Showing 321001 words to 324000 words out of 512766 words

Chapter 108 - Asanadin Makwabtaka Book 3 Hausa Novel Complete

Unknown   

27 Dec 2024

1634

ATM kawai wllh" dariya sosae Fauzy ke yi itama Aunty dariyar take ta farinciki,

"Ina ganin yakamata a kira su Hajiya a sanar masu game da shi" da sauri Fauzy tace "a'a Aunty ni ina ganin bai kamata a sanar dasu ba...." Katseta tay cikin d'aga murya tace to Saboda me, Fauzyn tace "Saboda ban son suma su saka rai kamar yadda kika saka tunda kinga ba wani abu ke tsakanin mu dashi ba kece kawai kike ganin sona yake"

ajiyar zuciya Aunty ta sauke "hakane, amman yanzu dole wani abun ya shiga tsakanin ku na fahimci in aka daka ta tashi ba ranar da zai fito ya bayyanar da abunda ke ran shi don haka ki zo gida inada Meeting da ke" Fauzy dake dariya tace duka ba yau ta dawo Makarantar ba tace eh tazo dai tana son ganinta,

"amman yanzu fa yamma tayi Aunty ko a bari sai gobe in an tashi Class direct sai in taho nan"

"Ok hakan yayi, yauwa in kika fito ki tsaya wurin mai gashin kazar nan na wurin Asibiti ki siyo mana dankwala dankwala guda ko ukku koma biyar sannan nasan baki rasa sanin inda ake saida su shawarma ki tsaya ki siyo mana har da pizza dasu ice cream ba sai kin siyo lemu ba tunda akwae anan ni kuma nan zan yi had'addan Abinci don wannan abun farincikin dole muyi Walima" dariya sosae Fauzy ke yi tace to sai ta turo kud'in da zata siyo abubuwan data lissafan aikuwa a hasale tace su kud'in da aka turo matan don ta kalle su ne ya turo mata, cike da ankararwa Fauzyn tace "amma Aunty an ta6a mashi kud'i kuwa....",

Katseta tay "ajiya ya baki su ne, ko rok'on shi kikai, koma rok'on shi kikai sun halatta a ci su tunda ya baki" Fauzy tace "a'a Aunty kar fa a tada lissafi daga baya" tsoki ta buga tace "aita tadawar da yake ance maki shi K'aramin mutum ne, su irin su da sun ba mutum abu suke mantawa, ke in ma yace a biya shin ai muna da hali sai mu saida gonar gado" ta k'arasa tana kyalkyatar dariya itama Fauzyn dariyar take don ta gane dalilin da yasa ta sako zancen gona Saboda labarin data bata ne na Maganar gonar data yi mashi, cikin dariya Fauzy tace "Aunty ta ina ta zama gonar gado ga mai ita a raye, tace "ai shima gada yayi a wurin kakan mu ko kinga ai ta gadon ce kenan" dariya suka saka gaba d'aya daga baya sukai sallama kafin ta kashe ta tambayi to tayi mashi godiya ma kuwa ta sanar da ita yak'i ya d'auka tace ta kyale shi to sai wani lokacin in sun k'ara yin magana sai tayi mashi.

A ranar da daddare misalin k'arfe goma da wasu mintuna Senator yazo kawo ma Hajiya da Fatuu Fura kamar ko yaushe, tana zaune a parlor ya shigo bayan ya zauna sun gaisa da fara'a ya tambayi yau ina yar taya ta hirar ya ganta ita kad'ai ko har tayi bacci, d'an ta6e baki Hajiya tay tace tana d'aki yau fushi take shiyasa ta k'unk'ume a cikin d'aki, cike da kulawa ya tambayi abunda yasa take fushin Hajiyar ta fad'i mashi zancen karatun ta ne so take su koma taci gaba da zuwa shine tace mata ba yanzu ba tunda ba yadda za'ai tayi tafiya mai tsawo a yanzu, d'an murmushi yay yace "ina ruwan Daughter lafiya ai tana gaba da komai, na fahimce ta tana da babbar hujja inaga abunda za'ai za'a tuntu6i Makarantar tasu in za'a iya yi man Alfarma sai taci gaba da yin karatun ta online zuwa a k'ara d'an lokaci ta k'ara samun lafiyar da zata iya yin tafiya ba tare da tunanin wata matsala ba" kai Hajiya ta jinjina mashi tace in zai yuwu to ayi hakan don ba K'aramin son karatun take ba in ba cigaba taga tayi ba ta dingi damuwa kenan kuma hakan ma na iya haddasa mata wata matsalar don ba'a son mai ciki da damuwa, kai ya jinjina mata tare da mik'ewa yace bari ya gan ta ya k'ara kwantar mata da hankali, a bakin Bedroom d'in ya tsaya yayi sallama, sau biyu yayi shiru ba'a amsa ba hakan yasa shi shiga, hango ta yay kwance ta lullube rabin jikinta da duvet nan ya gane tayi bacci, juyowa yay ya dawo cikin parlon bayan ya zauna ya sanar ma Hajiyar bacci take yace in ta tashi sai a k'ara kwantar mata da hankali in sha Allah yadda yace d'in yana tunanin zai yuwu tace to, yar hira suka ta6a kafin yay mata saida safe ya tafi.

*Bayan Wata Biyu*

A kwana a tashi ba wuya a wurin ubangiji gashi cikin Fatuu har yayi wata ukku lokacin watan Haisam d'aya da rabi da tafiya, Sosae take samun kulawa a wurin dukkan Mutanen gidan ko tari tayi sai an tambaye ta lafiya, haka ta bangaren Abinci kullum ne da safe zuwa dare sai an tambayi abunda take so ta ci wani lokacin ta fad'i wani lokacin kuma tace zata ci abunda aka yi, sosae take hutawa don ko tsinke wannan bata kaudawa hakan yasa ta kara yin k'iba kumatunta sun k'aru ga wani irin fari data k'ara kamar Madara dama ita ba ja bace fara ce ta yi wani fayau ga fatarta tayi wani irin lukui lukui, ta bangaren jikinta ma hips d'inta sun k'ara saidai boobs d'inta sunfi k'aruwa sunyi fam dasu ga cikin nata har ya fito ana ganin shi ba kamar in tasa kaya da suka kamata sosae ake ganin shi, suna yin waya da Vedio call da Haisam akai akai don kullum ne sai sun yi wani lokacin wuni suke suna wayar in suna Vedio call har cikin take bud'e mashi ya gani haka Fanan ma sosae tayi murna ganin cikin ya fara fitowa tai ta kafa mata sharudd'a kan cikin ita kuma taita dariya, bangaren su gwaggo ma kullum sai tayi waya ko Vedio call da su gaba d'aya Mino ta k'osa ta dawo kullum sukai waya sai ta tambayi yaushe zata dawo, haka bangaren karatunta kamar yadda Senator yace ta Online d'in yanzu take yi har su Assignment da test duk ana mata hakan yasa ta kwantar da hankalinta, bangaren Fauzy itama tana kiran Sameer ta gaishe da shi saidai ba akai akai ba gudun kar ta zaqe saidai suna yawan yin magana ta chat wani lokacin shike fara mata magana ya tambayi yadda take da karatunta wani lokacin kuma ita ke mashi magana ta gaishe da shi sai dae tun Vedio call d'in da sukai rannan basu k'ara yi ba, Aunty Mareeya duk sukai waya ko ta koma weekend sai ta tambayi ko yace yana son ta tace mata a'a ita basu wannan Maganar da shi ba sai tay dariya tace ai sannu bata hana zuwa.

Ranar lahadi lokacin cikin Fatuu ya k'ara sati guda suna zaune da daddare a parlor suna shan furar su da Dad yasa aka kawo masu don shi yayi tafiya tare da Mr. President basu K'asar dama shi na hannun daman shi ne ana hasashen ma shi ne d'an takarar shi da zai tsaida a Za6e mai zuwa, suna cikin shan furar Hajiya tace "Fateema ina ga fa barin ki zan yi anan don hankali na yayi gida na gaji da zaman Abujar nan dama Saboda ke ne in ba don haka ba ni ina zan zauna haka" idanu waje Fatuu data dakata da shan furar take kallonta har ta gama, a marairaice ta fara rok'onta kan to su tafi tare mana Hajiyar tace mata a'a tunda dai tana karatun ta lafiya lou ta zauna ta k'ara lokaci, kwa6e fuska tay nan da nan idanun ta sukai rau rau sun ciko da k'walla, tsam ta mik'e ta matsa gaban Hajiyar ta duk'a a gabanta ta fara mata magiyar su tafi tare don Allah wllh ita lafiya lau take jin ta ba abunda ke damunta in sha Allah lafiya lau zasu je, Hajiya dake kallonta tace ta tashi bata ga halin da take ciki bane zata duk'a haka, k'wallan ne suka fara zubo mata tace to don Allah zasu tafi taren, ce mata tay ta tashi ta zauna ta yunk'ura ta mik'e, bayan ta zauna cigaba da yin k'wallan tayi, ajiyar zuciya Hajiya tayi tace ita ba k'in tafiya da ita take ba kawai matsala take gudu da sauri Fatun tace "in sha Allahu Hajiya ba abunda zai faru tunda ban jin wani ciwo kuma zaki iya sawa ma Aunty ta duba ni" shiru tay tana kallonta ta cikin glasses d'inta fuskarta da d'an murmushi, tasan in ta tafi ta barta bazata kwantar da hankalin ta ba zatai ta damuwa ne dama hada k'arin hakan yasa ta zauna, ajiyar zuciya ta sauke tace Shikenan zata yi ma Dad magana kan hakan in ya amince cikin satin da za'a shiga sai su tafi dama shima jibi zai dawo, rok'onta ta shiga yi kan ai ita zata sa shi ya amincen don Allah Hajiyar nata dariya tana fad'in wai ba nan da Katsinar duk d'aya bane Fatun tace mata eh amman tayi missing d'in su gwaggo ne.

Ranar talata da daddare Senator ya dawo sai washe gari da safe wurin k'arfe tara ya samu shigowa gaisawa da Hajiya ya shirya cikin galleliyar shadda light blue babbar riga da yan ciki sai hula da Agogo da takalma mahad'in kayan sai baza uban k'amshi yake, lokacin tana cikin Bedroom ya shigo bayan yayi sallama an bashi izinin shigowa, tana zaune a bakin gado jikinta sanye da cotton d'in doguwar rigar bacci Fatuu kuma na kwance itama jikinta sanye da kayan bacci riga da wando sai hula bata dad'e da gama yin Breakfast ba ta dawo ta kwanta, yana niyyar zama a kan Carpet Hajiya tace ya zauna a bakin gadon mana, tun bayan da ya shigo Fatuu ta tashi zaune idonta a kanshi tana d'an murmushi bayan ya zauna ta gaishe dashi ya amsa mata da fara'a tay mashi an dawo lpy ya amsa shima ya tambayi jikinta tace mashi Alhamdulillah, k'ok'arin sauka ta fara yi daga gadon yace mata tayi kwanciyarta ba dad'ewa zai yi ba, duk da haka saida ta sauka ta koma kan Carpet ta zauna, gaisawa sukai da Hajiya tayi mashi an dawo lafiya, bayan sun gama gaisawar ne ya fara yi mata maganar tafiyarta da suka fara ta waya tun yana can, tambayarta yay game da Fatuu yace in tana ganin ba matsala sai su tafi taren cike da zolaya tace "ai ina ganin ta zauna kawai in ta samu kaman wata biyar sai ta koma" ta k'arasa Maganar had'i da satar kallon Fatuu, tana jin haka ta yamutsa fuska idanunta sukai rau rau, ganin Hajiya na kallon Fatun tana yar dariya yasa Dad d'in shima kai idon shi kanta kawai sai ganin k'walla sukai sun zubo mata sharr da sauri ta sunkuyar da kanta k'asa, d'an murmushi Dad yay calmly yace "Daughter ko baki jin dad'in zama da mu ne" da sauri ta girgiza mashi kai alamar a'a ba tare data d'ago ba,

"To kukan na miye?" Ya tambaya da fara'a, shiru tay bata ce komai ba ya sake cewa "Ko kina kewar yan uwanki ne?" Da sauri ta jinjina mashi kai,

"Ok, ki daina kuka kin ji za'a duba in dai hakan bazai ja wata matsala ba sai ku tafi tare" kai ta d'aga mashi yace to ta d'ago yaga in ta daina yin kukan, saida ta goggoge fuskar da hannu sannan ta d'ago yana murmushi yace to yaga itama tayi ta d'an yi murmushin Hajiya dake kallonta ma ta yi murmushi, daga baya yayi sallama da Hajiyar tayi mashi Allah ya huta gajiya.

Bayan fitowar shi part d'in Aunty ya nufa lokacin tana cikin d'aki ta koma ta kwanta da yake saida rana zata aiki, tana kishingid'e jikinta sanye da jallabiya kanta a bud'e yasha k'ananun kitso hannunta ruk'e da waya tana amsa kiran da shi ya tashe ta daga bacci ya shigo cikin d'akin da sallama, saida ta cire wayar sannan ta amsa mashi, nufar gadon yay ya zauna ta tashi da sauri tace ma wadda suke wayar tana zuwa, kallon shi tay da murmushi tay mashi barka da shigowa da yake a part d'in shi ta kwana sun gaisa, bayan ya amsa mata ne yay mata Maganar Fatuu yace yana son ta dubata taga in ba wata matsala zasu koma tare da Hajiya, a nutse ta fara mashi bayanin cewa a yanzu dai gaskiya lafiyar Fatun lau don tana duba ta akai akai ba wata matsala a tattare da ita sannan shi miscarriage yana iya faruwa unexpectedly koda ana kiyayewa wani lokacin hakanan ma sai ayi ita abunda take gani a barta ta bita sai a bita da Addu'a kawai tunda barin nata k'arshe zai jefa ta a damuwa ne kuma hakan ma had'ari ne a gareta, sosae tayi mashi bayani tare da nuna mashi duk abunda Allah ya k'addaro sai ya faru duk da kiyayewar nada kyau har ta bashi misali da zuwan su akwae cikin jikinta kuma k'arami ma sosae haka suka hawo jirgi kuma lafiya lou, sosae ya fahimta daga baya ya tafi.

A ranar da daddare lokacin da ya kawo masu Fura Hajiya na zaune tare da Fatuu a parlor tana zaune akan kujera 3 seater ta haye saman ta gaba d'aya ta mik'ar da k'afafu gefenta bowl d'in Fruit ne tana ta sha dama bata dad'e da gama cin Abincin dare na biyu ba, da sallama ya shigo da sauri Fatun ta fara k'ok'arin gyara zama ya d'aga mata hannu yace tayi zaman ta, a kujerar kusa da Hajiya ya zauna bayan ya d'aura ledojin furan kan c-table, gaisawa sukai da Hajiyar Fatuu ma ta gaishe da shi ya amsa yana mata murmushi, juyawa yay kan Hajiya yace mata in Allah ya kaimu ranar Friday zasu tafi ta d'aga mashi kai tace Allah ya kaimu, maido idon shi yay kan Fatuu dake kallon su yace "Daughter sai a shirya in Allah ya kaimu ranar Friday zaku tafi" ba shiri ta washe baki duk dimples d'inta suka lotsa dama ga kumatun sunyi Tubarkallah da sauri takai duka tafukan hannuwanta ta rufe fuska alamar taji kunya duk sukai dariya, Maganar akwatunan ta Hajiya tay ma Senator yace ba matsala zuwa kafin su tafi za'a yi gaba da su. Tun daren Fatuu ta fara had'a kaya a ranar kwanan farinciki tayi.

FRIDAY

Akace komai aka sa ma rana zai zo har ma ya wuce, cike da Nishad'i Fatuu ta tashi har Fuskarta ta kasa 6oye farincikin da take ciki na tafiyar su yau ba kamar da Haisam ya sanar mata da sun koma zai zo, gaba d'aya ta gama shiryawa lokacin tafiya kawai take jira dama tun jiya Alhamis aka tafin mata da dukkan kayanta iya yar jakar kayan da zata yi amfani dasu ce zata d'auka haka Hajiya ma an tafin mata da akwatin ta iya yar jaka ce ta rage mata, da yake Friday ne da wuri yaran gidan suka dawo daga Makaranta bayan an saukko daga Masallaci a tare gaba d'aya suka ci Abincin rana a dining table kowa yaci gayun Juma'a, bayan sun gama cikin parlor suka koma harda Dad aka hau yin hirar bakwana dasu Hajiya har Jidderh na cewa ba don Makaranta ba wllh da bin su zatai taje tayi rainon Baby duk akayi dariya Mom tace da yake yazo duniya ko, Aunty ma cewa tay tana ganin Idan cikin ya kai wata takwas kamata yay ta dawo nan Abuja ta Haihu duk kowa yace haka yakamata ita dae Fatuu murmushi kawai take a k'agare take da su tafi har gani take Lokacin ma bai gudu, sai da akai La'asar sannan duk suka tashi don yin salla daga an gama kuma za'a tafi rakasu Airport..............




_Littafin A Sanadin Makwabtaka part 2 Naira 300 ne za'a tura ma Mutum har part 1 ga mai so zai turo kudin ta wannan Account din, 1509618776, Zainab Bature Access Bank, za'a turo shedar biya ta wad'annan nos din 09013804524 ko 08169856268

89

~_*✊💋BOSS LADIES WRITERS💋✊*_~




.........Wuraren k'arfe biyar da rabi jirgin su Fatuu ya sauka a Airport d'in Katsina, Kawu Amadu da Tk da Mino ne suka zo tarbar su, Mino na sanye da riga da skirt na atampa ta yafa gyale a saman kanta sumarta a fake daga bayan kan yayi tudu sosae, gaba d'aya a k'agare take da taga Adda Fatuu din ta, lokacin da suka k'araso cikin Arrivals d'in Fatuu na sanye da Dubai Abaya fara Sol tasha adon stones tayi rolling veil d'in ta hannuwan ta sanye da yan hannunta na diamond da zobe sai k'afafun ta na sanye da takalma brown da suka hau da kalar aikin gaban rigar masu d'an tudu ne don Hajiya ta hanata saka masu tsini, in ka kalleta sai ka rantse bata san hanyar ruga ba balle har ayi zancen acan aka haifeta don gaba d'aya in ka ganta sai kace ba yar Nigeria ba ce ko kuma ace ruwa biyu, Hajiya ma na sanye da doguwar riga mai had'e da mayafi idanunta sanye cikin glasses, akan idon Mino suka shigo aikuwa da sauri ta mik'e ta nufe su da gudu Fatuu na hango su ta fara sakin murmushi, tana zuwa gaba d'aya ta tafi zata fad'a ma Fatun Hajiya tace "a hankali dai Ameenatu" hakan yasa ta dakata a gaban Fatun tana ta washe baki, hannu Fatuu ta kawo ta d'an rungumo ta bayan ta d'ago da ita tay mata sannu da zuwa tana ta murmushi ta amsa mata ta juya kan Hajiya ta gaishe da ita itama da murmushi akan Fuskarta ta amsa mata, lokacin su Kawu Amadu da Tk suka k'araso duk suna sanye da k'ananun kaya, gaishe da Hajiya sukai bayan ta amsa sukai mata an dawo lafiya kafin suka maida idanun su akan Fatuu, Tk na k'ok'arin gaishe da ita da riga shi gaishe dasu duk suka amsa sukai mata an dawo lafiya, bayan sun gama yan gaishe gaishen Tk ya amshi jakar Hajiya ita kuma Mino ta amshi ta

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login