Showing 363001 words to 366000 words out of 512766 words

Chapter 122 - Asanadin Makwabtaka Book 3 Hausa Novel Complete

Unknown   

27 Dec 2024

2317

jage da k'walla tace ma Mami bari tazo su je Hajiya ta tambayi ina tace mata gidan su Haulat d'in zata tayi ma innar su gaisuwa Hajiya tace mata ta bari ayi Magrib tunda ta kawo jiki sai suje gaba d'aya tace to, komawa tay ta zauna Mami ta mik'e tace masu ta tafi Hajiya tayi mata gaisuwa tace ta yi ma innar su kafin su zo Saude ma tayi mata gaisuwar ta tafi, mik'ewa Fatuu ta k'ara yi gaba d'aya duk ta rud'e Hajiya ta k'ara tambayar ya akai cikin muryar kuka tace mata fitsari take ji tace taje tayi ta shiga k'ara bata hak'uri tana fad'in ta kwantar da hankalinta kai kawai take d'aga mata Saude tace suje ta rakata d'akin Hajiya tace yauwa, saida ta rakata har cikin d'akin sannan ta fito ta koma Kitchen jikinta gaba d'aya yayi sanyi tausayin Haulat yakamata, bayan Fatuu ta fito daga toilet bakin gado ta nufa ta zauna ta kai hannu ta d'auki wayarta da taba Saude ta aje mata bayan sun shigo, Haisam ta shiga kira bayan ya d'aga ta gaishe dashi yana jin muryar ta ya gane ba daidai take ba ko amsa gaisuwar tata baiyi ba ya shiga tambayar ta lafiya Mike damunta, cikin kuka ta sanar mashi shima yaji abun sosae yayi mashi Addu'a kafin ya shiga rarrashinta yana kwantar mata da hankali shima sai faman ce mashi to take saida ya tabbatar ta kwantar da hankalin nata kafin sukai sallama, sai bayan da akai isha sannan suka fito don su tafi gaba d'ayan su sun sa dogayen hijabai harda Saude, Tk ne zai kai su a Motar Fatuu har Hajiya na fad'in ba don dare yayi ba ai da a k'asa suka lalla6a ko Fateema tayi exercise Saude tace to suje a k'asan tunda akwai wuta Hajiyar tace tunda dai ya fiddo Motar suje kawai ko don dare, a k'opar gidan su Fatuu Hajiya tasa ya tsaya tace ma Saude taje ta tambayi Dije in bata je ba ta fito su tafi tace to lokacin shagon Kawu Amadu a rufe yake da alama tunda ya tafi salla ya kulle shi, bada jimawa ba suka fito tare da gwaggon dama Saude gaba ta shiga, baya gwaggo ta shiga inda su Hajiya suke ta gaishe da ita ta amsa tayi mata jaje da gaisuwa, kallon Fatuu tay tace har yanzu kukan take ta girgiza mata kai kafin cikin disasshiyar murya ta gaishe da ita bayan ta amsa ta shiga kara bata hak'uri, lokacin da suka je gidan akwae mutane da suka zo gaisuwa innar ta tarbe su bayan duk sun zazzauna aka shiga gaisawa da yin gaisuwa, koda Fatuu tazo yi mata gaisuwar sai kawai ta fashe da kuka nan fa innar su Haulat d'in itama ta shiga matsar k'walla haka K'annan Haulat d'in suma duk suka dasa dama kuma auren Haulat d'in na zumunci ne duk dangi ne, mutane ne suka shiga basu hak'uri suna fad'in lokacin shi ne yayi yanzu Addu'a yafi buk'ata, daga baya sai ga Kawu Amadu tare da Tk sun shigo suma sukai masu gaisuwar, suna a gidan Baban su Haulat ya dawo daga Masallaci innar tasu ta fita tayo mashi magana ya shigo daga bakin k'opar ya duk'a nan aka shiga yi mashi gaisuwar yanata amsawa tare da yin godiya. Tun bayan da suka dawo Fatuu ke ta trying kiran Haulat ba ta shiga sai bayan da suka dawo part d'in su ita da Mino lokacin sun kwanta cikin sa'a sai gashi kiran ya shiga tana d'auka Fatuu ta saka mata kuka tana fad'in ashe abunda ya faru kenan cikin disasshiyar murya ta wanda yasha kuka Haulat d'in tace mata wllh, jajanta mata ta shiga yi tare da yi mata gaisuwa ganin yadda take ta Kuka yasa Haulat d'in ta shiga rarrashinta tana fad'in don Allah ta bari bata ga halin da take ciki ba Fatun tace wllh tausayin su take ji ba kamar Umma Salma duka yarinyar ko shekara bata yi ba Haulat d'in tace mata eh amman ta kusa saura wata d'aya, jajanta mata taci gaba da yi tana Addu'oi daga baya taba Mino itama tayi mata gaisuwa. Gwaggo da Kawu Amadu ne suka shirya tafiya gaisuwa Nijar Fatuu taso ace da ita za'a saidai itama tasan bazata iya yin wannan tafiyar ba a halin da take ciki, kwana biyu da yin rasuwar suka tafi suna can akai sadakar ukku kwanan su biyu suka juyo.

Bayan cikin Fatuu ya fita daga wata na bakwae ya shiga na takwas da sati d'aya Mom d'in su Haisam tazo tafiya da ita, kwananta biyu suka shirya tafiya bayan Fatuu tayi sallama da kowa Mino harda yar kwallar ta anata yi mata addu'o'in Allah ya sauketa lafiya lokacin da aka raka su Airport, Kusan gaba d'aya aka rakasu harda Hajiya dasu gwaggo Kawu Amadu da Saude da Mino su Aunty Mareeya da Fauzy kowa dai ita dai Fatuu sai d'an murmushi take zuciyarta nata saka mata abubuwa,

Alhamdulillah sun sauka garin Abuja lafiya har anje an d'aukko su sai faman murnar zuwan Fatun ake karma dai Jidderh dasu twins su ji, dole Jidderh ta matsa ta sauka a d'akin ta itama Fatun hakan yayi mata dad'i, washe gari Aunty ta tafi da ita Asibitin su aka yi mata awo don samun record d'in ta. Bayan dawowar ta Abuja Kusan doubling kulawar da take samu a Katsina akai mata, sosae ake ta haba haba da ita koda yaushe cikin tambayar abunda take so ake haka safe da dare cikin zuwa dubata ake duk wanda zai fita sai yazo ya dubata harda Dad da safe kafin ya fita sai yazo ya dubata haka in ya dawo ma da daddare sauran yaran gidan ma da safe kafin su tafi school duk sai sun zo sun dubata haka da sun dawo nan suke fara sauka bayan sun dubata sannan suje suyi wanka in aka shirya ma nan za'a dawo wurinta aci Abinci kullum Jidderh cikin fad'an an 6ata mata d'aki take gashi bata isa ta hana yaran gidan zuwa d'akin ba don ta kora su Mom da kanta ta maido su tace bata isa ta hana wani zuwa ba tunda ta rik'e Fatuu in kuma tana son a daina zuwan to saidai ta bari Fatuu ta bar d'akin ta kafe tace ba inda zata anan zata zauna har ta haihu tana fatan ma Allah ya kawo haihuwar da Sauk'i suna bacci kawai suga ta haihu har saida ta ba Mom da Aunty dariya suka ce to Allah ya sa ta haihu hakan dama Aunty tana d'akin Mom ta zo maido su Yasmeen da twins da aka kora daga d'akin, duk dare su Jidderh da Yasmeen dasu twins ke rakata strolling su zagaye gidan in ta gaji ta d'an rankwafa sai suma suyi hakan kaman sun yi sahun salla in ta mik'e sai su mik'e sosae suke bata nishad'i cike da shiririta ake yin tafiyar har a zagayo, haka in tana kwance ko zaune kan gado sai su zagaye ta suna mata hira ana mata tausa in wannan suka yi suka gaji sai su ba wannan, wani lokacin in tana kwance maida cikin nata suke kaman Tv suna kallon yadda yake motsi suyi ta faman kyalkyatar dariya suna fad'in wrestling ake tsakanin Hassan da hossein ko kuma Hassana da hosaina, gaba d'aya d'akin Jidderh ya koma dining area tun tana fad'a har ma ta gaji ta daina. Satin Fatuu biyu a Abujar lokacin cikin na gab da shiga wata tara Haisam yazo, lokacin da yay arba da Fatuu wani irin tausayin ta ne ya kama shi ganin yadda Baby d'in shi ta koma, bata yi wani muni ba saidai komai nata ya k'ara girma ga cikin ma Tubarkallah yayi girma sosae, a ranar ya maidata part d'in shi aikuwa washe gari Mom ta iske shi tace ba yadda za'ai ta zauna nan gaskiya shi bai ga halin da take ciki bane ya zata rink'a hawa bene, shima saida yay wannan tunanin don a jiyan yaga da k'yar ta hau saida ma ya taimaka mata gashi shi kuma gaskiya a wurin shi yake son ta zauna, k'arshe yanke dawowa k'asa yay daga k'asan part d'in Dad dama akwae wani ciki da parlon wanda wani lokacin Dad d'in ne ke amfani dashi ba kamar in yayi bak'i, a ranar aka sa masu aiki suka gyara part d'in fes suka tare, kulawa ta musamman Haisam ke bata tun bayan da ya dawo gashi kwata kwata bai nuna mata yana son wani abu ya shiga tsakanin su sosae yake d'aga mata k'afa to dama itama bata jin abun a kanta hakan ne ma yasa tun tana gidan Hajiya daya nuna zai zo sai tace yay zaman shi kada aga yana wasa da aiki hakan yasa ya d'auki lokaci bai zo ba, duk da haka sosae yake mata abunda yasan zata ji dad'i, a kwana a tashi har cikin Fatun ya shiga wata na tara, tun ranar da ya shiga aka fara saka ran haihuwar ta dama tuni Iya ta fara bata su maganin zak'i da sauran su haka akwae wanda gwaggo ta had'a mata ta taho dasu, shiru shiru ba haihuwa kaman tasan jiranta ake ko ciwon kai Fatun bata yi a haka har Edd d'inta ya wuce hakan ya fara tada masu hankali Aunty ta shiga nuna masu hakan ba matsala bane ai dama 2 weeks before ne ko after a d'an k'ara jira a gani in ya wuce haka kawai ayi mata Cs, itama Fatun da yake tasan hakan ba matsala bane bata wani damu ba, bayan sati guda da wucewar Edd d'in ta ranar ta kama lahadi ne gaba d'aya bata wuni a part d'in nasu ba sai dare ta dawo, Haisam ne ya taimaka mata kaman ko yaushe tashiga wanka bayan sun fito yana k'ok'arin taimaka mata ta shirya tace ya bari ta shirya yaje shima yay wankan, saida ya tambayi ta tabbatar zata iya lafiya lou tana murmushi tace mashi eh, bin shi da ido tay lokacin daya nufi toilet d'in wani irin tausayi yake bata tasan ba don bai buk'atar ta ba yake k'yale ta kawai Saboda tausayinta da yake ne, hakanan taji yau tana son wani abu ya shiga tsakanin su, lokacin daya fito har ta kwanta tana kallon shi da murmushi yake shiryawa shima yana yi yana kallon ta, bayan ya gama komai yay switching wutar dakin off ya nufi gadon, saida ya kunna lamp guda d'aya sannan ya hau gadon, zama yay daga gefen k'afafunta ya fara matsa mata su dama kullum haka yake mata har tayi bacci, yana cikin yi mata tausar yaga ta fara mashi wani salo lokacin daya fahimci mi hakan ke nufi ce mata yay ba komai kada ta damu amman ta nuna mashi lafiya lou ba komai, to daman dai a buk'ace yake da ita hakan yasa ya bata goyon baya, sosae suka faranta ran junansu duk da Fatuu tana yin wani abun ne kawai don ta faranta mashi shi kuma cike da taka tsantsan yake bi da ita, bayan tayi bacci ya tashi ya nufi toilet lokacin daya dawo shiryawa yay cikin jallabiya ya kabbara sallar Nafila don rok'on Allah ya Sauketa lafiya dama Kusan duk dare yana hakan, raka'a biyu yayi bayan ya gama Addu'oi ya koma gadon, rungumota yay ta baya dama a haka suke kwanciya ya lullube su...........

Around 2:00am

Wani irin fitsari ne ya tashi Fatuu dama ta saba tashi fitsari cikin dare sosae, zame jikinta tayi daga nashi ta lalla6a ta saukko kafin ta nufi hanyar toilet d'in da sauri don tana saukkowa taji kaman zai zubo mata, lokacin data duk'a don yin fitsarin wani kalan discharge da bata saba gani ba taga ya zubo mata amman sanin dama tana fitar da shi yasa bata maida kai ba, bayan ta gama fitsarin tayi tsarki ta fito, komawa tayi gado ta kwanta bata fi yan mintuna ba taji cikinta yay wani irin juyawa har saida ta cize baki, wani fitsarin taji ya kamata sosae da sauri ta saukko ta nufi toilet, koda ta duk'a don tayi d'an kad'an ya zubo tare da wani irin ciwo har saida tay d'an sautin rad'ad'i, da k'yar ta yunk'ura ta fito daga cikin toilet d'in ta koma gado, gaba d'aya kwanciyar ta gagareta don ciwon k'aruwa yake mata, wasa wasa tun tana a saman gado har ta kai ta saukko ta duk'e k'asa, duk abunan bata yi tunanin tada Haisam ba don gani take kaman ciwon zai lafa, tun tana juye juye har ta kai ta fara d'an yar fa hannu tana fad'in wash, ganin abun bana k'arewa bane don sai ma cigaba da yake yasa ta gane nak'uda ce take yi a wahalce ta fara kiran sunan Haisam tun dai bata d'aga murya har takai ta d'aga tana ta kiran sunan shi tana ya taimaka mata, ganin yak'i tashi yasa ta fara bubbuga katifa can acikin baccin ya jita a hankali ya fara bud'e idanun shi, daidai ya bud'e ta k'ara kiran sunan nashi tana ya taimaka mata, wata kalar wuntsilowa yay ya sauko da sauri ya zagayo inda take a durk'ushe shima ya duk'a ya shiga tambayar mike damunta hannuwan shi rarruke da ita, cikin ciwo tace mashi tana ganin kaman nakuda ce take a rud'e ya furta Ok bari ya fad'i ma Aunty, mik'ewa yay da sauri ya nufi k'opa har ya bud'e komi ya fad'o mashi a rai sai kuma ya kulle ya dawo cikin d'akin ya nufi wurin side drawer, wayar shi ya d'aukko ya dawo saitin Fatun ya fara k'ok'arin kiran ta, lokacin da wayar ta shiga duk bugu d'aya tare yake da fad'uwar gaban shi, sai faman sintiri yake a wurin saida wayar ta kusa yankewa sannan Aunty ta d'auka cikin muryar bacci ta ambaci sunan shi tare da tambayar lafiya a d'an rud'e yace mata Baby ce ke nak'uda da sauri tace to gata nan zuwa harda ce mata don Allah tayi sauri tana cikin ciwo sosae ta furta Ok gata nan, duk'awa yay ya tallabo Fatun fuskar shi har ta fara hautsinewa cike da tausayi yake ce mata sannu, after few minutes aka turo kopar Aunty ce ta shigo tana sanye da doguwar rigar bacci yana ganin ta ya mik'e yana nuna mata Fatun ta nufo su, a gabanta ta tsaya ta duk'a tana dubata tare da yi mata sannu, d'agowa tay tace ma Haisam nakuda ce da sauri yace to yanzu ya za'ai tace tana zuwa ya taimaka su d'aurata saman gado yace to, bayan sun d'aurata d'aukar abunda ta aje a bakin gado tayi wanda disposal gloves ce ta bud'e yar jakar ta ciro su ta fara k'ok'arin sama hannuwanta, bayan ta gama ta fara duba Fatun dama itama rigar bacci ce iya gwuiwa a jikinta, Haisam na tsaye yana ta kallon abunda take mata fuskar shi a a d'an yamutse sosae yake jin tausayin Fatun, bayan ta gama ta d'ago tana cire safunan tace mashi haihuwa ce amman da d'an saura, sake tambayar ta ya za'ai yayi tace tana ganin abunda yakamata shine su tafi Asibiti yaje ya d'aukko Mota bari ta shirya yace to ya nufi bedside don ya d'aukko makullai, har zai fita Aunty ta tsaida shi ta hanyar tambayar inda kayan haihuwa suke ya dawo ya bud'e mata wardrobe d'in bangon dake cikin d'akin inda kayan suke shirgi guda don ba abunda babu da ya danganci jariri dama tun kafin Mom taje ta taho da ita tuni an gama siyan komai na haihuwar da yawa ma daga Dubai aka siyo su Haisam ma ya taho da wasu trolley guda wanda shida Fanan suka je suka siyo su had'add'un kayan jarirai ne na gaske unisex wato wanda zasu yi ma mace da namiji komai guda biyu aka siya akwae saura ma da Fanan zata taho da su , bayan ya nuna mata ya juya da sauri ya tafi ita kuma ta fara fiddo abubuwan da za'a buk'ata anan kafin ta bud'e wurin kayan Fatuu nan ma ta d'auki abunda zata d'auka, a wata jaka ta zuba komai lokacin ya dawo yace mata ga Motar nan ya kawo bakin Entry tace to, gadon ta nufa yabi bayanta ta kai hannu ta taimaka ma Fatun ta mik'e kallon Haisam tay tace ya d'aukko mata hijab ko gyale da sauri ya furta Ok tare da juyawa, bayan ya kawo Hijab d'in ta zura mata kafin ta nuna mashi jakar kayan data za6a tace ya d'aukko tana rurruke da Fatun suka nufi hanyar fita yana biye da su, sai cije cijen baki Fatuu ke da nishi Aunty nata mata sannu haka ma Haisam, bayan sun shigo cikin parlon ta tuna da itama tana buk'atar mayafi tace ma Haisam ya aje jakar ya kamata suje Mota bari ta d'aukko mayafi, bata jima ba ta fito ta d'auro after dress a saman kayan baccin jikinta bata yi tunanin fad'i ma Mom ba don tasan ba lalle in tana a d'akinta ba, saida ta d'auki jakar sannan ta nufi k'opa lokacin data fita har ya saka Fatuu a bayan Motar shima yana zaune a wurin yana ta faman yi mata sannu, fitowa yayi ya koma gaba Aunty ta shiga baya ta kwantar da Fatun a jikinta yaja Motar da gudu suka nufi hanyar Gate,

Basu dad'e sosae ba Saboda gudun da yake shararawa suka iso Asibitin wanda babban private hospital ne kuma sananne, bayan sun shiga yana niyyar nufar parking space Aunty tace suje bakin entrance ya furta Ok ya nufi can, bayan ya parker a bakin kopar shiga cikin Aunty tace tana zuwa ta fito da sauri ta nufi shiga cikin Asibitin shi kuma ya fito ya koma bayan ya rungumo Fatuu a jikinshi yana cigaba da yi mata sannu kai kawai take d'aga mashi, bada dad'ewa ba Aunty ta fito Nurses guda biyu musulma da Christian na biye da ita sun turo Wheel chair Haisam na ganin su ya fito yana k'ok'arin fito da Fatun, bayan an d'aurata suka turata Aunty da Haisam suka rufa masu baya, Labour room suka nufa dama Aunty ta fad'a masu Vip zasu kaita suka

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login