Showing 303001 words to 306000 words out of 512766 words

Chapter 102 - Asanadin Makwabtaka Book 3 Hausa Novel Complete

Unknown   

27 Dec 2024

1658

ayi tunanin wani abu, da sauri ta mik'e buguzun buguzun suka nufi kopa,

Lokacin da Kishiyar Yaya ta shiga d'akin su Yadikkon bata isketa ba sai su Aysha kawai, da fara'a ta k'arasa wurin su ta tambaye su innar su suka ce mata ta fita taje ta dawo ta jinjina masu kai, a bakin gado ta zauna don ta jirata, bata jima sosae ba Yadikko ta dawo dama wurin gwaggo taje, a k'asa saman Carpet ta fara k'ok'arin zama ganin tana zaune a bakin gadon da sauri tace mata ya zata zauna a k'asa tazo ta zauna a bakin gadon mana Yadikkon na murmushi tace mata ai ba komai, gaisawa suka k'ara yi don sun gaisa da suka tashi, cikin nuna tsananin farinciki tace mata taji abun Alkhairin daya k'ara samun su a bakin innar su Altine taji dad'i sosae wllh, Addu'oi ta shiga yi Yadikkon sai murmushi take a cikin ran ta take amsawa Saboda nuna kunya ba kamar da Mino take y'a ta farko a wurinta, suna haka sai ga su Yaya sun turo k'opar kamar an jefo su gaba d'aya suka sauke idanun su cikin na kishiyar tata tana ganin su ta kauda fuskar ta, k'arasa shigowa ciki sukai ganin yadikkon zaune a k'asa yasa suma suka fara k'ok'arin zama a kan Carpet d'in, cikin girmamawa Yadikko tace masu don Allah su zauna a kan gado mana duk suka ce a'a bari dai suma su zauna a k'asan, gaisawa suka shiga yi sai faman washe baki suke kaman wad'anda akai ma Albishir da Aljanna su duk k'ok'arin da suke shine asan suna murna, bayan sun gama gaisawar ne suka shiga taya ta murna suna fad'in wllh sunyi farinciki jin abun Alkhairi da ya k'ara samun su, innar su Altine harda cewa ai ita d'azun tsabar farinciki ne ma yasa ta kasa cewa komai ta tashi da sauri ta nufi d'akin su don ta sanar ma dasu Yaya suma,

Yaya ma cikin washe baki take fad'in ita shiyasa bata ta6a k'alubalantar komawar su binni ba wllh Saboda tana ji a jikinta hakan zai zame masu Alkhairi ashe kuwa hakan ne aikuwa su Aysha ma sai a maida su can binnin suma kawai, jin hakan har saida kishiyar tata ta d'an yi guntun murmushi ta ta6e baki ita kanta Yaya da tayi maganar duk ta bi ta kama kanta har d'an d'aga kai tay ta kalli kishiyar tata ita dai Yadikko murmushi kawae take don gaba d'aya farinciki ya gama cikata, Mero ce ta fara tashi tana k'ara taya yadikko murna ta nufi k'opa ta bud'e ta fita, kallon juna Yaya da innar su Altine sukai duk sun yi kalar rashin gaskiya, mik'ewa Yaya tay tana washe baki tace ma Yadikko bari taje ta idasa kimtsa kaya jin haka yasa innar su Altine itama ta mik'e tace haka, bin su da ido yadikko tay har suka fita, lokacin da suka koma d'akin nasu Mero na zaune a bakin gado jakar kayanta a gabanta ko kallon su bata yi ba, wurin ta Yaya ta nufa ta tsaya daga gaban ta sai lokacin ta d'ago ta kalleta, cikin kwantar da murya Yaya tace "ina son ki sani Wallahi tallahi kwarankwasa gajimare ni bani na kashe Fatima Mahaifiyar Muhammadu ba, koda kika ji nace na muzguna mata har Allah ya amshi abun shi bawai nice na kasheta ba, nasan da zalunce ta tun bayan da Ard'o ya auro ta na fahimci ba K'aramin son ta yake ba na fara muzguna mata k'arshe na had'a mata da asirin daya sa Ard'on ya rink'a gudun ta duk aka tsaneta to bak'in cikin hakan ne ya haifar mata da ciwo har yay tsanani Saboda ba'a kulawa da ita k'arshe ta rasu, ita kuma Aisha Mahaifiyar inna wuro sau d'aya nayi yunkurin yi mata Asiri don in raba su Saboda tana yar binni tafi sauran matan Y'ayana komai amman sai boka yace man bazai iya ba Saboda tana da iskokai masu zafi bazasu bari Asiri yayi tasiri ba a kanta gara in rabu da ita don zasu iya maido shi kaina, to daga nan itama na rink'a nuna mata tsana har tazo ta kwanta ciwo akai tunanin na iskar ta ne ashe cuta ce a cikin cikinta amman ni wllh bani da sa hannu a cutar" idon Mero a kanta har ta gama sannan ta sauke ajiyar zuciya tace ai Mahaifiyar Muhammadu itace tay silar mutuwarta don haka alhakinta na akanta gashi ta rasu balle ta rok'e ta yafiyar abunda tayi mata, a k'arshe tace mata tana bata shawara ta tuba ta daina shirka don malamin su dake koya masu karatun Addini yace itace laifin da Allah bai yafewa in aka mutu ba'a tuba ba sannan kuma duk wanda ta zalinta tun wuri ta nemi yafiyar shi don Allah bai yafe hakkin wani a kan wani, cike da nadama Yaya tace to yanzu ya zatay da hakkin Fatima data mutu, shiru Mero tay can ta nisa tace to ita gaskiya bata sani ba amman zata tambayi malamin su kuma suma yakamata su rink'a zuwa karatun hakan zai sa su daina aikata wasu abubuwan, atare suka had'a baki wurin cewa to zasu rink'a zuwa da sun koma, a marairaice Yaya tace mata to don Allah zata rufa mata Asiri Meron tay d'an murmushi tace ai ita bata isa ta tona mata Asiri ba in Allah bai yarda ba in kuna yaso ko ba ta silar ta ba to sai asirin nata ya tonu, sosae jikin Yaya yay sanyi lakwas kamar an watsa ma kaza gishiri.

Bayan Fauzy ta gama shirin ta cikin bak'ar jallabiya tay rolling veil d'in ta, jakar wayarta ta d'aukko ba tare data bari kowa ya ankare ba don duk suna zaune a saman gado basu dad'e da gama yin murnar labarin da Mino ta shigo ta basu ba na neman auranta da akai, fitowa tay daga part d'in nasu ta nufi cikin gidan, part d'in Mom ta nufa lokacin data shiga a parlor ta isketa zaune itama jikinta sanye da jallabiya, tana murmushi ta kalli Fauzyn ta nufeta itama da murmushi akan fuskar ta, k'ok'arin zama take akan Carpet Mom ta nuna mata kujera tace ta zauna mana, bayan ta zauna gaishe da ita tay still da murmushi ta amsa mata, shiru suka d'an yi kafin tace mata ana ta shiri ko Fauzy ta d'aga mata kai a hankali tace eh tay Addu'ar Allah ya kai su lafiya ta amsa mata da Amin, shiru ta d'an yi kafin ta tambaye ta Zarah na nan tace mata eh ta shiga tana ciki, mik'ewa tay ta nufi hanyar Bedroom d'in, lokacin data shiga Fatuu na kishingid'e a gefen gado idon ta akan Tv tayi wanka tana sanye da doguwar rigar material mai red flowers ta yafa d'an jan gyale a kanta, jin sallama yasa ta kai idon ta kan kopar shigowa ganin Fauzy yasa ta washe baki tana gyara zaman ta, nufota tayi ta tsaya daga gabanta tana fad'in "mai ciki" dariya Fatun tay tayi mata alamar ta zauna da hannu, a gefenta ta zauna daga bakin gadon,

"Kina ta hutawa abun ki" Fauzy ta fad'a idon ta akan Fatun tana murmushi, itama murmushin take jin abunda tace sai kuma tace "wllh har na fara gajiya ma ni, daga ci sai kwanciya in nayi wani aiki to bai wuce zuwa toilet fa" yar dariya tay "tun yanzu, duka mi akai a bed rest d'in" d'an tura baki tay "wllh ji nike inama ku tafi da ni duk naji na damu da tafiyar da zaku yi" d'an shiru Fauzy tay tana murmushi sai kuma tace "ai ba yadda za'ai a tafi dake tunda ga halin da kike ciki, amman yanzu ni abunda ma yafi damuna shine ya za'ai da School kinsan ranar Wednesday d'in nan zamu koma tunda dama hutun 2 weeks ne" yanayin fuskar Fatun ne ya d'an canza tace "nima harda ita yasa na damu nike jin dama in bi ku, amman zan ma Hubby magana kan hakan tunda bai yuwuwa in zaune anan ana can ana karatu tunda ba wani ciwo nike ba ba sai na dad'e anan ba gaskiya" kai Fauzy ta jinjina,

shiru suka d'an yi sai kuma Fauzy tace "sai muka ji abun farinciki an nemi auren Mino wllh nayi matuk'ar murna baki ji ba" fad'ad'a murmushi Fatuu tay tace "wllh abun fa abun farinciki, ke ni farko ma da baffa ya kira ni ya sanar man tsabar mamaki kasa rufe baki nay jin abun kamar wasa duka yaushe suka had'u amman har an tsaida magana, sosae na taya Mino murna don Nameer sam bai da matsala wllh"
"Haka abun Allah yake matuk'ar ya k'addaro abu sai kiga ya faru aita mamaki" kai Fatuu ta d'aga,

"da rabon zamu k'ara zuwa shan wani shagalin don wllh bazan 6oye maki ba na nishad'antu da dukkan shagalin da akai kar ma dai dinner d'in nan duk aka zauna sai an tada zancen ta"

"Ai naga har wak'e ki akai Hajiya Fauziyya mai ruwan Naira, wai ni don Allah ina kika samu wad'annan kud'in da kika rink'a man wanka da su" Fatuu ta tambaya tana murmushi idon ta akan Fauzy, murmura mata ido tay tace itama samun su tay daga sama, kafin Fatun tace wani abu ta d'ago jakar da ta shigo da ita ta mik'a mata, amsa Fatuu tay ta bi jikinta da kallo kafin ta maido kallon kan Fauzy alamar rashin fahimta, ce mata tay ta duba abun ciki, hannu ta kai ta fiddo kwalin wayar saida tay d'an jimm tana kallo shi kafin ta fara k'ok'arin bud'e shi, bayan ta fiddo wayar bin ta tay da kallo tana d'an Jujjuya ta,
"Wannan irin wayata ce" kai Fauzy ta d'aga mata,
"ta waye?" Fatuu ta tambaya, shiru Fauzy tay tana d'an murmushi Fatun nata kallon ta alamar jiran Karin bayani,

"tawa ce wai, Cousin brother d'in Ya Haisam ya siya man" wani kallon rashin fahimta Fatuu ke bin ta da shi tace mata wane cousin brother d'in nashi, jimm Fauzy tay kafin ta bata amsa da "Sameer" a wani slow Fatuu ta fara bud'a idanunta tare da bakin ta duk a lokaci d'aya har saida taba Fauzy dariya,

"Sameer fa kika ce! Wai wane Sameer d'in kike nufi?" ce mata tay wanda dai ta sani,

"kina nufin wai Sameer Sameer d'an Governor???" Kai Fauzy ta jinjina mata, k'ara bud'e baki Fatuu tay idanu waje cike da tsantsar mamaki take kallon Fauzy tama kasa magana can ta sauke numfashi ta furta "this is unbelievable! Sameer ya siya maki wannan wayar! amman wai...taya akai kuka san juna ma tukun" Fauzy sai dariya take ganin yadda kan Fatun ya d'aure, labarin yadda akai suka san juna ta fara bata tiryan tiryan har da kud'in lik'in da ya bata zuwa jiya da ya bata wayar, lokacin data gama fad'i mata hannu Fatuu ta kai ta rufe bakinta tana dariya,

"Yau da alama so kuke ku kashe ni da mamaki, Mino da Nameer an tsaida Maganar Auren su yanzu kuma ga ke da Sameer, wayyo dad'i kashe ni" Fatuu tay Maganar tana yarfa hannu, Fauzy dake ta dariya tace mata ai ita fa ba wani abu ke a tsakanin su ba, katseta Fatuu tay tace "ke dalla ai daga haka ake farawa, ga misali nan tsakani na da hubby dana fasa mashi glass duk da ni daga haka zumunci ne ya k'ullu kema shine zai k'ullu amman na soyayya in sha Allah" ta k'arasa Maganar sai faman washe baki take itama Fauziyyar dariya take can Fatuu tace "Allah ubangiji ya tabbatar da abun nan kai, wllh sai nafi kowa farinciki, zan so in ga Fuskar mayaudarin nan Muntari yake kowa, wannan babban kamu haka ai nasan wllh sai ya girgiza in ma bai zauce ba, kinsan da yawan mutane basu son su rabu da kai suga kuma kazo kaci gaba" girgiza kai Fauzy tay tana ta dariya jin sunan da Fatun ta kira Mujaheed,

"Wai ku sai faman Maganar soyayya kuke haka ma Aunty Mareeya duk ta bi ta rud'e, nifa bai ce yana sona ba, mutumin da in banda harara da tamke fuska ba abunda yake man wannan ne son?"

"Ai kin san kowa da kalar nashi salon soyayyar ba kamar da shi ga yadda halin shi yake, amman mutum kamar Sameer da kwata kwata bai shiga harkar mutane yake maki haka kuma tun farko ga abunda ya had'a ku laifi kikai mashi amman shine harda baki kud'in lik'i da yi maki Maganar yaushe zaki aure uwa uba ya siya maki wannan tsadaddar wayar, haba Fauzy, kema dai kin so a ja Maganar ne kawae Allah, ai koda baki soyayya kefa ba yar primary ko Secondary bace ko Yaya ne zaki gane in mutum na son ki, ke dai Allah ya tabbatar mana yasa komai yazo cikin Sauk'i kamar nasu Nameer, aikuwa zanje in zuge Aunty Mareeya ta koya maki yadda zaki kama mana shi a hannu don na lura kina buk'atar lakca gaskiya duk Muntarin nan yasa kin rasa karsashi ta wannan fannin kuma irin su Sameer sai anasa karsashi a yin love da su" dariya sosae Fauzy ke yi tana fad'in Allah ya shirye ta, tambayar ta tayi har su Haulat sun shirya ne suma tace mata eh ba wanda bai shirya ba, sake tambayar ta tay taga Mom da zata shigo tace mata eh tana a parlor zaune, maida wayar Fatuu tay tana fad'in Allah yasa Alkhairi ya tabbatar masu da abunda suke fata, saukkowa daga gado Fatun tay tace mata suje tana son zuwa part d'in Hajiya ne, a tare suka fito har lokacin Mom na zaune a cikin parlon, kai idon ta tay kan su tana kallon su da d'an murmushi suka nufo ta, daga d'an can nesa da ita suka zauna Fatuu tay mata sannu ta amsa mata, shiru sukai tana son yin magana ta kasa Mom data fahimci hakan tana murmushi tace "ya akai Daughter ko akwae wani abu ne?" a sanyaye tace mata dama part d'in Hajiya take son zuwa zata bada sak'o, jinjina mata kai tay tace Ok taje amman ta kula tana murmushi ta d'aga mata kai, har zasu mik'e tace yama sunan Fauzy suka fad'i mata,ce mata tay ta tayata kulawa tana murmushi tace mata to, bayan sun fito daga part d'in Fauzy tace ma Fatuu wai wannan cikin nata in ta haihu shine jika na farko a gidan ko tace mata eh, Fauzyn tace haba shiyasa wannan gata haka wani abun ma sai an haiho babyn ita dai Fatuu murmushi kawae take, bayan sun iso part d'in Hajiyar a parlor suka tsaya suna gaisawa da Mutanen ciki duk akai ma Fatun ya jiki ta amsa, wucewa sukai bedroom da sallama Fatuu ta shiga Fauzy na biye da ita, Hajiya na zaune a bakin gado gwaggo kuma nata had'a kaya duk suka amsa masu sallamar tasu, ciki suka shigo fuskar Hajiya a sake take kallon su haka gwaggo ma data d'ago tana kallon su, daga gefen gadon suka tsaya suna gaishe dasu bayan duk sun amsa Hajiya ta nuna masu bakin gado tace su zauna mana sun toge anan, duk suka zauna,

"Hala an zo bankwana da Dije, ai da kin bari zata iske ki can sai kuyi bankwanan" Hajiya ce ta fad'a Fatun tay murmushi kawae haka Fauzy da gwaggon, tana son yi ma gwaggon Magana amman ta kasa sai bin ta da ido take, ganin yadda take ta kallon ta yasa tace mata ya akai, juya harshe tay ta fad'i mata abunda take son fad'i mata dama Haulat take son ba kyautar atampa a cikin kayanta, itama cikin harshen fulatancin tace mata itama tana son a bama su Yaya amman taga kayan duk manya ne kar ayi ba daidai ba,

"In sirri kuke son yi ai sai kuce in baku wuri ba ku canza harshe ba in d'auka gulmata kuke" Hajiya ta fad'a ta d'an kwa6e fuska duk sukai dariya, gwaggo ce tay mata bayanin cewa wai tana son ba k'awar ta atampa ne shine itama take ganin ya dace a ba su Yaya da yadikkonta amman bata san ko zasu iya hakan ba, hannu Hajiya ta kai ta ruk'e ha6a tace "Oni yasu, to Dije mi zai hana, ai kaya yanzu sun zama naku waya isa ya hana kuyi yadda kuke so da su in banda abun ki" gwaggo na murmushi tace dama wai taga kayan manya ne Hajiyar tace to ko manyan ne fa ai dai nata ne ko, kuma ai akwae atampopi suna nan da ba'a d'in ka ba tasan k'ilan bai wuce ma don hakan yasa ba'a d'inka su ba tunda yawancin kayan duk an d'inka, duk abunda zaku bada ku bada ba ruwan kowa da wannan" godiya gwaggo tayi mata tana yar dariya sai kawai ma Hajiyar ta mike ta nufi hanyar fita, Fauzy gwaggo tay ma magana ta mik'e taje suka sauke akwatunan, na kayan suka fiddo bayan an bud'e gwaggo tace ma Fatuu ta zo ta d'aukar ma Haulat d'in, wata atamfa mai golden tayi kyau sosae ta d'aukar mata, Su Yaya da Kishiyar ta da Yadikko suma duk atampopin aka d'aukar masu, ta Yadikko ma glitter ce mai kyau, wani lace tasa aka d'aukar ma k'annanta su Aysha sai k'awarta Zainab ma ta d'aukar mata wata sarka da yan kunne masu kyau dama ankon lace d'inta ta bar mata, su Aunty Mareeya ma da Feenah da Saude yan kunne fashion aka d'aukar masu kai da gani kasan zasu yi kud'i don ba k'ananu bane, akwatin cosmetics tasa Fauzy ta bud'e mata ta k'ara ma su Aysha da kayan shafa, gudun abun kar yay yawa yasa gwaggo da fullanci tace mata a bar su haka Fatun tace da su Baffan ta take son d'aukar ma shadda tace mata a'a an basu ta k'yale su in ma tana son basu ta bari a basu daga baya, Fatun tace to bari a basu ko turare ta

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login