Showing 189001 words to 192000 words out of 512766 words
Chapter 64 - Asanadin Makwabtaka Book 3 Hausa Novel Complete
Unknown
27 Dec 2024
1628
kai ta yawo da yaro tunda saida na je Abuja sannan muka taho nan" Hajiya tace to miye tunda ba'a k'afa za'ai yawon ba tace a'a in suna so in akai masu hutu sa zo,
"Amman dai nasan banda uwar ji da kai aka nuna ana son zuwa ko" still dariya take tace "Wai Farha, aikuwa kaman kin sani ko in gaida ki bata ce ba" ta6e baki Hajiya tay "taji da shi, nima ba son tace tana gaida nin nike ba tunda inada wanda suke gaida nin ta rik'e kayanta ban so" haka suka cigaba da hira cike da raha. Duk wannan abun Fatuu na Makaranta bata dawo ba daga can ma Hostel zata wuce sai Fauzy ta shirya zasu taho tare a sauketa a gidan Aunty Mareeya sai ta dawo tunda akai Break dama ta kira Tk ta sanar dashi don Kada yazo in an tashin shima kawai sai ya wuce cikin gari bai ma san su Senator d'in sun zo ba, tare da Hajiya Maryam d'in suka tafi Masallaci sallar juma'a, bayan an gama nan fa aka fara tururuwar zuwa gaishe dasu da yake da yawa sun santa wasu kuma sai sun zo gaida Hajiyar suke sanin wacece wasu ma ba sai an fad'a masu ba tunda ga kama nan, bayan sun dawo ne suka zauna cin Abinci, suna cikin ci Senator ya dawo ya nufo Dining area d'in Hajiya tace ya zauna su ci Abinci yana murmushi yace mata sunci Abinci tare da Governor, d'an 6ata fuska tay tace to itama sai yaci nata tunda don su akai yana yar dariya yace tuba yake zai ci ba sai ta 6ata rai ba yaja kujera ya zauna duk sukai dariya,
Bayan sun gama cin Abincin suka dawo parlor nan Hajiya Maryam tace mata tunda Yayan ya dawo sai ta fad'a masu abunda yasa ta buk'aci ganin su, numfasawa Hajiya tay ta gyara zaman glass d'in fuskarta sannan ta fara Magana a nutse "Farko dai muyi ma Annabi salati" gaba d'aya suka amsa da sallallahu alaihi wa sallam, bayan kowa yayi taci gaba "dalilin kiran ku abu ne ya taso wanda dole kuna da buk'atar sani ko ba don komai ba don halin rayuwa, ta wata fuskar ba lalle ku kalle shi a matsayin abun Alkhairi ba amman ina fatan ku natsu kuyi amfani da hankalin ku ku kar6e shi a matsayin Alkhairin domin duk abunda kaga Allah yayi to mai kyau ne" dakatawa tay tana maida numfashi duk sun natsu suna sauraronta Hajiya Maryam na gefen ta yayin da Senator ke facing d'in su acan d'ayan bangaren, Maganar da tayi yasa duk suka k'osa su ji miye abun da take son sanar da su d'in, kasa hak'uri Hajiya Maryam tay tace "muna jin ki Hajjaju" sauke yar ajiyar zuciya Hajiya tay ta d'aura "Haisam ne yayi aure, kuma yanzu haka da nike maku magana Matar tashi na zaune a gidan nan acan part d'in nashi" har saida Hajiya Maryam ta d'an zabura ta d'ago sosae idon ta akan Hajiya da alamun d'aurewar kai tace "Mi kike fad'a haka Hajjaju, Wane Haisam d'in yayi AURE!!!" tace mata wane Haisam ta sani banda d'an su, da tsananin mamaki akan fuskar ta tace "To ni ban gane mi kike nufi da yayi aure ba, ai dama duk mun san da yayi aure ko" d'an ta6e baki Hajiya tay kafin tace "dana ce yayi aure baki ji nace Matar na a cikin gidan nan ba, ko dama nan yake zaune da Matar tashi da kuka san ya aura?" da alama bakunan kowannen su ya mutu, shi dai Senator bin su da ido kawai yake ya jingine bayan shi da kujera yatsun hannun shi na had'e cikin na juna, Bayanin Yadda Al'amarin ya kasance Hajiya ta shiga yi masu tiryan tiryan har ta gama ba wanda ya katse ta sannan furiously Hajiya Maryam tace "kenan don uban shi har ya isa yayi aure without our Knowledge, Saboda bamu da amfani a wurin shi bai d'auke mu da daraja ba ko mi!!!" a tsananin fusace tayi Maganar har huci take, kallon Senator tay tace "Yaya kana ji fa, wai yaron nan har ya kai yayi aure bada sanin mu ba!" d'an girgiza kai kawai yay still bai yi magana ba, "ke kuma Hajjaju ya aikata wannan d'anyen aikin har ki goya mashi baya kisa ya zauna da ita, tunda matsayin taimakon ta yayi to miyasa bazai saketan ba zaki bashi dama suci gaba da zama" a fusace idanunta akan Hajiya tay Maganar, Hajiya data kwa6e fuska tace "to miye amfanin sakin nata tunda abu ya shiga tsakanin su har rabo ya shiga tsakani...." A zafafe Hajiya Maryam ta katse ta don da ta ambaci rabo tamkar ta watsa mata ruwan zafi taji cikin k'unar zuciya tace "Don Allah ki daina wannan Maganar Hajjaju, wane rabo ba kince ya zube ba to cigaba da zama da itan na minene???"
"Amman dai kinsan in aka saketa ai ba ai mata Adalci ba, da ya aure tan ai matsayin zai taimaka mata akai dashi ba'a yi dashi wani abu zai shiga tsakanin su ba ko, to tunda har hakan ya kasance sai a rungumi Al'amarin ai fatan ya zama Alkhairi ta yuwu dama Allah ya k'addara auren ba don su rabu bane" girgiza kai Hajiya Maryam ta shiga yi tana cigaba da yin huci can tace "Impossible wllh, bazai cigaba da zama da ita ba, duka yaushe yay Aure da za'a ce wai har ya k'ara, k'arin ma na wulakanci da kaskanci, dole mu nuna mashi bashi ke iko da kan shi ba akwae masu iko dashi da zai je yayi gaban kan shi, in ba iskanci ba da ya raina mutane a ina na ta6a jin irin wannan taimakon" idanunta har sun sauya kala tsabar 6acin rai, kallon Senator tay "Yaya kana jin rainin wayau ko, dole ma a raba su wllh kawai a kira shi ya saketa!!!" tana rufe baki Fatuu ta sawo kai cikin parlon da sallama tana sanye da jallabiya ta yafa veil d'inta duk suka maida idanun su kanta, nan take ta ja ta tsaya tana bin su da ido itama, da hannu Hajiya tay mata alamar ta k'araso ta nufe su a d'arare don kuwa duk ta gane su, tana zuwa bakin kujerun ta toge duk tasha jinin jikin ta ganin yadda suke bin ta da ido ba kamar Hajiya Maryam wadda bacin rai ke kwance k'arara akan fuskarta, Hajiya ce tace "ki k'araso mana Fateema" shiga tay duk ta kame kanta, nuna mata kujera Hajiya tay alamar ta zauna maimakon ta zauna samanta sai ta duk'e saman carpet daga d'an nesa da Hajiyar, fuska a sake tace "an dawo?" Kai ta d'aga mata,
"amman ya akai baki shigo tun d'azu kin ci Abinci ba?" Cikin rawar murya tace "a..ai yanzu na dawo, na tsaya a Hostel ne wurin Fauzy mun yi Assignment" da k'yar ta k'arasa sakamakon mugun kallon da Hajiya Maryam ke jefa mata don kuwa ta santa tasan itace Matar Haisam d'in, tuni zuciyarta ta hau bugu da k'arfi da k'arfi, kai Hajiya ta jinjina sai kuma ta sake cewa "baki gaida bak'i ba to, kin gane su?" Kai ta d'aga mata alamar eh ta kalli Hajiya Maryam cikin rawar murya ta gaida ta tay mata banza, juyawa tay kan Senator dake ta kallon ta shima ta gaida shi ya jinjina mata kai kawai, juyowa tay kan Hajiya Maryam ta k'ara gaishe da ita aikuwa ta zabga wani uban tsoki ta mik'e ta nufi hanyar barin Parlon a fusace da sauri Fatuu ta fara k'ok'arin matsawa saidai ko kafin ta bata hanya ta cimmata aikuwa ta ham6are ta gefe ta wuce Fatun ta bugi kujera sosae aikuwa nan take ta fashe da kuka don ba K'aramin buguwa tayi ba, yamutsa fuska Hajiya tayi ta bi Hajiya Maryam d'in da kallo har ta shige Corridor sannan ta girgiza kai ta maido idon kan Fatuu ta mik'a mata hannu alamar ta matso ta jawo jiki tana cigaba da yin kuka tana gogewa da gyalen jallabiyar ta da ya zame daga saman kan, rarrashinta ta shiga yi tana bata hak'uri hannun ta guda a saman shoulder d'inta ta d'agota ta zaunar da ita akan kujerar kusa da ita tana cigaba da rarrashin ta, tana cikin goge k'wallan ta kai idonta kan Senator suka had'a ido kawai sai gani tay yay mata alamar tazo da kan shi, dakatawa tay tana kallon shi ya d'aga hannu ya k'ara kiranta Hajiya da ta gani tace taje ana kiranta ta mik'e a d'arare ta nufe shi, bayan ta isa gaban shi tana k'ok'arin zama akan carpet ya nuna mata kujerar kusa da shi yace ta zauna, zama tay tana cigaba da goge Fuskar ta tana yar ajiyar zuciya, a nutse cike da dattako ya fara magana,
"Kiyi hak'uri kin ji, ranta ne a 6ace shiyasa tay maki hakan amman Kada ya dame ki, nasan ba ki rasa sanin cewa in rai ya 6aci mutum na iya aikata komai ko?" Kai ta d'an jinjina mashi, d'an murmushi yayi "Good, a wani School kike ne?" Still muryar ta rawa take don wani irin kwarjini ne dashi ta bashi amsa, jinjina kai yay "da kyau, kinyi nisa a Karatun ne?" tace "Eh ina aji biyu kuma mun kusa yin Exam" nan ma kan ya jinjina yace "sai ku shiga aji ukku kenan, ai kaman daga nan ma zaku gama ko don nasan kaman karatun 3 years ne" kai ta d'aga mashi a sanyaye tace eh, "kice watarana in bani lafiya za'ai man Allura kenan, koma har kin iya yanzu?" ya d'an bud'a mata ido sak irin yadda Haisam ke yi dabarbarcewa tay don bata tsammaci ganin hakan daga gare shi ba tace eh ta iya, wani kallo yay mata irin na baka yarda da Mutum ba yace "kai, ki fad'a man gaskiya fa, ko don Kada ince baki da k'ok'ari kika ce hakan" da sauri tace "Allah da gaske nike na iya harda sa drip ma da d'inki" jinjina kai yay yana murmushi yace "kice Daughter d'in nawa mai k'ok'ari ce kenan" d'an waro ido tay baki a d'an bud'e take kallon shi ya d'age mata gira yace ko bata da k'ok'arin da sauri tace tana da shi, kai ya jinjina taji yace taje taci Abincin da sauri tace to ta mik'e ta nufi hanyar barin cikin parlon duk suka bita da ido Hajiya na d'an murmushi dama tunda suke Magana dashi take kallon su tana murmushi, Ajiyar zuciya ya sauke ya kai hannu ya shafi fuskar shi yana kallon Hajiya yace "She's so cute" Hajiya dake murmushi tace mashi haka take sai ma ya zauna da ita tana da dad'in zama sosae, nan ta shiga bashi labarin rayuwar da sukai da Haisam a baya, Maimakon ta shiga Kitchen d'aukko Abincin sai ta zille ta bi ta kopar baya ta fuce, bata bi ta 6angaren da d'akin Hajiya yake ba tabi ta d'ayan 6angaren tana tafiya cikin sauri ta d'an d'age kasan rigarta tana yi tana waigen bayanta ta nufi part d'in su.........
_Littafin A Sanadin Makwabtaka part 2 Naira 300 ne za'a tura ma Mutum har part 1 ga mai so zai turo kudin ta wannan Account din, 1509618776, Zainab Bature Access Bank, za'a turo shedar biya ta wad'annan nos din 09013804524 ko 08169856268
[5/8, 19:28] +234 901 700 4868: ASM Bk2069
~_*✊💋BOSS LADIES WRITERS💋✊*_~
*DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI*
.........Tana fitowa daga cikin gidan tay ma Tk dake cikin Mota alama da hannunta nan take ya fahimci mi hakan ke nufi ya bud'e kopar Motar da sauri ya fito, bud'e mata K'opar bayan yay tana zuwa ta shige ya maida kopar ya rufe mata ya d'an d'age gira tare da bud'a ido ya koma yaja suka tafi, sai faman jinjina kai take tana cije lower lip d'in ta tana d'an huci,
Tana fita Amadu ya matsa gaban gwaggo ganin yadda idanunta sukai ja shima har lokacin ran shi a 6ace yake, kallon shi tay tace miyasa yayi abunda yayi ma Hajiya Maryam, cikin 6acin rai yace "to gwaggo sai mu zuba mata ido taci mana mutunci son ranta, miye laifin mu a ciki ko kuwa don muna talakawa" yar ajiyar zuciya ta sauke "kar ka manta ita d'in ko wacece, ko ba komai Mutanen nan nada k'ima da daraja a idon mu hakan da kayi mata bai kamata ba don kamar rashin kunyan ne, duk abunda ta fad'a ta fad'a ne cikin 6acin rai don tana ganin an mata ba daidai ba" dakata tay tana numfasawa idanunta na kallon gefe shi kuma nashi na akan ta, cigaba tay "Wllh abunda nike ta fargabar faruwar shi kenan, nasan dole irin hakan ya biyo baya shiyasa naso tun farko ace an tuntu6e su sun san da Maganar a nemi amincewar su tukun...." Dakatawa ta k'ara yi ta d'age ido sama, ganin yadda duk ta damu yasa Amadu cewa "Kar ki wani saka ma kan ki damuwa, tunda Hajiya tun farko ita ta nuna abar mata komai nasan in sha Allah zatayi abunda ya dace komai na d'an lokaci ne zaki ga ya wuce" girgiza kai tay ba tare data kalle shi ba tace dole tayi wani abu don ita bazata so silar hakan ace an samu rashin Fahimta ba yanzu na Hajiya Maryam d'in aka gani ba'a san ya sauran Yan'uwan nashi suma zasu d'auki Al'amarin balle kuma ita Matar tashi, tambayar ta yay to mi zata yi ta bashi amsa da abunda ya dace daga haka ta juya ta nufi d'aki ya bi bayanta yana ce mata ta kwantar da hankalinta ba sai tace zatayi wani abu ba yasan Hajiya bazata bari a cutar da Fatuu ba, tana shiga d'akin ta nufi gado ta zauna a baki Amadun ma ya shigo ya zauna gefen ta yaci gaba da rarrashin ta kan kar tace zata yi wani abu don anzo anyi masu barazana su yi Addu'a kawae, ce mashi tay to kawae daga baya da ya ga ta d'an saki ranta ya tashi ya tafi, Zaune tay a wurin tana tunanin abunda ya kamata tayi don ganin Auren ya rabu, k'arshe ta yanke zuwa ta samu Hajiya ta rok'e ta kawae a hak'ura da Auran, tana son ta kira Fatun taji halin da take ciki amman bata so taji abunda hankalin ta zai k'ara tashi wata zuciyar ta raya mata tunda ita bata kira ta ba k'ilan ba abunda ya faru da ita don Hajiya bazata bari ayi mata wani abu ba da wannan tunanin taji hankalin ta ya d'an kwanta.
Bayan sun iso G.r.a sun shiga cikin gidan a gaban kopar shiga ya parker, bayan ta bud'e ta fito ta nufi ciki, Parlon Senator ta wuce wanda Had'add'an gaske ne ya tsaru ta samu wuri ta zauna, ganin bai a ciki yasata kiran shi ta sanar mashi ta iso, bada dad'ewa ba ya fito yana sanye da farar Jallabiya tun bayan daya dawo daga Masallaci ya koma ya kwanta zuwanta ne yanzu ya taso shi, a kujerar gefen ta ya Zauna Fuskar shi a sake ta gaishe dashi ya amsa daga haka tay shiru kanta a k'asa tana kallon Carpet 6acin rai bayyane akan fuskar ta, tambayar ta yayi tayi breakfast ne tace mashi a'a sai ta isa yace bari dai a kawo mata tayi anan, bata ce komai ba ya matsa can daga gefen kujerar inda landline take aje saman wani table, kira yay ya bada Umarnin akawo Breakfast, after some minutes sai ga wani cook ya shigo hannun shi ruk'e da babban tray dama aikin shi kenan girka ma Senator d'in Abinci in yazo bada iyalin shi ba, har zai kai inda dining table yake Senator yace mashi ya kawo nan, gaishe da Hajiya Maryam yay ta amsa k'asa k'asa ba tare da ta kalle shi ba ya d'aura a saman c-table Senator yace ya ja mata shi gabanta, saida yayi mata Magana sannan ta fara ci shi kuma ya fara daddana wayar shi da ya fito da ita, bata wani ci sosae ba ta cire hannunta ganin haka yasa Senator yi mata magana tace mashi ta k'oshi, k'ara kiran cook d'in yay yazo ya kwashe kayan, shiru suka yi Senator na cigaba da danna wayar can ya d'ago ya ajiye ta agefen shi yay yar ajiyar zuciya a nutse ya fara mata Magana yace miyasa zata tafi, kallon shi tay tace mashi ba komai kawae ta canza ra'ayi ne, shiru yayi yana kallon ta da d'an murmushi ita kuma idanunta na k'asa tana kallon Carpet har lokaci fuskar ta ba annuri,
cigaba yay "nasan don abunda ya faru ne, ina son ki kwantar da hankalin ki abi komai a sannu sannan ayi fatan hakan ya zama Alkhairi kaman yadda Hajiya ta fad'a bamu san mi Allah ya 6oye a tattare da Al'amarin ba" kallon shi tay cikin 6acin rai tace "Kenan kaima Yaya goyon bayan auren kake?" d'an murmushi yay yace mata kawae yayi nazarin Maganar Hajiya ne shiyasa, Fuska a yamutse tace "Yanzu shikenan ya nuna bamu da iko dashi ya yi gaban kan shi sai kuma a k'yale shi hakan Yaya ai cin Fuska ne, gaskiya dole mu nuna mashi ba a komai yake da iko da kan shi ba kawai asa ya saketa" ta k'arasa tana d'an Jujjuya kai, numfasawa yay yace "ni ina ganin hukuncin da Hajiya ta yanke akan shi ya nuna ana da iko dashi, yaje yayi aure ba tare da sanin mu da niyyar zai saki Yarinyar kinga in aka sa ya sake ta shine yay abunda ran shi ke so amman matsa mashi ya zauna da itan hakan zai sa dangin yarinyar su san ana da iko dashi kuma mu ba k'ananun mutane bane, sakin ta kuma hakan gaskiya ina ganin zai zama k'aranta" idanun ta ne suka ciko da k'walla cikin karyayyar murya ta fara fad'in gaskiya ita bata goyi bayan yaci gaba da zama da ita ba duka yaushe yayi aure kuma in ma Auren zai k'ara wannan ai bata dace da shi ba ba sa'ar auren shi bace, shiru Senator yay still da d'an