Showing 183001 words to 186000 words out of 512766 words
Chapter 62 - Asanadin Makwabtaka Book 3 Hausa Novel Complete
Unknown
27 Dec 2024
1643
jiya tay yar dariya tace mata zata ci Allah sannan ta fito,
Hajiya Maryam na fitowa sukai kacibus da Saude data dawo daga part d'in su Fatuu, gaishe da ita tay ta d'aga mata kai kawai ta mik'a mata trolley d'in tace ta biyo ta dashi, suna fitowa harabar gidan tay mata nuni da parking space da hannunta tace ta kai shi can ta je ta kirawo mata Tk tace mashi ya jirata anan, amsa mata da to Saude tay ta nufi parking space d'in tana tafiya tana waiwayen ta ganin ta nufi part d'in su Fatuu, Har Fatuu taje dining area d'in ta tuna da bata d'aukko cup da sauran abunda zata buk'ata ba ta juyo ta nufi Kitchen, hannunta ruk'e da plate da tea cup da spoon a saman shi ta fito zata koma dining, tana fitowa daga corridor zatai kwanar dining area taji an turo kopar parlon da sauri ta kai idonta suka shiga cikin na Hajiya Maryam, wani mummunan Fad'uwa gaban ta yay ba shiri ta saki abun hannunta nan take cup d'in yay tsalle ya fad'o ya d'aki tile ya tarwatse, tsaye tay cak ta zaro idanu zuciyar ta na wani irin harbawa ganin yadda Hajiya Maryam d'in ke jefa mata wani kallo fuskar ta ba d'igon annuri, daurewa kawai Fatuu ke yi amman jikinta har ya fara rawa daga ta ciki a yadda take ji tamkar ta watsa da gudu ta shige d'aki, cikin parlon ta k'araso tana tafiya a k'asaice ta tsaya a tsakiyar parlon, d'an d'aga murya tay tace ma Fatun ta k'araso wurinta ne ta d'an girgiza mata kai kafin ta fara tahowa cikin parlon a d'arare, a d'an nesa da ita ta tsaya murya na d'an rawa ta gaishe da ita tay mata banza still idanun ta na akanta ba alamun sauk'i a cikin su, cike da yarinta ta Fatuu tay tunanin wai ko don bata ce mata ta zauna ba yasa tay tsaye cike da k'arfin hali tace mata ta zauna aikuwa tamkar ta watsa mata wuta ta k'ank'ance ido a fusace tace "Samun wuri! Wato Ni zaki kalla ki ce ma in zauna! daga gidan ku aka kawo kujerun ko kuwa?" Da sauri ta girgiza mata kai a hankali tace tayi hak'uri....a zafafe ta amshe "Ke zan ce ma kiyi hak'uri ki tattara ki bar gidan nan don kuwa bai dace da ke ba baki samu kar6uwa ba, idan kuwa kika k'i to kuwa kin tattaro ma kan ki abunda bazaki iya d'auka ba, in ba ganganci irin naku ba k'auyawan mutane ke ko a mafarki kin isa kiyi kishi da d'iyata balle kuma a zahiri, wato har kuna da k'warin gwuiwa har haka ko? Fad'a man Asiri kukai ma shi don yaci gaba da zama dake ko??" a rud'e Fatuu ta hau girgiza mata kai aikuwa ta daka mata wata uwar tsawa "K'arya kike! dole Asiri ku kai mashi shi da Hajiya shiyasa har ta goyi bayan yaci gaba da zama dake" kuka Fatuu ta saka tana fad'in wllh su ba Asiri sukai masu ba Hajiya ce tasa yaci gaba da zama da ita, wani kallon rashin Arzik'i take bin ta da shi tun daga sama har k'asa, ada Haushin ta take ji yanzu kuwa abun sai ya juye zuwa tsana can ta buga wani uban tsoki ta d'aga yatsa tana nunata tace "To zan baki shawara tun cikin Arzik'i ki fita daga rayuwar shi, kice baki son cigaba da zama da shi idan ko ba haka ba to rayuwar ki zaki jefa a matsala don kuwa provided that am alive d'iyata bazatai kishi da ke ba da kowa ma, idan har baki d'auki shawarata ba kika fita daga rayuwar su ta lalama ba to zaki danasanin da har ki mutu bazaki daina ba don sai na salwantar da kaskantacciyar rayuwar ki, ta yadda ko kallon gidan nan aka baki shawarar kiyi sai kin zagi wanda ya baki shawarar balle ta kai ki ga cigaba da zama a cikin shi, kinsan Asirin ma mataki mataki ne iya nauyin jakar mutum iya girman wanda za'ai mashi, if u wise enough nasan zaki abunda ya dace" daga haka ta juya, har tayi d'an taku ta dakata ta juya ta kai hannu ta ruk'e kunnanta guda ta furta "idan kunne ya ji to gangar jiki ta tsira!!!" daga haka ta nufi k'opa ta fuce, Fatuu na ganin ta fita ta juya da gudo ta nufi Bedroom, Lokacin data fito bakin part d'in su a parking space ta hango Tk tsaye jikin Mota har ya saka trolley d'in nata ciki, da yatsa tay mashi alamar ya fito da Motar ta tsaya a wurin, yana tsayar da Motar ta bud'e baya ta shiga yaja suka fita su Officer na d'aga mata hannu a K'ok'arin su na su gaishe da ita don ta saba yi masu Alheri bata ba Tk Umarnin ya tsaya ba hakan yasa ya wuce, Suna zuwa gab da gidan su Fatuu ta nuna gidan tana tambayar Tk nan ne gidan su waccan yarinyar da aka kai gidan Hajiya ko yace mata eh, Umarnin ya tsaya a gaban gidan ta bashi, bayan ya tsaya ta bud'e kopar ta fito tace mashi tana zuwa, cike da isa ta nufi gidan Tk dake kallonta ta cikin glass ya girgiza kai a fili ya furta "Allah ya kad'e fitina", a bakin kopar shiga cikin gidan ta tsaya tana bin tsakar gidan da yake wayam ba kowa da kallo, Sallama tayi shiru ba'a amsa ba hakan yasa ta d'aga murya tace "ina masu gidan nan?" Amadu ne ya fito daga cikin d'akin shi yana sanye da jallabiya, wani kallon rashin Arziki ta bi shi dashi shima kallonta yake don ya ganeta, gaishe da ita yay bata amsa ba tace mashi ina take da alamun rashin Fahimta ya tambaye ta wa ya lura da yanayin ta kaman ba Arzik'i, "Kai da waye a gidan?" Ta tambaya ta yamutsa fuska, kafin ya bata amsa gwaggo ta fito daga cikin d'aki hannunta ruk'e da tsintsiya dama shara take shiyasa bata ji sallamar ta ba, juyawa Hajiya Maryam tay ta kalli Gwaggo data tsaya bakin k'opa tana kallon su don ta lura kaman ba lafiya ba,
"In k'araso ne?" Hajiya Maryam d'in ta tambaya tana kallon gwaggon shekeke, aje tsintsiyar da parker gwaggo tay ta nufo su, daga gaban Hajiyar ta tsaya da k'ak'alallen murmushi don tana kallon Fuskar ta tasan akwai matsala, gaishe da ita tay kaman bazata amsa ba sai kuma kaman an mata dole ta amsa daga haka gwaggo tayi shiru, d'an matsowa gaba tay yadda gwaggon zata jita da kyau, cikin isa ta fara Magana, "Mun ji abunda ya faru tsakanin d'an mu da jikar ki, to na zo inji cigaba da zaman su tare na minene? Taimakon ta yay to don mi zaku goyi bayan su cigaba da zama ko baku san yana da Mata bane?" Shiru gwaggo tay kanta k'asa abunda take ta fargaba game da Auren kenan don sarai tasan wacece Hajiya Maryam, cigaba tay "in dai kunsan halacci to bai kamata ku goyi baya ba, tun farko yakamata ace kun yi Magana akan ya saketa kaman yadda ku kai da shi, saidai kuma in dama akwae wata a k'asa kuna so kuyi amfani da damar don cimma wata manufa, to idan dai hakane wannan ba matsala bane ki fad'i man ko nawa kike so zan baki ta ruwan sanyi ki raba jikar ki da mijin Y'ata don bata kai tayi kishi da ita ba balle har ta zame mata matsala!" Yar ajiyar zuciya gwaggo ta sauke cikin kwantar da murya ta fara bata hak'uri tace ita wllh basu da wata manufa akan auren hasali ma itama bata goyi bayan auren ba tun da farko kawae don abun ya juye ne kuma Hajiya ta nuna tana so, a zafafe ta katseta da fad'in "tunda baki goyi baya ba sai kema ki nuna baki so, ba jikar ki bace ke kike da cikakken iko da ita!" D'an jim gwaggo tay yanayin fuskar ta ya sauya a sanyaye tace "Kiyi Hak'uri, Hajiya tana da girma ne a wuri na bazan iya musa mata ba" tamkar ta gaya mata magana taji a hasale tace "to kin mata biyayya don tana so mu kuma sauran dangi yanzu bamu so ba muyi Na'am da auren ba don haka bazamu kar6e ta ba sai ki maido abun ki in dai da gasken ba ki da wata manufa akan auren, bijire ma hakan daidai yake da bijirema Farincikin kowannan ku, zan iya k'arar da duk wani abun da na Mallaka akan bijirema hakan don kuwa ba zan ta6a zuba ido wata kaskantatta ta zama shamaki ga farincikin Y'ata, tana son Mijinta shima kuma yana son ta don haka basu buk'atar wata ta shigo rayuwar su, a shawarce sai kiyi abunda ya dace" ta k'are Maganar tana jinjina kai had'i da kanne ido,
ba K'aramin 6aci ran Amadu yay ba ganin yadda take ta gaya ma Mahaifiyar shi Magana daurewa kawai yake yana danne zuciyar shi, tana zuwa ga6ar data kira Fatuu da Kaskantatta yaji bai iya jurewa ya matso inda suke rai 6ace yace "Hajiya gaskiya ita ba kaskantatta bace, don tana talaka hakan ba yana nufin bata da galihu ba, a wurin Ubangiji duk d'aya muke wanda yafi tsoron shi yafi bauta mashi shi ya fi ba wai mai kud'i ba ko nasaba kawai mutane ne ke bambantawa, in Allah yayi mutum mai kud'i ba hakan na nufin yafi son shi ba ko rayuwar shi tafi amfani ba haka talaka ma ba yana nufin Allah bai son shi ba ko rayuwar shi bata da amfani, ki sani gaba d'ayan mu Allah yayi mu a yadda muke ne don mu bauta mashi don haka gaba d'ayan mu rayuwar kowa talaka ko mai kud'i nada amfani, kuma Maganar aure ai bamu muka sa ya aureta ba, hasali ma bamu san yadda akai ba saidai muka ji zai aureta balle kice ko dama da niyya, sannan Maganar zaman su ma bamu muka rok'a ba tun farko shi ya k'i sakin ta aka zo kuma aka buk'aci zasu ci gaba da zama tare Saboda biyayyar mu ga wadda ta buk'ata muka amince, in zaki ga laifin mu kan hakan shi miyasa bazaki ga laifin shi ba da tun lokacin bai bijire ya nuna bazai cigaba da zama da ita ba, mi yasa tun farko bai saketa ba kaman yadda akai dashi ba, Maganar hallaci kuma ai shi muka yi, ya aureta don ya taimaketa daga baya kuma an buk'aci suci gaba da zama a tare in muka k'i ai kinga mun yi butulci kenan amincewar da mukai kuma hallaci mu kai domin d'an halak shi yake maida Alkhairi da Alkhairi, Yanzu tunda baku amince da auren ba duk miye abun zuwa da tada jijiyar wuya kusa ya sake ta mana........! A fusace ta kai hannu zata wanka mashi mari ya goce Fuskar shi a tamke yana huci nan da nan Fuskar shi tay jajir kaman an watsa jini abunka da Fari, itama Hajiya Maryam d'in huci take tana mashi wani kallo mai cike da tsantsar 6acin rai zuciyarta tana boiling da burning a lokaci guda, cikin wata irin murya ta nuna kanta da yatsa manuni tace "ni kake gaya ma magana haka!!!" D'an tura baki yay yace "ni ba Magana na gaya maki ba saidai in ke kika d'auka haka amman duk abunda na fad'a ai daidai ne, ikon baro gidan nata na a hannun ku sai ku sa ta......." Tsawa gwaggo ta kwatsa mashi cikin harshen fulatanci tace ya bar wurin, wani kalan murmushin yaro bai san wuta ba sai ya taka Hajiya Maryam tayi tace "ki k'yale shi, yay man duk rashin kunyar da ya iya ai gada yay tun daga tushe, kowa ya san baku da kunya ai, bama iya hakan kuka tsaya ba gashi nan kun addabi K'asar mu" idonta da suka sauya kala akan shi tay Maganar nan da nan idanun gwaggo suka ciko da k'walla, nuna shi tay da yatsa tace "Ni ba sa'ar yin ka bace, kaff dangin ku ma ba sa'ar yi na, idan kaci gaba da yi man rashin kunya You will definitely find ur self behind BARS....!!!" A tsiyace ta furta Kalmar Bars d'in ta cize hak'ora, Shiru yay bai ce komai ba gwaggo na girgiza mashi kai alamar kar ya tanka sai huttai yake kamar wanda yay gudu da gani dai ba k'aramar zuciya gare shi ba, juyawa tay kan gwaggo ta had'e yatsanta biyu suna making sound tace "Zan yi komae don Farincikin Y'ata in kuma tabbatar bata samu wata matsala ba in kin so zaki iya yin hakan ga Jikar ki......." Tana kaiwa nan ta juya cike da tafiyar isa ta nufi hanyar k'opa ta fice........
[5/8, 19:28] +234 901 700 4868: ASM Bk2067*
_Destiny may be delayed but cannot be changed...._
*DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI*
.........Tana zuwa bakin corridor ta hango shi zaune akan L-shape inda Haisam ke zama, da sauri ta maida idanun ta k'asa ganin ya zuba mata ido, a d'ayan side d'in ta zauna sai lokacin ta d'ago ta kalle shi still kallon ta yake a sanyaye ta gaishe da shi ya amsa, shiru suka d'an yi kafin taji ya fara magana, "dama mun had'u da H,Zakee a Airport ne ban ga kin rako shi ba har nike tambayar shi kina ina yace kina gida shine nace bari in zo mu gaisa" d'an d'agowa tay ta kalle shi da k'ak'alallen murmushi bata ce komai ba, shiru suka d'an k'ara yi ganin yanayin ta yasa shi cewa "Mom Zarah ko akwae wani abu ne u look abnormal" k'walla ne suka taho mata da sauri ta maida fuskarta k'asa had'i da girgiza mashi kai alamar babu komae, bin ta da ido yay kaman mai nazarinta can ya kira sunanta ta amsa ba tare da ta kalle shi ba yace ta d'ago, saida tay d'an jimm kafin ta d'an d'ago suna had'a ido k'wallan suka zubo mata sharr kawae sai tasa mashi kuka ta kai hannu ta rufe bakinta, a d'an rud'e yace "Subhanallahi, Mom Zarah Mike faruwa ne pls tell me" girgiza mashi kai ta hau yi cikin kukan tace mashi ba komae bata lafiya ne, tambayar ta yay Mike damunta tace kan ta ke ciwo, shiru ya d'an yi yana kallon ta ya cije lower lip d'in shi can yay sigh yace "ba gaskiya kika fad'a man ba Mom Zarah, in har baki lafiya na tabbatar H,zakee bazai tafi ya barki a halin ciwo ba koda kuwa baki fad'a mashi cewa baki lafiya ba nasan zai yi noticing don yana d'aya daga cikin Mutanen da suka karance ki sosae kusan ma zan iya cewa yafi kowa karantar ki, so don't hesitate ki fad'a man in akwae wata matsala" cire hannun data rufe bakin tay ta fara goge k'wallan tana yi tana kallon shi tana d'an bud'e baki, gaba d'aya tama rasa to mi zata ce mashi bata san ta ina zata fara ba,
"Ko mun fara 6oye ma juna abu ne?" Cikin muryar kuka tace "ba kai ne ka fara ba, ka 6oye man cewa shi miji nane" d'an shaking kan shi yay tun a Asibiti ya fahimci bata ji dad'in abun ba, "am very sorry for dat Mom Zarah, kaman yadda na fad'a maki haka aka tsara so bai kamata ace na fad'a maki ba tunda bamu san yadda Al'amarin zai kasance ba, duk da muna fatan auren ya d'ore ba lalle hakan ya faru ba kuma kinga in kika sani sai kin fi shiga mawuyacin hali fiye da farko, da naga bai sake ki ba kaman yadda aka tsara lokacin na fara sama rai na auren zai d'ore, a lokacin da abu ya shiga tsakanin ku da ace kin fad'a man da tabbas zan bayyana maki komai ne to amman sai baki sanar man ba kema kika 6oye man har abu mara dad'i yazo ya faru, amman nasan haka Allah ya k'addaro komae ba mu isa mu canza ba, yanzu shikenan abar shi a munyi ma juna laifi, kiyi hakuri nima kuma nayi hakuri sai muci gaba kaman farko, in kina da wata matsala feel free ki fad'a man ta yuwu in iya taimaka maki ko yaya ne, kinsan ance a Problem shared is a problem half solved" idon ta a kanshi tana ta kikkifta su a kokarin ta na ta dakatar da cigaba da yin kukan, ce mata yay yana Jin ta ta fad'i mashi Mike damun ta ta fara motsa baki cikin karyayyar murya tace "ba wani abu bane Ya Abbas, kawai dai na fahimci Ya Haisam bai sona ne, ya za6i yaci gaba da zama dani ne don dalili biyu, ko don abunda ya faru tsakanin mu ne yana ganin in bai cigaba da zama dani ba bai man Adalci ba ko kuma k'ilan Hajiya ce ta matsa mashi amman ba wai don yana son yin rayuwar Aure dani bane" da k'yar take tattaro kalaman take fad'i mashi, shiru yayi daga Maganar da tayi ya fahimci komae dama kuma tafiyar Haisam d'in tasa shi kokonton in wani abu ya shiga tsakanin su, nannauyar ajiyar zuciya ya sauke yama rasa ta ina zai fara shi kanshi ya rasa gane ma Haisam d'in game da auran, jin yayi shiru yasa Fatuu cigaba da Magana a sanyaye "I decided to get out of his life tunda ba son zama yake dani ba ni bazan so in zame mashi matsala ba, yayi man dukkan Alkhairi a rayuwata bai kamata in hana mashi kwanciyar hankali ba" girgiza kai Abbas yay "kar kice haka Mom Zarah nasan dole ki shiga damuwa game da hakan amman ina ganin mu bashi lokaci tunda kinga duka sati guda kenan da kasancewar ku tare" da alamun bacin rai tace "to Ya Abbas wane lokaci zamu bashi abunda komai a bayyane yake da yana sona ba zai tafi ya barni ba, koda ta kama ma ya tafin ai a k'alla zai man bayani kan dalilin tafiyar da kuma lokacin da zai dawo, amman fa jiya da