Showing 402001 words to 405000 words out of 512766 words
Chapter 135 - Asanadin Makwabtaka Book 3 Hausa Novel Complete
Unknown
27 Dec 2024
1622
da sauri tace "a'a wllh Yallabai mun iya indai yadda ake sauke glass d'in kowacce Mota ne tunda dai muma muna da yan motocin nan, kuma koda ma ace ni ban iya bane ai d'ayar da muke tare ita dole ace ta iya tunda matar Cousin d'in Angon ce d'an Senator Ali Zakee nasan baku rasa sanin shi" kai ya jinjina mata tace to har itama tayi tayi ta kasa sauke shi balle ace sun yi k'auyanci, yanayin yadda take Maganar ne ya basu dariya don sun fahimci yar barkwanci ce, driver d'inne yace mata basu yi k'auyanci ba ta nan gaba ake sauke glass d'in da sauri tace Yauwa koda taji to a sauke masu don Allah Security d'in yay mata alamun ta koma ciki ta janye kan nata ya sak'o nashi inda suke ya mik'a yatsa yana nuna mata wani wuri a jikin k'opar Motar da ita kanta abun kallo ce yace mata in tana son yin magana da su nan zata latsa sai kawai ta fad'i abunda take son ayi ba sai ta lek'a ba ta jinjina mashi kai kafin tace kenan kamar yanzu da take son a sauke glass tana latsa wurin sai tace ayi haka yace mata Yess zata ga glass d'in ya sauka ta washe baki tana fad'in Allahu Akbar shima yar dariyar yay sai kuma ya nuna mata screen yace ga system nan in suna so sai suyi kallo ya shiga nuna mata yadda zata kunna yace akwae Movies a ciki saidai ba masu yawa bane amman in tana so zata iya connecting da wayarta sai ta kalli duk abunda take so har internet zata iya hawa tayi chat d'inta anan yana bayanin yana nuna mata yadda zata yi k'arshe kuma ya nuna mata game yace ga kuma game nan in tana son yi tayi mashi wani kallo tace sai kace dai wata k'aramar yarinya yay yar dariya, duk abun nan idon Fauzy na akan Mujaheed Fatuu dai kallon abunda ake nuna ma Aunty take tana yar dariya, bayan ya gama nuna mata ya maida kan shi kawai sai jin Maganar shi sukai ta karad'e bayan ta cikin wata yar speaker yana tambayar glass d'in wane side za'a bud'e masu ta bashi amsa da na hagu tana rufe baki glass d'in ya fara sauka, bin Mujaheed da kallo Fauzy tay gabanta ya hau d'an fad'uwa ganin yadda yay wani iri kamar ba shi ba Aunty kuwa yamutsa mashi fuska ta shiga yi tana hararar shi Fatuu ma bin shi tayi da kallo a ranta ta d'an ji mamakin ganin shi haka don ba haka Fauzy ta bayyana mata shi ba tace mata d'an gayu ne yanzu kuwa duk gashi ya cika mashi fuska gashi ya zumbula wata jallabiya sai kace liman, ganin irin Kallon da Fauzyn ke mashi ne ya bashi k'warin gwuiwa ya tunkaro Motar da sauri, saida ya kusa isowa kawai Aunty ta danna wurin da aka nuna mata da sauri tace a rufe glass d'in sai gashi ya fara rufewa slowly, burki Mujaheed yaci ya zuba ma Fauzy ido yayin da glass d'in ke rufewa, kallon Aunty Fatuu tayi da sauri tace "Aunty wannan ne Mujaheed d'in?" Fuska a Yamutse ta kwa6e baki ta bata amsa da eh shine banzan ko uban me ma yazo yi nan sai kuma tace koda yake gara da yazo ya gane ma idanun shi, yanayin fuskar Fauzy kaman zata yi kuka dama kuma shi ta gama yi ta kalli Aunty tace "Aunty da baki mashi haka ba zai zama kaman kin wulak'anta shi...." Tun kafin ta rufe baki ta katseta a fusace "au wai ke nan baki ji dad'in abunda nayi ba kike nufi komai, naji dad'i in har hakan da nayi mashi zai zama wulak'anci a gare shi da akwae wulak'ancin ma da yafi wannan to shi zan mashi, ke har kin manta da irin wulakancin da yayi maki zaki wani ce an mashi wulakanci",
11abu Fauzy ta had'iya k'walla suka zubo mata cikin karyayyar murya tace "abun da yay man d'in k'aruwa nayi ko raguwa Aunty, ni wllh na yafe mashi komai yayi man tun ma ba yanzu ba" ta6e baki Aunty tayi bata ce komai ba Fauzyn ta juya tana k'ara kallon shi yana a tsaya inda ya ja ya tsaya yana kallon Motar ya marairaice Fuska tare da had'e hannuwan shi ya d'an d'aga su sama alamar rok'o, kallon Aunty Fauzy tay tace "Aunty don Allah kisa a bud'e da alama akwae abunda yake so ya fad'a man ki bari muji miye don Allah baki ga yadda ya koma ba duk yayi wani iri kamar ba shi ba" wani uban tsoki taja rai 6ace tace "Wllh baza'a bud'e ba har yana da wani abun fad'i maki, to yace maki uban me kuma Maganar canzawa ya dad'e bai lalace ba wllh ko a kwalar vest d'ita, yanzu haka hakkin ki ne ke bibiyar shi tun ba'aje ko ina ba don haka ba abunda zance in ma hakan ne sai Allah ya k'ara in ma da k'ari ya k'ara mashi, Sakaran banza sakaran wofi" tana rufe baki Fauzy ta fashe da kuka, waro ida Aunty tay da tsananin mamaki tace "ke, mi nike gani haka, wai wanccan d'in kike ma kuka Saboda Maganganun da nayi to mi kike nufi da hakan??" Girgiza kai Fauzy tayi cikin kuka tace ita wllh ba abunda take nufi kawai dai ya bata tausayi ne don da gani yana cikin matsala mutumin da yake d'an gayu d'an Kwalisa a gan shi haka" ta6e baki Aunty tay tace ita dai ta sani, magiya Fauzy ta k'ara mata kan tasa a bud'e aikuwa a fusace Aunty tace "Wallahi tallahi baza'a bud'e ba, in kuma kikai wasa yanzun nan zan buk'aci a kirawo man Mijin naki ince ke kike son ganin shi da gaggawa yana zuwa in fad'i mashi abunda ke faruwa, kindai sani ai basai na fad'i maki ba tsaff zai kakkarya shi sai muga ta tsiyar tausayi, in ba ma yana mahaukaci ba shine zai wani jawo k'afafu kamar shebur wai zai yi magana dake wato shi ga mara ta ido ko duk abunda yay maki shine har zai wani nemi yin magana dake to kuwa yanzun nan zan sa a koya mashi kunyar da bai da ita" ta k'arasa tare da yin k'wafa, wani irin kuka mai sauti Fauzy ta saka dama k'iris take jira acikin ranta ta shiga tunano tun daga farkon had'uwarta da Mujaheed d'in yadda ya rink'a mata d'awainiya da tana Makaranta, sam lokacin ba ta tuno da sharrin shi ba sai Alkhairan shi, suna haka suka ji Muryar Security d'in ta cikin speaker d'in bayan yana tambayar lafiya wake kuka ne haka mike faruwa, zaro ido Aunty Mareeya tayi da sauri ta kai hannu ta jawo Fauzy jikinta tana k'ok'arin rufe mata baki tana fad'in ta bani kuji zata ja mata sharri taja a d'aureta, duk da yanayin da Fatuu take ciki na karyewar zuciya saida tayi yar dariya, k'ara tambayar su lafiya akai koda matsala ne da sauri Aunty ta latsa wurin Maganar ta bashi amsa da a'a ba komai amaryar ce ke kukan rabuwa da gida, wannan karon sosae ta ba Fatuu dariya, rarrashin Fauzy ta shiga yi tana fad'in Shikenan tayi hak'uri itafa duk Maganganun data yi 6acin rai ne yasa tayi su kuma bata ga amfanin tayi magana da shi ba tunda ita yanzu Matar aure ce ta rabu dashi kawai, cikin muryar kuka tace ba cewa tayi zata saka a kirawo mata Sameer ba ya kakkarya shi da sauri Aunty tace wllh duk cika baki ne ita tama fara kiran shi ta fad'i mashi haka yazo duk ya tarwatsa taron da rocket, dariya Kawai Fatuu ke yi a ranta ta raya yau Aunty ta tuno da rocket, suna haka aka ba motocin izinin tafiya a Kusan tare duk suka tashi jin haka yasa Fauzy d'agowa da sauri tana kallon Mujaheed d'in Motocin suka fara tafiya a jere gaba Motar Security ce haka k'arshe ma sannan a tsakiya ma abun dai gwanin burgewa nima dai ina a cikin ta yan jarida, tun bayan da Motocin suka fara tafiya Mujaheed yaji tamkar da jinin jikin shi suke tafiya a Hankali ya fara ganin jiri ya kai hannu ya dafe goshin shi ganin haka yasa Usman nufo shi da sauri ai ko kafin ya k'araso Mujaheed d'in ya tafi gaba d'aya zai kife cikin zafin nama ya tare shi duk wannan abun akan idon Fauzy dake ta kallon su ta glass da yake Motocin a slow suke tafiya, tana ganin haka ta juyo cikin kuka take ce ma Aunty ga Mujaheed d'in can ya fad'i kawai sai ta jawota jikin ta tana fad'in zai tashi ne in kuma ya wuce daga haka Allah ya jik'an shi.
Tafiya ce ake me cike da kwanciyar hankali daga baya Fauzyn ta sake bayan Fatuu ta rarrasheta Aunty ta kunna masu kallo suna ta yi abun su, lokacin da suka zo Zaria ne Aunty tace ita dai wllh k'ishi take ji yakamata ace ko wace Mota an aje lemuna da ruwa Fatuu tace ko ta tambaye su k'ilan ba'a rasawa tace to, latsa wurin tayi tace pls suna buk'atar ruwa kawai sai ji tayi an bata amsa da ta duba akwae a cikin Fridge, zaro ido Aunty tay ta d'an kakkali cikin Motar ita dai bata ga wani Fridge ba, tambayar su tayi anan bayan fridge d'in yake yace mata eh mana,
"to gaskiya saidai kuyi hak'uri kun d'aukko yar k'auye nidai wllh ban ganshi ba" ta fad'a tana k'ara kallon wurin, suna jiyo d'an sautin dariyar shi kafin yace Ok bari a bud'e masu daga can yana rufe baki kawai sai gani sukai daga d'an kasan dukkan seats d'in gaban ya bud'e har saida Aunty ta d'an firgita hakan saida yaba Fauzy dariya, d'an karamin fridge ne a jikin dukkan seats d'in kowanne akwae lemuna da ruwa harda snacks a ciki, tambayar Aunty akai yanzu ta gani ko tana dariya tace masu eh sai sunyi hak'uri abun ne ya had'u da yar k'auye suna jiyo dariyar shi, gaba d'ayan su lemu da snack suka d'auka suna sha harda Fauzy Aunty nata washe baki tana fad'in ikon Allah ashe da rabon zata shiga Mota fridge da aketa fad'i, suna cikin ci ne tace to wai yanzu kuma in suka zo suna buk'atar toilet fa tunda sun ci abu, kafin wani ya bata amsa ta sake cewa koda yake k'ilan ma ai baza'a rasa toilet d'in ba acikin Motar, dariya taba Fatuu tace "kai Aunty Mareeya sai kace dai wani jirgi" da sauri tace "ai wannan kaman jirgin ce mai tafiya kan titi kiga fa yadda take da abubuwa kar ki mamakin toilet d'in ma akwai nan da mun tambaya kina iya ganin sun ce akwae" Fatuu dai dariya kawai take cikin disasshiyar murya Fauzy tace don Allah sudai kada ta wani tambayi ko akwai toilet tayi mata wani kallo tace "to your Excellency kada inta bada ku ko " tura mata baki Fauzy tayi ba tare data ce komai ba ta kai hannu ta dafa Shoulder d'inta tace "sai faman wani sha man k'amshi kike ko duk don Mujaheed ne?" Kai ta d'an girgiza mata kawai ba tare data ce komai ba, sai dai tun bayan da suka taho ya tsaya mata a rai sai tunanin halin da yake ciki take da kuma abun da ke damunshi ya hautsine haka.
Alhamdulillah sun iso Kaduna Lafiya, government House d'in nan aka nufa dasu dama an shirya nan za'a tsaya a huta kafin a wuce, bayan sun huta an ci Abinci masu salla sun yi suka d'aura tafiyar. Sai bayan sallar Magrib suka iso garin Abuja, tun a gate d'in gidan da aka nufa dasu suka fara shan kallo Fauzy na ganin cikin gidan ta glass ta gane gidan da Sameer ya ta6a kawo ta ne, gaba d'aya Motocin saida aka shiga dasu cikin gidan, bayan duk an parker aka fara fitowa nan fa kowa ya shiga ba idon shi hakkin shi banda wanda suka san gidan da kuma wanda gidan ba abun kallo bane a wurin su, kowa dai cikin yan kawo Amaryar bai hana idon shi hakkin shi ba ta hanyar bin ko ina na gidan da kallo tare da jinjina ma had'uwar shi a cikin zuciya, Aunty na ruk'e da Fauzy suka nufi hanyar shiga cikin gidan kamar yadda aka basu izini suna cikin tafiyar ne k'asa k'asa da murya Aunty tace ma Fauzy nan ne gidan da Sameer ya ta6a kawo ta ko ta d'aga mata kai tace dama tana gani tayi tunanin hakan don taga yayi kaman yadda ta fasalta mata, saida suka zo bakin entrance d'in gidanne PA din Hajiya Zainab wadda da ita akaje bikon Amarya ta d'an dafa kai tace an samu matsala an manta ba'a bada card d'in da za'a bud'e gidan ba Mom ta tambayi to yanzu ya za'ai da sauri tace bari ta kira Her Excellency d'in, su dai su Aunty jugum sukai kowa na Al'ajabin jin sai da kati za'a bud'e kopar, bayan ta kirata itama nuna rashin jin dad'i tayi tace ta manta ta bada card d'in ne amman bari ta bud'e masu daga nan PA d'in tace Ok, hak'uri taba mutane na an barsu a tsaye bayan sun gama wayar tace gashi nan za'a bud'e, ba'a d'au wani lokaci ba suka ji kopar tayi wani d'an sauti PA din tace yauwa gashi nan an bud'e, ba sai na fad'i mamakin yan kawo Amarya ba, ana bud'ewa aka bada izinin a shiga PA d'in na gaba suka fara shigowa cikin passageway d'in, ita kopar falon dake anan k'asa lafiya lou ta bud'e masu ita kafin a shigar da Fauzy saida ta saci kallon hanyar benen da suka hau da Sameer, Jama'a kuzo kuyi kallon parlor mai sunan falo Aljannar duniya kenan, ashe dai yan kawo Amarya basu ga komai ba sai yanzu, wato wani irin tsararre kuma had'addan Falo ne daya jik'u da tsadaddun kayan alatu masu girgiza mutum, iya luntsuma luntsuman Sofas d'in dake cikin shi abun kallo ne ga wani musulmin Carpet dake malale a cikin shi wanda ya hau da kayan cikin Parlon, a tak'aice dai Idan nace zan tsaya bayyana had'uwar parlon to kuwa saidai in hak'ura da zuwa wurin dinner wadda za'a je da daddaren nan ni kuma gaskiya ina son ba idanuna hakkin su don haka na bar ma kowa ya fassalta had'uwar parlon a cikin zuciyar shi saidai nasan duk hasashen mutum ba lalle ya hasasho ainihin yadda yake ba tunda ba zuwa kai ba, gaba d'aya yan kai Amarya sakin baki sukai suna k'are ma falon kallo wasu na jinjina kai yayin da wasu suka kasa rufe baku nan su, ba anan aka sauke su na wani corridor aka nufa dasu sai gasu sun k'ara shigowa wani parlon, duk da bai kai had'uwar na farkon ba amman dai shima ba k'arya ya jiguna komai na cikin shi navy blue da milk ne sosae shima ya tsaru, anan aka sauke su duk suka zazzauna su Mom suka hau yi masu sannu da zuwa cikin washe baki suke amsawa, nuna masu d'akunan da zasu yi amfani dasu aka yi suna ta godiya duk suka tashi don suyi salla, bayan sun gama ne aka kawo masu lafiyayyen Abinci da lemuna aka sanar dasu in sun gama za'a tafi dinner suyi shiri lokacin Mom ta shigo tayi masu sallama tace zasu je suyi shirin dinner aka shiga k'ara yi mata godiya tanata fara'a take amsawa Fatuu ma sallama tayi masu Saboda kayan da zata saka suna can gidan tace ma Fauzy sai sun had'u wurin dinner d'in, bayan sun huta ne PA tazo da wadda zata yi ma Fauzy kwalliya harda kayan da zata saka ba 6ata lokaci aka fara. K'arfe goma saura aka zo d'aukar su ba'a bar kowa ba Amarya Fauzy ta sha kyau ba k'arya wani rantsattsan material ne golden brown aka yi mata fitted gown data hau jikinta sosae, lokacin da suka isa wurin dinner d'in shima dai ya had'u over da gani Naira ta sha kuka wurin tsara Hall d'in, tunda aka fara hidiman bikin Fauzy bata ga Sameer ba sai yanzu a wurin dinner d'in shima dai ya had'u sosae yana sanye da bugaggun Suit da suka hau da shigar Fauzyn, zuwa k'arfe goma da rabi kowa ya hallara har da uwar ango wato Hajiya Zainab tazo wurin, manyan mutane aka had'a a wurin hakan yasa ko ina ka juya jami'an tsaro ne mata da maza sosae aka zo kasantuwar wannan ce hidimar su ta farko, ba'a yi tak'amaimai anko guda ba gaba d'aya kowa da kalar wanda sukai saidae gaba d'aya lace ne aka saka kamar yan gidan su Haisam kalar lace din su d'aya haka ta bangaren su Sameer suma kalar nasu daban har kakar su ta zo da sauran dangin su yan Ethiopia haka yan Qatar ma sun zo, su Aunty Mareeya da sauran yan gidansu suma lace d'in su daban haka dai duk akayi ankon wasu kuma lace d'in su ne suka saka daban kamar su gwaggo da Aunty Feenah da Haulat dasu Zainab kowa lace d'in shi ya saka amman ita Mino irin nasu Fatuu ta saka ita ta d'inka mata Nameer dai bai samu zuwa ba don yana gab da fara yin Final Exams d'in shi, sosae kowa yayi kyau angwaye ma su Haisam duk wankan Suit sukai, ba 6ata lokaci aka shiga aiwatar da activities d'in dinner d'in abun gwanin k'ayatarwa. Gab da za'a tashi ne aka rarraba wata k'atuwar jaka mai d'auke da hoton Fauzy da Sameer cikinta uban souvenirs ne iri iri Aunty Mareeya aka ba na dangin su ta rarraba masu sauran da suka rage ta yanke aika ma Mamar su, Sai wurin k'arfe d'aya saura aka tashi abun sai godiyar Allah don an ci an sha an nishadantu yadda yakamata dinner ce da zata tsaya ma mutane a rai Aunty Mareeya dai taci uwar sabada kamar yadda ta ci alwashi kowa ka gani san barka yake dangin su Fauzy sai k'ara tayata