Yaya ta yunk'ura ta mik'e tace mata ta taso suje su nuna suna farinciki kar